A cewar shugaban kwamitin, Katsina na kuma goyon bayan batun sauke wasu ikon gwamnati daga matakin tarayya zuwa jihohi, saka sarakunan gargajiya a cikin kundin tsarin mulki da kuma sake fasalin harkokin kuɗi.

Sanata Ibrahim ya shaida wa kwamitin cewa an tattara dukkan ra’ayoyi da buƙatun jama’ar Katsina, tare da gabatar da su a cikin takardar matsayar.

Tun da farko, yayin da yake ƙaddamar da taron jin ra’ayoyin jama’a, shugaban kwamitin majalisar dattawa kan gyaran kudin tsarin mulki ya buƙaci a riƙa yin irin wannan taron lokaci zuwa lokaci domin ya dace da halin da ake ciki.

Sanata Barau Jibrin, wanda shi ne mataimakin shugaban majalisar dattawa, ya tabbatar da cewa dukkan abubuwan da aka tattara daga gwamnati, ƙungiyoyi da jama’a za a gabatar da su a gaban majalisar domin yin doguwar tattaunawa.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: gwamnati

এছাড়াও পড়ুন:

INEC Ta Gudanar da Taron Masu Ruwa da Tsaki Kafin Zaɓen Cike Gurbi na Babura/Garki

A wani ɓangare na shirin gudanar da zaɓen cike gurbi na Babura/Garki a Majalisar Tarayya, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) reshen Babura ta shirya muhimmin taron masu ruwa da tsaki domin tabbatar da sahihin zaɓe mai inganci da haɗin kai.

 

A jawabinsa yayin taron, jami’in zaɓe na ƙaramar hukumar Babura, Malam Hafiz Khalid, ya gabatar da cikakken jadawalin ayyukan zaɓen.

Ya jaddada muhimmancin haɗin kai da gaskiya a kowane mataki, yana mai bayyana zaɓen a matsayin aikin gama gari da ke buƙatar goyon bayan duk masu ruwa da tsaki.

 

Mahalarta taron sun bayar da shawarwari masu amfani tare da gabatar da muhimman tambayoyi da suka shafi inganta sahihanci da nasarar zaɓen.

 

Wasu daga cikin batutuwan da aka tattauna sun haɗa da shirye-shiryen kayayyakin aiki, tsaro, wayar da kan masu zaɓe, da sauransu.

An kammala taron da sabunta ƙudurorin haɗin guiwa daga dukkan mahalarta, wajen tabbatar da gudanar da zaɓen cike gurbi cikin lumana, ‘yanci, adalci, da sahihanci a yankin Babura/Garki.

 

Wakilin Rediyon Najeriya  ya bayyana cewa, taron da aka gudanar a ofishin INEC na Babura, ya samu halartar masu ruwa da tsaki da suka haɗa da Hakimin Babura, jami’an tsaro, wakilan jam’iyyun siyasa, jami’ai daga Ƙungiyar Direbobin Ƙasa (NURTW), Ƙungiyar Masu Motocin Haya (NARTO), ƙungiyoyin farar hula (CBOs), da sauran jami’an INEC.

 

Usman Muhammad Zaria

 

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sauya Sheƙa: Sanatoci Biyu APC Ke Buƙata Wajen Samun Kashi Biyu Cikin Uku A Majalisar Dattawa
  • Kwamitin Tantance Makarantun Gaba da Sakandire Na Bogi Ya Yi Wa Yankin Funtua Dirar Mikiya
  • Ƴansanda Sun Ƙwato Mota Da Aka Sace, Gami Da Cafke Dillalan Ƙwayoyi A Jigawa
  • Tinubu Ya Sauke Gawuna A Matsayin Shugaban Kwamitin Gudanarwar BUK, Ya Maye Gurbinsa Da Kaita 
  • Majalisar Dokokin Sokoto Ta Aike Wa  Kwamishina Sammaci, Duba Dalili
  • An Zaɓi Saidu Yahya A Matsayin Shugaban Hukumar Yaƙi Da Cin Hanci Ta Kano
  • Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Shirya Taron Bita Ga Kansiloli
  • INEC Ta Gudanar da Taron Masu Ruwa da Tsaki Kafin Zaɓen Cike Gurbi na Babura/Garki
  • Yanzu-yanzu: Sanata Dino Melaye Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP