Manoma Sun Caccaki Tinubu Kan Ƙarfafa Shigo Da Shinkafa Da Masara Daga Ƙasashen Waje
Published: 3rd, August 2025 GMT
A zagayen duba farashin kayayyakin da aka gudanar a kasuwannin ƙasar nan, ya nuna cewa, farashin 50-kilogramme na buhun shinkafa ƴar gida ana sayar da shi ne a kan naira dubu 65,000 zuwa naira 68,000, inda kuma ake sayar da masara kan naira dubu 35,000 zuwa 37,000 a kan kowani buhu, yayin da na ƙasashen waje ke kaiwa naira 83,000 kan buhu guda.
Wannan gagarumin ragin da aka samu ya sanya manoman cikin gida na nuna hakan a matsayin ƙalubale ga ci gaba da noman a Nijeriya.
Sai dai kuma babban matsalar da ake fuskanta a harkar noma a Nijeriya shi ne tsadar takin zamani da sauran kayan aikin gona a Nijeriya, lamarin da ke sanya abun da manoman cikin gida ke fitarwa na tsada, amma kuma in sun kai kasuwa farashin nasu sai ya yi gogayya da na ƙasashen waje lamarin da ke sanya jama’a zaɓar na ƙasashen waje musamman saboda rashin gyara yayin dafawa.
da yake magana kan wannan lamarin, Farfesa Godwin Oyedokun na jam’iyar Lead City da ke Ibadan, ya ce rubibin sayen shinkafa da masarar ƙasashen waje fiye da na cikin gida a kasuwanni na matuƙar shafan manoman cikin gida kuma hakan na sanyaya gwiwar ƙoƙarinsu na gogayyar wadata ƙasa da abinci.
Ya ce a maimakon a bar manoma su ci gaba da kokawa wanda hakan ba ci gaba ne ga ƙasar nan, akwai buƙatar gwamnatin tarayya ta nemi manoman su zauna tare da jin damuwowinsu gami da daukan matakan shawo musu kansu domin amfanun kowa a ƙasar nan.
“Ina bai wa gwamnati shawara ta samar da tsare-tsaren da za su taimaki amfanin gonan cikin gida da ake samarwa, kamar samar da tallafi, samar rance, zuba hannun jari a ɓangaren noma da fasahohin zamanin da za su taimaka wa manoma, hakan zai sanya suke fitar da amfani gona cikin sauƙi.”
Babban shehin malamin bokon ya kuma ce bai wa manoma damarmakin shiga kasuwannin yadda ya kamata zai taimaka musu wajen samun farashi na adalci, ya kuma nemi a horas da manoma kan dabarun noma na zamani da amfani da fasahohi domin ƙara sauƙaƙa harkokin noma a ƙasar nan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Masara ƙasashen waje
এছাড়াও পড়ুন:
Za a fara yi wa ɗaliban jami’o’i gwajin ƙwaya — Gwamnatin Nijeriya
Gwamnatin Nijeriya ta bayanna cewa za ta soma yi wa ɗaliban jami’o’in ƙasar nan gwajin miyagun ƙwayoyi a wani mataki na daƙile yaɗuwar ta’ammali da ƙwayoyin.
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya NAN ya ruwaito cewa, Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya tare da haɗin gwiwar Hukumar Yaƙi da Fataucin Miyagun Kwayoyi NDLEA ne za su jagoranci aikin.
Sarkin Gudi na Jihar Yobe, Isa Bunuwo Ibn Khaji ya rasu Gwamnatin Jigawa ta horas da malamai 20,000 fasahar sadarwar zamaniHakan na zuwa ne bayan ganawar Shugaban Hukumar NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya da kuma ministan ilimin ƙasar, Olatunji Alausa a jiya Laraba.
Ɓangarorin biyu sun kuma amince da ɓullo da daftarin koyar da darasin ilimin ta’ammali da ƙwayoyi a makarantun sakandiren ƙasar.
Buba Marwa wanda ya jagoranci tawagar jagororin hukumar NDLEA ya bayyana cewa gwajin ƙwayar zai shafi duk ɗaliban jami’o’in da sabbin da za su shiga.
Yayin da yake jawabi a wajen ganawar, Buba Marwa ya ce za su mayar da hankali ne kan makarantun ƙasar, waɗanda ya ce akwai miliyoyin yara da ke ƙarƙashin kulawar ma’aikatar ilimin ƙasar.
Buba Marwa ya ce rashin daƙile ta’ammali da miyagun ƙwayoyi daga wajen ƙananan yara ya taimaka wajen jefa matasan ƙasar cikin ayyukan ta’addanci da fashin daji da sauran miyagun laifuka.
Ya bayyana mummunan tasirin shan miyagun ƙwayoyi a kan matasan ƙasar, yana mai cewa yaƙi da miyagun ƙwayoyi yaki ne don ceton rayukan matasan Nijeriya.
Marwa ya ce a yanzu hankalin hukumar zai fi karkata ne zuwa makarantu da cibiyoyin ilimi, yana mai ƙarawa da cewa akwai miliyoyin yaran Nijeriya da ke ƙarƙashin kulawar ma’aikatar ilimi, kuma wannan abu ne mai matuƙar muhimmanci.
Shugaban hukumar ta NDLEAn ya ce a dalilin goyon bayan da suka samu karkashin Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu a tsawon shekaru biyu da suka gabata, hukumar ta kama mutane 40,887 da ake zargi da aikata laifuka, ta daure 8,682, kuma ta kwace tan 5,507 na miyagun ƙwayoyi.
A cewarsa, tun daga watan Janairu bara, an ƙwace ƙwayar tramadol da ta wuce ƙwaya biliyan ɗaya, wanda kudinta ya fi naira tiriliyan ɗaya.
Shugaban NDLEA ya jaddada cewa Shugaba Tinubu yana kuma tallafa wa hukumar wajen gina cibiyoyi bakwai na gyaran masu fama da shan miyagun ƙwayoyi, baya ga sauran cibiyoyi 30 da ke karkashin umarnin NDLEA a faɗin ƙasa.