Shirin ACRESAL Zai Samar Da Injinan Ban Ruwa Masu Amfani Da Hasken Rana A Jigawa
Published: 3rd, August 2025 GMT
A kokarin da Gwamnatin Jihar Jigawa ke yi na kara habbaka harkokin noma, shirin ACRESAL yace sami amincewar gwamnatin na siyo injinan ban ruwa masu amfani da hasken rana guda 3,000 domin tallafawa manoma.
Shugaban Shirin na Jihar, Malam Yahaya Kafin Gana ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse.
Yana mai cewar, samar da injinan ban ruwa masu amfani da hasken rana ga manoman na da nasaba da bunkasa aikin gona a jihar Jigawa.
A cewar sa, shirin ACRESAL na jihar ya sami sahalewar gyaran karin wasu cibiyoyin renon itatuwa guda 3 a sassan jihar.
Malam Yahaya Uba Kafin Gana ya kara da cewar, cibiyoyin renon itatuwan da za’a gyara sune na garuruwan Birnin Kudu da Kafin Hausa da kuma na Gadar Kazaure.
Yana mai nuni da cewar baya ga gyaran cibiyoyin, har Ila yau za’a kuma a samar musu da rijiyoyin samar ruwan sha masu amfani da hasken rana.
Kafin Gana, yace nan bada jimawa ba za su sake zakulo wasu cibiyoyin renon itatuwa guda 5 domin mayar da su irin na zamani.
Yace shirin ya kuma siyo karin Injinan yasar kogi guda 2 domin mara baya ga guda 2 da ake dasu a ma’aikatar kare muhalli ta jihar Jigawan.
Kazalika, ya ce shirin zai samar da hasken wutar lantarki mai amfani da hasken rana a garuruwan Matamu da Safa da Galaucimi da Hannun Giwa da Kwazalewa da Tozarya dake kananan hukumomin Birniwa da Birnin Kudu da Miga da Kafin Hausa da Kazaure har ma da Sule Tankarkar.
Usman Mohammed Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa amfani da hasken rana
এছাড়াও পড়ুন:
Jihar Jigawa Ce Ta Fara Biyan Kudaden Kujerun Aikin Hajjin 2026- NAHCON
Hukumar Aikin Hajji ta Kasa NAHCON ta yi kira ga jihohin kasar nan da su yi koyi da Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa wajen tare kujerun aikin hajji domin baiwa Maniyatan su damar sauke farali.
Kwamishina a hukumar mai kula da shiyyar arewa maso yamma , Sheikh Muhammad Bin Usman yayi wannan kiran a lokacin da ya kai ziyarar aiki a Dutse, babban birnin Jihar.
Sheikh Muhammad Bin Usman yayi bayanin cewar, ya zama wajibi ga sauran hukumomin Alhazan kasar nan da su yi koyi da Gwamna Umar Namadi wajen bai wa hukumomin Alhazai bashin kudade domin tare kujerun aikin Hajji ga maniyata.
Yana mai nuni da cewar, a halin yanzu, jihar Jigawa ce ta farko wajen biyan kujerun aikin Hajjin 2026 a fadin kasar nan.
Babban malamin ya kuma yabawa Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa Alhaji Ahmed Umar Labbo bisa namijin kokarin sa wajen shirye shiryen aikin Hajji akan lokaci.
Da ya waiwayi batun hadaya kuma, Sheikh Bin Usman yace a duk fadin kasar nan, jihar Jigawa ce take da lasisin yin Hadaya ga maniyata.
Ya ce ita kadai ce tilo take samarwa da maniyatan ta masauki a kusa da harami sabanin wasu hukumomin alhazai da suke yayatawa.
A na shi jawabin, Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ce wannan shi ne karo na uku da Gwamna Umar Namadi ke bai wa hukumar rancen kudi domin tare kujerun aikin hajji.
Ya ce makasudin bada rancen kudaden shi ne domin bai wa maniyatan jihar damar sauke farali.
A don haka, Labbo yace tuni hukumar ta ci gaba da rijistar maniyatan aikin Hajjin 2026 tare da bada tabbacin hukumar na ci gaba da rike kambunta wajen gabatar da aikin hajjin.
Kazalika, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya shawarci sauran hukumomin Alhazai su kara himma wajen biyan kudaden kujerun da aka ware musu akan lokaci.
Ya kuma yaba wa NAHCON da Gwamnatin jihar bisa hadin kai da goyon bayan da suke baiwa hukumar a kowanne lokaci.
Usman Mohammed Zaria