An yi wa Jalo Daudu a sarautar Tafarkin Gombe
Published: 3rd, August 2025 GMT
Mai Martaba Sarkin Gombe, Alhaji Dakta Abubakar Shehu Abubakar III, ya naɗa Dakta Ibrahim Jalo Daudu sarautar Tafarkin Gombe.
Dakta Daudu, wanda ya taɓa riƙe muƙamin Babban Sakatare na Tarayya da Kwamishinan Lafiya na farko a Jihar Gombe.
Sauyin Yanayi: Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da shirin dashen bishiya miliyan 5 Sake zaɓen Tinubu zai lalata makomar Najeriya — El-RufaiDaga baya ya zama Shugaban Ma’aikata a Gwamnatin Jihar Gombe, sannan ya riƙe wasu manyan muƙamai a Fadar Shugaban Ƙasa.
Yanzu haka, shi ne Kwamishina a Hukumar Kula da Ayyukan Ma’aikata na Ƙasa, inda yake wakiltar Jihohin Adamawa, Gombe da Taraba.
Dakta Daudu ya fito ne daga gidan sarauta a Gombe, kuma kakansa shi ne Hakimin Gombe na farko bayan masarautar ta koma zuwa birnin Gombe a yanzu.
Har ila yau, shi ne Ɗan Masanin Funakaye.
Sarautar Tafarki na ɗaya daga cikin manyan sarautun gargajiya a ƙasar Hausa.
Ana bai wa ɗan Sarki ko babban ɗan uwansa sarautar, kuma zai dinga bai wa Sarki shawara ko gyara idan ya zama dole.
Mai riƙe da wannan sarauta yana da damar shiga fada kai-tsaye da bai wa Sarki da masarauta shawara.
Asalin sarautar Tafarki ta samo asali ne tun zamanin Hausa Bakwai, kuma an ce mutum na farko da aka bai wa wannan sarauta shi ne Musa, a lokacin Sarkin Katsina Umaru Dallaje.
Yayin da yake sanar da naɗin, Sarkin Gombe, ya bayyana Dakta Daudu a matsayin mutum mai ƙwarewa, kuma wannan ne ya sa ya dace da wannan matsayi domin bai wa masarautar shawara.
Dakta Daudu, ya nuna farin ciki da godiyarsa ga Sarkin Gombe da majalisarsa, inda ya ce zai yi amfani da wannan dama wajen yi wa al’umma hidima cikin gaskiya da riƙon amana.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Naɗi Sarauta sarki Tafarkin Gombe
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Me dokar kasa ta ce kan karin wa’adin aiki da Shugaban Kasa ke yi?
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Karin wa’adin aiki da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa Kwanturola Janar na Hukumar Hana Fasa Kwauri ta Kasa, Bashir Adewale Adeniyi na ta shan suka daga mutane daban-daban.
Yayin da wasu ke ganin abin da shugaban ya yi da cewa ya dace, wasu kuwa na ganin hakan ya yi hannun riga ga tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasa.
Shin ko me dokar kasa ta ce game da wannan karin wa’adi da shugaban kasan ya yi?
NAJERIYA A YAU: Tinubu ya yi wa Arewa adalci a ayyuka da mukamai — Bayo Onanuga DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aureWannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan