Leadership News Hausa:
2025-09-19@04:03:27 GMT

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Da Dama A Kauyukan Zamfara

Published: 4th, August 2025 GMT

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Da Dama A Kauyukan Zamfara

Akalla mutane 11 ne aka kashe a harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a unguwannin Kagara da San-Isa da ke karamar hukumar Kaura-Namoda a jihar Zamfara. Majiyoyi daga yankunan biyu sun shaida wa wakilinmu cewa an kai hare-haren ne a unguwannin Kagara da San-Isa tare da wasu kauyukan da ke kewaye. Waɗanne Ƙasashe Ne Suka Amince Da Kafa Ƙasar Falasɗinu? Sanata Shehu Buba Ya Ƙaddamar Da Rabon Taki Da Rigakafin Shanu A Bauchi Wata majiya daga dan garin Kagara wanda ya bayyana sunansa da Abubakar Sani ya shaidawa LEADERSHIP cewa ya rasa ‘yan uwansa guda biyu a harin wanda ya afku a ranar Asabar din da ta gabata.

Ya ce, ‘yan fashin da suka yiwa kauyen su kawanya da misalin karfe 6:30 na yammacin ranar Asabar, sun yi awon gaba da shanu da sauran kayayyakin mutane tare da yin garkuwa da maza da mata zuwa cikin daji. Da yake zantawa da LEADERSHIP ta wayar tarho, wani mazaunin garin, Ahmed Dan-Isa ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun kashe akalla mutanen kauyen 9 a ranakun Asabar da Lahadi da safe tare da yin garkuwa da wasu da dama da suka hada da maza da mata. Ahmed wanda ya ce ya tsere daga hare-haren ‘yan bindigar, amma ya ce, maharan sun mamaye kauyukan ba tare da fargabar jami’an tsaro ba. Ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta tarayya da su taimaka ta hanyar kubutar da daukacin Kaura-Namoda daga mummunan halin da take ciki. Kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansanda (PPRO) na rundunar, Yazid Abubakar ya ci tura, domin lambar wayarsa a kashe take a lokacin hada wannan rahoto.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Zamfara Ta Nemi Karin Tallafi Ga ‘Yan Gudun Hijira

Gwamnatin Jihar Zamfara ta roki Hukumar Raya Kasashen Waje ta Kasa (FCDO), Premier Urgence Internationale (PUI), da sauran masu ruwa da tsaki da su kara tallafa wa ‘yan gudun hijirar da ke jihar.

 

Kwamishinan Bada Agaji na Jiha Alhaji Salisu Musa Tsafe ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake jawabi ga mahalarta taron na kwana guda kan shirin ceton rayuka da karfafawa da kuma juriya (LEARP) wanda kungiyar FCDO ta dauki nauyin shiryawa a Abuja.

 

A wata sanarwa dauke da sa hannun Daraktan Yada Labarai na Ma’aikatar, Bashir Kabiru Ahmad, Kwamishinan ya bayyana cewa a halin yanzu jihar na karbar dubban ‘yan gudun hijira daga al’ummomi sama da 1,008 a fadin kananan hukumomin 14, kamar yadda aka gani a cikin rajistar zamantakewa na jihar.

 

Alhaji Musa Tsafe ya bayyana cewa, tallafin da ake bukata ya hada da bangarorin Rayuwa, Karfafawa, samun tallafin Kudi da Manufofi da sauran abubuwan da za a iya yi da nufin rage radadin halin da ‘yan gudun hijira  ke ciki a jihar.

 

Alhaji Tsafe ya yabawa abokan aikin raya kasa bisa yadda suke ci gaba da tallafawa ‘yan gudun hijira da sauran marasa galihu a Zamfara.

 

A cewarsa, aikin da aka tsara domin aiwatar da shi da kungiyar Premier Urgence International (PUI) za ta yi zai kasance muhimmin taimako ga al’ummar jihar Zamfara.

 

Ya bayyana taron a matsayin wani ci gaba a kokarin jihar na inganta rayuwar ‘yan gudun hijira da marasa galihu musamman mata da yara.

 

 

Alhaji Tsafe ya tabbatarwa da abokan huldar cewa jihar Zamfara karkashin Gwamna Dauda Lawal ta samar da tsarin siyasa da samar da yanayin da kungiyoyin agaji ke gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

 

REL/AMINU DALHATU.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ‘Yan Gwgawarmaya Sun Kashe Sojojin HKi 4 A Gaza
  • ’Yan sanda sun kama mutum 9 kan yin garkuwa da kansu
  • Gwamnatin Zamfara Ta Nemi Karin Tallafi Ga ‘Yan Gudun Hijira
  • An kashe ’yan ta’addan IPOB da yawa a Imo — ’Yan Sanda
  • ’Yansanda Sun Kama Mutane 9 Kan Yin Ƙaryar Sace Su A Jihar Neja
  • Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno
  • Kungiyar Human Rights Watch; Isra’ila Ta Kashe ‘Yan Jarida Fiye Da 30 A Kasar Yemen Ne Da Gangan  
  • ‘Yan Bindiga Sun Yi Wa Hakimi Yankan Rago A Zamfara
  • ’Yan ‘Mafiya’ na ƙoƙarin kashe matatar man fetur da na gina —Ɗangote
  • NAJERIYA A YAU: Matsayin Doka Kan Hawa Mumbari Ba Tare Da Izinin Gwamnati Ba