Gwamnan Yobe ya naɗa Gadaka a matsayin sabon Sarkin Gudi
Published: 3rd, August 2025 GMT
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da naɗa Hon. Ismaila Ahmed Gadaka a matsayin sabon Sarkin Gudi, bayan rasuwar Alhaji Isa Bunuwa Madugu Ibn Kaji.
Sabon Sarkin na Gudi, Ismaila Ahmed Gadaka, ya shahara da ƙwarewa a fannoni da dama.
Sojoji sun ceto malamin Jami’a da aka sace a Taraba Ma’aikatan jinya sun dakatar da yajin aiki a faɗin NajeriyaYa taɓa zama ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Fika/Fune daga 2011 zuwa 2019, kuma kafin nan ya yi aiki a matsayin Kwamishina a Jihar Yobe daga 2007 zuwa 2010.
Gadaka, ƙwararren ma’aikacin banki ne, inda ya yi aiki da bankuna irin su UBA da Standard Trust Bank, inda ya kai matsayin Manajan Kasuwanci.
Kafin naɗa shi Sarki, ya riƙe sarautar Yariman Gudi, a masarautar.
Yanzu haka, yana shugabantar hukumar gudanarwar Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Yawuri, a Jihar Kebbi, da kuma Kwamitin Kula da Ayyukan Gwamnatin a Ƙananan hukumomin Jihar Yobe tun daga 2024.
Gwamna Buni, ya bayyana cewa yana da tabbacin sabon Sarkin zai kula da martabar masarautar Gudi, ya kuma tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan al’umma.
Ya kuma aike da saƙon ta’aziyyarsa ga masarautar Gudi da iyalan marigayi Sarkin, tare da taya sabon Sarkin murna bisa wannan sarauta da ya samu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Masarautar Gudi Sabon Sarki sabon Sarkin
এছাড়াও পড়ুন:
An kama mabaraci da kuɗaɗen ƙasar waje a Ilorin
Hukumar jin daɗin jama’a ta Jihar Kwara tare da haɗin gwiwar Hukumar Gyaran Hali ta Najeriya sun kama wasu mabarata a titunan Ilorin, ciki har da wasu da aka samu da kuɗaɗen ƙasashen waje.
Daga cikin waɗanda aka kama akwai wani mabaraci mai suna Musa Mahmud daga Jihar Kano, wanda aka samu da takardar daloli.
Musa Mahmud ya shaida wa manema labarai cewa wani ne ya ba shi takardar Dala a Abuja.
Jami’ai sun bayyana damuwa kan yadda masu bara ke riƙe da kuɗaɗen da ba su dace da yanayin rayuwarsu ba.
Mutuwar majinyata: Asibitin Aminu Kano na roƙon KEDCO ya dawo da wutar lantarki Cire tallafin man fetur shi ne abin da ya dace —Sarki Sanusi II“Za mu bincika asalin waɗannan kuɗaɗen da kuma dalilin da ya sa suke da su,” in ji Adebayo Okunola, shugaban cibiyar gyaran hali a Jihar Kwara.
Jami’an gwamnati sun kwashe kusan mutane 40 daga wuraren da suka haɗa da Tipper Garage, Offa Garage, Tank da Geri Alimi Roundabout.
Jami’an sun ce bakwai daga cikin waɗanda aka kama an taɓa kama su a baya, amma sun koma tituna bayan an sako su.
Kwamishinar jin daɗin jama’a ta jihar, Dakta Mariam Imam, ta ce adadin masu bara da aka kama ya ragu sosai idan aka kwatanta da na baya, inda ta ce suna sauya dabaru don su guje wa kama.
Ta roƙi jama’a da su daina ba wa masu bara kuɗi kai tsaye, su maida gudummawarsu ta hanyar wuraren ibada da gidajen marayu.
Jami’an gyaran hali sun ce za a tilasta wa waɗanda aka kama su yi aikin tsaftace tituna a matsayin horo da kuma darasi.
Wasu daga cikin masu barar sun roƙi gwamnati da ta tausaya musu, ba su da wata hanyar rayuwa sai bara.