2025-10-16@00:12:39 GMT
إجمالي نتائج البحث: 494
«farashin kaya»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Farashin kayan miya, musamman kayan gwari ya yi tashin gwauron zabo a yayin da Babbar Sallah ta bana ta kawo jiki. Kuɗin kayan lambu ya ninka sau uku a cikin mako biyu, a yayin da Babbar Sallar ta zo wa iyalai da dama a Najeriya a hagunce, a sakamakon fama da matsananciyar matsalar tsadar rayuwa. Wannan hauhawan farashin, wana ta zarce abin da aka saba gani a lokutan rani, ya kasaara ƙarfin iyalai yin sayayya domin girki abincin Sallah, wanda hakan ya haifar da damuwa, musamman a jihohin Kano, Taraba, Kwara, da Jigawa. Tsadar da ba a taɓa gani ba a Kano Al’umma a Jihar Kano sun koka bisa mummunan tasirin wannan tsadar rayuwa. Wani ma’aikacin gwamnati mai ’ya’ya biyar,...
Masu sayar da rago a jihar Zamfara sun nuna damuwarsu kan rashin samun ciniki gabanin bikin Eid-el-Kabir, duk da cewa ana samun dabbobi a kasuwanni. Shugaban kungiyar masu sayar da dabbobi ta jihar Zamfara, Malam Saidu Ibrahim Gusau ya bayyana haka a wata tattaunawa da gidan rediyon Najeriya a Gusau. Malam Gusau ya bayyana cewa, duk da cewa ana samun raguna da yawa, amma an samu karancin masu saye. Sai dai ya bayyana fatan cewa lamarin zai iya gyaruwa yayin da bukukuwan Sallah ke kara gabatowa. “Amma idan abubuwa sun ci gaba da haka, to gaskiya, akwai matsala ta gaske,” “Har yanzu, na yi imani cewa da sauran kwanaki abubuwa za su iya canzawa, in...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wasu ’yan daba sun yi wa Mataimakin Firinsifal na wata makarantar sakandare dukan tsiya a wani mummunan harin da suka kai masa saboda ya hana wani ɗalibi satar jarabawa. A yayin da ake ci gaba da jarabawar kammala sakandare ta WASSCE da ake yi a halin yanzu ne, Mista Rotifa, mataimakin shugaban wata makaranta mai zaman kanta mai suna Child Development College da ke Akure, hedikwatar Jihar Ondo, ya hana ɗalibin satar amsa. Bayan haka ne ’yan daban sun tsare Mista Rotifa suka yi masa dukan kawo wuƙa bayan sun jawo shi daga motar ’yan sanda, kafin a ceto shi a kai shi asibiti. Lamarin ya faru ne bayan Mista Rotifa ya ƙwace wayar salula da wani ɗalibi ke amfani...
Ya buƙaci shugabannin haɗakar su fara tsarin kafa sabuwar jam’iyyar da za ta kasance mai suna ɗaya, falsafa ɗaya, da tsarin shugabancin da zai haɗa kan kowa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ma’aikatar lafiyar kasar Sudan ta bayyana cewa: Ana ci gaba da daukan matakan ganin an shawo kan ci gaba da yaduwar masifar kwalara a kasar Gidan talabijin na Al-Alam ya watsa rahoton cewa: A halin da ake ciki a fannin kiwon lafiya a birnin Khartoum fadar mulkin kasar bayan bullar cutar kwalara yana ta kokarin ya shawo kan matsalar tare da killace mutanen da suka kamu da cutar a wurare na musamman a babban birnin kasar Khartoum, rahotonni sun bayyana cewa: Cutar ta bazu cikin sauri a birnin. Sannan ma’aikatar lafiya ta Sudan da kungiyoyi da dama suna ci gaba da kokarin shawo kan cutar don kada ta zama annoba wadda za ta yadu zuwa jihohi da dama. Wakilin gidan...
Hon. Nasiru ya kara da cewa Gwamna Radda ya yi kokari wajen yaki da matsalolin tsaro wanda suka addabi Jihar Katsina, inda ya bayyana cewa ana samun sauki sosai a wannan bangare. Ya ce gwamnati ta gyara makarantu da asibitoci a fadin Jihar Katsina, inda aka maida su na zamani tare da daukar ma’aikatan lafiya da kuma malaman makaranta da yawansu ya kai 7,000, wanda ya ce ko haka aka tsaye suna da hujja da dalilin mara masa baya. Idan za a iya tunawa a makon da ya gabata ne, ‘yan majalisun tarayya guda 15 dukkansu na jam’iyyar APC suka ayyana Gwamna Radda a matsayin wanda za su goya baya a zaben 2027. Sai dai kuma ana dora ayar tambaya...
A nasa jawabin, shugaban kwamitin shirya musabakar karatun alkurani na karamar hukumar Igabi, Malam Abubakar Sadik Muhammad (Abu Asim), ya ce duk irin nasarar da kwamitin ya samu, ya samu ne bisa goyon bayan da Honarabul Yusuf Ibrahim Zailani yake ba su. Ya ce shi ne kashin bayan samun nasarar da suka yi a fadin duniya. Ya bukaci daukacin iyaye da su kara zage damtse wajen ganin ‘ya’yansu sun samu ilimi nagartacce da kuma sanya ido wajen kula da tarbiyyarsu. Haka zalika, kwamitin shirya musabakar karatun alkurani ya karrama Zailani da lambar yabo bisa irin gudummawar da yake bai wa addinin Musulunci a ciki da wajen Jihar Kaduna. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
Bayan mintuna 90 na wasan ba tareda wani ya doke wani ba sai alkalin wasa ya bayar da damar bugun daga kai sai mai tsaron raga, Jamaica ta ci kwallaye 4 inda Nijeriya ta ci dukkan kwallaye 5 da yan wasan suka buga, hakan ya sa yaran na Eric Chelle suka lashe gasar Unity Cup ta bana da ta kunshi kasashen Ghana, Trinidad And Tobago, Jamaica da Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
“Gane amfanin lamarin da ya shafi ilimi shi yasa, Gwamna Lawal ya kaddamar da dokar ta baci a bangaren ilimi a watan Nuwamba 2023,matakin da aka dauka an yi sa’a ya haifar da da mai ido a bangaren ilimi a Jihar Zamfara. “Fiye da makarantu 500 aka y masu kwaskwarima da samar masu abubuwan da suka kamata tun lokacin da aka kaddamar da dokar ta bacin.An horar da Malaman makarantun gwamnati,ana kuma ci gaba dayin hakan. “Saurin biyan kudaden bashi da Hukumomin WAEC da NECO ya kawo kwanciyar hankali ga daliban da suka kammala makaranta da rubiuta jarabawa, sai dai basu samu ci gaba da karatu ba saboda Hukumomin jarabawar sun rike masu sakamakon jarabawar da suka yi. Daga...

Cutar Kwalara Ta Yadu A Sudan Baya Ga Matsalar Tashe-Tashen Hankulan Da Suke Ci Gaba Da Yuduwa A Kasar
Cutar kwalara ta yadu a Sudan, kuma ‘yan tawayen dakarun kai daukin gaggawa sun kai hare-hare kan asibitoci biyu a Jihar El Obeid na kasar Sudan na ci gaba da fama da tabarbarewar yanayin tsaro da lafiya bisa la’akari da abubuwan da ke faruwa a baya-bayan nan. A bangaren tsaro kuma, Dakarun Kai Daukin Gaggawa na Rapid Support Forces sun kai hare-haren bama-bamai a wasu asibitoci biyu da wasu unguwanni a birnin El Obeid da ke Arewacin Kordofan a tsakiyar kasar Sudan. Wata majiyar soji ta bayyana cewa: Dakarun kai daukin gaggawa sun afkawa Asibitin Al-Daman da kuma Jami’an lafiya da ke tsakiyar birnin da manyan bindigogi. Sojojin Sudan sun tabbatar da cewa: Sun yi luguden wuta kan sansanonin dakarun...
Ya ce a nemi bayani daga wurare daban-daban kamar Kungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomin Nijeriya (NULGE) da Ma’aikatar Kudi, ya kara da cewa sakataren gwamnatin tarayya shi ne shugaban kwamitin aiwatar da hukuncin. Abubuwan da mutane yawa suke gnin ya janyo jinkirta aiwatar da hukuncin shi ne, shigar da sabon sharadi daga Babban Bankin Nijeriya (CBN), wanda ke bukatar dukkanin hukumomin gwamnati 774 su bayar da akalla shekaru biyu na rahotannin kudinsu kafin su iya karbar kasafin kudadensu kai tsaye daga asusun gwamnatin tarayya. Babban bankin ya bayyana cewa dole ne gwamnatocin kananan hukumomi su cika bukatun kafin su bude asusu don kura musu kudadensu kai tsaye. Ka’idojin da aka gindaya wa kananan hukumomin ya kara janyo tsaiko wajen jinkirta aiwatar...
Wasu jami’an diplomasiyyar turai sun yi wa gwamnatin Benjamin Netanyahu da cewa za ta fuskanci Karin matsin lamba idan har ba ta sauya halayyarta akan Gaza ba. Jaridar “Washington Post” ta Amurka ta ambato jami’an diplomasiyyar turai suna cewa; sabon tsarin da ake yin aiki da shi na raba kayan agaji a Gaza, ya juya ya zama harigitsi kuma ana bude wuta akan mutane da hakan ya yi sanadiyyar jikkatar Falasdinawa da dama.” Har ila yau jami’an diplomasiyyar na turai sun ce, ko kadan ba su da aniyar bayar da kayan agajinsu ga masu tafiyar da tsarin da su ne Isra’ila da Amurka.” Bugu da kari, majiyar diplomasiyyar ta tarayyar turai ta ci gaba da cewa; Hotunan masu ban tsoro...
Kasar Faransa ta ce daga ranar daya ga watan Yuli mai zuwa ta haramta shan sigari a wuraren taruwar jama’a. Kasar ta ce wuraren da haramcin ya shafa sun hada da makarantu da tashoshin mota ko na jirgi, wuraren shakatawa, wuraren wasanni ko kasuwanni saboda kada yara kanana su gani. Yadda ambaliyar Neja ta ci mutum 12 ’yan gida daya NAHCON ta kammala jigilar maniyyata aikin hajjin 2025 Ministar Lafiya da Iyali na kasar, Catherine Vautrin ce ta bayyana hakan a ranar Alhamis, inda ta ce, “Dole a daina shan sigari a wuraren da yara suke. “’Yancin shan sigari ya kare ne a inda ’yancin yara na shakar tsaftatacciyar iska ya fara,” kamar yadda ministar ta shaida wa jaridar Ouest-France...
PUNCH Metro ta tuna cewa a kwanakin baya jami’an hukumar EFCC shiyyar Ilorin sun kama wasu mutane 17 da ake zargi da damfarar yanar gizo a cikin hadaka a Kananan Hukumomin Ilorin da Ifelodun na jihar. Oyewale ya ce an tare wadanda ake zargin ne a madatsar ruwa ta Asa da yankin Jami’ar Al-Hikmah da yankin Gaa-Odota da ke Ilorin da kuma yankin Ganmo da Amoyo na jihar. “Kamen da aka yi a ranar Talata, 13 ga Mayu, 2025, ya biyo bayan bayanan sirri da aka samu wanda ya alakanta wadanda ake zargin da ayyukan damfara ta Intanet a jihar. Sanarwar ta kara da cewa, “Kayan da aka kwato daga hannunsu da aka kama sun hada da manyan motocin alfarma...
Sanarwar bayan taron koli na hadin gwiwar Sin da kungiyar tarayyar kasashen kudu maso gabashin Asiya wato ASEAN, da kwamitin hadin gwiwar kasashen Larabawa na yankin Gulf wato GCC, ta jaddada burin sassan uku na bunkasa hadin gwiwar raya tattalin arziki, musamman ta hanyar gudanar da cinikayya marar shinge, da kammala yarjejeniyar gudanar da cinikayya cikin ’yanci tsakanin Sin da da GCC. Idan mun waiwayi wannan sanarwa ta hadin gwiwa, za ku gano manufofin da sassan uku ke fatan cimmawa, wadanda suka hada da fatan dunkule shiyyoyinsu waje guda, da kara yin tafiya tare, da neman samun ci gaba mai dorewa. Karkashin wadannan burika, sassan uku za su yi amfani da fifikonsu wajen cimma moriyar juna da karfafa kawance a...
Ɗaruruwan ɗalibai ne suka suka tsallake rijiya da baya a lokacin da ajujuwan da suke rubuta jarabawar kammala sakandare (SSCE) a ranar Laraba. Lamarin ya faru ne a makarantar sakandiren gwamnati da ke Namne a Ƙaramar hukumar Gassol a Jihar Taraba. Ko kwabo ban ciyo bashi ba tun da na zama Gwamnan Kaduna – Uba Sani Ambaliyar ruwa ta kashe sama da mutum 50 a Neja Ajujuwan sun rufta musu a lokacin da aka yi ruwan sama kamar da baƙin ƙwarya da iska. Ɗaliban da masu kula da jarrabawar sun maƙale a cikin ajujuwan da suka rufta na tsawon sa’o’i kafin wasu mazauna garin su kuɓutar da su. Wani mazaunin garin Alhaji DanAzumi Lauris ya shaida wa Daily Trust cewa,...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A yau shekara biyu ke nan cif tun bayan da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karɓi mulkin Najeriya a matsayin shugaban ƙasa na 16 tun bayan samun ‘yancin kai. Daya daga cikin abubuwan da shugaban kasar ya fara yi yayin jawabin karbar mulkin shi ne sanar da kawar da tallafin man fetur. Yayin da yake cika shekaru biyu, ana ci gaba da muhawara mai zafi game da irin nasarorin da aka samu da kalubalen da ake fuskanta da kuma yadda al’ummar ƙasa ke amfana da tsare-tsaren gwamnati. NAJERIYA A YAU: Matsalolin Da Suke Tarnaki Ga Kananan Yara A Najeriya Da Hanyoyin Magance Su DAGA LARABA: “Sai Na Tara Kudin Cin Abinci Na...
A ci gaba da tafka laifukan yakin da HKI take yi a Gaza,Fiye da Falasdinawa 60 ne su ka yi shahada a jiya Laraba. A wani harin da sojojin mamayar su ka kai a yankin Jabaliya, Falasdinawa 5 sun yi shahada, yayin da wani adadi mai yawa su ka jikkata. Wani jirgin sama maras matuki ya kai wani harin a unguwar “Shuja’iyya” wnada ya yi sanadin shahadar mutum daya, sai kuma wasu shahidan 4 a unguwar “Shari’u 5”, da kuma wasu shahidan 4 a garin “Bani-Suhaila”. Wasu rahotannin sun ce, ‘yan sahayoniyar sun kai wasu hare-haren a garin ‘Abasan al-kabira’ da ya yi sanadin shahadar mutum daya da kuma jikkatar wasu masu yawa. A yankin Qizan kuwa, ‘yan sahayoniyar sun...
Shugaban rundunar mayakan sama ta kasa,Air Marshal, Hassan Abubakar, ya bukaci tsoffin daliban makarantar ‘ya’yan sojoji dake Zaria watau NMS da su kasance masu kwazo da da’a a duk inda suke kamar yadda suka koya a makarantar. Ya bayyana haka ne lokacin da ya ke jawabi a matsayin Babban bako na musamman a wurin bukin cika shekara 71 da aka gudanar a filin faretin RSM Zakari Kumasi dake harabar makarantar a zaria. Shugaban rundunar mayakan saman ya bayyana cewa makarantar ta NMS ta yi fice wajen baiwa yara horo a fannonin karatu da kuma ilimin aikin soja wanda hakan ya sa ta samar da manyan sojoji da dama har ma da shi a ciki. Air Marshal Abubakar ya ce bukin...
Babbar Kotun Musulunci a Jihar Kano ta yanke wa Shafiu Abubakar hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda cinna wuta a wani masallaci a kauyen Gadan, Karamar Hukumar Gezawa, yayin da jama’a ke tsaka da jam’in sallar asuba a ranar 15 ga Mayu, 2024. Harin ya yi sanadiyar mutuwar mutane 23 tare da raunana wasu. An samu Shafi’u da laifuka hudu, ciki har da kisan kai da kuma barna ta hanyar gobara. Baya ga hukuncin kisa, alkali ya ba da umarnin a yi masa bulala 150, tare da biya tarar N1,500, sannan kuma a kwace babur dinsa mai kafa uku, inda za a sayar, a yi amfani da kudin da aka samu wajen gyaran masallacin da ya lalace. Yayin shari’ar, masu...
Wani bafalasdine ya rasa ransa, bayan da harsasai da sojojin yahudawa suka cilla masa a garin Ariha na yankin yamma da kogin Jordan sun fada a kansa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran Falasdinawa WAFA ya na fadar haka a yau Talata, ya kuma kara da cewa Mohammed Yahya Asi Jalaytah ya yi shahada ne bayan da albarusan da sojojin suka cilla masa sun fada a kansa sun kuma ji masa munanan raunuka. Labarin ya kara da cewa bayan tsakiyar dare ne sojojin yahudawan suka soma barin wuta da bindigogi da kuma jefa hayaki mai sa hawaye a kan Falasdinawa a garin Ariha, Inda albarusai suka sami Asi Jalaita suka kuma kasashe shi. WAFA...
Ya ce: “Ya kamata ku nazarci Shugaban Ƙasa sosai. Za ku iya faɗin ra’ayoyin ku; zai saurare ku, amma a ƙarshe shawarar da zai yanke tasa ce. Ina ganin ya dace mu gane hakan.” Yayin da yake bayani kan taken taron, ministan ya ce Shugaba Tinubu na da cikakkiyar niyya wajen aiwatar da Shirin Sabunta Fata — wanda tsari ne da ya mayar da hankali kan jin daɗin talaka da fitar da cikakken ƙarfin Nijeriya. “Shirin Sabunta Fata na da nufin kawo sauyi mai ma’ana ga rayuwar al’ummar Nijeriya ta hanyar muhimman matakai da za su fitar da cikakken ƙarfin Nijeriya, ta hanyar da ba a taɓa gani ba,” inji ministan. Idris ya bayyana cewa Shugaba Tinubu...
Daga Bello Wakili Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Yada Labarai da Ayyuka na Musamman, Mista Tunde Rahman, ya bayyana jerin goyon bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke samu daga cikin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin shaida mai karfi kan tsare-tsaren da gwamnati ta aiwatar cikin shekaru biyu da suka gabata. A yayin wata tattaunawa da ya yi da Radio Nigeria a Abuja, Mista Rahman ya ce goyon bayan da ke fitowa daga gwamnoni na APC, ‘yan majalisar dokoki da shugabannin jam’iyya, na nuna karuwar amincewa da sauye-sauyen tattalin arzikin da Shugaba Tinubu ya aiwatar. Ya ce wannan ya hada da cire tallafin fetur da daidaita farashin canjin kudade. “Wadannan goyon bayan suna da matukar...
Fastan nan mai suna Rev. Azzaman David, shugaban majami’ar The King Worship Chapel da ke Kaduna, ya rasu a wani hatsarin mota a ranar Asabar yayin dawowarsa daga Makurdi, jihar Benue zuwa Kaduna. Shugaban ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN) na Jihohin Arewa 19 da FCT, Rev. John Joseph Hayab, ya tabbatar da mutuwar fastan, inda ya bayyana cewa al’ummar Kirista ta yi hasarar babban jarumi. “Evangelist Azzaman ya kasance mai himmar wa’azi, mai kare addinin Kirista, kuma mai fafutukar kare hakkin masu ƙaramin ƙarfi. Rayuwarsa ta kasance cikin jarumtaka da ƙwarin gwuiwa ga gaskiya da adalci,” in ji Hayab. CAN ta yi wa iyalansa, da ‘yan cocinsa, da duk wanda rayuwarsa ta shafa ta’aziyya, tare da addu’ar Allah ya ba...
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “A ƙoƙarinsa na yin garambawul a fannin ilimi a jihar Zamfara, Gwamna Dauda Lawal ya biya duk wani bashi a bangaren ilimi da gwamnatocin baya a jihar suka ƙi biya “Rashin biyan kuɗin jarabawar WAEC da NECO ya haifar da koma-baya ga makarantun gwamnati a faɗin jihar Zamfara, wanda hakan ya sa Zamfara ta kasance a baya a fannin ilimi a faɗin Nijeriya. “Da sanin matsalolin da ke tattare da harkar ilimi, Gwamna Lawal ya kafa dokar ta-baci a fannin ilimi a watan Nuwamba 2023, matakin da ya samar da sakamako mai kyau ga bangaren ilimi a jihar Zamfara. “Sama da makarantu 500 ne aka gyara tare da samar da kayan aiki tun bayan...
Gwamnatin Jihar Gombe ta sanya hannu kan yarjejeniyar Naira biliyan uku domin gina mayankar dabbobi ta zamani a garin Gombe. Hakan wani bangare ne na shirin inganta kiwon dabbobi da tsaftar abinci da kuma rage matsalolin kiwon dabbobi (L-PRES) wanda Bankin Duniya ke tallafa wa. Shirin L-PRES na da nufin kyautata harkar kiwon dabbobi da sarrafa nama cikin tsafta a jihar. An kulla yarjejeniyar ce tare da kamfanin Lubel Nigeria Limited da wa’adin kammalawa na watanni 9, zuwa watan Fabrairun shekarar 2025. An gudanar da bikin sanya hannu kan yarjejeniyar a ofishin L-PRES da ke G.R.A, a Gombe, inda shugaban shirin na jihar, Farfesa Usman Bello Abubakar, ya bayyana wannan aiki a matsayin babban ci-gaba a jihar. Sojoji sun kashe mayaƙan...
Mai magana da yawun ‘yansandan jihar, James Lashen, ya tabbatar da cewa an kashe mutane huɗu a harin, yayin da babu wani ɗansanda da ya jikkata a faɗan da suka yi da maharan. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Kara Haske kan Batun Inganta Sinadarin Uranium Da Zamanta Da Amurka
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bayyana sabbin ci gaban da aka samu a tattaunawar da aka yi a birnin Roma Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya jaddada cewa: Ana gudanar da zagaye na biyar na tattaunawa ba na kai tsaye ba tsakanin tawagar Amurka da na Iran a cikin yanayi na kwarewa. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana a yau Juma’a cewa: Tattaunawar tana gudana cikin kwarewa da kwanciyar hankali, yana mai cewa abin da ake yadawa a kafafen yada labarai hasashe ne da baya da tushe ko inganci kuma baya da bambanci da shaci fadi. A yau Juma’a da yamma ne aka fara shawarwarin da ba na kai tsaye ba karo na biyar...
Daga Bello Wakili Dukkan ‘yan majalisun tarayya daga Jihar Katsina sun bayyana goyon bayansu ga Gwamna Umar Dikko Radda domin ya sake tsayawa takara a wa’adin mulki na biyu karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben shekarar 2027 mai zuwa. An bayyana wannan matsaya ne a lokacin wani taron hadin gwiwa da ‘yan majalisar suka gudanar, inda Honourable Sada Soli, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Jibia da Kaita, ya yi magana a madadin takwarorinsa. Ya bayyana cewa wannan shawara ta samo asali ne daga nazarin hadin gwiwa da suka yi kan nasarorin da gwamnan ya samu da kuma goyon bayan da al’ummar jihar suka nuna daga kowane bangare. ‘Yan majalisar sun yaba da irin salon shugabanci na Gwamna...
Mataimakin Daraktan Ayyuka na Operation Haɗin Kai, Kyaftin Reuben Kovangiya, ya tabbatar da kashe ‘yan ta’addan, yana mai cewa Sojojin na ci gaba da kai hare-hare kan ‘yan ta’addan. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Nahiyar Afirkan a karkashin tarayyar Afirka ta kafa cibiyar dake kula da sararin samaniya domin tattara bayanai, wacce ke da matsuguni a birnin “alkahira’ na Masar. Sabuwar cibiyar dai ta fara aiki ne a watan da ya gabata,kuma za ta rika musayar bayanan da take tattarawa da cibiyoyin kasashen da suke a fadin nahiyar. Haka nan kuma cibiyar za ta kyautata ayyukanta ta hanyar harba taurarin dan’adam a sararin samaniya da kafa cibiyoyin bibiyar yanayi domin yin musayarsu da kasashen nahiyar da kuma wajenta.
Wani dattijo mai aikin kwashe shara da ya shekara 40 yana tara kuɗin domin zuwa aikin Hajji ya samu cika burinsa a bana. A karshe dattijoin dan qasar Indosauke ya samu damar zuwa sauke farali inda ya isa Kasa Mai Tsarki tare da matarsa. Wanni dattijon wanda ya nuna tsananin juriya da jajircewa ya bayyana yadda kwashe shekara 40 yana tara 1,000 na kuɗin ƙasarsu a kullum, domin tara kuɗin da zai sauke farali shi da mai ɗakinsa. A yayin da ake yake hira da Kamfanin Dillancin Labarai na kasar Saudiyya bayan isarsu ƙasar domin sauke farali, dattijoin ya bayyana cewa tun ashekarar 1986 ya fara tara wannan kuɗi bayan samun goyon bayan matarsa. Dangote ya sake...
Ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar da taron manema labarai a yau Laraba, inda jami’in ma’aikatar kasuwancin kasar da ke da ruwa da tsaki ya bayyana cewa, aiwatar da matakan da suka dace bisa “Ayyuka guda goma” na hadin gwiwa da Afirka, ya haifar da sakamako mai kyau, wanda ya zuba babban kuzari ga hadin gwiwar Sin da Afirka. Mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin Tang Wenhong ya bayyana cewa, an riga an tattauna tare da kasashen Afirka sau da dama, an kuma amince da tsarin “Kasa daya, manufa daya” wajen tsarawa da aiwatar da matakai. Rashin Tsaro: Matasa Sun Yi Zanga-zangar Toshe Babbar Hanya Saboda Satar Mutane A Edo Za A Gudanar Da Baje Kolin...
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa wasu daga cikin sojoji da ’yan siyasa na taimaka wa ƙungiyar Boko Haram ta hanyar ba su bayanai. A wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na News Central, Zulum ya ce gwamnatinsa za ta ɗauki matakin da ya dace kan duk wanda ke taimaka wa ’yan ta’adda. Hajjin 2025: Kashi 79 na maniyyatan Najeriya sun isa Saudiyya – NAHCON Gwamnati za ta sayar da gidaje 753 da EFCC ta ƙwato a hannun Emefiele Ya ce: “Akwai masu bai wa Boko Haram bayanaj a cikin sojoji, ’yan siyasa da sauran jama’a. Za mu ƙarfafa leƙen asiri, kuma mu ɗauki tsattsauran mataki a kansu.” Gwamna Zulum ya ce dole...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka. Sharhin bayan labarammu nay au zai yi Magana dangabe da “Tattaunawar shirin Nukliyar kasar Iran da Amurka yana tanga-tanga’ wanda ni tahir amin zan karanta. Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana cewa, da alamun tattaunawa tsakanin kasar ta kuma Amurka dangane da shirin nukliyar kasar Iran ba zai je ko in aba, saboda yadda bangaren Amurka a cikin kafafen yada labaransu, daga ciki har da jakadan Amurka kan al-amuran gabas ta tsakiya, kuma shugaban tawagar Amurka a tattaunawar wato Steve Witkoff ya fito a kafafen yada labarai na Amurka yana fadar cewa duk wata yarjeniyar da za’a cimma da kasar Iran nan gaba dole sai...
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya amince da sayen ƙarin motoci guda 10 don taimaka wa sojoji da ’yan sa-kai wajen yaƙi da ’yan Boko Haram da ISWAP. Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyara da ya kai Kala-Balge, inda ya gana da ƙungiyoyi daban-daban. An kashe makiyaya 2 a wani hari a Filato Yadda ’yan sanda suka kashe dan fashi suka kwato bindigogi 7 a Abuja Ya ce za a bai wa ’yan sa-kai motoci shida ƙirar Toyota Hilux, ciki har da CJTF, mafarauta da ’yan banga, sannan za a bai wa sojoji ƙarin motoci huɗu masu bindiga. Zulum, ya kuma raba wa iyalai 10,000 da ke fama da talauci a yankin kayan abinci, yawancin waɗanda...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, sharhin bayan labarummu zai yi magana dangane da taron tattaunawa ta Tehran wanda aka bude a ranar Lahadi 18 ga watan mayu a nan Tehran. A ranar Lahadi 18 ga watan Mayu da muke ciki ne aka bude taron tattaunawa da ta Tehran ta farko a nan Iran, don tattauna batutuwan da suka shafi kasashen yankin yammacin Asiya. Inda shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan da kuma ministan harkokin wajen kasar Iran suka gabatar da jawaban farko a taron. An sami halattan baki daga kasashe 53 daga cikinsu akwai jami’an gwamnatoci wadanda suka hada da ministoci masana da shuwagabannin cibiyoyin bincike da bada shawarori na kasashen duniya da dama. Daga cikin bakin akwai ministan...
Akalla manoma 90 ne mayakan kungiyoyin Boko Haram da ISWAP suka kashe a Jihar Borno cikin watani biyar da suka gabata. Mayakan kungiyar sun kuma yi garkuwa da wasu da dama baya ga wadanda suka tsallake rijiya da baya a hare-haren kungoyiyoyin da raunin harbi. Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa kungiyoyin ‘yan ta’addan sun kai hare-haren ne a tsakanin watan Janairu zuwa Mayun nan da muke cikin na shekarar 2025. Hari na baya-bayan nan shi ne wanda mayakan kungiyar ISWAP suka yi ritsa manoman da ke aiki a gonakin wake suka yi wa mutum 50 kisan gilla a yankin Karanti da ke Karamar Hukumar Kukawa a ranar Alhamis, 15 ga watan Mayu. Gwamnatin Kano ta dakatar da haska shirin...
Gobara ta tashi a Kwalejin Karatun Alƙur’ani da ilimin addinin Musulunci mallakin fitaccen malamin nan, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, da ke Rafin Albasa, a Jihar Bauchi, inda ta ƙone ginin makarantar da kayan cikinta. Binciken wakilinmu ya gano cewa gobarar ta lalata bene mai ɗakuna da dama ciki har da ofisoshi, ajujuwa, ɗakunan gwaje-gwaje, ɗakunan kwamfuta, da ɗakunan karatu. Jami’in Sibil Difens ya mayar da N800,000 da wata Hajiya ta zubar a Adamawa Yadda ’ya’yan shugabanni ke musu yaƙi da ’yan adawa An kuma rasa kayan sawa na malamai da ɗalibai, katifu, barguna da sauran kayayyakin amfanin yau da kullum. Har yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba. Sai dai daraktan makarantar, Sayyadi Aliyu Sise Dahiru, ya ce sun...
Jiragen na sojojin HKI sun kai hari ne dai a yau Lahadi a kan hanyar da ta raba tsakanin garin Beit-Yahun da Bent-Jubail dake kudancin kasar. A garin Kafar-kalla ma wani jirgin saman marar matuki ya jefa bama-bamai masu sauti a kusa da wani gida da dama an rushe shi. Harin na sojojin HKI yana cikin ci gaba da keta hurumin kasar Lebanon da take yi wanda ya wuce 2000 tun daga tsagaita wutar yaki a ranar 27 ga watan Nuwamba na 2024. Bugu da kari HKI ta girke sojojinta a cikin wasu wurare 5 dake kan iyaka,wanda shi ma keta karjejeniya ce. Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hizbullah ta sha yin kira ga gwamnatin kasar da ta yi duk abinda...
Bayan da wani matashi ɗan shekara 33 ɗan kasar Japan mai suna Honkon ya yi tarin kuɗi na tsawon shekaru 10 don siyan motar da yake mafarki — na wata sabuwar mota ƙirar Ferrari 458 Spider — sai ya zauna yana kallon yadda motar take ƙonewa cikin sa’a ɗaya da tuƙa ta a karon farko. Kafofin sada zumunta na ƙasar Japan sun yi sharhi game da rahoton baƙin ciki na Honkon, matashin da ya kasance mai shirya wakoki, wanda ya kashe makudan kuɗi game da mafarkin sayan motarsa ta Ferrari, sai dai ya kalle ta tana ci da wuta a ranar da ya tuƙa ta a karon farko. ISWAP ta kashe manoma sama da 50 a Borno Guguwar raba Masarautar...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murna ga shugaban Iraqi Abdul Latif Rashid, wanda kuma shi ne shugaban karba-karba na majalisar shugabannin kasashen kungiyar Larabawa, tare da taya murnar kaddamar da babban taron kungiyar na 34, a birnin Baghdad na Iraqi. Xi Jinping ya bayyana cewa, cikin shekaru sama da 80 da kafata, kungiyar kasashen Larabawa ta kasance mai mayar da hankali kan inganta hadin kai da karfafa yankin Larabawa da furta matsalolin kasashen da inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaba a yankin Gabas ta Tsakiya. Ya kara da cewa, a shirye kasar Sin take ta hada hannu da kasashen Larabawa wajen zurfafa aminci da ingiza hadin gwiwar moriyar juna da kara musayar...
Sojoji da mafarauta don halaka mayaƙan Boko Haram biyar tare da daƙile wani hari da ’yan ta’addan suka kai a ƙauyen Warambe da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza a Jihar Borno. Warambe na daga cikin yankunan da mazanaunansu suka dawo da zama a baya-bayan nan, kuma mayaƙan Boko Haram sun sha yin yunƙurin kurɗawa cikinsa. Shugaban mafarautan wanda ɗan asalin garin ne ya ce a safiyar Juma’a ne maharan suka nemi shiga ƙauyen, “amma muka gana su, muka kashe mutum biyar daga cikinsu. An miƙa makaman da muka ƙwato daga hannunsu ga sojoji.” Sanata Mohammed Ali Ndume mai wakiltar Kudancin Borno, ya jinjina wa ƙoƙarin jami’an tsaron, musamman wajen ɗaukar mataki cikin gaggawa yana mai ba su ƙwarin gwiwar su ƙara...
A lokacin da yake jawabi a wurin ƙaddamarwar, Gwamna Lawal ya bayyana cewa da hawansa mulki a watan Mayun 2023, ya ci karo da tsarin kiwon lafiya da ya tabarbare saboda rashin kulawa. Ya ce, “Gwamnatinmu, ƙarƙashin ginshiƙan shirye-shiryen ceto, nan da nan ta fara tantance abubuwan da asibitoci ke buƙata, inda sakamakon ya zama abin tsoro kuma ya nuna akwai jan-aiki. “Alal misali, a jihar da ke da mutane kusan miliyan 6 tare da tarin ƙalubale, na’urar duban ɗan tayi ɗaya ce kawai a cikin dukkan cibiyoyin da gwamnati ta mallaka, kuma shi ma duk faci ne a jikinsa da salataf ko’ina! Nan take na ayyana dokar ta-baci a bangaren kiwon lafiya don dawo da ababen more rayuwa, samar...
“Don haka, idan kuna tunanin cewa taron bayanin ministoci, kamar yadda wasu ke yaɗa cewa za a mayar da shi zuwa wajen ƙasar, ba gaskiya ba ne. “Wannan dandamali da Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai take samarwa, nan ne inda abin ke faruwa, a nan ƙasar.” Taron ya samu halartar Ministar Harkokin Al’adu da Tattalin Arzikin Ƙirƙira, Hannatu Musawa; da Ministan Ruwa da Tsaftace Muhalli, Farfesa Joseph Utsev, da kuma Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi. Sanata Umahi, wanda aka ruwaito ba daidai ba cewa yana daga cikin ministocin da za su gabatar da nasarorin Gwamnatin Shugaban Ƙasa Tinubu a wani taro a London, ya goyi bayan furucin Idris, yana mai cewa rahoton ba gaskiya ba...
Harajin ya kuma kai kasa da kimanin kaso 11 a cikin dari, wanda ya kai kasa da wanda ake karba, idan aka kwatanta da duniya. “Abinda muka yi shi ne, mun cire daukacin ma’aikatan da karbar kasa kaso uku a cikin darei a cikin tsarin na karabar harajin,” Inji tsohon Shugaban LLP. Ya shedawa manyan Malaman Makaranta da Jami’an da ke katbar haraji hakan ne, a wani taro da aka gudanar a jihar Legas Nijeriya dai, ta kasance kasar da sama da alumominta miliyan 8o, ke fama da kangin talauci. Hakan ya kuma kara haifar da hauhawan farashin kayan masarufi, musamman yadda kayan suka tashi a 2024, kafin su sauka zuwa kaso 24.2 a cikin dari. Kazalika, hauhauwan farashi da...
Mun bijoro da wannan batun kalubalen da manoman ke ci gaba da fuskanta ne, musamman duba da cewa, kakar noman bana, ta karato, musamman ganin cewa, an fara samun saukar Ruwan sama, a wasu sassan kasar nan, inda kuma tuni, mahara suka mamaye wasu yankunan kasar da ake yin noma. Akasarin fadin kasar nan, musamman a yankunan Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma duba da cewa, wadannan yankunan biyu, sun yi fice wajen yin noma, amma abin takaici, ‘yan bindiga daji, ‘yan ta’adda da kuma wasu Fulani Makiyaya, sun mayar da wadannan yankunan fagen daga, inda suka kashe manoma da kuma lalata amfanin gonakansu. Bugu da kari, wadannan bata garin sun kuma kone wasu gidajen alumomin da ke a...
A ranar Alhamis din nan, wasu hadiman shugaban kasa kan harkokin yada labarai sun kai ziyara hedikwatar hukumar ta NOA inda suka yi amfani da damar wajen lekawa daya daga cikin kayayyakin tarihin Nijeriya a baya – ofishin marigayi shugaba Shagari. Bayan kammala ziyarar, daya daga cikin hadiman shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Temitope Ajayi, ya wallafa hotunan a shafinsa na Facebook domin bayyana abin da suka gani. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
“Ofishina ya cika da tarin jama’a suna ta kiraye-kiraye kan wannan mummunan sakamakon da aka samu a jarabawar JAMB ta 2025. “ASUU za ta kalubalanci wannan sakamakon a gaban babbar kotu idan JAMB ta gaza sake duba sakamakon da kuma bai wa dalibai makin da suka cancanta.” In ji shi Ya yi kira ga gwamnonin jihohin Kudu-maso-Gabas da su tashi su kalubalanci abin da ya kira da rashin adalci domin hana dalibai daga shiyyar samun shiga manyan makarantu a kasar nan. LEADERSHIP ta ruwaito cewa, shugaban JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, a ranar Laraba ya bayyana shirin sake gudanar da jarabawar ga dalibai da suka fito daga jihohin Kudu maso Gabas da Legas. Daga kanmu, magana ta...
Oloyede, wanda ya bayyana tangardar a matsayin “zagon kasa” ga shirin jarabawar UTME ta 2025, ya ce, wadanda abin ya shafa za su fara samun sako a wayar salularsu daga Hukumar daga ranar Alhamis, 15 ga Mayu, 2025. Daga cikin dalibai miliyan 1.9 da suka zana jarabawar UTME ta shekarar 2025, sama da miliyan 1.5 aka bayar da rahoton, sun samu maki kasa da 200 daga cikin mafi girman maki 400, lamarin da ya haifar da damuwa a bangaren ilimi na kasar. UTME ta wannan shekara, ta gamu da koma baya sosai, wanda ya haifar da damuwa tsakanin ɗalibai, iyaye, da malamai. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai...
Sakamakon rikicin siyasa a jihar, ne ya sanya Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Gwamna Fubara, mataimakinsa, da dukkanin ‘yan majalisar dokar Jihar Ribas na tsawon watanni shida. Haka kuma, Shugaban ƙasa ya ayyana dokar ta-baci a Jihar Ribas tare da naɗa mai riƙon kwarya da zai shugabanci jihar na tsawon wannan lokaci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kasar Siriya ta rikide daga Jihadi da zaluncin gwamnatin mamayar Isra’ila zuwa ga kulla kyakkyawar alaka da gwamnatin ‘yan mamaya Gaskiya ta fara bayyana daya bayan daya, sannan makirci da makarkashiyar kungiyoyin masu dauke da makamai bisa da’awar gudanar da jihadi a Siriya suka fara bayyana ga al’umma, masu da’awar jihadi sun kama hanyar fitar da Siriya daga cikin sahun masu fada da makirce-makircen yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya ta hanyar kulla kyakkyawar alaka da su, da janyewa daga duk hakkokin kasar Siriya da gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta mamaye na Siriya a baya-bayan nan. Manufar samar da sabuwar gwamnatin masu da’awar jihadi, kamar yadda aka sani, ita ce tabbatar da tsaron babban sansanin Amurka mafi girma a yanking abas ta tsakiya,...

Sanarwar Hadin Gwiwa Ta Bayan Taron Tattauna Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka
Kasar Sin za ta sauya matsaya kan adadin harajin fito da ta ayyana kan hajojin dake shiga kasar daga Amurka karkashin sanarwar sashen haraji na hukumar kwastam mai lambar 4 ta 2025, ta hanyar dage karin kaso 24 bisa dari a wa’adin farko na kwanaki 90, tare da wanzar da karin kaso 10 bisa dari kan kayayyakin, da jingine sauyin harajin fiton karkashin tanajin sashen haraji na hukumar kwastam mai lambar 5 na 2025, da sanarwar sashen haraji na hukumar kwastam mai lamba 6 na 2025. Kazalika Sin za ta aiwatar da dukkanin matakai na hukuma wajen dage sauran matakan ramuwar gayya da ba na karin haraji ba da ta ayyana kan Amurka tun daga ranar 2 ga watan Afirilun...
’Yan bindiga sanye kayan ’yan sanda sun kai hari a wata makarantar sakandaren gwmanati inda suka harbe wani malami har lahira sannan suka sace mata uku a Jihar Zamfara. Cikin matan da aka sace har da matar malamin a wannan mummunan lamari ya faru a Makarantar Sakandare ta Gwamnati da ke Raka, a ranar Asabar. Wani jami’in gudanarwa na makarantar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa maharan sun shiga harabar makarantar ne ta wata ƙofa da ke bayan katangar makarantar. “Sun mamaye harabar makarantar sanye da cikakkun kayan ’yan sanda, da hula da takalman roba. Sun yi amfani da kofar da ke bayan katangar wajen shiga da kuma guduwa bayan harin,” in ji shi. Rahotanni sun nuna...
Kungiyar Magajunan Gari Na Kasashen Asiya Ta Zabi Birnin Esfahan na tsakiyar kasar Iran a matsayin cibiyar yawan bude ido na wannan shekara ta 2025. Manufar zaben birnin Esfahan a wannan karon shi ne gabatar da shi ga kasashen Asiya saboda sa mutanen Nahiyar Asiya su su ziyarci kasar da kuma birnin don sanin dumbin wuraren tarihin da suke cikin birnin da kuma kewayensa. Labarin ya bayyana cewa birnin Esfahan ayana daga cikin birane mafi tsufa a kasar , sannan yana dauke da wuraren kallo da kuma bude ido a cikin birnin Har’ila yau labarin ya kammala da cewa ana da kayakin tarihi kimani 200,000 a cikin birnin, sannan wasu 1940 na kayakin tarihin kasar, hukumar UNESCO ta zama wurare...
A Talatar makon jiya ce Inter Milan ta ƙara lalata wa Barcelona mafarkinta na ɗaukar Kofin Zakarun Turai a shekaran nan, bayan an yi kare-jini-biri-jini tsakanin kungiyoyin guda biyu a wasan kusa da na karshe. An tashi wasan ne da ci 4-3 a San Siro gidan Inter Milan bayan sun yi 3-3 a gidan Barcelona. Lautaro Martinez da Hakan Calhanoglu ne suka fara zura wa Inter ƙwallo a ragar Barcelona. Za a kwaso ’yan Nijeriya 15,000 da ke gudun hijira a ƙetare Matakan da gwamnonin Arewa suke so a ɗauka kan matsalar tsaron yankin Davide Frattesi ne ya ci ƙwallon da ta bai wa Inter nasara a cikin ƙarin lokaci, bayan ƙwallon ne kuma aka kaure da ruwan sama. Barça,...

Bayan Cin Kamfanin META Tarar Dala Miliyan 220: Sun Yi Bazaranar Katse Kafofin Facebook, WhatsApp, Da Instagram A Nijeriya
BBC ta rawaito cewa, babban abin da ke damun kamfanin na Meta shi ne, yadda al’amarin ya shafi Hukumar Kare Bayanan Sirri ta Nijeriya (NDPC), wanda kamfanin ke zargin karya dokokin kare bayanan sirrin kasar. Baya ga tarar Hukumar FCCPC, hukumar ta NDPC ta ci tarar kamfanin Meta dala miliyan 37.8, bisa zargin satar bayanan sirri, yayin da hukumar kula da tallace-tallace (ARCON) ta fitar da wani hukuncin daban na dala miliyan 37.5, kan abin da ta kira da cewa, tallan da ba a ba da damar aiwatar da shi ba. Daga cikin ka’idojin da ake da su, akwai bukatar kamfanin na Meta ya samu izini kafin tura bayanan ‘yan Nijeriya zuwa kasashen waje, yanayin da kamfanin ke ganin “ba...
Dubban daruruwan mutane a kasar Yemen sun fito kan tituna suna bayyana jin dadinsu da samun nasara a kan kasar Amurka a yakin da suka dau makokinni suka fafatawa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa an daw makonni jiragen yakin Amurka suna kai hare-hare kan wurare daban daban a kasar Yemen da sunan tilastawa kasar dakatar da kaiwa jiragen ruwan Amurka da kuma na HKI wucewa da tekun Red sea don tallafawa mutanen Gaza, wadanda HKI take masu kissan kare dangi da kuma hana shigar abinda zuwa cikin gaza don kashesu da yunwa. A ranar Laraban da ta gabata ce shugaban kasar Amurka Donal Trump ya fito ya fadawa duniya kan cewa, ya cimma yarjeniya da...
Ƙungiyar Allied Group of Nasarawa Professionals (AGNP), wadda ta ƙunshi ’yan kasuwa da masu sana’o’in hannu, ta goyi bayan tsohon Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Mohammed Adamu, wanda ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Gwamnan Jihar Nasarawa a 2027. A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a ofishinta da ke Keffi, AGNP ta ce matakin da Adamu ya ɗauka na tsayawa takara ya sanya al’ummar jihar cikin farin ciki. ’Yan sanda sun kama harsasai 500 a Filato Jami’an tsaro na ba da gudunmawar aikata miyagun laifuka a Nijeriya — Zulum “Wannan lokaci ne na kyawawan fata ga jiharmu,” in ji ƙungiyar. Ƙungiyar ta yi alƙawarin tattara ƙuri’u aƙalla miliyan daya domin mara wa Adamu baya a zaɓen. AGNP ta yaba...
Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik al-husy ya bayyana cewa kisan kiyashin da HKI take yi wa Falasdinawa a tsawon watanni 19 a jere, shi ne laifi mani muni akan bil’adama da ya faru a cikin karni daya. Sayyid Abdulmalik al-Husi ya kuma ce, abinda ya kara munin wannan laifin shi ne yadda yake faruwa a tsakiyar duniyar musulunci,kuma dukkanin duniya tana Kallon abinda yake faruwa. Shugaban na kungiyar Ansarullah ya kuma ce, a baya, ba a Kallon laifuka irin wadannan kai tsaye ta talbijin amma a yanzu ana Kallon ta akwatin talabijin. Shugaban kungiyar ta “Ansarullah” ya kuma yi gargadin cewa da akwai sakamakon da zai biyo bayan wadannan manyan laifuka,yana mai kara da cewa. Alummar musulmi,...
Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kasim, ya bayyana cewa mutanen kasar Lebanon zasu ci gaba da gwagwarmaya da HKI wacce ta ke mamaye da wasu kasashen larabawan yankin har zuwa nasara. Tashar talabijibn ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Sheik Kasim yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar ta kafar bidiyo a taron da aka fara gudanarwa a yau a makarantar Darushafia dake birnin Qom. Taron na Qom yana Magana dangane da “Makarantun Hauza a Qum, Juyin juya halin musulunci a Iran da kuma Gwagwarmaya’. Sheik Kasim ya kara da cewa mutanen kasar Lebanon sun fara gwagwarmaya ne bayan gwamnatin HKI ta mamaye kasarsu, sannan bayan sun sami jagoranci da tunanin Imam Khumaini (q)...
Wasu yan jaridu masu bincike a kasar Amurka sun gano sunan sojan HKI wanda ya bindige yar rahoton tashar Aljazeera ta kasar Qatar a shekara ta 2022 a lokacinda take Shirin bada rahoton hare-harenn da sojojin yahudawan suke kaiwa kan wata unguwa ta Falasdinawa a birnin Jenin na yankin yamma da Kogin Jordan. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wadanda suka shirya film na tattara bayanai yadda aka kashe Shirin Abu Akela wato ‘ Zeteo’ dake da cibiya a birnin Washington na kasar Amurka na cewa sunan sojan HKI ta ya kashe Shirin shi ne Alon Skajio, wanda shima daga baya an kashe shi a birnin na Jenin daga bayan a wani farmakin da sojojin yahudawan suka...
Shugaban kasar Sin, Xi Jinping ya aike da wasikar taya murna ga taron musayar al’adu da cudanyar al’umma da aka shirya domin murnar cika shekaru 80 da samun nasarar yakin turjiya da jama’ar kasar Sin suka yi a kan zaluncin Japan da kuma kazamin yakin ceton kasa na tsohuwar tarayyar Soviet. A cikin sakon nasa, Xi ya yi nuni da cewa, shekaru 80 da suka gabata, al’ummomin kasar Sin da na kasar Rasha sun bayar da gudummawa mai tarihi da ba za a taba mantawa da ita ba wajen samun nasarar yaki da zaluncin danniya a duniya, tare da kulla kakkarfar alaka da ba za a iya kassarawa ba ta hanyar sadaukar da jini, wadda ta kafa tubulin raya dangantakar...

Sharhin bayan Labarai: Mahangar Iran Dangane Da Tattaunawa Kan Shirinta na Makamashin Nukliya Na Zaman lafiya
Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayana labarummu na yau zai yi magana dangane da ‘Mahangar Jumhuriyar Musulunci na Iran ta yadda za’a kai ga fahintar juna a tattaunawanta da kasar Amurka da suke yi wanda ni tahir amin zan karanta. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi a wata tattaunawa ta wayar tarho da tokwaransa na kungiyar tarayyar turai wato Kaja Kallas, ya bayyana mata yadda bangarorin Amurka da Iran za su kai ga cimma yarjeniya dangane da shirin makamashin nukliya na kasarsa. Ministan ya kara da cewa tun kimani shekaru 20 da suka gabata ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran bangaren tattaunawa dangane da shirin nukliyar kasar ta zaman lafiya. Kuma batun shirin nukliyar kasar Iran tana daga cikin ayyuka...
Al’ummar garin Izge da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza ta Jihar Borno sun fatattaki ’yan ƙungiyar Boko Haram bayan kai musu hari a ranar Laraba. Ƙungiyar ‘yan ta’addan ta kuma kashe wani kaftin ɗin soji a harbin na ba zata. Jami’an tsaro na ba da gudunmawar aikata miyagun laifuka a Nijeriya — Zulum Jami’an tsaro na ba da gudunmawar aikata miyagun laifuka a Nijeriya — Zulum Sarkin Gwoza Mohammed Shehu Timta ya ce ’yan ta’addan sun afka musu ne da ƙarfe 1:00 na dare. “Da gaske ne Boko Haram sun afka wa garinmu. Kuma an yi rashin sa’a wani kaftin ɗin soja ya rasa ransa. “Jami’an tsaronmu na sa-kai sun samu nasarar kashe ‘yan ta’addan uku. Sauran sun gudu sun bar...
Gwamnatin Sudan ta katse dangantakar diflomasiyya da (UAE), bisa zarginta da goyan bayan dakarun RSF. A cikin jawabin da aka watsa a talabijin, Ministan Tsaron Sudan, Yassin Ibrahim ya bayyana cewa Sudan ta “katse dangantakar diflomasiyya da UAE,” tare da janye jakadanta da rufe ofishin jakadanci da konsulat dinta a kasar . Da yake magana a gidan talabijin na gwamnatin kasa, ministan tsaron Sudan, Yassin Ibrahim Yassin, ya zargi Abu Dhabi da keta hurumin ‘yancin Sudan ta hanyar mara baya ta fuskar soji ga RSF, ciki har da samar da makamai, da jiragen yaki marasa matuka, da makamai masu linzami wadanda aka kai hari da su a baya-bayan nan a tashar jiragen ruwa, da filin jiragen sama, da kuma tashoshin...
Sai dai, rikice-rikicen cikin gida da matsalolin tsaro da tattalin arziƙi sun sa gwamnatin ke ci gaba da yin gyare-gyare don samar da hanyoyin da za su ba ta kariya da cikakken iko kan harkokin leƙen asiri da tsaro. Wannan mataki yana iya nuni da cewa Nijar na ƙoƙarin zama mai dogaro da kai a fannin tsaro, ko kuma tana neman ƙawancen da zai fi dacewa da manufofinta na cikin gida da waje. Duk da haka, ƙwararru na ganin cewa hakan na iya janyo sabon matsin lamba daga ƙasashen duniya da ƙungiyoyin yanki kamar ECOWAS. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu...
Gwamnatin Sudan da ke da goyon bayan sojoji ta katse dangantakar diflomasiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), tana bayyana ƙasar a matsayin mai katsalandan, a cewar Ministan Tsaron Sudan, Yassin Ibrahim. A cikin jawabin da aka watsa a talabijin ranar Talata, Ibrahim ya bayyana cewa Sudan ta “katse dangantakar diflomasiyya da UAE,” tare da janye jakadanta da rufe ofishin jakadanci da konsulat ɗinta a ƙasar Gulf ɗin. Dalilin faɗuwar ɗalibai a jarabawar JAMB bana — Ministan Ilimi Inter Milan ta kori Barcelona daga Gasar Zakarun Turai Ya zargi UAE da take hurumin Sudan ta hanyar “ƙawarta”, wato Rundunar RSF, wacce ke yaƙi da sojojin Sudan tun watan Afrilu 2023. “Dukkan duniya ta shaida, fiye da shekaru biyu, laifin kai hari...

Sharhin bayan Labarai: Ci Gaban Harkokin Kasuwanci Tsakanin Iran Da Kasashen Waje Duk Tare Da Takunkuman Kasashen Yamma
Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da “Bankasar tattalin arzikin Iran duk tare da takunkuman tattalin arziki masu tsanani wadanda kasashen yamma musamman Amurka suka doramata, wanda ni tahir amin zan karanta. ////…A dai-dai lokacinda gwamnatin kasar Amurka take barazanar zata hana sayan danyen man fetur daga kasar Iran kwatakwata, sannan take barazanar zata farwa kasar da yaki saboda shirin na makamashin nukliya, sabbin rahotanni sun bayyana cewa iran tana gaba a fitar da kayaki kasuwanci zuwa kasar China sannan ita ce ta 9 a duniya wajen samar da kwan kaji da sauran tsuntsaye. Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran ya bayyana cewa, yawan danyen man fetur wanda kasar Iran take sayarwa kasar China...
Yau Litinin ne kotun kasa da kasa ta ICJ za ta yanke hukunci kan karar da Sudan ta shigar kan Hadaddiyar Daular Larabawa. Khartoum ta kai karar UAE a gaban kotun kasa da kasa da ke birnin Hague, inda ta zarge ta da hannu wajen kisan kiyashin da ake yi wa al’ummar Masalit, sakamakon zarginta da goyon bayan dakarun (RSF) da suka shafe shekaru biyu suna yaki da sojojin Sudan. Khartoum na zarginsu da kasancewa masu goyan bayan kisan kare dangi” da ake ci gaba da yi wa al’ummar Massalit na Darfur, saboda zarginsu da goyon bayan dakarun gaggawa na Janar Hemedti (RSF). Khartoum na fatan alkalan kotun su umurci Hadaddiyar Daular Larabawa da ta daina goyon bayan kungiyar RSF,...
Rahotonni na cewa mayaƙan Boko Haram sun kai kashe dakaru huɗu yayin wani hari da suka kai sansanin soji a Jihar Yobe. Aminiya ta ruwaito cewa ’yan bindigar sun ƙaddamar da hari kan sansanin soji na “27 Task Force Brigade” da ke garin Buni Yadi, a yankin Ƙaramar Hukumar Gujba da tsakar daren Asabar. Abin da ya hana ni cika alƙawarin da na yi wa ma’aikata — Gwamnan Sakkwato Lakurawa sun kashe ’yan bijilanti 11 a Sakkwato Harin na zuwa ne kwana guda bayan Ƙungiyar Gwamnonin Arewa maso Gabashin ƙasar sun gudanar da taro a Damaturu, babban birnin jihar da nufin magance matsalolin yankin, ciki har da matsalar tsaro. A baya-bayan nan mayaƙan Boko Haram da na ISWAP na neman...
Assalamu alaikum masu sauraro, sharhin bayan labarammu zai yi magana ne a kan Aya. Shahid Mttahari, shahidi na farko daga cikin malamai jagororin juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran a shekara 1979. A jiya Jumma ce 2 ga watan Mayu na wannan shekara ta 2025 aka yi juyayin shahadar malami na fadrko wanda ya kai ga shahada bayan nasaral juyin juya halin musulunci a nan iran. Aya. Murtadha Muttahari, malami marubuci sannan jagora mai farkar da mutane a Iran da sauran kasashen duniya ta hanyar alkalaminsa da kuma jawabansa na shekaru masu yawa. Kafin juyin juya halin musulunci a nan Iran shekaru 46 da suka gabata, Aya, Muttahari ya zama fitilla ga mutane da dama a nan kasar...
Dakta Abdulmalik ya ce, a halin yanzu gwamnatin jihar na da likitoci 99 kadai ne, wadanda ke kan tsarin albashi, ya kara da cewa; adadin da ake bukata kuma sun kai kimanin 180 zuwa 200. “Likitoci ukun da suka bar aiki, sun dawo bayan karin albashin likitocin da gwamnan ya yi a baya-bayan nan. Don haka, a da muna da likitoci 96, amma bayan karin albashin da gwamnan ya yi, uku da suka bar aikin sun dawo. Saboda haka, a halin yanzu muna da likitoci 99. Kazalika, muna da bukatar kari, domin kuwa kimanin likitoci 180 zuwa 200 muke bukata.” Saboda haka, hukumar ta ce; tana kokarin samar da wata manhaja da za ta bai wa marasa lafiya,...
A cikin jawabin sa a taron, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana wasu manyan fa’idoji da kuma irin barazanar da ke tattare wajen amfani da AI a cikin ɗakunan buga labarai. Ya ce duk da cewa AI na taimaka wa ‘yan jarida a Nijeriya wajen saurin bayar da rahoto, da nazarin bayanai da gudanar da bincike, yana da matuƙar muhimmanci a yi amfani da wannan sabuwar fasahar cikin hankali da bin ƙa’idoji. Ya ce: “A yayin da muke rungumar aikin jarida da fasahar AI, dole ne mu tabbatar da cewa ba za a tauye ‘yancin jarida ba, illa ma a ƙara ƙarfafa shi.” Ministan ya kuma ba da sanarwar cewa Nijeriya...
Wakilinmu ya ce mayaƙan “Operation HADIN KAI” sun fafata da maharan lokacin da suka kai hari Buni Gari. Rundunar sojin ƙasa ta tabbatar da faruwar lamarin a shafinta na sada zumunta da safiyar yau Asabar. A cewarta, “Mayaƙan Operation HADIN KAI suna ci gaba da fafatawa da mayaƙan ISWAP a Buni Yadi.” Rahotannin sirri sun bayyana cewa jami’an sojin sun samu taimako daga mafarauta da ƴan bijilanti kafin daga baya maharan su gudu. Har yanzu, ba a san adadin asarar da aka yi ba sakamakon harin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
Hedikwatar ’yan sandan Gada da ke Jihar Sakkwato ta gano wasu shanu 25 da ake zargin an sace ko kuma sun ɓace daga hannun masu su. An gano dabbobin ne a wani dajin da ke kan iyaka da ƙaramar hukumar Sabon Birni ta jihar a ranar Alhamis, bayan da hukumomin yankin suka samu labarin. ’Yan kungiyar asiri: Mutum 95 sun shiga hannu a Edo Shettima zai halarci bikin rantsar da sabon shugaban ƙasar Gabon Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, Ahmad Rufa’i ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, inda ya ce an gano dabbobin ne bayan da Alhaji Muhammad Kyari ya bayar da rahoton cewa akwai shanun da suka ɓace. Sanarwar...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Cibiyar samar da kyakyawan yanayin yin kasuwanci na Fadar Shugaban Kasa da hadaka da NPA ne, suka shirya taron kaddamarwar, “Ana sa ran a zangon farko na 2026, aikin na NSWP zai fara fara aiki wanda tuni, Fadar Shugaban Kasa ta amince da kwangilar domin a wanzar da aikin,” Inji Dantsoho. Ya kuma bayar da tabbacin cewa, za a rinka gudanar da ganawa akai-akai da masu ruwa da tsaki domin gudanar da hada-hadar kasuwanci a cikin Tashoshin Jiragen Ruwan kasar a cikin nasara. Ya sanar da cewa, zuba hannun jari a kayan aiki Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar, samar da kayan aiki na fasahar zamani da sauransu, za su taimaka wajen kara habaka kasa da kuma gudanar da...
Wata ƙungiyar matasa mai suna “North-East Coalition Against Terrorism” ta yi maraba da Major General Abdulsalam Abubakar, sabon kwamandan yakin Operation HADIN KAI (OPHK), inda ta bayyana cewa tana fatan zaman lafiya ya dawo yankin. A cikin wata sanarwa da Ismail Mustapha da Sakatare Danlami Bukar suka rattaba hannu, ƙungiyar ta ce Sojojin Nijeriya a ƙarƙashin babban Hafsan Soja Janar Chris Musa za su ci gaba da matsa lamba kan mayakan. Ta kuma yi kira ga al’ummar yankin su ba sabon kwamandan goyon baya. Boko Haram Sun Kashe Masu Kamun Kifi 18 A Borno Sojoji Sun Harbe Mutane Biyu Har Lahira Da Ake Zargi Ɓarayin Mota Ne A Filato Ƙungiyar ta gargadi matasa su ƙi tayin shiga ƙungiyoyin da ba...
Amurka ta kawo ƙarshen cire haraji kan wasu kayayyaki da ba ma su tsada ba da ake shiga da su ƙasar daga China. A baya Amurkawa na iya sayan kayayyakin China da ba su haura dala 800 ba, idan za su yi oda ta intanet ba tare da wani haraji ba, amma yanzu za su biya kashi 120. Ana sa ran harajin zai fara aiki nan take, kuma wasu Amurkawa masu sayayya za su ji a jikinsu. Hakazalika su ma yawancin kamfanonin China da ke samar da kayan da shigar da su can.
A wurin mu Malikawa, mun dauki watannin nan guda uku a matsayin lokacin Hajji, wasu kuma sun ce a’a, daga kwana goman farkon nan na Zhul-hijja, lokacin ya kare, to amma kuma idan aka yi la’akari za a ga cewa akwai sauran ibadodin Hajjin da suka shige wadannan kwanakin goma irin su Jifa da ake dawowa Mina a yi bayan Sallar Idi da Dawafin bankwana. Shi ya sa Malikawa muka dauki watannin ukun baki daya a matsayin lokacin Hajji. Kuma Ibn Hazan ya goyi bayan haka, don ba za a dauki wata biyu da kwana goma a ce musu watanni uku ba. Kamar yadda bayani ya gabata, Hajji ba a ko ina ake daura haramar yin sa ba, yana...

Ranar Maleriya Ta Duniya: ‘Yan Nijeriya Na Kashe Naira Tiriliyan 1.156 Duk Shekara Wajen Sayen Magunguna
Binciken LEADERSHIP ya nuna cewa, duba mara lafiya guda daya tak da ke dauke da cutar Maleriyar da ba ta yi karfi sosai ba a asibitin gwamnati, na lashe kimanin Naira 17,000, tsakanin ganin likita, yin gwaje-gwaje da kuma magunguna. Wadannan kudade sun kai kimanin Naira tiriliyan 1.156 da ake kashewa a kan wannan cuta, amma asalin kudaden sun zarta haka, musamman idan Maleriyar ta yi kamari, za a iya kashe ninki uku ko sama da haka na wannan kudi. Yayin da duniya ke yin wannan biki na ranar Maleriya, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta nanata cewa, cutar na ci gaba da zama barazana, musamman a yankuna masu fama da zafi, duk da cewa; cuta ce da...

Hamas Ta Yi Allah Wadai Da Matsayin Amurka Na Goyon Bayan Haramta Hukumar Kula Da ‘Yan Gudun Hijiran Falasdinawa Ta UN
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi Allah wadai da matsayin Amurka na goyon bayan haramta hukumar kula da ‘yan gudun hijira falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi Allah wadai da matsayin Amurka na goyon bayan haramtacciyar kasar Isra’ila kan haramta hukumar kula da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa da ayyukan ba da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya “UNRWA”, tana daukan wanan a matsayin Amurkia na ci gaba da nuna son kai da goyon bayan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ‘yar mamaya da kuma rashin mutunta dokokin kasa da kasa da yarjejeniyar jin kai. A cikin wata sanarwar manema labarai da ta fitar jiya Alhamis, kungiyar Hamas ta yi nuni da cewa: Shigar da Amurka...
Ma’aikatan jihar Ribas sun hallara a sakatariyar kungiyar kwadago ta kasa, NLC da ke Fatakwal domin bikin ranar ma’aikata ta 2025 a ranar Alhamis. Dama kungiyar ta NLC, tuni ta sanar da cewa, ba za ta gudanar da bikin murnar ranar ma’aikata ba kamar yadda aka saba yi a filin shakatawa na Isaac Boro, inda a al’adance kungiyoyin kwadago daban-daban ke gudanar da tattaki a filin domin murnar wannan rana ta 1 ga watan Mayu. Gobara A Haramtacciyar Wurin Ajiye Man Fetur Ta Ci Rayukan Mutane 5 A Jihar Ribas Aikin Gina Tashar Jirgin Ƙasa A Kano Yana Ci Gaba Gadan-gadan A maimakon haka, ma’aikatan sun taru ne domin nuna goyon bayansu ga Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakinsa da ‘yan...
’Yan siyasar yankin Arewa na ganin dole sai da goyon bayansu ɗan takara zai yi nasara a zaben Shugaban ƙasa. Hakan na zuwa ne bayan tsohon maitaimaka wa shugaban ƙasa a fannin siyasa, Alhaji Hakeem Baba-Ahmed ya yi wata hira, inda yake cewa, nan da wata shida yankin zai fitar da matsayarsa. An ɗaure ’yar shekara 80 a kurkuku saboda dukan jikarta da silifas Dalilin da manyan ’yan siyasa ke barin NNPP — APC Duk da cewa Hakeem ba shi ne mai magana da yawun al’ummar yankin ba, amma ana kallon sa a matsayin daya daga cikin manya a yankin, saboda tsohon matsayinsa na mai magana da yawun Kungiyar Dattawan Arewa (NEF). Tsarin siyasar kasar nan ya sa dole ne...
A Kaduna, an kama wasu mutane uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, ciki har da wani da ya ce ya koma jihar ne domin kafa sabuwar ƙungiya bayan an kama abokan aikinsa a Kwara. Haka kuma, an kama wasu biyu da ke ɗauke da bindigogi. ‘Yansanda sun gano makamai da dama, ciki har da bindigogi ƙirar AK-47 da AK-49, da kuma wasu makamai da aka ƙera a gida. Wannan aiki na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na yaƙar garkuwa da mutane da safarar makamai a faɗin ƙasar. Kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya ce ana ci gaba da bincike, kuma za a gurfanar da waɗanda ake zargi a kotu da zarar an kammala binciken. Ya kuma yaba da goyon...
Dabbobi sama da miliyan guda ne ake sa ran za a yi wa rigakafi a fadin karamar hukumar Babura da ke jihar Jigawa. Shugaban karamar hukumar Babura, Alhaji Hamisu Muhammad Garu, ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da aikin rigakafin dabbobi na bana. A cewarsa, fiye da tumaki da awaki miliyan daya da shanu dubu ashirin ake sa ran za a yi wa rigakafi a fadin karamar hukumar. Ya jaddada cewa karamar hukumar na da cikakken shiri da kudurin tallafawa sauyin noma na Gwamna Umar Namadi, domin inganta rayuwa da tattalin arzikin al’ummar jihar. Shugaban ya jaddada muhimmancin masu kiwon dabbobi su bada hadin kai yayin aikin rigakafin domin tabbatar da lafiyar dabbobinsu. Alhaji Hamisu Garu ya kuma nuna jin...
“Gwamnati ta amince da hada hannu da shugabannin al’umma na cikin gida domin tabbatar da tsaro. “Muna gode muku kan abin da kuke yi. Amma muna bukatar Sarakuna su yi magana da mutanenmu kan kokarin da dukkanmu muke yi don kare al’ummominmu daga masu kutse.” Gwamnan ya yi kira da a inganta hadin gwiwa a tsakanin al’umma da hukumomin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyi. Mataimakin Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kwara, Alhaji Ibrahim Bologi II, wanda shi ne Etsu Patigi, ya yaba wa gwamnan bisa hada gwiwa da su domin tabbatar da tsaro a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
Aƙalla wasu mutum 10 mafarauta sun rasa rayukansu yayin aikin ceto a ƙauyen Kopire da ke Ƙaramar Hukumar Hong ta Jihar Adamawa. Shugaban ƙungiyar mafarautan Nijeriya reshen Arewa maso Gabas, Shawulu Yohanna ne ya tabbatar wa Aminiya hakan a ranar Talata. Wani abin fashewa ya kashe mutum 26 a Borno An dawo da wutar lantarki a Sifaniya da Portugal A cewarsa, ajali ya katse hanzarin mafarautan ne yayin wani arbatu da mayaƙan Boko Haram da suka yi musu kwanton ɓauna a jeji. Ya bayyana cewa, mafarautan sun tunkari maharan ne bayan samun bayanan sirri da ke nuna cewa suna shirin kai hari. “Abin takaicin shi yadda ake yi wa Gwamnan Borno ƙafar ungulu a ƙoƙarin da yake yi na ganin...
An fara kasuwar baje koli na kayakin kasuwancin da ake samarwa a cikin Iran ko IRAN EXPO 2025, karo na 3 a nan Tehran. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kasuwar baje koli na Iran EXPO 2025 zai jawa masu zuna jari daga kasashen Afirka. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya fadawa kamfanin dillancin labaran IP kan cewa Kasuwar ta bana dai, za ta tara kamfanonin masu samar da kayaki daga yankuna daban daban na kasar Iran da dama, kuma akwai fatan cewa wannan kasuwar ta zama mabudi ga kyautatuwan tattalin arzikin kasar. EXPO dai ita ce kasuwar baje koli na kayakin kasar Iran mafi girma wanda ake gudanarwa a ko wace shekara, sannan...
Ana ci ga ba da zaman dar-dar a kasar Burkina faso, bayan da shugaban kasa mai ci Ibrahim traure ya sake tsallaka rijiya da baya, a wani kokarin juyin mulki wanda bai sami nasara ba a makon da ya gabata. Shafin yanar gizo na labarai ‘Africa News’ya nakalto radiyo Faransa RFI yana fadar cewa an bankado juyin mulkin ne bayan da dukkan bakin da aka gayyata a ranar 22 ga watan Afrilu zuwa wani taro sun kasa halattan taron. Wanda ya nuna shakku kan abinda aka kulla a cikin taron. Labarin ya kara da cewa a cikin yan kwanaki masu zuwa mutanen kasar zasu fito zanga-zanga don nuna goyon bayansu ga shugaban Traore. Har’ila yau ana gudanar da bincike a...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana a yau Litinin cewa, babu wata tattaunawa da aka yi ta wayar tarho tsakanin shugabannin kasashen Sin da Amurka a baya-baya nan, haka kuma bangarorin biyu ba su cimma wata yarjejeniya ko su tuntubi juna game da batun haraji ba. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban kasar Siriya ya ki amincewa da bukatar kurdawan kasar daga dakarun Democradiyyan kurdawa wato (SDF), na samar da tsarin tarayya a kasar bayan kifar da gwanatin Basshar Al-Asab. Jaridar The Nation ta nakalto shuga Al-Ahmad Sharaa yana fadar haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa tsarin tarayyar barazana ce ga hadin kan kasar ta Siriya sannan tsarin tarayya ya sabawa yarjeniyar da aka kulla da kurdawan a baya-bayan nan. A wani taron da suka gabatar a makon da ya gabata, jam’iyyar kurdawan kasar ta Siriya (SDC) ta fadawa “ The National ” bayan taron kan cewa suna bukatar tsarin tarayyar a kasar Siriya don shi ne kadai zai tabbatar da hakkinsu a kasar. A cikin watan maris...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A shekarar bara, ’yan kasuwa, musamman masu hadahadar kayan abinci da na amfanin gona a Nijeriya, kakarsu ta yanke saka, saboda tashin gwauron zabon da kayan a kasar. Galibin wadannan amfanin gona na kasuwanci ana fitar da su zuwa kasashen a duniya. Hukumar Bunkasa Fitar da Kayayyaki ta Nijeriya (NEPC) ta sanar a watan Agusta na shekarar ta 2024, cewa Najeriya ta samu gagarumin ci-gaba a fannin fitar da kayayyaki da ba na man fetur ba a watanni shidan farkon shekarar, inda ta samu kudin shiga kimanin dala biliyan 2.7. Yawan bukatar kayan a kasuwannin duniya ya kawo hauhawar farashin kayan abinci na yau da kullum da amfanin gona na kasuwanci. An kuma yi hasashen cewa farashin zai ci gaba...
Kwamishina CP Ibrahim Maikaba ya yaba da ƙoƙarin jami’ansa, yana kuma ƙara jaddada niyyar rundunar na yin aiki tare da al’umma domin samar da tsaro. Ya buƙaci mutane su riƙa bai wa rundunar sahihan bayanai a kan lokaci domin taimaka wa yaƙi da laifuka. Rundunar ta kuma fitar da lambobin da za a iya kira idan aka ga wani abu da ba a gamsu da shi ba; 08034805544, 07032490813 da kuma 09053872244 Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
’Yan kasuwar kayan abinci sun bayyana yadda suke tafka asara bayan sun saye wasu kaya sun ajiye suna jiran samun tuna mai tsoka idan kayan sun yi tashin gwauron zabo. A shekarar bara, ’yan kasuwa, musamman masu hadahadar kayan abinci da na amfanin gona a Nijeriya, kakarsu ta yanke saƙa, saboda tashin gwauron zabon da kayan a ƙasar. Galibin waɗannan amfanin gona na kasuwanci ana fitar da su zuwa ƙasashen a duniya. Hukumar Bunƙasa Fitar da Kayayyaki ta Nijeriya (NEPC) ta sanar a watan Agusta na shekarar ta 2024, cewa Najeriya ta samu gagarumin ci-gaba a fannin fitar da kayayyaki da ba na man fetur ba a watanni shidan farkon shekarar, inda ta samu kuɗin shiga kimanin dala biliyan 2.7....
“Rashin samar da daidaito a hada-ahadar kasuwanci, ya kasance abinda ya sanya Hukumar ta NPA ke cazar kudaden gudanar da aiki da yawa,” Inji Dantsoho. Dantsoho wanda Janar Manaja na sashen hudda da jama’a da gudanar da tsare-tsare na Hukumar NPA Miista Seyi Iyawe Akinyemi ya wakilce shi a wajen taron, ya ce, NPA ta bai wa kamfanini biyar Lasisi a jihar Legas, bisa kokarin da take yi, na bunkasa fitar da kaya zuwa waje ta hanyar amfani da Tashoshin ta. Sai dai, ya sanar da cewa, Hukumar na duba yuwuwar samar da rangwamen cazar kudaden, musamman domin ta kara inganta ayyukanta. Ya yi nuni da cewa, Tashoshin Jiragen Ruwa waje ne da ke taimaka wa wajen...