HausaTv:
2025-08-03@13:57:31 GMT

Iran Da Japan Suna Iya Jagorantar Duniya Don Rabata Da Makamai Kare Dangi

Published: 3rd, August 2025 GMT

Ministan harkokin wajen kasar Aran Abbas Aragchi ya bayyana cewa JMI da kuma kasar Japan suna iya jagorantar kasashen duniya zuwa ga rabata daga makaman kare dangi.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Ministan yana fadar haka a wani rubutu da yayi, wanda kuma aka buga a jaridar Asahi Shimbun ta kasar Japan.

Ya kuma kara da cewa, kasashen biyu an yi amfani da makaman kare dangi a kansu. Y ace kamar yadda Amurka ta yi amfani da makaman nukliya kan kasar Japan a shekara ta 1945 a karshen yakin duniya na biyu, haka nan Sadam ya yi amfanin da makaman guba a kan iraniyawa a kallafeffen yakin da suka fafata na shekaru 8 a tsakaninsu.

Arachi ya ce, kasashen biyu a matsayin kasashen da aka yi amfani da makaman kare dangi a kansu suna iya samar da wata motsi a duniya wacce za’a iya kaiwa ga lalata dubban makaman kare dangi a duniya.

Ministan yayi wannan rubutun ne don taya kasar Japan jejen kashe dubban mutanen kasar da makaman nukliya a shekara 1945, wanda a yau yake cika shekaru 80 da faruwa.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kungiyar Hamas Ta Bayyana Cewa Ba za ta Ajiye Makamanta ba Sai Bayan samar Da Kasar falasdinu August 3, 2025 Kungiyar Hamas Ta Wallafa Hotunan bidiyo Na Fursinan HKI tsare A Gaza August 3, 2025 Sojojin HKI, Daga Jiya Zuwa Yau lahadi Kadai Sun Kashe Falasdinawa 62 August 3, 2025 Pezeskkian Ya Ce: Suna Fatan Musayar Kasuwancin Tsakanin Iran Da Pakistan Ta Haura Dala Biliyan 10 August 2, 2025 Araqchi: Abokantaka Da Ke Tsakanin Iran Da Pakistan Wata babbar Jari Ce Nan Gaba August 2, 2025 Jaridar Isra’ila Ta Ce: Gwamnatin Mamayar Isra’ila Ta Sha Kashi A Yakin Gaza   August 2, 2025 Dakarun Yemen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Lod Da Ke Haramtacciyar Kasar Isra’ila August 2, 2025 Rahoton Majalisar Dinkin Duniya Ya Yi Gargadi Kan Barazanar Kungiyoyin ‘Yan Ta’adda A Afirka August 2, 2025 Shugaba Pezeshkiyan Ya Yi Juyayin Shahadar Haniya Bayan Shekara Guda Da Shahada August 2, 2025 MDD: HKI Ta Kashe Falasdinawa Fiye Da 100 A Cikin Kwanaki 2 A Lokacinda Suka Karban Abinci August 2, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: makaman kare dangi kasar Japan

এছাড়াও পড়ুন:

Iran ta yi gargadi game da makirce-makircen Isra’ila na kawo cikas ga tsaron yankin


Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila na da burin kawo cikas ga harkokin tsaro a yankin, yana mai kira ga daukacin kasashen yankin da su yi taka tsantsan wajen tunkarar irin wannan makirci.

Araghchi ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da mataimakin firaministan Hadaddiyar Daular Larabawa kuma ministan harkokin wajen kasar Sheikh Abdullah bin Zayed Al Nahyan a ranar Juma’a.

Ministan na Iran ya ce gwamnatin Isra’ila ta saba da dabi’a ta  son kai da rashin bin doka da oda.

Manyan jami’an diflomasiyyar Iran da na Hadaddiyar Daular Larabawa sun tattauna kan sabbin abubuwan da ke faruwa a yankin musamman halin da Falasdinu ke ciki.

Har ila yau Araghchi da Nahyan sun yi musayar ra’ayi game da hanyoyin inganta dangantakar kasashnsu a fannonin siyasa, tattalin arziki da kasuwanci daban-daban.

Sun jaddada bukatar yin amfani da damar da kasashen biyu suke da ita wajen fadada alaka a cikin batutuwan da suka shafi moriyar kasashen biyu.

A watan Yulin da ya gabata ne dai sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Akbar Ahmadian da kuma mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa Tahnoun bin Zayed Al Nahyan suka bukaci hadin kan kasashen yankin don tabbatar da tsaro a yankin baki daya, bayan shafe kwanaki 12 na hare-haren wuce gona da iri da Isra’ila da Amurka suka kai wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Firayim Ministan Senegal Ya Bayyana Sabon Shirin Farfado Da Tattalin Arzikin Kasar August 2, 2025 Gaza: Witfkoff ya yi rangadi a wuraren da Amurka ta kafa domin tallafi August 2, 2025 ‘Yan Sudan dama na komawa gida bayan gudun hijira na tsawon shekaru a Masar August 2, 2025 Iran Ta Ce Batun Neman Dakatar Da Tace Uranium Zai Rusa Duk Wata Jarjejeniya Da Ake Son Cimmawa August 1, 2025 Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Yi Watsi Da Duk Wani Zarge-Zargen Neman Bata Mata Suna August 1, 2025 Limamin Sallar Juma’a Ya Ce; Iran Zata Mayar Da Isra’ila Kufai Idan Ta Sake Kai Hari Kan Kasarta August 1, 2025 Kasar Slovenia Da Haramta Tura Makamai Zuwa Haramtacciyar Kasar Isra’ila August 1, 2025 Kasar Spain Ta Bayyana Abin Da Ke Faruwa A Gaza A Matsayin Abin Kunya Ga Bil’Adama August 1, 2025 Iran ta yi watsi da zargin gwamnatocin turai na yunkurin kashe wasu mutane a kasashensu August 1, 2025 Mali da Rasha sun tattauna kan hadin gwiwar makamashi August 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • IRGC Tace Bata Amince Da Kasashen Biyu A Kan Kasar Falasdinu Ba
  • Pezeskkian Ya Ce: Suna Fatan Musayar Kasuwancin Tsakanin Iran Da Pakistan Ta Haura Dala Biliyan 10
  • Araqchi: Abokantaka Da Ke Tsakanin Iran Da Pakistan Wata babbar Jari Ce Nan Gaba
  • Rahoton Majalisar Dinkin Duniya Ya Yi Gargadi Kan Barazanar Kungiyoyin ‘Yan Ta’adda A Afirka
  • Shugaban Ansarullah: Amurka Tana Da Hannu A Ta’asar Da HKI Take Aikatawa A Gaza
  • Kungiyar Wasan Taekwondo Ta Guragu Ta Iran Ta Zama Zakara A Asiya Karo Na 10 A Jere
  • Iran ta yi gargadi game da makirce-makircen Isra’ila na kawo cikas ga tsaron yankin
  • Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Yi Watsi Da Duk Wani Zarge-Zargen Neman Bata Mata Suna
  • Kasar Slovenia Da Haramta Tura Makamai Zuwa Haramtacciyar Kasar Isra’ila