2025-11-27@20:48:46 GMT
إجمالي نتائج البحث: 7034

«lambar yabo»:

    Sufeto Janar na ’Yan sandan Nijeriya, Olukayode Egbetokun, ya sanar da cewa sun aiwatar da umarnin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu na janye dakarunsu daga gadin ɗaiɗaikun mutane da ake kira VIP. IG Egbetokun ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai a yau Alhamis, yana mai cewa zuwa yanzu sun janye dakaru 11,566 daga gadin manyan mutane a faɗin Nijeriya. Mbappe ya ci ƙwallaye 4 rigis a wasan Madrid da Olympiacos An rantsar da sabon shugaban kasa a Guinea-Bissau bayan juyin mulkin sojoji “Wannan karon za mu aiwatar da umarnin da kyau saboda umarnin shugaban ƙasa ne,” in ji shi. “Babu wani gwamna, ko minista, ko abokaina da za su kira su takura min saboda sun san cewa umarnin...
    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana jimaminsa kan rasuwar babban malamin addinin Musulunci Sheikh Dahiru Usman Bauchi, lamarin da ya ce ya kaɗu matuƙa da ya samu labarin. Tinubu ya ce jagoran na ɗarikar Tijjaniya mutum ne mai daraja da ƙima, sannan ya bayyana shi a matsayin madubi wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa. Rasuwarsa za ta ba babban giɓi a Najeriya,” in ji shugaban. Shi ma Tsohon ɗan takarar shugabancin Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana rasuwar Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi a matsayin rashi babba ga al’ummar Musulmi na Najeriya da ma Afirka baki ɗaya. A wata sanarwa da Atiku ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, ya bayyana marigayin da babban malami wanda ya koyar da addini...
    Iran ta yi Allah wadai da matakin gwamnatin Ostiraliya na ayyana Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC) a matsayin “mai tallafawa ta’addanci,” “Matakin da gwamnatin Ostiraliya ta dauka wani abu ne mai laifi ne mai hadari, wanda aka tsara a karkashin gwamnatin Sahayoniya don karkatar da hankalin jama’a daga kisan kare dangi da aka yi a Gaza,” in ji Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran a cikin wata sanarwa da aka fitar a yau Alhamis. Gwamnatin Ostiraliya ta sanya IRGC a matsayin “mai tallafawa ta’addanci” bisa zarge-zargen da ba su da tushe na cewa IRGC ta shirya kai hare-hare kan Al’ummar Yahudawa na Ostiraliya. Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta yi Allah wadai da wannan shawarar da babbar murya, tana mai Allah...
    Shugaban Afirka ta kudu, Cyril Ramaphosa ya soki kalaman takwaransa na Amurka Donald Trump na cewa ba zai gayyace shi taron kasashen gungun G20 mafiya karfin tattalin arziki na duniya a shekara mai zuwa a Florida. Ramaphosa ya ce abin takaici ne yadda Trump ke ci gaba da daukar matakai bisa labaran da ba na gaskiya ba ko kuma aka yi musu kwaskwarima. A cikin wata sanarwa da ya fitar, Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ba zai gayyaci Afirka ta kudu taron na badi ba, da Amurka zata karbi bakunci, kuma ya nanata sukar da yake yi wa Afirka ta kudun, kan zargin cewa an aikata kisan kiyashi a Afirka ta Kudu a kan tsirarun fararen fata. Amurka ta...
    Kasashen Faransa, Jamus, Italiya, da Burtaniya sun yi Allah wadai da “karuwar yawan tashin hankalin” da yahudawa ‘yan gudun kama wuri zaman ke yi wa fararen hular Falasdinawa, tare da yin kira ga Isra’ila da ta kare al’ummar Yammacin Kogin Jordan. “Wadannan hare-haren dole ne a daina su. Suna kawo cikas ga kokarin da ake yi na tabbatar da zaman lafiya da kuma tabbatar da tsaron Isra’ila mai dorewa,” in ji ministocin harkokin waje na kasashen hudu a cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa. Sun kuma yi maraba da ” bayyanannar adawar” da shugaban Amurka Donald Trump ya nuna kan yunkurin mamaye Yammacin Kogin Jordan kuma sun sake nanata adawarsu “ga duk wani nau’in mamayewa, ko na bangare, ko na...
      An sake tabbatar wa ma’aikatan Gwamnatin Tarayya FG da suka yi ritaya cewa za a biya su wani bangare na kudaden ariyas a cikin wannan watan, kamar yadda hukumomin da abin ya shafa suka yi alkawari. Mataimakin Sakataren ƙungiyar masu karɓar fansho ta ƙasa, Alhaji Ahmed Gazali, ya bayar da wannan tabbaci yayin da ake tattaunawa da shi ta wayar tarho daga Abuja. Alh. Ahmed Gazali, ya yi bayanin cewas daraktan dake kula da kudade na ofishin akanta janar na tarayya ya tabbatar da daukan matakin hakan na biyan kudaden. Ya bayyana fatan ganin kudirin FG na gaggauta biyan kudade, domin dakatar da duk wata zanga zanga wanda hakan bai dace ba ga ma’aikatan da suka yi ritaya domin...
    Ɗan wasan gaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid, Kyalian Mbappe ya samu nasarar zura kwallaye huɗu rigis a ragar Olympiacos a wasan mako na biyar na kofin zakarun nahiyyar turai da suka buga a yammacin jiya Laraba. Real Madrid dai caskara Olympiacos 4-3 ne a wasan, lamarin da ya ba ta damar haɗa maki 12 cikin fafatawa biyar. Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi ta bar babban gibi a Najeriya – Tinubu An rantsar da sabon shugaban kasa a Guinea-Bissau bayan juyin mulkin sojoji Kawo yanzu dai Mbappe ya shiga gaban Victor Osimhen na Galatasaray wajen yawan zura ƙwallaye a raga a gasar ta kakar nan, inda Mbappe ya ke da 9, yayin da Osimhen wanda ke fama da rauni...
    Daga Usman Muhammad Zaria  Shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kudu a Jihar Jigawa, Dr. Builder Muhammad Uba, ya aiwatar da wani aiki na da naira miliyan biyar domin tallafa wa aiwatar da Shirin Tallafawa Yara Mata  (AGILE) a yankin. Aikin ya hada da gyaran ajujuwa biyu da samar da muhimman kayan aiki, ciki har da injunan dinki, injin yin surfani wato (monogram) da shirin AGILE ya bayar kyauta wanda Dr. Uba ya shirya, ya taimaka wajen ganin an fara amfani da shi, tare da samar da janareta da tabarmi domin inganta koyarwa da horo. Wannan ci gaban ya biyo bayan wani bincike da tawagar AGILE ta jihar Jigawa ta gudanar a baya, inda ta bayyana cewa wuraren koyon sana’o’in na...
    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana kaduwa da rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci kuma jagoran Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi. Fitaccen malamin ya rasu a Bauchi ranar Alhamis yana da shekaru 101. Abubuwa 20 da ya kamata ku sani game da Sheikh Dahiru Bauchi Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban Amurka A cikin wata sanarwa da Kakakin shugaban, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya bayyana Sheikh Dahiru Bauchi a matsayin jagoran da ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa, wa’azi da jagorantar al’ummar Musulmi. Tinubu ya ce rasuwar malamin ba wai asara ce ga iyalansa da almajiransa kawai ba, har ma ga ƙasa baki ɗaya. “Sheikh Dahiru Bauchi malami ne, uba ne kuma murya ce ta daidaito...
    Majalisar Wakilai a ranar Alhamis, ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta yi amfani da diflomasiyya da duk wasu hanyoyi don tabbatar da dawowar tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan lafiya daga Guinea Bissau, bayan juyin mulkin sojoji a ƙasar.  Wannan kuduri ya biyo bayan amincewa da kudurin gaggawa da Shugaban Masu Rinjaye na majalisar, Farfesa Julius Ihonvbere, ya gabatar. Ihonvbere ya shaida wa Majalisar cewa Jonathan, wanda ya je ƙasar domin sa ido kan zaɓe, ya makale bayan juyin mulkin, yana mai cewa gwamnati ta nemo hanyoyin da za su tabbatar da dawowarsa lafiya. Muna tafe da karin bayani…
    Daga Sani Sulaiman   Gwamnan Jihar Taraba, Dr. Agbu Kefas, ya yi jimami kan rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya rasu a ranar Alhamis 27 ga watan Nuwamban 2025, yana da shekaru 102. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai bai wa gwamnan shawara na musamman kan Yada Labarai da Hulda da Jama’a, Mista Emmanuel Bello, ya sanyawa hannu. Gwamnan ya ce rasuwar wannan babban malami babban rashi ne ga kasa, yana mai nuna cewa a wannan lokaci ne ake matuƙar bukatar irin gudummawar da yake bayarwa, duba da kalubalen da kasar ke fusfuskanta. Ya kara da cewa marigayi Sheikh ya koyar da ilimi da zai ci gaba da jagorantar kasa kan...
    A ranar Alhamis, 27 ga watan Nuwamban 2025 ce Allah ya yi wa fitaccen malamin addinin Musuluncin nan kuma jigo a Darikar Tijjaniyya a Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi rasuwa. Ya rasu yana da sama da shekaru 100 a duniya. Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa Sheikh Dahiru Bauchi: Malamin da zuri’arsa ta fi kowacce yawan mahaddata Alkur’ani Baya ga tarin iliminsa da yawan shekaru, akwai wasu tarin baiwa da Allah Ya ba malamin, wadanda ba kowa ne ya san da su ba. Aminiya ta yi nazari a kansu, inda ta zakulo muku abubuwa 18 da ya kamata ku sani a kansa. Ga wasu daga ciki: Ya fi kowa yawan zuri’ar da ta haddace Alkur’ani a duniya, inda...
    Kwamandan rundunar soja ta “Sayyidush-shuhada” dake Tehran Janar Qurbani Muhammad Wali Zadeh ya bayyana cewa; makamai masu linzami da Iran take da su ne, da kuma jiragen sama marasa matuki suke takawa makiya birki.” Janar Qurbani Muhammad Wali Zadeh ya kuma ce; Albarkacin sadaukar da jinanai da shahidai su ka yi ne da kuma kwazon kwararrun masana, su ka sa Iran samun wannan karfin da take da shi. Wali Zadeh wanda ya halarci taron girmama rundunar sa-kai ta Basiji da kudancin birnin Tehran, ya kara da cewa, Iran ta samu matsayin da take da shi ne a wannan lokacin daga jihadin shahidai da tsayin dakar al’ummar Iran, sannan kuma ya kara da cewa; A halin yanzu karfin Iran a fagen...
    Daya daga cikin ‘ya’yan babban malamin addinin musulunci a Najeriya Sayyid Ali Dhahiru Usman Bauchi ne ya tabbatar wa da jaridar “Daily Trust” rasuwar malamin. Sayyadi Ali ya furta cewa: ” Tabbas Shehi ya koma ga mahaliccinsa, mu duka daga Allah muke, kuma zuwa gare shi za mu koma.” Haka nan kuma ya kara da cewa, Lokaci ya yi da shehun malamin zai huta,kuma mun gode wa Allah da ya yi mana komai, ya tsawaita rayuwar shehi har zuwa wannan lokacin. Shi dai Shehu Dhariu Usman Bauchi an haife shi ne a 29 ga watan Yuni na 1927, ya kuma rasu yana dan shekaru 97 a wannan Alhamis din 27/ ga watan Nuwamba 2025. Gabanin rasuwarsa ya kasance daya daga...
    Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Bauchi, a matsayin babban rashi ga al’umma. Gwamnan ya bayyana malamin a matsayin jagoran haɗin kai, zaman lafiya, da fahimtar juna tsakanin Musulmi da mabiya addinai daban-daban. ’Yan sanda sun gano harsasai 210 a kan titin Zariya-Funtuwa Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa A cikin saƙon ta’aziyya da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Mukhtar Gidado, ya sanya wa hannu, gwamnan ya ce Gwamnatin Jihar Bauchi tana alhinin rasuwar malamin. Dahiru Bauchi, ya rasu da safiyar ranar Alhamis, 27 ga watan Nuwamba, 2025 a Bauchi, yana da shekara 102. Gwamnan, ya ce Sheikh Dahiru Bauchi babban malami ne na addinin...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta gano harsasai 210 da aka jefar a kan babbar hanyar Zariya zuwa Funtuwa, a unguwar Dogo Itace da ke Samaru, Zariya. Lamarin ya faru ne lokacin da DPO na Samaru tare da tawagarsa suke sintiri a kan hanyar. Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa Juyin mulki ya rutsa da Jonathan a Guinea-Bissau Jama’ar yankin ne suka kira rundunar cewar fasinjojin wata mota ƙirar Volkswagen Golf mai launin baƙi sun jefar da wata jaka, sannan suka tsere. Da jami’an rundunar suka isa, sun tarar da jakar da aka jefar. Bayan gudanar da bincike, sun gano harsasai 210 na ɗangon 7.56mm. DPO ɗin yankin ya sanar da sauran jami’an rundunar da ke kan hanyar...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A cikin shekarun nan, matsalolin tsaro a Najeriya—kamar ta’addanci, da garkuwa da mutane, da rikicin manoma da makiyaya, da kuma ayyukan ’yan bindiga—suna kara ta’azzara, lamarin da ya sanya al’umma da masana tsaro ke tambayar wace hanya ta fi dacewa gwamatani ta yi amfani da shi wajen kawo karshen wadannan matsaloli da suka ki ci suka ki cinyewa tsawon shekaru.   Yayin da wasu ke ganin amfani da karfin soji ne kadai hanyar da zai kawo karshen wannan matsala, wasu na ganin tattaunawa ne kadai mafita, wasu har ila yau na ganin idan aka yi amfani da gaurayen biyun zai fi dacewa. NAJERIYA A YAU: Irin Radadin Da Masu Cutar Amosanin Jini Ke...
    Bayan an zabi kasar Iran a matsayin mamba a kwamitin zartarwa na hukumar yaki da makaman guba ta duniya, wato ‘ the Chemical Weapons Convention (CWC)’ da kuriun jimillar yan majalisar, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa Iran zata yi amfani da damar da ta samu na bin hakkin mutanen kasar Iran dangane da makaman guba wadanda Sadam Husain ya yi amfani da su a kan mutanen kasar a yakin shekaru 8 (1980-88). Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a taron CWC a birnin Hague a ranar Talatan da ta gabata. Ya kuma kara da cewa Iran zata bukaci a hukunta kasashen da suka taimakawa Sadam Husain a wajen...
    Wata cibiyar bincike mai suna “Frensic Architecture’ ta bada sanarwan cewa, HKI tana fakewa da tsagaita budewa juna wuta a Gaza a matsayin dama ta sake shata kan iyakoki a zirin gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta nakalto cibiyar tana cewa a halin yanzu HKI ta maida ‘koren layin da Trump ya shata a shwarar tsagaita wuta da ya gabata na tsaida yaki a Gaza a matsayin sabon taswirar Gaza. Labarin ya kara da cewa an Trump ya gabatar gabatar da wannan shawarar ce don sake tsuge fadin gaza, wanda kuma a halin yanzi sojojin hki suna hana Falasdinawa a gaza zuwa kusa da layin da suka shata, kuma duk wanda ya matso kusa da shi suka...
    Tsohon shugaban tarayyar Najeriya Goodluck Jonathan a halin yanzu yana birnin Bissau babban birnin kasar Gunea Bissau bayan da sojoji suka kwace mulki suka kuma hana shiga da fita daga kasar. Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta bayyana cewa tsohon shugaban kasar da daruruwan masu sanya ido a zaben da aka gudanar a kasar a makon da ya gabata sun kasa ficewa daga kasar bayan juyin mulkin. Labarin ya kara da cewa sojojin da suka yi juyin mulkin sun kwace iko da kasar ne a dai-dai lokacinda ake irga kuri’un da aka kada a zaben da aka gudanar a cikin yan kwanakin da suka gabata. Kafin juyin mulkin dai yan takaran shugaban kasa a zaben shugaba Umaro Sissoco da kuma...
    Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya maƙale a Guinea-Bissau bayan da sojoji suka yi juyin mulki tare da karɓe ragamar mulkin ƙasar. Jonathan da sauran baƙi baƙi masu sanya ido kan zaɓen da aka gudanar, ba za su iya barin ƙasar ba domin sojoji sun rufe iyakokin ƙasar baki ɗaya, tare da dakatar da zaɓen gaba ɗaya. Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban Amurka Andrea Thompson ta zama mace mafi ƙarfi a duniya Lamarin ya samo asali ne bayan manyan ’yan takara biyu sun yi iƙirarin samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana. Ba jimawa wasu dakarun sojin ƙasar suka hamɓarar da gwamnatin farar hula ta ƙasar. Sun kuma sanar da dokar hana fita da...
    An kulle Fadar Shugaban Kasar Amurka ta White House tare da wasu gine-ginen gwamnati da dama, sakamakon harbin ɗan bindigar da ya raunata sojoji biyu a kusa da fadar. A yayin, an harbe masu tsaron fadar biyu har lahira. Gwamna Patrick Morrisey da farko ya ce an kashe sojojin, amma daga baya ya ce yana samun “rahotanni masu karo da juna” game da halin da suke ciki, yana mai da cewa za a fitar da ƙarin bayani idan an tabbatar. A cikin wani rubutu a shafin X, ya ce, “Yanzu muna samun rahotanni masu cin karo da juna game da halin sojojin biyu, kuma za mu bayar da ƙarin bayani idan mun samu cikakken rahoto. “Addu’o’inmu suna tare da waɗannan...
    Daga Isma’il Adamu  Gwamna Dikko Radda na Jihar Katsina ya sanya hannu kan kudirin kasafin kudin jihar na 2026 na Naira Biliyan 897, makonni uku bayan gabatar da shi a gaban majalisar dokokin jihar. Yayin rattaba hannu a Fadar Gwamnati da ke Katsina, a gaban ‘yan majalisar dokokin jihar, gwamnan ya jinjinawa majalisar bisa gaggawar amincewa da kasafin, tare da tabbatar da cewa za a aiwatar da shi yadda ya dace. Ya bayyana cewa kashi 82 cikin ɗari na kasafin an ware shi ne ga manyon ayyuka(capital expenditure), yayin da kashi 18 cikin ɗari aka ware ga ayyukan yau da kullum(recurrent expenditure), rabo wanda ya ce ya fi abin da doka ta baya ta tanada, wadda ke bukatar kada kudaden gudanarwa...
    Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta bukaci maniyyatan aikin hajjin 2026 da su gaggauta biyan kudin kujerun su kafin ranar 24 ga watan gobe. Darekta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana haka jim kadan bayan kammala taro da shugabannin sassa na hukumar da shugabannin shiyya da sauran ma’aikatan hukumar a Dutse babban birnin jihar. Yana mai cewar, hukumar aikin hajji ta kasa wato NAHCON ta bayyana ranar 5 ga watan Disamba da ta kayyade a matsayin ranar rufe biyan kudin kujerun aikin Hajjin 2026 a fadin kasar nan. Ya bayyana cewar ranar itace ranar karshe da hukumar aikin Hajji da Umrah ta kasar Saudiyya ta kayyade na biyan kudin kujerun...
    An naɗa Andrea Thompson, ’yar ƙasar Birtaniya, a matsayin mace mafi ƙarfi a duniya. Wannan na zuwa ne bayan tabbatar da cewa wanda aka bayyana a matsayin zakara — Jammy Booker — tun da farko namiji ne da aka sauya masa halitta zuwa mace, lamarin da ya sa aka soke nasararsa bisa saɓawa dokokin gasar. Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro Real Madrid za ta yi karon-batta da Olympiacos a Gasar Zakarun Turai Thompson mai shekaru 43, ta karɓi lambar yabon ne daga masu shirya gasar nunin ƙarfi ta duniya, kwanaki biyu bayan kammala bikin a Arlington da ke birnin Texas na Amurka, wanda aka gudanar a daga 20 zuwa 23 ga watan Nuwamba. Gasar nuna ƙarfin ta...
    Daga Bello Wakili Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-baci kan harkar tsaro a duk fadin kasar, sakamakon karuwar kalubalen tsaro da ake fuskanta. Shugaban ya ce za a dauki sabbin jami’an tsaro nan ba da jimawa ba, wadanda suka hada da na sojiin, ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro — domin karfafa matakan tsaron kasa. A karkashin sabon umarnin, an bai wa Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ikon daukar karin jami’aaidubu ashirin,  wanda hakan zai kawo yawan sabbin  jami’an da za a dauka bana zuwa dubu hamsin. Shugaban kasar ya kuma amince a yi amfani da sansanonin horas da matasa masu yi wa kasa  NYSC a matsayin wuraren horaswa na wucin gadi, sakamakon gyare-gyaren da ake yi a...
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro da ta addabi dukkan sassa a Nijeriya. Cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin wannan Larabar mai ɗauke da sa hannunsa, Tinubu ya bayyana cewa dole ne a ɗauki matakan gaggawa da suka dace domin fuskantar barazanar tsaro da ke ƙaruwa ƙasar nan. Shugaban ya bayar da umarnin ɗaukar ƙarin jami’an tsaro da suka haɗa da jami’an ’yan sanda 20,000, lamarin da zai ƙara adadin jami’an da za a ɗauka zuwa 50,000, bayan umarnin da ya bayar a ranar Lahadi na ɗaukar jami’an tsaro 30,000. Real Madrid za ta yi karon-batta da Olympiacos a Gasar Zakarun Turai Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa sunayen jakadu Haka kuma, Tinubu...
    Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya dawo Abuja daga birnin Luanda na Angola, inda ya halarci taron AU–EU karo na 7 a madadin Shugaba Bola Tinubu. Ya wakilci shugaban kasa a taron G20 na 2025 da aka yi a Johannesburg, Afirka Ta Kudu. A Angola, Shettima ya karanta sakon Shugaba Tinubu wanda ya sake jaddada bukatar Afrika na samun kujerun dindindin da ikon zartarwa a Majalisar Dinkin Duniya. Ya kuma bukaci Tarayyar Turai su hada kai da Afrika wajen samar da tsare-tsaren zaman lafiya da tsaro. Shugaba Tinubu ya tabbatar da kudirin Nijeriya na ci gaba da inganta zaman lafiya, tsaro da mulki na gari a Afrika, tare da yin aiki da Tarayyar Turai domin samun daidaito da kwanciyar...
    A yammacin nan ne ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid za ta kece raini da Olympiacos a ci gaba da Gasar Zakarun Turai, duk da rashin wasu manyan ’yan wasanta biyu. Babban mai tsaron ragar Madrid, Thibaut Courtois, da ɗan wasan baya Dean Huijsen, na fama da jinya, lamarin da zai hana su buga wannan muhimmin wasa. Sojoji sun yi juyin mulki a Guinea-Bissau Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa sunayen jakadu Yanzu haka jerin ’yan wasan Madrid da ke jinya sun haɗa da: Thibaut Courtois, Dean Huijsen, Antonio Rüdiger, David Alaba, Franco Mastantuono, da Éder Militão. Tun bayan zuwan sabon kocin Real Madrid, Xabi Alonso, Courtois ya riƙe ragamar tsaron raga a dukkan wasanni 17 da suka buga a...
    Jakadan kasar Aljeriya a kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya yayi tir da abin da ya kira zalunci isra’ila da kuma ci gaba da kai hare-hare kan mutane kasashen labanon, Syria, da Gaza da kuma gabar yammacin kogin jodan , yayi kira ga majalisar dinkin duniya da ta dauki mataken gaggawa wajen dakatar da wadannan hare haren, kuma akwai dubban laifuffukan da Isra’ila ta aikata da ba’a manta ba kuma ba’a dauki wani mataki a kai ba. Aljeriya ta yi wannan bayanin  ne bayan karuwar sukar da ake yi a kwamitin tsaro game da mataken da isra’ila ke dauka a daidai lokacin da ake cikin matsala game da isar da taimakon agaji ga alummar gaza. A taron da kwamitin tsaro...
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro da ta addabi dukkan sassa a Nijeriya. Cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin wannan Larabar mai ɗauke da sa hannunsa, Tinubu ya bayyana cewa dole ne a ɗauki matakan gaggawa da suka dace domin fuskantar barazanar tsaro da ke ƙaruwa ƙasar nan. Shugaban ya bayar da umarnin ɗaukar ƙarin jami’an tsaro da suka haɗa da jami’an ’yan sanda 20,000, lamarin da zai ƙara adadin jami’an zuwa 50,000. Haka kuma, Tinubu ya bai wa rundunar sojin ƙasa da sauran hukumomin tsaro umarnin ɗaukar ƙarin jami’ai. Sanarwar ta ce za a yi amfani da sansanonin masu yi wa ƙasa hidima NYSC a matsayin wuraren horas da sabbin ’yan sandan....
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro da ta addabi dukkan sassa a Nijeriya. Cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin wannan Larabar mai ɗauke da sa hannunsa, Tinubu ya bayyana cewa dole ne a ɗauki matakan gaggawa da suka dace domin fuskantar barazanar tsaro da ke ƙaruwa ƙasar nan. Shugaban ya bayar da umarnin ɗaukar ƙarin jami’an tsaro da suka haɗa da jami’an ’yan sanda 20,000, lamarin da zai ƙara adadin jami’an zuwa 50,000. Haka kuma, Tinubu ya bai wa rundunar sojin ƙasa da sauran hukumomin tsaro umarnin ɗaukar ƙarin jami’ai. Sanarwar ta ce za a yi amfani da sansanonin masu yi wa ƙasa hidima NYSC a matsayin wuraren horas da sabbin ’yan sandan....
    Babban sakataren tsaron kasar Iran Dr Ali Larijani a shafinsa na X ya soki siyasar Amurka a lokacin ziyararsa a kasar Pakistan kuma ya jaddada cewa Tehran tana son ayi gaskiya a duk tattaunawa da za’a yi. Kalaman na larijani yana nuna matsayar iran ne kan diplomasiyar iyakoki, yace yanci da mallaka wasu abubuwa ne da babu sulhu a kansu, don haka duk wata tattaunawa da Amurka dole ne ta zama cikin yanci da daidaito, za’a iya tattaunawa amma ta gudana ba tare da nuna fifiko ba. Amurka tana kokarin nuna kanta a matsayin wadda za ta kawo sauyi a kowanne lamari na duniya, amma wannan wani nau’i ne na yaudarar kai, don haka mun yarda da tattaunawa ta gaskiya...
    Shugaba Bola Tinubu ya aike da sunan mutum uku zuwa Majalisar Dattawa, domin tantance su a matsayin sabbin jakadan Najeriya. Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ne, ya sanar da haka a zaman majalisar na ranar Laraba. Sojoji sun yi juyin mulki a Guinea-Bissau Jami’an tsaro sun ƙaddamar da shirin murƙushe ’yan bindiga a Kaduna Waɗanda aka zaɓa su haɗa da Kayode Are daga Jihar Ogun, Aminu Dalhatu daga Jihar Jigawa da kuma Ayodele Oke. Bayan karanta takardar Tinubu, Akpabio ya ce, “Sunaye uku ne zuwa yanzu, tabbas sauran za su biyo baya.” Tun bayan ɗarewarsa kan mulki a 2023, Tinubu bai naɗa jakadu ba har yanzu. Mutane da dama sun daɗe suna ƙorafin kan jinkirin naɗa jakadun. Amma wasu na...
    Daga Salihu Tsibiri Tsohon shugaban masu rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya bayyana tabarbarewar tsaro da ake fuskanta, wato ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma hare-haren ’yan bindiga, a matsayin barazana ga  siyasar ƙasar nan gabanin zaɓen 2027. Ya yi wannan tsokacin ne a jawabinsa yayin bude zaman taron musamman na yini biyu da Majalisar Wakilai ta shirya kan halin tsaro da ƙasar ke ciki. Alhassan Ado Doguwa, wanda ya yaba da ayyukan da hukumomin tsaro ke ci gaba da gudanarwa, ya ce halin da Arewa ke ciki abin takaici ne ƙwarai, la’akari da yawan mutanen da ke hannun masu garkuwa da kuma waɗanda ke rayuwa cikin tsananin rashin tabbas. Tsohon shugaban ya jaddada cewa duk da cewa...
    Jami’an tsaro a Jihar Kaduna, sun fara gudanar da babban samame domin kawar da ’yan ta’adda da ’yan bindiga a wasu ƙananan hukumomin jihar. A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya fitar, ya ce an gudanar da aikin tare haɗin gwiwar sojoji, DSS, NSCDC, KADVS, da kuma ƙungiyoyin sa-kai da mafarauta. Tukur Mamu ya karbi N50m daga kuɗin fansar harin jirgin kasan Kaduna – DSS Zulum ya ba kowanne ɗalibin Borno da ke karatu a Indiya tallafin N500,000 Aikin ya shafi ƙananan hukumomin Makarfi, Hunkuyi da Ikara. Rundunar ta ce manufar wannan samame shi ne “share dukkanin maɓoyar miyagu, rushe sansanonin da suka kafa, da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankunan...
    Hukumar tsaro ta DSS ta zargi dan jarida kuma mai shiga tsakani da ’yan ta’addar da suka sace fasinjojin jrigin kasan Kaduna-Abuja a shekarar 2022, Tukur Mamu, da karbar Naira miliyan 50 daga kudin fansar fasinjojin. Ana zargin Tukur Mamu da karbar kudin ne daga jagoran ’yan bindigar da ake kira da “Shugaba”. Zulum ya ba kowanne ɗalibin Borno da ke karatu a Indiya tallafin N500,000 Ko sisi ba a biya ’yan bindiga ba kafin su saki ɗaliban da suka sace – Gwamnan Kebbi Mamu na fuskantar tuhumar laifukan ta’addanci, ciki har da karɓar kuɗin fansa daga iyalan waɗanda aka yi garkuwa da su a harin jirgin Kaduna na ranar 28 ga Maris, 2022, hulɗa da kuɗaɗen ’yan ta’adda, hana...
    Majiyar ‘yan hamayyar siyasar kasar Uganda sun sanar da cewa, jami’an tsaron kasar sun kama magoya bayan Bobi Wine dake takarar shugabancin kasar 300 a tsawon yakin neman zabe. Mai magana da yawun Bobi Wine dan takarar shugabancin kasar ya fada a jiya Talata cewa; jami’an tsaron kasar sun kama fiye da mutane 300 da suke goyon bayansa tun da aka fara yakin neman zabe daga watan Janairu zuwa yanzu. Bob Wine wanda shahararren mawaki ne ya juye zuwa dan siyasa, yana yin takara a karo na biyu da shugaban kasar mai ci, Uweri Musaveni. A zaben 2021 Bob Wine wanda sunansa na yanke shi ne Robert Kyagulanyi,, ya zo na biyu. Kakakin jam’iyyarsa ta NUP,ya ce, a cikin wannan...
    Kungiyar ta kasa da kasa mai gudanar da a ayyukan agaji, ta sanar da janye ma’aikatanta daga asibitin Darfur, bayan da aka bude musu wuta, ya kuma kai ga kashe daya daga cikin masu aikin agaji. Kungiyar ta yi kira ga rundunar kai daukin gaggawa RSF da ta tabbatar da tsaro da kuma kiyaye lafiyar ma’aikatan agaji. Bugu da kari kungiyar ta ce mutumin da aka kashe  a ranar 18 ga watan nan na Nuwamba ma’aikaci ne a ma’aikatar kiwon lafiya ta Sudan. Asibitin Zalnagi yana a jihar Darfur ta tsakiya ne da a halin yanzu ke karkashin ikon  rundunar “RSF. A nata gefen, jami’a mai kula da tafiyar da ayyukan kungiyar ta “ Likitoci Ba Tare Da Iyaka Ba.” ...
    Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a ranar Litinin ya ziyarci ɗaliban jihar da ke karatu a ƙasar Indiya, inda ya ba kowannen su tallafin Naira 500,000. Gwamnan, wanda ke ziyarar aiki a Indiya, ya fara ganawa da waɗanda suka ci gajiyar shirin tallafin karatu na jihar a Jami’ar Sharda da ke Noida. Ko sisi ba a biya ’yan bindiga ba kafin su saki ɗaliban da suka sace – Gwamnan Kebbi Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Oyo saboda aikata kisan kai Ya tabbatar musu da jajircewar gwamnatinsa wajen kula da walwalarsu domin samun nasarar karatunsu, sannan ya gargade su da su mai da hankali kan karatun nasu. Ya ce, “Na zo nan yau saboda dalili ɗaya,...
    Gwamnan Jihar Kebbi, Nasiru Idris, ya ce ko sisi gwamnati ba ta biya waɗanda suka yi garkuwa da ɗalibai mata 25 na sakandaren gwamnati ta Maga da ke jihar ba. Ya bayyana hakan ne a taron manema labarai da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar a ranar Talata, inda ya tabbatar da kubutar da ɗaliban da aka sace a farkon makon nan. Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Oyo saboda aikata kisan kai An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a Kebbi Ya ce, “An karɓo ɗalibanmu da aka yi garkuwa da su a Maga. Shugaban ƙasa ya ba jami’an tsaro umarni su gano inda yaran suke, kuma su kubutar da su. Muna tabbatar wa...
    Pars Today – Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran, yana mai jaddada muhimmancin Pakistan a yankin, ya ce haɗin gwiwa tsakanin Tehran da Islamabad a fannoni daban-daban yana taimakawa wajen kawo kwanciyar hankali da zaman lafiya a yankin Ali Larijani, Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran, ya ce da sanyin safiyar Talata da ya isa Islamabad cewa Pakistan muhimmiyar ƙasa ce a yankin kuma tana da matsayi mai kyau wajen tasiri ga yanayin tsaro na yankin. A cewar Pars Today, ya ƙara da cewa a matsayinta na maƙwabciyar gabas ta Iran, Pakistan ma tana taka rawa a al’adu, kuma dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu ta daɗe tana da zurfi kuma ta tarihi. Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Jamhuriyar Musulunci...
    Jami’an tsaro na kasar Siriya karkashin gwamnatin rikon kwarya ta HKI sun budewa masu zanga zangar lumana wuta a yankunan bakin ruwa na kasar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a jiya Talata ce, a garuruwan Tartus, Lazikiyya da lardin Lantakiya mutane suka fito zanga zanga ta lumana inda suke neman adlci ga Alawiyawa da sauran kananan addinin da mazhabobi a yankin. Har’ila yau da sakin wadanda gwamnati take tsare da su. Amma jawabin gwamnatin Jolani ga masu zanga-zangar shi ne aman wutan bindigogi da hayaki mai sa hawaye a kama masu zanga-zangar da dukan wasu daga cikinsu. Labarin ya kara da cewa matsalolin tsaro sun tarbarbare a yankin bakin ruwa na kasar Siriya sosai, tare...
    Shugaban kungiyar Ansar Allah a Yemen, Sayyed Abdul-Malik al-Houthi, ya aika da sakon ta’aziyya ga Sakatare Janar na Hezbollah, Sheikh Naim Qassem, kan shahadar babban  kwamandan dakarun kungiyar Haitham Ali al-Tabtabai da abokansa. Huthi ya jaddada cewa laifin da aka aikata a kansu, tare da hare-haren da ake kai wa Lebanon da Zirin Gaza, yana nuna irin girman kai da Isra’ila ke da shi ne. Sayyed al-Houthi ya kara da cewa shahid al-Tabtabai ya yi kokari matuka wajen cimma manyan-manyan nasarori, kuma ya ba da gudummawa ga hanyar gwagwarmaya don taimakon  gaskiya da wadanda aka zalunta, ya kara da cewa tasirin rawar da ya taka a cikin gwagwarmaya zai ci gaba da wanzuwa a cikin lamirin gwagwarmaya da zaluncin Isra’ila...
    Jami’an tsaro na kasar Siriya karkashin gwamnatin rikon kwarya ta HKI sun budewa masu zanga zangar lumana wuta a yankunan bakin ruwa na kasar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a jiya Talata ce, a garuruwan Tartus, Lazikiyya da lardin Lantakiya mutane suka fito zanga zanga ta lumana inda suke neman adlci ga Alawiyawa da sauran kananan addinin da mazhabobi a yankin. Har’ila yau da sakin wadanda gwamnati take tsare da su. Amma jawabin gwamnatin Jolani ga masu zanga-zangar shi ne aman wutan bindigogi da hayaki mai sa hawaye a kama masu zanga-zangar da dukan wasu daga cikinsu. Labarin ya kara da cewa matsalolin tsaro sun tarbarbare a yankin bakin ruwa na kasar Siriya sosai, tare...
    Jakadan kasar Aljeriya a MDD ya gabatar da jawabi a kwamitin tsaro na majalisar a jiya Talata, inda ya yi tir da hare-haren da HKI take ci gaba da kaiwa kan Gaza, da Lebanon duk tare da yarjeniyar da ta cimma na tsagaita wuta da kungiyoyin Hizbullah da Hamas. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Ammar Ben Jamaa jakadan kasar Aljeriya a MDD yana cewa HKI ba ta mutunta yarjeniyoyin da ta cimma da kasashen Larabawa a yankin,  sannan masu shiga tsakanita da wadannan kungiyoyin sun kasa tabuka wani abu na ganin bangarorin biyu sun mutanen hakkin ko wani banagare. Jamaa ya kara da cewa a halin yanzu HKI tana kai hare-hare a kan kasashen larabawa da...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A cikin ‘yan shekarun nan, batun garkuwa da mutane ya zama babban kalubale ga tsaro a Najeriya da wasu ƙasashen duniya. Lokacin da mutane suka fada hannun masu garkuwa, iyaye da ‘yan uwa sau da yawa suna fuskantar babban zabi mai wahala: biyan kudin fansa don sakin wanda aka sace ko tsayawa da kafafun tsaro har zuwa samun taimakon hukumomi. Shin ko ya kamata alumma su cigaba da biyan kudin fansa idan an yi garkuwa da ‘yan uwansu? NAJERIYA A YAU: Irin Radadin Da Masu Cutar Amosanin Jini Ke Fuskanta DAGA LARABA: Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka Sace Wannan shine batun da shirin Najriya A Yau...
    ’Yan bindiga sun yi garkuwa da aƙalla mutum 11 mazauna garin Isapa da ke kusa da Eruku a Ƙaramar Hukumar Ekiti ta Jihar Kwara. Harin ya faru ne sa’o’i kadan bayan sakin wasu masu ibada da aka yi garkuwa da su suna tsaka da ibada a coci. An haramta cin naman Kare da Kyanwa a Indonesia An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a Kebbi A cocin CAC da ke Ekuru, ana gudanar da bikin godiya domin murnar ’yantar da mambobi 18 da aka yi garkuwa da su kusan wata guda da ya gabata, sai ’yan bindiga suka kutsa suka yi garkuwa da mutum 38 bayan sun harbe uku har lahira. Sabon harin, wanda ya faru da misalin...
    Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin Jihar Jigawa ta kammala shirye-shiryen yi wa  yara sama da miliyan daya da rabi ‘yan ƙasa da shekaru biyar allurar rigakafin shan inna zuwa karshen watan  Nuwamba a jihar. Shugaban  Hukumar Kula  Lafiya a Matakin Farko ta Jihar (JSPHCDA), Dakta Shehu Sambo, ya bayyana haka a taron tattaunawa da manema labarai na yini guda da aka shirya,  tare da hadin gwiwar Hukumar Kula da Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, a Dutse, babban birnin jihar. Dakta Sambo, wanda Mataimakin Mai wayar da kan jama’a na hukumar, Malam Nura Ado ya wakilta, ya ce ana sa ran adadin yara 1,516,244 ne za a yi wa rigakafin a wannan watan. Ya ƙara da cewa rigakafin...
    An ceto ’yan matan nan 24 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Makarantar sakandaren Gwamnati ta GGCSS da ke yankin Maga da ke Jihar Kebbi. Gwamnan jihar Kebbi Nasiru Idiris a taron manema labarai a ranar Talata fadar gwamnatin jihar ya tabbatar da an karɓo ɗalibban da aka sace a farkon makon nan. Ya ce “an karɓo ɗiyanmu ’yan makaranta waɗanda aka yi garkuwa da su a Maga. Shugaban ƙasa ya baiwa jami’an tsaro umarni a tafi a gano inda yaran suke kuma a karɓo su muna tabbatar wa uwayen yara da al’ummar Kebbi yara sun dawo. “Muna godiya ga shugaban ƙasa da jami’an tsaro musamman sojoji da ’yan sanda da Sibil difens da sauransu da suka...
    Daga Bello Wakili  Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bayyana farin cikinsa bisa dawowar ’yan mata 24 da ’yan ta’adda suka sace a Maga, Jihar Kebbi. ’Yan ta’addan sun kai hari makarantar  ranar 17 ga wantan Nuwamban 2026, inda suka yi awon gaba da ’yan matan, jim kaɗan bayan wata rundunar soji ta bar harabar makarantar. Lamarin Kebbi ya haifar da wasu sace-sace makamanta a Eruku da ke Jihar Kwara da kuma Papiri a Jihar Neja. An sako dukkan mutune 38 da aka sace a Eruku ranar Lahadi, inda a wannan ranar ce shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) Jihar Neja ya ce an samu yara 50 daga cikin ɗaliban makarantar Katolika da suka ɓace a gidajen iyayensu. Shugaba Tinubu ya...
    Mahukunta a Jakarta, babban birnin Indonesia, sun haramta sayarwa da cin naman karnuka, kyanwa da jemagu, a wani yunƙuri na daƙile yaɗuwar cutar nan ta Mahaukacin Kare da a Turance ake kira rabies. Da yake jawabi a wannan Talatar, Gwamnan Jakarta, Pramono Anung, ya sanar da rattaba hannu kan dokar da ke hana duk wani nau’in kasuwanci ko mu’amala da waɗannan dabbobi a matsayin abinci. An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a Kebbi Kano Pillars ta kawo ƙarshen wasanni 8 ba tare da nasara ba Dokar wadda za ta fara aiki bayan wa’adin watanni shida, ta ayyana cewa duk wanda ya karya ta zai iya fuskantar hukunci daga kan gargaɗi na rubuce har zuwa janye lasisin kasuwanci...
    Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya gabatar da kasafin kuɗi na shekarar 2026 na sama da naira biliyan 900 ga Majalisar Dokokin jihar. Yayin gabatar da kasafin da aka lakaba wa suna “Kasafin Kirkire-kirkire da Sauyi Don Cigaban Jigawa II,” Gwamna Namadi ya ce za a ware sama da naira biliyan 693.4, wanda ya kai kimanin kashi 76 cikin 100, don ayyukan raya kasa. Gwamnan ya kuma ce sama da naira biliyan 208 za su tafi ne ga ayyukan yau da kullum. A cewarsa, an ware sama da naira biliyan 310 ga bangaren ilimi da lafiya, yayin da kimanin naira biliyan 186 za su tafi ga hanyoyi da sufuri. Malam Umar Namadi ya ƙara...
    ’Yan Majalisar Tarayya daga yankin Kudu sun yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi wa jagoran ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, afuwa bayan da kotu ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai. Kungiyar ’Yan Majalisar Wakilai daga yankin Kudu maso Gabas ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya yi amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi, wajen yi wa Nnamdi Kanu afuwa wanda kotu ta same shi da laifin ta’addanci. Alƙali James Omotosho na Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ne ya yanke hukuncin, inda ya same shi da laifi a kan tuhumar da ake masa guda bakwai, sannan ya yanke masa hukuncin daurin rai da rai. Tuni aka tura Nnamdi Kanu...
    Rahotanni na cewa ’yan bindiga sun sace wasu mutum takwas a garin Biresawa da ke Karamar Hukumar Tsanyawa ta Jihar Kano a daren jiya na Litinin. Wata majiyar da ta tabbatar da lamarin ta shaida wa Aminiya cewa maharan sun shiga garin tsakanin 11 na dare zuwa 12 na tsakar dare, inda suka yi awon gaba da maza biyu da mata shida. ’Yan bindiga sun yi yi garkuwa da mutane 11 a Kwara Chelsea za ta kece raini da Barcelona a Gasar Zakarun Turai Wani ɗan uwa ga waɗanda aka sace, Kabiru Usman, ya ce maharan sun zo ne a ƙafa ɗauke da makamai, suka kuma yi garkuwa da matarsa Umma, ɗiyarsa mai shekara 17, da matar ɗan’uwansa da wasu...
    Daga Musa kutama , kalaba Hasana Aminu matashiyar jaruma ce a Masana’antar Kannywood, wacce ta fito a finafina da dama ciki har da fim xin A Duniya da wasu fitattun finafunan Hausa. A zantawarta da Aminiya, Hasana Aminu wadda aka fi sani da suna Nabila ta ce, a halin yanzu tana tauna taura biyu ne a baka Ga yadda girar su ta kasan ce: Sunan Jarumar? Sunana Hasana Aminu, amma an fi sani na da suna Nabila a Masana’antar Kannywood da ke Kano Ta yaya kike gwama karatu da kuma kasuwanci da harkar fim? Eh, to farko ko da na shigo Masana’antar Kannywood sai na ga ai ashe ma ina da damar da zan iya yin karatu yayin da kuma...
    Gwamnonin jihohin  Arewa 19 za su gudanar da muhimmin taro a ranar Asabar, 29 ga Nuwamba, domin tattauna matsalolin tsaro da suka addabi yankin. Mai bai wa Gwamnan Nasarawa shawara na musamman kan harkokin jama’a, Peter Ahemba, ne ya sanar cewa, taron gwamnonin Arewa da aka shirya a Kaduna zai samu halartar manyan sarakunan gargajiya. “Manufar taron ita ce samar da matsaya ɗaya wajen fuskantar matsalolin tsaro da ke damun yankin, tare da tsara hanyar magance su,” in ji shi. Ya ƙara da cewa, za a yanke muhimman shawarwari a taron domin tabbatar da tsaron yankin. ’Yan Majalisar Kudu sun roƙi Tinubu ya yi wa Nnamdi Kanu Afuwa Amarya ta yi wa angonta yankan rago bayan kwana 3 da aurensu...
    Gwamnatin kasar ta Gambia ta sanar da bai wa jagoran ‘yan hamayyar kasar ta Kamaru Isa Chiroma mafaka bisa dalilai na “‘yan adamtaka”. A wani bayani da ma’aikatar harkokin waje ta kasar Gambia ta fitar, ta bayyana cewa; Chiroma dan shekaru 76 ya isa babban birnin kasar Panjul a ranar 27 ga watan Febrairu a karkashin wata yarjejeniya da aka cimmawa a tsakanin kasashen yankin domin lalubo hanyar warware takaddamar siyasar da kasar Kamaru take fama da ita. Tun bayan da Chiroma ya fice daga kasar ta Kamaru, ya nufi kasar Najeriya, mahukunta a kasar tasa suke kiran da a kama shi. Sai dai maimakon haka, gwamnatin kasar ta Najeriya ta cimma matsaya da mahukuntan kasar Gambia akan a bai...
    Ministan harkokin wajen na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakci wanda yake ziyarar aiki a kasar Oman ya gana da manzon musamman na MDD a kasar Yemen Hans Grundberg a jiya Litinin  ya yi tir da yadda Haramtacciyar Kasar Isra’ila take keta dokoki tana kai wa kasashen wannan yankin hare-hare. Haka nan kuma ministan harkokin wajen na Iran ya kuma nuna kin amincewar jamhuyriyar musulunci ta Iran da yadda ake ci gaba da killace kasar Yemen, yana mai yin gargadi akan sakamakon da zai biyo bayan keta doka da ‘yan Sahayoniya suke yi da shi ne ci gaba da hargitsi da fadace-fadace a wannan yankin. A nashi gefen manzon musamman na MDD a kasar Yemen ya bukaci ganin Iran ta...
    ’Yan Majalisar Wakilai daga yankin Kudu sun yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi wa jagoran ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, afuwa bayan da kotu ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai. Kungiyar ’Yan Majalisar Wakilai daga yankin Kudu maso Gabas ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya yi amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi, wajen yi wa Nnamdi Kanu afuwa wanda kotu ta same shi da laifin ta’addanci. Alƙali James Omotosho na Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ne ya yanke hukuncin, inda ya same shi da laifi a kan tuhumar da ake masa guda bakwai, sannan ya yanke masa hukuncin daurin rai da rai. Tuni aka tura Nnamdi Kanu...
    Ana zargin wata amarya da yi wa angonta yankan rago kwana uku bayan ɗaurin aurensu a Jihar Katsina. Angon mai suna Abubakar Abdulkarim da aka fi sani da Dan Gaske, ana zargin ya rasa ransa bayan da amaryar ta yi amfani da wuƙa wajen halaka shi. Shaidu sun ce ta yi masa mummunan rauni a wuya wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa. Angon da amaryarsa suka daura aure ne a ranar Alhamis, 18 ga Nuwamba, 2025, amma farin cikin aure ya rikide zuwa makoki a ranar Lahadi da rana lokacin da lamarin ya faru. Gobarar tankar mai ta ƙone gidaje a Jihar Neja NAJERIYA A YAU: Irin Radadin Da Masu Cutar Amosanin Jini Ke Fuskanta Wani ɗan uwansa mai suna Aminu...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Cutar amosanin jini wacce aka fi sani da cutar sikila na cigaba da barazana ga rayukan masu dauke da ita. Wannan cuta na saka masu ita da ‘yan uwan su cikin halin ha’ula’i, a wasu lokutan ma tana haifar da rasa rayukan wasu dake dauke da ita. Rahotannin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) sun nuna cewa, kusan yara 300,000 ne ake haifa da cutar Sikila a duk shekara a fadin duniya, inda yankin Kudu da Sahara a Afirka ke dauke da kashi 75% na wannan yawan. A Najeriya kadai, ana kiyasta cewa fiye da yara 150,000 ake haifa da cutar Sikila a kowace shekara — hakan ya sa Najeriya ke da mafi yawan...
    Wata tankar mai ta yi gobara a wani gudan mai a yankin Tungan-Bunu da ke Ƙaramar Hukumar Rijau a Jihar Neja, lamarin da ya janyo ƙonewar gidaje da kadarori da masu yawa. Shaidu sun ce gobarar ta tashi ne a lokacin da tankar take shirin sauke mai a ranar Litinin da yamma, inda wutar ta bazu zuwa gidajen da ke kusa. Duk da cewa babu wanda ya rasa ransa, lamarin ya haifar da firgici inda mazauna yankin suka yi ta tserewa suka bar gidajensu yayin da tankar ke ci da wuta. Tankar mai ta yi hatsari a hanyar Lapai-Agaie Amurka za ta tallafa wa Nijeriya daƙile matsalar tsaro Mayaƙan Boko Haram sun fille kan mata 2 a Borno A wani...
    Shugaban kasar Sudan kuma babban kwamandan sojojin kasar Janar Abdulfattah Alburhan, ya yi watsi da shawarar Amurka ta kawo karshen yaki a kasarsa wanda ya lakume rayukan mutane da dama, ya kuma raba kasar gida biyu a cikin watanni kimani 30 da suka gabata. Shafin yanar gizo na labarai ‘AfricaNews’ ya nakalto Burhan yana fadar haka a ranar Lahadi jim kadan bayan ganawarsa da tawagar kasar Amurka wacce ta gabatar masa da shawarar, ya kuma bayyana ta a matsayin mafi munin shawarar tsagaita budewa juna wuta da aka gabatar masa ya zuwa yanzun.   Burhan ya zargi Massad Boulos mai bawa shugaban kasar Amurka a kan al-amuran nahiyar Afirka da da kokarin rusa sojojin kasar Sudan da kuma bawa yan tawaye...
    Miliyoyin mutanen kasar Iran sun gudanar da jana’izar shahidai kimani 300, a duk fadin kasar, a dai-dai lokacinda ake makokin shahadar diyar manzon Allah (s) Fatimah Azzahra (s). Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, shahidan, wadanda har yanzun ba’a tantance su ba, an ganosu a wurare daban-daban a cikin kasar Iran inda suka yi shahada a yakin shekaru 8 tsakanin Iran da Iraki a farko-farkon nasarar juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran. (1980-1988). Ya zuwa yanzu dai an gano gawakin shahidai fiye da 45,000, sannan akwai wasu fiye da 2000 wadanda ake neman inda suke a cikin kasar ta Iraki. Labarin ya kara da cewa a nan Tehran kadai an yi jana’izar shahidai 100....
    Shugaban kasar Sudan kuma babban kwamandan sojojin kasar Janar Abdulfattah Alburhan, ya yi watsi da shawarar Amurka ta kawo karshen yaki a kasarsa wanda ya lakume rayukan mutane da dama, ya kuma raba kasar gida biyu a cikin watanni kimani 30 da suka gabata. Shafin yanar gizo na labarai ‘AfricaNews’ ya nakalto Burhan yana fadar haka a ranar Lahadi jim kadan bayan ganawarsa da tawagar kasar Amurka wacce ta gabatar masa da shawarar, ya kuma bayyana ta a matsayin mafi munin shawarar tsagaita budewa juna wuta da aka gabatar masa ya zuwa yanzun.   Burhan ya zargi Massad Boulos mai bawa shugaban kasar Amurka a kan al-amuran nahiyar Afirka da da kokarin rusa sojojin kasar Sudan da kuma bawa yan tawaye...
    Kungiyar Hamas wacce take iko ga Gaza ta yi gargadin kan cewa, hare-haren da HKI take kaiwa a kan dukkan fadin Gaza a halin yanzu suna iya kawo karshen yarjeniyar zaman lafiya da ta cimma da ita. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin kungiyar Hazem Qassem yana fadar haka a jiya Litinin ya kuma kara da cewa, kungiyar Hamas ta aiwatar da dukkan sharuddan tsagaita wuta wadanda aka dora mata, amma bangaren HKI ya ci gaba da keta tsagaita wutar tare da hare-haren da take kaiwa kan yankuna daban-daban na zirin Gaza, hare-haren da suka kai daruruwan Falasdinawa ga shahada ya zuwa yanzu. Qassem ya ce tuni kungiyar ta shaidawa jami’an gwamnatin kasar Masar kan abinda...
    Gwamnonin jihohin kudu maso yammacin Najeriya sun bada sanarwan cewa lokacin kafa yansandan jihohi ya yi, har’ila yau dakuma karfafa kula da dazuzzukan kasar saboda magance matsalolin tsaro da suka addabi kasar. Jaridar Daily Trust ta nakalto gwamnonin na fadar haka a jiya Litinin bayan taron gwamnonin shiyar kudu maso yammacin kasar da suka gudanar a birnin Ibadan na jihar Oyo. Gwamnonin 6 sun yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aika masu gadin dazuzzuka a shiyar kudu maso yammacin kasar don tabbatar da tsaronsu , sannan gwamnonin jihohin guda  shida ne zasu dauki nauyin kula da jami’an tsaron.  Labarin ya kara da cewa shugaban gwamnonin kuma gwamnan jihar Lagos Babajide Sanwo-Olu ne ya karanta jawabin bayan taron...
    Gwamnatin Najeriya ta ce Amurka ta amince za ta ƙara faɗaɗa haɗin gwiwar tsaro tsakaninsu, wanda ya haɗa da samar da karin bayanan sirri, makamai da sauran kayan yaƙi, domin ƙarfafa yaƙi da ’yan ta’adda da ƙungiyoyin masu tayar da kayar baya a ƙasar. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Mashawarci na Musamman ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu kan Bayar da Bayanai da Tsara Dabaru, Bayo Onanuga ya fitar a ranar Litinin. Atiku ya karɓi katin jam’iyyar ADC a hukumance Jarumin fina-finan Indiya Dharmendra ya rasu Wannan dai ya biyo bayan jerin tattaunawa da aka gudanar a Washington tsakanin manyan jami’an Najeriya da na Amurka, domin zurfafa dangantakar tsaro da ƙulla sabbin hanyoyin haɗin gwiwa. Tawagar Najeriya ƙarƙashin...
    Ƙungiyar kare hakkin Dan adam ta Amnesty International ta zargi gwamnatin Najeriya da gaza kare yara kanana a fadin kasar, yayin da ake ci gaba da samun karuwar hare-hare da sace-sacen mutane da ake kai wa wasu makarantu a arewacin kasar. Amnesty ta ce ta na nuna damuwa akan yadda gwamnatin Najeriya ke kara nuna gazawa a wajen kare rayukan mutane da dukiyoyinsu musamman ma yara ‘yan makaranta. Isa Sanusi, shi ne daraktan kungiyar ta Amnesty International a Najeriya, ya shaida wa manema labarai cewa, abin da ke faruwa yanzu ya nuna cewa ilimi zai kara samun koma fiye da baya, sai dai bisa ga yadda abubuwa ke faruwa a yanzu na rashin tsaro da satar dalibai abin zai kara...
    Manzon musamman na majalisar dinkin duniya kan kasar Yamen yayi kira ga kasar iran ta ci gaba da nuna goyon bayan kokarin da duniya ke yi wajen ganin zaman lafiya ya ci gaba da wanzuwa a kasar Yamen Han Grungdbag wakilin majalisar dinkin duniya  yayi wannan kira ne a lokacin ganawarsa da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi a birnin muscat na kasar Oman. Grundberg ya bayyanawa Araqchi ci gaban da aka samu kan batun kasar yamen kana yayi kira Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View...
    Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Kwamred Shehu Sani, ya ce umarnin Shugaba Tinubu na janye ’yan sanda daga gadin manyan mutane zai iya zama magana kawai babu aiki. A daidai wannan lokaci na ƙara yawaitar rashin tsaro, Shugaba Tinubu ya ce yana sa ido sosai kan al’amuran tsaro a faɗin ƙasa tare da jajircewa wajen kare ’yan Najeriya. A wani taro da ya yi da hukumomin tsaro a ranar Lahadi, Shugaban Ƙasa ya bayar da umarnin cewa a janye ’yan sanda da ke gadin manyan mutane. A cewar mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, daga yanzu rundunar ’yan sanda za ta mayar da jami’anta kan ayyukan tsaro na asali. Yau Atiku zai karɓi katin zama ɗan...
    Jam’iyyar PDP ta yi soki matakin rufe makarantu da Gwamnatin Tarayya da wasu jihohi suka ɗauka sakamakon yawaitar sace-sacen dalibai, tana mai gargaɗin cewa hakan na iya taimaka wa ’yan ta’adda cimma burinsu. A taron manema labarai da aka gudanar a Abuja a ranar Lahadi, kakakin jam’iyyar, Ini Ememobong, ya ce, ya buƙaci Shugaba Tinubu da ya ajiye muƙaminsa idan ba zai iya kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya. “Muna sake tunatar da Shugaba Tinubu da gwamnatin APC cewa tsaron rayuka da dukiyoyi shi ne aikin farko na kowace gwamnati. Duk lokacin da gwamnati ta kasa yin wannan aiki, dole ta nemi taimako—na cikin gida ko na waje—ko kuma ta yi murabus idan tana da gaskiya da shugabanci,” in ji...
    Mayaƙan Boko Haram masu biyayya ga Ali Ngulde sun fille kan mata biyu a yankin Dutsen Mandara da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza a Jihar Borno. Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa mayaƙan sunyi wa matan kisan gilla ne bisa zargim yin shirka.   Ƙungiyar ta kama matan ne da layu a lokacin bincike, inda a bidiyo da suka fitar, mayakan suka ce hakan shaida ce ta bin hanyar da suka kira haramtacciya. An kai matan zuwa tsaunuka, aka aiwatar da hukunci a bainar jama’a domin tsoratar da mutane da kuma tilasta bin koyarwar ƙungiyar. Rahotanni sun nuna cewa ɓangaren Ali Ngulde ya ƙara tsaurara matakan hukunci a ’yan watannin nan, inda ake kai hare-hare kan mutanen da ake zargi da sihiri, leƙen...
    Fitaccen jarumin masana’antar fina-finan Indiya ta Bollywood, Dharmendra Deol da aka fi sani da Dharam Ji, ya mutu yau Litinin yana da shekaru 89 a duniya. Dharam ya riga mu gidan gaskiya ne kwanaki gabani cika shekaru 90 bayan fama da doguwar jinya mai alaƙa da numfashi kamar yadda kafofin labarai suka ruwaito. Slot na fuskantar matsin lamba saboda rashin kataɓus a Liverpool Ɗaya daga cikin ’yan matan da ISWAP ta sace a Borno ta tsere A watan Nuwambar nan ne labaran ƙanzan kurege suka riƙa yaɗuwa cewa jarumin ya mutu a daidai lokacin da ake jinyar sa a asibitin Breach Candy da ke birnin Mumbai na ƙasar ta Indiya. Bayanai sun ce tun dai cikin watan Oktoban da ya gabata,...
    Daga Bello Wakili Gwamnatin Tarayya ta ce tattaunawa da tawagarta ta yi da jami’an Amurka ta kara karfafa huldar tsaro tsakanin kasashen biyu tare da bude sabbin hanyoyin hadin gwiwa domin kara kare ‘yan Najeriya. Tawagar, karkashin jagorancin Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, ta  gana da manyan jami’an Majalisar Dokokin Amurka, Ofishin Bangaren Addini na Fadar White House, Ma’aikatar Harkokin Waje, Majalisar Tsaro ta Kasa da Ma’aikatar Yaki a birnin Washington DC A yayin tattaunawar, tawagar ta musanta zargin kisan kare dangi a Najeriya, tana mai jaddada cewa hare-haren da ake samu na shafar al’umma ne daga bangarori daban-daban na kabilu da addinai. Ta ce irin wannan kuskuren fassarar halin da ake ciki na haifar...
    Kociyan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool, Arne Slot, na fuskantar matsin lamba saboda rashin kataɓus da ƙungiyar ke fama da shi a bayan nan. A yammacin jiya Lahadi ne Nottingham Forest ta je har filin wasa na Anfield, inda ta lallasa Liverpool da ci 3-0 a wasan mako na 12 na gasar Firimiyar Ingila. Mayaƙan Boko Haram sun file kan mata 2 a Borno Ɗaya daga cikin ’yan matan da ISWAP ta sace a Borno ta tsere Forest ta samu nasarar ce ta hannun Murillo a minti na 33, sai Nicolo Savona a minti na 46, sannan Morgan Gibbs-White ya ƙara na uku a minti na 78. Sakamakon wannan rashin nasarar, Liverpool ta sauka zuwa mataki na 11 da maki 18,...
    Yundunar ’Yan Sandan Jihar Borno ta tabbatar da cewa ɗaya daga cikin ’yan mata 14 da ƙungiyar ISWAP ta sace a Ƙaramar Hukumar Askira-Uba ta kuɓuta, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin gano sauran 13. A sanarwar da ya fitar dangane da irin ƙoƙarin da Jami’an tsaron ke yi na ceto sauran ‘yan matan 13 da ke hannun ‘yan ta’addan, kakakin rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya ce, shugaban gundumar Huyum ya bayar da rahoto a ranar Asabar 22 ga Nuwamba cewa waxanda ake zargin mayaƙan Ƙungiyar ISWAP ne suka sace ‘yan matan, yayin da suke aiki a wata gona a gundumar Mussa. Tawagar ’yan sanda, sojoji, Sibiliyan JTF, da mafarauta da ’yan banga nan da nan suka fara...
    Daga Ali Muhammad Rabi’u  Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kwara ta sanya ranar 1 gawatan Disamba a matsayin wa’adin karshe na biyan kudin kujerar aikin Hajji na shekarar 2026, wanda ya kai sama da naira miliyan 7 da dubu 600. A cikin wata sanarwa, Babban Sakataren Hukumar, Alhaji Abdulkadir Abdulsalam, ya jaddada cewa babu tabbaci yiwuwar karin wa’adi. Sanarwar ta ce  hukumar za ta tura kudaden Hajji ga Hukumar Aikin  Hajji ta Kasa (NAHCON)  domin cika wa’adin da Hukumar Hajjin Saudiyya ta gindaya. Haka kuma ta tabbatar da cewa fara aikin visa wato takardar izinin shiga kasar Saudiyya  zai kasance a watan Fabrairu 2026, kuma duk wani jinkiri na iya hana maniyyaci  samun damar zuwa aikin Hajjin na 2026....
    Mahukunta a tarayyar Nigeria sun sanar da cewa a tsakanin kananan yara 303 na makarantar Majami’ar Roman Katolika da aka sace a jihar Niger, 50 daga cikinsu sun gudu, sun kuma isa wurin iyalansu. Masu tafiyar da makarantar ne su ka sanar da hakan a jiya Lahadi tare da kara cewa shekarun yaran da su ka gudu shekarunsu suna a tsakanin 10 ne zuwa 18. Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya  (CAN) a jihar Niger, Rev. Busul Dauwa Yohanna ne ya sanar da haka, sannan ya kara da cewa: “A halin yanzu da akwai sauran raya 253 da malamai 12 da basu satar mutanen suke rike da su.” A gefe daya shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmad Tinibu ya sanar da tseratar da...
    Mayaƙan Boko Haram masu biyayya ga Ali Ngulde sun fille kan mata biyu a yankin Dutsen Mandara, Gwoza (Borno), bayan sun zarge su da yin shirka.   Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa ƙungiyar kama matan ne da layu a lokacin bincike, inda a bidiyo da suka fitar, mayakan suka ce hakan shaida ce ta bin hanyar da suka kira haramtacciya. An kai matan zuwa tsaunuka, aka aiwatar da hukunci a bainar jama’a domin tsoratar da mutane da kuma tilasta bin koyarwar ƙungiyar. Rahotanni sun nuna cewa ɓangaren Ali Ngulde ya ƙara tsaurara matakan hukunci a ’yan watannin nan, inda ake kai hare-hare kan mutanen da ake zargi da sihiri, leƙen asiri, ko kuma yunkurin tserewa. Sace ɗalibai: Idan ba zai iya...
    Jam’iyyar PDP ta yi soki matakin rufe makarantu da Gwamnatin Tarayya da wasu jihohi suka ɗauka sakamakon yawaitar sace-sacen dalibai, tana mai gargaɗin cewa hakan na iya taimaka wa ’yan ta’adda cimma burinsu. A taron manema labarai da aka gudanar a Abuja a ranar Lahadi, kakakin jam’iyyar, Ini Ememobong, ya ce, ya buƙaci Shugaba Tinubu da ya ajiye muƙaminsa idan ba zai iya kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya. “Muna sake tunatar da Shugaba Tinubu da gwamnatin APC cewa tsaron rayuka da dukiyoyi shi ne aikin farko na kowace gwamnati. Duk lokacin da gwamnati ta kasa yin wannan aiki, dole ta nemi taimako—na cikin gida ko na waje—ko kuma ta yi murabus idan tana da gaskiya da shugabanci,” in ji...
    Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Kwamred Shehu Sani, ya ce umarnin Shugaba Tinubu na janye ’yan sanda daga gadin manyan mutane zai iya zama magana kawai babu aiki. A daidai wannan lokaci na ƙara yawaitar rashin tsaro, Shugaba Tinubu ya ce yana sa ido sosai kan al’amuran tsaro a faɗin ƙasa tare da jajircewa wajen kare ’yan Najeriya. A wani taro da ya yi da hukumomin tsaro a ranar Lahadi, Shugaban Ƙasa ya bayar da umarnin cewa a janye ’yan sanda da ke gadin manyan mutane. A cewar mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, daga yanzu rundunar ’yan sanda za ta mayar da jami’anta kan ayyukan tsaro na asali. Yau Atiku zai karɓi katin zama ɗan...
    Yayan kungiyar yan ta’adda ta ‘the Islamic State West African Province (ISWAP) ta bada sanarwan kamawa da tsare yan mata 13 a karamar hukumar Askira-Uba na jihar Borno a jiya Lahadi. Jaridar Daily Trust ta Nageriya ta nakalto Abdullahi Askira dan majalisar dokokin jihar Borno mai wakiltan Askira yana tabbatar da labarin ya kuma kara da cewa ISWAP ta kama wadan nan yan mata wadanda suke da shekaru tsakanin 13-19 ne a lokacinda suke aiki a gonakinsu a gundumar Mussa na karamar Hukumar ta Askira. Jaridar ta kara da cewa wannan satar yan mata da yan makaranta ya biyo bayan irinsu da suka yi a makarantar mata ta Maga a karamar hukumar Wasagu na jihar Kebbi da kuma na makarantar...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A shekarar 2014, bayan tashin hankalin da ya biyo bayan sace ɗaliban Chibok da kuma yawaitar hare-hare kan makarantun yankin Arewa maso Gabas, gwamnatin tarayya tare da haɗin gwiwar ƙasashen duniya ta ƙaddamar da wani muhimmin shiri mai suna Safe School Initiative.   Manufar wannan shiri ita ce tabbatar da cewa dalibai suna iya zuwa makaranta cikin tsaro ba tare da fargabar hare-hare daga ‘yan ta’adda ko ‘yan bindiga ba. NAJERIYA A YAU: Ba A Yi Ma Nnamdi Kanu Adalci Ba- Emmanuel Kanu DAGA LARABA: Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka Sace Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne akan wannan shiri da...
    Shugaban kasan Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin janye jami’an ƴansanda dake gadi ko rakiyar manyan mutane domin mayar da su aikin tsaro. Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar ya fitar Mr Bayo Onanuga, da yammacin wannan Lahadi, ya ce daga yanzu za’a rika tura jami’an ƴansanda ne gudanar da ayyukan ƙasa. Tinubu ya bayar da umarnin ne yayin ganawar da ya yi da shugabannin tsaron ƙasar da suka haɗa da rundunar sojin sama, da na ƙasa da na ruwa da Darakta Janar na ma’aikatar tsaro ta DSS da kuma Sufeto Janar na ƴansanda Kayode Egbetokun. Sanarwar ta ce, daga yanzu duk mutumin da ke son jami’an tsaro su yi gadinsa to ya nemi...
    Ana zargin wasu ’yan bindiga da kashe wani fitaccen ɗan kasuwa, Alhaji Muhammad Bakoshi, lokacin da suka kai hari garin Zalau da ke Ƙaramar Hukumar Toro a Jihar Bauchi. Bayan kai hari, sun sace ɗaya daga cikin matansa, Hannatu Muhammad. Tinubu ya dakatar da ’yan sanda daga tsaron manyan mutane a Najeriya An ceto mutum 38 da aka sace a cocin Kwara — Tinubu Wani mazaunin yankin, Shamsuddeen Hashimu Zalawa, ya shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar sun je gidan mutumin da tsakar dare. Ya ce sun dinga harbe-harbe ba ƙaƙƙautawa, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin firgici. Ya ƙara da cewa sun nufi gidan Bakoshi kai-tsaye, wanda hakan ya sa wasu ke zargin ko turo su aka yi....
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bai wa ’yan sanda umarnin daina tsaron manyan mutane a faɗin Najeriya. Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ne, ya bayyana hakan a ranar Lahadi. ’Yan sanda sun ƙaryata jita-jitar kai wa coci hari a Gombe ’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda 5 a Bauchi Onanuga, ya ce daga yanzu ’yan sanda za su mayar da hankalinsu ne aikin kare al’umma da yaƙar ’yan ta’adda. An ɗauki wannan mataki ne a wani taron tsaro da aka gudanar a Abuja, wanda manyan shugabannin tsaro suka halarta, ciki har da shugabannin ’yan sanda, sojin sama, sojin ƙasa da hukumar DSS. Sabon tsarin ya nuna cewa duk wani babban mutum da yake buƙatar tsaro dole ne,...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta ce labarin da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta na kai wa cocin ECWA da ke Kashere hari, ba gaskiya ba ne. Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi ne, ya bayyana haka, inda ya ce sun bincika tare da gano cewar jita-jita ce. Ya ce DPO na Pindiga da shugaban ofishin ’yan sanda na Kashere, sun tuntuɓi wani dattijo da ya halarci cocin domin yin addu’a a ranar Lahadi. Dattijon ya shaida musu cewa babu wani abu da ya faru, kuma ’yan sanda suna harabar cocin tun safe a domin kula da sha’anin tsaro kamar yadda suka saba. Rundunar ta ce yaɗa irin wannan jita-jitar na iya tayae da hankalin jama’a. Ta kuma ce ta...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, ta tabbatar da mutuwar wasu jami’anta guda biyar a ƙauyen Sabon Sara da ke Ƙaramar Hukumar Darazo, sakamakon harin da wasu ’yan bindiga suka kai. Kakakin rundunar, CSP Ahmed Wakil ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranae Lahadi. An ceto mutum 38 da aka sace a cocin Kwara — Tinubu Ɗalibai 50 da aka sace a Neja sun kuɓuta — CAN “‘Yan sanda biyar sun rasu, biyu sun jikkata, amma an yi nasarar kashe wasu daga cikin ’yan bindigar a ƙauyen Sabon Sara, Ƙaramar Hukumar Darazo, a jihar Bauchi.” Wakil, ya ƙara da cewa, “Ma’aikatanmu suna jajircewa kuma sun samu nasarar kashe wasu daga cikin ’yan bindigar yayin musayar wuta.” Ya bayyana ’yan...
    Ma’aikatar lafiya a Lebanon ta ce mutum biyar ne suka rasa rayukansu a wani sabon harin Isra’ila a Kudancin babban birnin Kasar, inda kuma ta raunata kimanin fararen hula 28. A cewar ofishin Firayim Minista Benjamin Netanyahu, harin an kai shi kan “babban hafsan sojojin Hezbollah,” Ali Tabataba’i, wanda Isra’ila ke zarginsa da “jagorantar ƙarfafawa da kuma ba da makamai” ga kungiyar. Shugaban Lebanon Michel Aoun ya yi Allah wadai da harin, yana mai cewa ya nuna rashin halin ko kula da gwamnatin Tel Aviv ke yi wa kiraye-kirayen kasashen duniya na dakatar da keta haddi a kasar Lebanon. Ita ma kungiyar Jihadin Musulunci ta Falasdinu ta yi Allah wadai da harin, tana mai daukar alhakin al’ummar duniya. An ruwaito...
    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cewa an ceto masu ibada 38 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a cocin Eruku da ke jihar Kwara. Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Tinubu ya kuma tabbatar da kubutar dalibai 51 cikin 315 da aka sace a jihar Neja. “Godiya ga jami’an tsaronmu a ‘yan kwanakin nan, an ceto dukkan masu ibada 38 da aka yi garkuwa da su a Eruku na jihar Kwara,” in ji shi. Sai dai ba yi karin bayani ba kan yadda aka ceto su. “Ina ci gaba da bin halin da ake ciki kan yanayin tsaro a kasa baki daya kuma ana ba ni bayanai akai-akai daga inda abubuwan...
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewar an ceto dukkanin mutanen da mahara suka sace a wata coci a yankin Eruku na Jihar Kwara. ’Yan bindigar sun sace masu ibadar ne a ranar Talata, lokacin da suka kai hari cocin Christ Apostolic Church (CAC) da ke Oke Isegun a Eruku, wani gari da ke iyaka da Kogi a Karamar Hukumar Ekiti ta Jihar Kwara. ISWAP ta sace ’yan mata 13 a Borno Barin jama’a su kare kansu ne ke rura rashin tsaro — Sojoji A cikin wani sako da Tinubu ya wallafa a X a ranar Lahadi, ya ce yana bibiyar yanayin tsaro a fadin kasar nan, kuma zai tabbatar da cewa gwamnatinsa ta kare ’yan Najeriya. An yada bidiyon...
    Mayaƙan ISWAP sun sace wasu ’yan mata a Ƙaramar Hukumar Askira-Uba a Jihar Borno. Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Borno, Abdullahi Askira, ya tabbatar da sace ’yan matan. Ɗalibai 50 da aka sace a Neja sun kuɓuta — CAN An rufe duk makarantu a Kebbi Ya ce an sace ’yan natan ne yayin da suke aiki a gonakinsu da ke yankin Mussa. A cewarsa, ’yan matan guda 13 masu shekaru tsakanin 15 zuwa 20 sun tafi gona domin girbe amfanin gonarsu, sai maharan suka yi awon gaba da su. Tun da farko an mayar da mutanen Huyim zuwa Mussa saboda matsalar rashin tsaro a garuruwansu. Sai dai ya ce ɗaya daga cikin ’yan matan da aka sace ta tsere kuma...
    Rundunar Sojin Najeriya, ta ce barin jama’a da aka yi don su kare kansu ne ke rura wutar rikici a Jihar Filato. Birgediya Janar MA Etsy-Ndagi, Shugaban Hulɗar Sojoji Da Fararen Hula ne, ya bayyana haka a lokacin da yake hira da ’yan jarida a Jos. An rufe duk makarantu a Kebbi Ma’aikatan lantarki na shirin shiga yajin aiki a faɗin Najeriya  Ya ce barin al’umma domin su kare kansu bai haifar da ɗai mai ido ba, illa ƙara tsananta rikice-rikice. Jihar Filato na fama da rikice-rikice tun daga shekarar 2001, inda mutane da dama suka rasu, wasu kuma suka jikkata. Wasu ƙungiyoyi a jihar sun yi kiran da a bar jama’a su kare kansu saboda yawan hare-hare da suke...
     Taron na kasar Brazil akan muhalli wanda shi ne karo na 30 ya amince da bayar da tallafin kudade ga kasashe masu karancin kudaden shiga domin fuskantar matsalar dumamar yanayin duniya.  Mahalarta taron da su ka fito daga kasashen duniya mabanbanta, wadanda suke fafutukar ganin an shawo kan matsalar da ake fuskanta a duniya ta sauyin yanayi. Sai dai kuma bayanin da aka fitar bai yi Ishara da tasirin makamashin man fetur da dangoginsa a matsayin wadanda suke taka rawa wajen gurbata yanayin duniya. Sabanin da aka sami a tsakanin tarayyar turai da kuma kasashen larabawa masu arzikin man fetur ne ya sa aka jinkirta yin magana  man fetur din da dangoginsa. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login...
    Ƙungiyar Ƙwadago ta Ma’aikatan Wutar Lantarki ta Ƙasa (NUEE) ta yi barazanar dakatar da dukkan ayyukan samar da wutar lantarki a faɗin Najeriya, sakamakon harin da ta ce jami’anta sun fuskanta a Jihar Imo. Ƙungiyar ta bayyana cewa wasu jami’an ’yan sanda ɗauke da makamai ne suka kai wa ma’aikatanta hari a Egbu 132/33kB Transmission Substation da ke Owerri, Jihar Imo, lamarin da ya janyo fargaba da tayar da hankali ga ma’aikatan da ke wurin. Fiye da yara miliyan 400 na fama da talauci a duniya — UNICEF An gano wurin da ’yan bindiga ke tsare da ɗalibai 25 da aka sace a Kebbi A wata sanarwa da sakataren ƙungiyar na ƙasa ya fitar, NUEE ta ce wannan hari na...
    161-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa, shiri wanda yake kawo maku, kissoshi wadanda suka zo cikin Alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Mrtada Muttahari, ko kuma cikin littafan Mathnawa na maulana Jalaluddeen Rumi. Ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau. ////… Ma dalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-Haddan dan Aliyu (a) dan Fatimah (s) diyar manzon Allah (s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata, mun bayyana yadda wasu...
    Zabebben magajin garin birnin NewYork na kasar Amurka Zohran Mamdani, a haduwarsa ta farko da shugaban kasar Amurka Donal Trump a birnin Washington ya bayyana cewa HKI tana aikata kissan kiyashi a gaza, sannan mutanen NewYork basa son ganin gwamnatin Amurka tana amfani da kudaden harajin da suke biyu wajen tallafawa gwamnati wacce take aikita kissan kiyashi a duniya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto magajin garin birnin NewYork musulmi na farko na cewa yana son shugaban Trump ya karkata kudaden da yake kashewa kan sojojin Amurka wadanda suke yake-yaken da masa da wani amfani ga mutanen kasar Amurka zuwa magance talaucin da Amurka suke fama da shi a cikin gida musamman masu kwana a waje a...