Dangote Ya Ɗauki Nauyin Bikin Baje Kolin Gidajen Afrika Da Mahalarta Ƙasashe 21
Published: 3rd, August 2025 GMT
A cewar sanarwar, AIHS za ta taimaka wajen haɓaka tambarin dangote da haɓaka dabarun haɗin gwiwa tare da masu ruwa da tsaki.
Kodinetan shirin Barista Festus Adebayo ya shaida wa manema labarai cewa, za a iya cike giɓin gidaje a ƙasar ta hanyar haɗin gwiwar Haɗin kan Jama’a masu zaman kansu (PPP).
Ya ce: “Kwarewa da haɗin gwiwa su ne manyan abubuwan da muka a gaba, idan aka yi la’akari da saurin ci gaban fasaha a cikin gine-ginen gidaje, samar da kudaɗe da kuma inganta tsarin.
Ya ce taken taron na wannan shekara, Maimaita Gidaje Ta Hanyar Sabuntawa, wanda daidai yake da ainihin darajar kamfanin.
Barista Adebayo ya ce yana da ƙwarin gwiwar cewa haɗin gwiwa da kamfanin Simintin dangote zai taimaka wajen magance matsalar ƙarancin gidaje a ƙasar.
Ya ce sama da kashi 82 cikin 100 na mahalartan suna riƙe da matsayi na yanke shawara, tare da tabbatar da masu hulda kai tsaye tare da mutanen da ke da ikon saye.
Idan dai za a iya tunawa, Cibiyar Gine-gine ta Nijeriya (NIOB) da masu ruwa da tsaki a harkar gidaje sun bayyana kamfanin dangote a matsayin daya daga cikin manyan hanyoyin bunƙasa gidaje a Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Tarayya ta raba wa talakawa N330bn — Ministan Kuɗi
Ministan Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziƙi, Wale Edun, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta raba wa talakawa Naira biliyan 330 a matsayin tallafi.
Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Abuja, inda ya ce an raba kuɗin ne ta Ofishin Tsare-tsaren Jin-ƙai na Ƙasa (NASSCO), domin rage wa talakawa wahalar cire tallafin mai da sauyin musayar kuɗaɗen waje.
An kashe ’yan ta’addan IPOB da yawa a Imo — ’Yan Sanda ’Yan bindiga sun sako ma’auratan da suka sace a Katsina bayan biyan N50mA cewarsa, aƙalla gidaje miliyan 19.7 (sama da mutum miliyan 70) aka sanya a Rajistar Tsarin Tallafa Wa Talakawa, kum tallafin ya kai ga gidaje miliyan 15.
“Zuwa yanzu, gidaje miliyan 8.5 sun samu aƙalla Naira 25,000 sau ɗaya, wasu kuma sun samu sau biyu ko uku.
“Sauran gidaje miliyan bakwai za su karɓi tallafin kafin ƙarshen shekara,” in ji Edun.
Ya ƙara da cewa ana biyan tallafin ne ta hanyar banki ko asusun wayoyi, ta hanyar amfani da lambar NIN na kowane wanda zai ci gajiyar.
Ministan, ya ce za a ci gaba da saka shirin a cikin kasafin kuɗin shekara-shekara domin ya ɗore.
Shugabar NASSCO, Hajiya Funmi Olotu, ta bayyana cewa dalilin biyan tallafin kashi-kashi, shi ne saboda umarnin Shugaba Bola Tinubu na haɗa tsarin da lambar NIN, domin tabbatar da gaskiya.
“Ba a raba kuɗi a hannu kai tsaye kamar da. Yanzu ana biyan kuɗi ne kai tsaye ta asusun banki. Wannan ne ya sa wasu gidajen suka riga suka karɓi sau ɗaya, biyu ko sau uku,” in ji ta.