2025-10-16@00:15:17 GMT
إجمالي نتائج البحث: 494
«farashin kaya»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Sojoji sun samu nasarar kai wani gagarumin farmaki kan maboyar ’yan ta’addan da suka addabi manoma da mazauna wasu ƙauyuka a Jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Nijeriya. Bayanai sun ce dakarun sojin na sama da ta ƙasa, waɗanda ke ƙarƙashin rundunar Operation Fasan Yamma da ke sintiri a Arewa maso Yamma domin kawar da masu tayar da ƙayar baya, sun hallaka sama da ’yan ta’adda 400 a yayin wannan samamen. Za a gyara tarbiyar tubabbun ’yan daban Kano Direba ɗaya ya tsira a hatsarin tankokin dakon iskar gas a Zariya Majiyoyi sun bayyana cewa ’yan ta’addan, waɗanda ke fakewa a dajin Makakkari tare da shugabanninsu daban-daban, sun dauki haramar kai hari kan wani ƙauye ne kafin sojojin su...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jami’an Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), sun kai samame a Ɗakin Karatun Olusegun Obasanjo da ke Abeokuta, a Jihar Ogun, inda suka kama wasu matasa da ake zargin ’yan damfara ne. Samamen ya faru ne da safiyar ranar Lahadi a sashen otal na ɗakin karatun. ’Yan bindiga sun kashe gomman mutane a ƙauyukan Sakkwato An ɗaure tsohon Firaminista Succes Masra shekaru 20 a Chadi Gidan Obasanjo na musamman yana cikin harabar ɗakin karatun. Wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, ya nuna yadda wasu matasa ke gudu domin ka da EFCC ta kama su. Rahotanni sun ce jami’an EFCC sun ƙwace sama da motoci 20 tare da wasu kayayyaki masu daraja. Wani jami’in...
Ali Akbar Velayati mashawarcin jagoran juyin juya halin Musulunci da Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan harkokin kasa da kasa ya tabbatar da cewa “Jamhuriyar Musulunci tana adawa da shirin kwance damara na kungiyar Hizbullah” yana mai jaddada cewa Iran a ko da yaushe tana goyon bayan al’ummar kasar Labanon da kuma gwagwarmayarsu. Da yake magana da kamfanin dillancin labarai na Tasnim na Iran a ranar Asabar, Velayati ya ce bijiro da batun kwance damarar Hizbullah ba sabon abu ba ne a Lebanon. “Kamar yadda wannan yunƙurin ya gaza a baya, wannan karon ma ba za iyi nasara ba, kuma ‘yan gwagwarmaya zasu ci gaba da yin tsayin daka a kan manufofinsu da kuma dakile wannan makirci,” in ji shi. Ya...
Al’ummar Japan na gudanar da bikin tunawa da ranar harin Nagasaki da ya faru shekaru 80 da suka gabata, wani hari da ke zama irinsa na farko kuma mafi muni da duniya ta taba gani. Tarihi ya nuna cewa Amurka ce ta fara harba makamin Nukiliya a garin na Nagasaki kwanaki uku bayan na garin Hisroshima a wani ɓangare na dakatar da yaƙin duniya na biyu.! Harin na ranar 9 ga watan!!!!!!!mutane dubu 70 a take bayan mutane 140 da suka mutu kwanaki uku da suka gabata a harin na Hiroshima. An yi ittifakin cewa wannan shine harin da ya tilastawa Japan miƙa wuya a ranar 15 ga watan Agustan wannan shekarar, matakin da ya kawo ƙarshen yaƙin. Bayanai sun...
Wata babbar kotu a Jihar Borno, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Aisha Kumaliya, ta yanke wa Kalthum Mustapha hukuncin ɗaurin shekara uku a gidan gyaran hali bayan samun ta da laifin aikata damfara. Hukumar EFCC ta bayyana cewa, an fara gurfanar da Kalthum a ranar 13 ga watan Mayu, 2024. Tsohon Ministan Noma Audu Ogbeh ya rasu Fashewar gurneti ya kashe yara uku a Borno Ana tuhumarta da karɓar kuɗi Naira miliyan 1.35 daga hannun Muhammad Lawan Sani, Abubakar Umar, da Yusuf Jafar domin samar musu da kayan abinci da ake amfani da su wajen ciyar da yara masu fama da rashin abinci mai gina jiki. Sai dai ba ta kawo kayan ba kuma ba ta mayar musu da kuɗinsu ba. A...

Shin Amurka Ta Manta Da Azabar “Babban Koma-Baya” Tare Da Haraji Mafi Yawa a Lokacin Na Tsawon Kusan Karni?
Cin zarafin Amurka ta hanyar haraji ya kuma lalata amincinta tsakanin sassan kasa da kasa. A halin yanzu, fannin shigar da kayayyaki na Amurka ya yi kasa zuwa kashi 13% kacal a kasuwannin duniya. Har ila yau, a jiya Alhamis 7 ga wata, bayanai sun nuna cewa, a cikin watanni bakwai na farkon shekarar nan, cinikayyar kayayyaki ta Sin ta ci gaba da nuna kyakkyawan ci gaba, inda ta samu karuwa tsakaninta da kasashe membobin kungiyar ASEAN, da Tarayyar Turai, da Afirka, da Asiya ta Tsakiya, wanda ke nuna karfin juriya da kuzari. Hakan ya kuma tabbatar da cewa, cin zarafi ta hanyar haraji ba zai haifar da alfanu na dogon lokaci ba, maimakon haka, budadden tsarin hadin gwiwa...

Wa’adin Da Shugaban Amurka Ya Gindaya Na Kawo Karshen Yaki A Ukraine Ya Karato Ba Tare Da Alamun Karewarsa Ba
Shugaban Amurka ya aike da jakada zuwa Rasha tare da yin barazanar sanyawa Moscow takunkumi Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da cewa: Manzonsa na musamman Steve Witkoff zai ziyarci kasar Rasha a mako mai zuwa, yayin da wa’adin da ya sanyawa Moscow na kawo karshen yakin da take yi da Ukraine ke gabatowa. A halin da ake ciki kuma, ana ci gaba da gwabza yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine, inda Moscow ta sanar da lalata jiragen Ukraine guda 18. Yakin da ake yi a Ukraine na kara kamari zuwa ci gaba mai hatsari a daidai lokacin da wa’adin da shugaban Amurka Donald Trump ya gindaya wa Rasha ke gabatowa, da kuma halayensa na tunzura jama’a,...
Tawagar ƴan wasan kwando na matan Najeriya ta lashe gasar ƙwallon kwando ta Afirka karo biyar a jere, lamarin da ya sa ta kafar tarihin wannan bajinta a Afirka. Tawagar D’Tigress ta samu nasara ne a wasan ƙarshe bayan doke Mali da ci 78-64 domin ɗaukar kofin gasar karo na bakwai a tarihi. Ƴan wasan Najeriyar sun kankane gasar ƙwallon kwandon Afirka, inda suka yi nasara sau 29 a jere a duka wasan da suka buga ba tare da rashin nasara ba tun 2015. Nasarar D’Tigress na zuwa ne kimanin mako guda bayan da tawagar Super Falcons ta ƴan wasan ƙwallon kafar matan Najeriya ta lashe gasar ƙwallon ƙafar matan Afirka, karo na 10 a tarihi.
Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Gusau/Tsafe ta tarayya Kabiru Amadu (wanda aka fi sani da Mai Palace) ya shirya taron addu’a na musamman ga jihar Zamfara da Najeriya baki daya, domin neman zaman lafiya da cigaba mai dorewa. Taron addu’o’in wanda ya gudana a babban masallacin Juma’a na Tudun Wada da ke Gusau, ya hada malaman addinin Musulunci, da sarakunan gargajiya, da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa, da kuma daruruwan al’ummar jihar baki daya, duk sun ba da hadin kai wajen ganin an samar da zaman lafiya mai dorewa a jihar. A nasa jawabin, Kabiru Mai Palace, ya bayyana taron a matsayin wani shiri na ruhi da nufin neman taimakon Allah wajen magance matsalar rashin...
Rundunar Sojin Najeriya tare da haɗin gwiwar jami’an Hukumar DSS sun ceto Injiniya Joshua Saleh, wani malami a Jami’ar Taraba, wanda ’yan bindiga suka sace. An sace malamin ne a ranar 31 ga watan Yuli, 2025, a hanyar Chinkai–Kente zuwa Wukari, da ke Ƙaramar Hukumar Wukari a Jihar Taraba. Sai an samar da ’yantacciyar ƙasar Falasɗinu za mu ajiye makamai — Hamas An ƙara hakimai 6 a Masarautar Katsina Bayan samun sahihan bayanai, sojoji da DSS suka fara bincike tare da ƙoƙarin ceto shi a wurare da dama, ciki har da Kente, Sondi 1 da 2, Yaku, da Warawa. A cewar Laftanar Umar Muhammed, mai magana da yawun rundunar, sojojin sun yi arangama da ’yan bindigar, inda suka yi musayar...
Ƙungiyar Ma’aikatan Jinya ta Najeriya (NANNM), ta dakatar da yajin aikin gargaɗi na kwanaki bakwai da ta fara a faɗin ƙasar nan. Ƙungiyar ta bayyana hakan ne cikin wata takarda da shugabanta ƙasa, Haruna Mamman, da sakatarenta, T.A. Shettima, suka sanya wa hannu. Rufe gidan rediyo ya haifar da cece-ku-ce a Neja Jami’ar Umaru Yar’adua ta kori ɗalibai 57 kan satar jarabawa Sun fara yajin aikin ya fara ne a ranar Laraba tare da niyyar shafe kwanaki bakwai suna yin sa. Ma’aikatan jinyar sun shiga yajin aikin ne saboda ƙarancin albashi, ƙarancin ma’aikata, da kuma rashin ingantattun wuraren aiki. Wannan yajin aiki na zuwa ne a daidai lokacin da likitoci ke takun saƙa da gwamnati kan batutuwan suka shafi jin...
Shugaban kasar Iran Masuod Pezeshkiya ya yi juyayin shahadar Isma’ila Haniyya marigayi shugaban kungiyar Hamasa a nan Tehran shekara guda kenen. Ya kuma jaddada cewa JMI ba za ta taba manta da shi ba. Tashar talabijin ta Presstv ta nakalto shugaban yana bayyana wannan juyayin a ranar da Haniya yake cika shekara guda da shahada, sannan shahadarsa ya zo dai dai da ranar da Pezeshkiyan ya fara shugabancin kasar. Labarin ya kara da cewa shugaba Pezeshkiyan ya bayyana haka ne a shafinsa na X ya kuma kara da cewa a ranar da na fara aiki a matsayin shugaban kasa kenen, makiya HKI da kuma Amurka suka sanyamu cikin bakin ciki tare da kashe bakommu wanda ya zo ya taya mu...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ruwan sama kamar da bakin kwarya tare da iska mai karfi da aka tafka a kwanan nan ya yi sanadin mutuwar mutane 44, yayin da wasu tara suka bace a birnin Beijing, kamar yadda aka bayyana a wani taron manema labarai da ya gudana a yau Alhamis. A yayin taron manema labarai da gwamnatin birnin Beijing ta gudanar a yau game da rigakafin ambaliyar ruwa da bayar da agajin gaggawa, an bayyana cewa, bala’in ambaliyar ruwan da ya auku kwanan nan ya shafi mutane sama da 300,000 tare da lalata gidaje 24,000 a birnin Beijing. Sai dai, yanzu haka birnin na Beijing na kara kokarin farfado da wutar lantarki, da share tituna, da kai muhimman kayayyaki ga mazauna yankin da...
Hukumar kula da da’ar ma’aikata ta sanar da cewa, a halin yanzu ana iya bayyana kadarorin ma’aikatan ta hanyar yanar gizo, wani mataki da aka tsara domin saukaka aikin da kuma kara yin lissafi. Daraktan ofishin na jihar Jigawa Abubakar Bello ne ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci shugaban ma’aikatan jihar Alhaji Muhammad K. Dagaceri a ofishin sa. Abubakar Bello ya jaddada cewa sabon shirin na da nufin rage dinbin aikin dake gaban ma’aiakata da kuma saukaka tantance kadarorin domin yaki da cin hanci da rashawa a cikin tsarin. “Mun sauya dabara zuwa rajista ta yanar gizo don bayyana kadarorin, muna ba wa mutane damar kammala aikin daga gidajensu. Duk da haka, muna neman goyon...
Ministan ya kuma ce ƙasarsa na shirin sanya hannu a wata takarda don neman goyon bayan sauran ƙasashe wajen ganin an kafa ƙasar Falasɗinu da Isra’ila. A taron Majalisar Ɗinkin Duniya da aka gudanar na kwana biyu, ƙasashe 125 sun amince cewa hanyar warware rikicin Gaza ita ce kafa ƙasashe biyu, wato Falasɗinu da Isra’ila. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Dakarun Operation Haɗin Kai da ke Arewa maso Gabas, sun ɗakile wani sabon hari da mayaƙan Boko Haram suka kai a Jihar Borno. Sun kai harin ne yankunan Konduga, Bama da Gwoza. Shugaban hukumar zabe ta jihar Bauchi ya rasu Adadin Falasdinawan da Isra’ila take kashewa a Gaza yanzu ya haura 60,000 ’Yan ta’addan sun yi yunƙurin tarwatsa gadar da ke kan hanyar Marte zuwa Dikwa ta hanyar dasa bama-bamai. Amma sojoji sun gano abubuwan fashewa guda 17 da suka dasa a ƙarƙashin gadar kuma suka cire su. A yayin daƙile harin, sojoji sun kashe ’yan ta’addan Boko Haram guda tara, sannan sun ƙwato bindigogi ciki har da AK-47 da bindigar PKT. Kakakin rundunar sojin a Maiduguri, Kyaftin Reuben Kovangiya,...
Jam’iyyar APC reshen Jihar Zamfara ta taya sabon mai martaba Sarkin Katsinar Gusau, Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello, murnar hawansa karagar mulki a matsayin Sarkin Katsinan Gusau na 16. Jam’iyyar a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren yada labaranta, Yusuf Idris Gusau, ta bayyana sabon sarkin a matsayin mai tarihi da kuma nadin sarautar Allah, wanda ya zo ne jim kadan bayan rasuwar mahaifinsa, marigayi sarki, Alhaji Ibrahim Bello. Sanarwar ta nuna cewa Alhaji Abdulkadir kyawawan halaye na gaskiya, kwazonsa, sadaukarwa, biyayya ga mahaifinsa da ya rasu, da kuma mutunta al’umma ta kowane hali, sun nuna shi ne wanda ya cancanta. A cewar sanarwar, wannan shi ne karo na farko a tarihin masarautar da wani...
Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da zagayen farko na makon lafiyar mata da jarirai da jarirai (MNCHW) na shekarar 2025 tare da raba fakiti 6,000 na kayan haihuwa da na’urar (C/S) 500 ga cibiyoyin lafiya a fadin jihar. Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya wakilta shi ne ya jagoranci bikin kaddamar da shirin a hukumance da aka gudanar a cibiyar lafiya matakin farko na Birji da ke karamar hukumar Madobi. Ya yi nuni da cewa, wannan aikin ya hada da na rigakafi na yau da kullun ga yara, karin sinadarin Vitamin A, Rarraba gidajen sauro masu maganin kwari ga mata masu juna biyu. Gwamna Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatin sa na karfafa...
Sauran sun haɗa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro Nuhu Ribadu, tsoffin gwamnoni, ministoci da hafsoshin tsaro. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Mahara sun kashe akalla mutane biyar a Dajin Madam da ke yankin Karamar Hukumar Alkaleri ta Jihar Bauchi. Wannan na zuwa ne bayan a makon jiya ’yan bindiga sun kutsa kauyukan da ke kusa da garin Mansur a karamar hukumar, inda suka kashe mutane hudu, suka kwashe kayayyaki a shagunansu. Daga bisani ’yan sanda sun sun bi su, inda suka fatattake su suka gudu zuwa cikin kungurmin Dajin Madam. Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed ne ya sanar da mutuwar mutanen a yayin taron zaman lafiya da aka gudanar a garin Nahutan Darazo a kokarinsa na sasanta rikicin baya-bayan nan tsakanin manoma da makiyaya da ya yi sanadin jikkatar wassu mutane a Darazo. Gwamnan ya kuma nuna matuqar damuwarsa kan...
An fara shigar da kayyakin agaji zuwa Zirin Gaza wadanda galibi ta sararin samaniya aka rika jefawa da jirage daga kasashen Jordan da Hadaddiyar Daular Larabawa. Arshiyan Kohen, kakakin ma’aikatar tsaron Isra’ila ya ce, za a dakatar da farmakin soji na tsawon sa’o’i 10 a kowace rana a wasu sassan Gaza tare da ba da damar samun sabbin hanyoyin ba da agaji. DW ya ruwaito cewa ana ci gaba danka kayayyakin tallafin a hannun kungiyoyin agaji na kasa da kasa da suke ci gaba da ayyukan rarrabasu. Tinubu ya bai wa ’yan ƙwallon Nijeriya mata kyautar kuɗi da gida da lambar yabo An kashe ’yan ta’adda 45 a Neja Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Gutteress ya siffanta wannan matakin da...
Ma’aikatar kula da sashen ayyukan jigilar kayayyaki ta kasar Sin ta ba da rahoton cewa, a cikin rabin farkon bana, an samu ci gaba mai yawa a bangaren, kamar yadda alkaluman hukuma suka nuna a jiya Lahadi. Hukumar raya ci gaban kasa da gudanar da gyare-gyare, wacce take da alhakin tsara tsare-tsaren tattalin arzikin kasa ta yi bayanin cewa, kudin da ake kashewa a ayyukan jigilar kaya ya kai kaso 14 cikin dari na GDPn kasar a watanni shida na farkon shekarar, inda ya ragu da kaso 0.1 cikin dari idan aka misalta da na rubu’in farko, kuma ya ragu da kashi 0.2 bisa dari a mizanin shekara-shekara. A cewar hukumar, wannan na nuni ne da sakamakon farko da aka...
A ƙoƙarinta na daƙile cin zarafin mata da yara, Ma’aikatar Harkokin Mata ta Jihar Gombe, ƙarƙashin jagorancin Kwamishina Asma’u Mohammed Iganus, ta gabatar da kundin dokar hana cin zarafi mata (GBV) ga Mai Martaba Sarkin Gombe, Alhaji Dokta Abubakar Shehu Abubakar III, domin samun goyon bayan sarakunan gargajiya wajen aiwatar da dokar a matakin ƙasa. Taron da aka gudanar a zauren Ƙaramar Hukumar Gombe ya samu halartar manyan jami’ai, sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma. LP za ta ceto Nijeriya daga halin da APC ta jefa ta — Nenadi Usman Rashin abinci mai gina jiki ya kashe yara 650 a Katsina — MSF A wajen taron, Kwamishinar ta jaddada cewa dokar na buƙatar goyon bayan al’umma gaba ɗaya, musamman sarakunan gargajiya,...
Shuwagabannin kungiyoyin musulmi a kasar Amurka sun fara daukar matakan tsaro a masallatai da wuraren taro da kuma makarantun musulci saboda yawan samun wasu magoya bayan yahudawa suna yawaita shiga irin wadannan wurare suna lalatasu. Shafin yanar gizo na labarai ‘ArabaNews” ya bayyana cewa a jihohin Texas da Califonia, masu goyon bayan yahudawan sun lalata masallatai da dama sun kuma sace abubuwa da dama a cikinsu. Edward Ahmed Mitchell, mataimakin sakataren kungiyar ‘ Council on American-Islamic Relations’ wata kungiyar kare hakkin musulmi a Amurka ya shaidawa Arabnew kan cewa tun bayan fara yaki a Gaza shekaru kimani biyu da suka gabata, musulmi a Amurka suka fara fuskantar sabon kiyayya daga wadanda basa son musulmi a kasar. Edword yace abu mafi...
A wani lamari makamancin haka da ya faru a Jihar Taraba, a watan Yuli, 2025, da misalin karfe 11:45 na rana, jami’an ‘yansanda sun amsa kiran da aka yi musu na satar mutane a hanyar Wukari, jim kadan a bayan jami’ar tarayya ta Wukari. Wata farar mota kirar Toyota bas dauke da fasinjoji 17 daga Enugu zuwa Yola, wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi musu kwanton bauna. Jami’an ‘yansanda tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro sun yi gaggawar kai farmaki inda lamarin ya faru. Da ganin tawagar jami’an tsaro na zuwa, sai masu garkuwar suka yi bar wadanda abin ya shafa suka gudu cikin daji. An ceto dukkan fasinjoji 17 ba...
A jiya Juma’a ne dai wanda ya isa birnin Beirut ya yi kira ga al’ummar kasar da su yi riko da hadin kan kasa da dukkanin bangarorinsu, sannan kuma su ci gaba da zage damtse wajen kalubalantar makiyar kasar Lebanon,musamman ‘yan sahayoniya. Goerge Ibrahim Abdullah wanda kuma ya gabatar da taron manema labaru a garinsu na “Qubyat’ ya kara da cewa; Kamar yadda mu ka kasance garkuwa mai bayar da kariya ga kasa, za mu ci gaba da zama haka’ sannan kuma ya kara da cewa: Saboda jinanen Shahidai kasar Lebanon za ta iya kalubalantar dukkanin hatsurran da take fuskanta.” Har ila yau, ya bayyana cewa;sojojin kasar Lebanon suna da mazajen da za su iya kare kasa,illa iyaka abinda ya...
Kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin bil adama ta Siriya ta tattara bayanan mutuwar mutane 1,400 a loardin Sweida na Siriya Siriya, Faransa da Amurka sun sanar da wata taswirar hadin gwiwa don tabbatar da zaman lafiya a Siriya, bayan tattaunawar da ba a taba ganin irinta ba a birnin Paris na Faransa, wadda ta hada ministan harkokin wajen gwamnatin rikon kwarya na Siriya Asaad al-Sheibani, da takwaransa na Faransa Jean-Noel Barrot da manzon Amurka na musamman a Siriya Tom Barrack. Sanarwar ta hadin gwiwa da aka fitar bayan taron na bangarorin uku, ta tabbatar da goyon bayan shirin mika mulki ga gwamnatin kasar Siriya da karfafa hadin kan al’umma, musamman a birnin Sweida da ke arewa maso...
Kwanan nan jam’iyyar PDP ta gudanar da taron kwamitin zartarwa karo na 100 da aka gudanar ranar 30 ga Yuni, PDP ta warware rikicin da ya dade yana ci mata tuwo a kwarya na batun mukamin sakataren jam’iyyar na kasa wanda ta tabbatar da Sanata Samuel Anyanwu a matsayin sakataren jam’iyyar. Duk da wannan warware batun, Atiku da wasu magoya bayansa sun fice daga jam’iyyar sakamakon rashin warware rikicin gida na jam’iyyar. A ranar 1 ga Yuli, Atiku da Peter Obi da Rotimi Amaechi da Nasir El-Rufai, da wasu sun kulla hadaka a karkashin jam’iyyar ADC, sun ce sun yi wannan hadakar ne domin kalubalantar APC a zaben 2027. A matsayin wani bangare na wannan yunkurin hadin gwiwa, sun nada...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya fara tattauna masifar da ta faru a Gaza tare da jaddada kawo karshen kisan kiyashi yanki Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da wani sabon zama domin tattauna batutuwan da suke faruwa a Gaza da kuma tabarbarewar al’amuran jin kai a yankin, inda ake ci gaba da yin kiraye-kirayen gaggauwa da kuma kira ga kasashen duniya da su dauki kwararan matakai na kawo karshen bala’in da ya biyo bayan yakin kisan kare dangi a yankin. Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira da a hanzarta dakatar da tilastawa al’ummar Gaza gudun hijira kamar yadda ta bukaci gwamnatin mamayar Isra’ila da ta ba da damar kai agajin jin kai ga al’ummar Zirin Gaza. Mataimakin babban...
Hukumar da ke Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) a ranar Laraba ta ce ta gano wani dakin ajiye kayayyaki da aka makare da lita 88,560 na sinadaran hada bama-bamai a Kano. Shugabar hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta bayyana hakan lokacin da take yi wa manema labarai jawabi a kofar rumbun da ke unguwar Kwakwaci a karamar hukumar Fagge da ke jihar. Mojisola, wacce Daraktan Bincike da Tabbatar da Bin Doka na hukumar, Dokta Martins Iluyumade ya wakilta, ta ce dakin na dauke ne da lita 60,000 na sinadarin sulphuric acid, sai kuma lita 28,560 na nitric acid da kuma wasu jarkoki 330 da aka riga aka rabar wa mutanen da ba a san ko su...
Yar wasan gaba ta Nijeriya, Chinwendu Alozie, ce ta tabbatar da nasara da kwallon da ta jefa kafin tashi daga wasan. Wannan nasara ta ba wa tawagar ta Justin Madugu damar kaiwa wasan ƙarshe na gasar. Yanzu haka, Super Falcons za su kara da ƙasar da za ta yi nasara tsakanin Moroko, wacce ke masaukin baki, da Ghana, a wasan da za a buga daga baya a yau Talata. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Alkaluma da aka fitar a hukumance sun nuna cewa, kasar Sin ta samar da sabbin guraben aikin yi miliyan 6.95 a rabin farko na bana, inda ta cimma kaso 58 bisa dari na burinta na shekara. Kakakin ma’aikatar kula da ma’aikata da walwalar al’umma ta kasar Sin Cui Pengcheng ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai a yau Talata, inda ya ce a watan Yuni, yawan wadanda ba su da aiki a birane ya tsaya kan kaso 5 bisa dari, watau bai sauya ba daga yadda ya kasance shekara 1 da ya wuce. Kasar Sin na da burin adadin marasa aikin yi ya tsaya kan kaso 5.5 a bana, tare da burin samar da guraben aikin yi sama...
Ko za ka iya fada wa masu karatu dan takaitaccen tarihinka? An haife ni a Unguwar Adakawa cikin birnin Kano, na yi makarantar firamare a Adakawa, daga nan kuma na tafi zuwa makarantar sakandire (Gwammaja One), bayan na sauke Alkur’ani, daga baya na tafi sai na wuce zuwa ‘School of Health Technology’ ta Kano. Bayan nan, sai kuma na tsunduma harkokin kasuwanci da siyasa, kazalika ina da mata biyu da kuma ‘ya’ya goma a halin yanzu. Kamar wane irin kasuwanci kake yi? Ina harkar takalma ‘yan Kofar Wambai, wadda ita ce sana’ar dana fara koya, sannan kuma ita ce sana’ar da dangina suke yi. Me ya ja hankalinka har ka tsunduma cikin masana’antar Kannywood? Tun ina yaro...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ana zargin wani direban tirela ya gudu da buhunan masara 463 da aka aike shi da su, bayan da ya bai wa ɗan rakiyarsa guba a cikin shayi a yankin Maraban Jos da ke Jihar Kaduna. Wani ɗan kasuwa da ke safarar hatsi daga Jihar Kano zuwa kamfanoni a sassa daban-daban na Nijeriya, Injiniya Jamilu Haruna, ya shaida wa Aminiya cewa direban da ya ɗora wa masara buhu 463 domin kaiwa kamfanin Olam da ke Ilorin a Jihar Kwara, ya gudu da kayan. “Kuɗin kayan sun kama Naira miliyan miliyan ashirin da ɗaya da dubu ɗari shida da tamanin da shida da ɗari huɗu. “Wallahi jarin nawa ke nan ɗungurungum na dora a motar,” in ji ɗan kasuwar, wanda ya...
Har ila yau, manufar ita ce; don rage yawan asarar da manoma ke tabkawa, bayan sun yi girbin farko da kuma jawo hankalin matasan kasar, domin su rungumi aikin na noma; musamman wanda za su yi, su samu riba. Kaddamar da Taraktocin na zuwa ne, daidai da lokacin da kasar ke ci gaba da fuskantar hauhawar farashin kayan abinci, wanda ya kai sama da kashi 30 cikin 100, duba da cewa; noman da ake yi a karkara na ci gaba yin karanci. Idan har an rabar da wadannan Taraktoci yadda ya dace tare da horar da manoman da za su amfana, an kuma tabbatar da ana bai wa Taraktocin kulawar da ta kamata da sayar da su cikin rahusa, hakan...
A daya bangaren kuma Fita zuwa wani yanki daban da ba naka a halin yanzu, yana da nasa fa’idar. Domin kuwa, na ziyarci wasu jihohi uku kwanan nan; wadanda labarai a kansu babu dadin ji. Jihohin su ne, Delta, Inugu da kuma Zamfara, wadanda galibi labaransu marasa dadi ne ta fuskar siyasa, ta’addanci da sauran munanan laifuka. Daga labarun da ake samu yau da kullum, za ka yi tsammanin cewa; wadannan jihohi tuni sun tashi daga aiki, amma daga ziyarar da na kai musu; na ga abubuwan ban mamaki, tsoratarwa da kuma hadari duk da ke dauke cikin wannan labari. Duk da cewa, kowace jiha akwai abubuwan da ta fi bai wa muhimmanci, su ma kamar sauran jihohin; suna...
Mai taimaka wa Sarkin Bayero kan harkokin yada labarai, Khalid Uba, ya shaida wa LEADERSHIP cewa magoya bayan Sarkin Bayero ba su da makamai. Uba, wanda ya zanta da wakilinmu ta wayar tarho, ya ci gaba da cewa babu wani daga cikin tawagar Sarkin Bayero da ke dauke da wani makami, sai dai an tilasta musu dakile harin. A cewarsa, wannan ba shi ne karo na farko da Sarkin Bayero ya taba bi ta wannan hanyar ba. “Bayan isowarmu daga gidan Dantata domin jaje, wasu matasa sun mamaye titin da duwatsu da makamai a Kofar Kudu. “Lokacin da muka isa Kofar Kudu, sai suka fara jifan mu, amma aka yi sa’a, mun yi nasarar fatattakar su zuwa cikin gida, kuma...
Sojojin kasar Yemen sun bada sanarwan kai hare-hare kan tashar jiragen sama na Bengurion na HKI tare da amfani da makamai masu linzami samfurin Balistic. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto majiyar sojojin Yemen na cewa, sun kai hare-hare da makamai masu linzami ka tashar jiragen sama na Ben gurion kuma zasu ci gaba da kai wadan nan hare-hare har zuwa dakatar da kissan kiyashin Falasdinawa a Gaza. Yahyah Saria kakakin sojojin kasar ta Yemen sun bayyana cewa, sojojinsa sun yi amfani da makamai masu linzami samfurin Bilistic maim suna Zulfikar wanda kuma ya fadi a kan tashar jiragen saman na Lod Airport kusa da Yafa ko tel’aviv. Ya ce makamin ya sami bararsa kuma ya sa...
Idris ya ce: “Ko da yake muna jaddada ‘yancin kowane ɗan Nijeriya na amfani da ‘yancin sa na shiga ko kafa ƙungiya da faɗar albarkacin baki kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, yana da muhimmanci a fayyace cewa gwamnatin Shugaba Tinubu ba za ta bari harkokin siyasa ko hayaniyar ‘yan siyasa su karkatar da ita daga aikin da ta sa a gaba ba.” Ministan ya ce ko da yake ana ta raɗe-raɗi a kafafen yaɗa labarai game da sabuwar haɗakar siyasar adawa da ke tasowa, Shugaban Ƙasa Tinubu yana ci gaba da maida hankali ne kan Shirin Sabunta Fata domin ciyar da ƙasa gaba. “Hayaniya a kafafen yaɗa labarai kan fitowar wata sabuwar haɗakar siyasa abin fahimta...
Kakakin dakarun rundunar Izzudden-Qassam ya bayyan cewa: ‘Yan gwagwarmaya sun tarwatsa wani mutum-mutumi da sojojin mamayar Isra’ila suka makare da harsashai dauke da makami mai linzami a lokacin da ake shirya shi A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, kakakin rundunar sojin Qassam bangaren sojin kungiyar Hamas Abu Obeida, ya yi bayyana cewa: ‘yan gwagwarmaya sun nuna jarumtaka wajen tunkarar makircin ‘yan mamaya mai sarkakiya a gwagwarmayar Beit Hanoun, inda suka kara raunana martabar sojojin mamaya tare da rusa makircinsu.. Kakakin rundunar sojin Qassam Abu Obeida, ya kara da cewa: Hadadden aikin na Beit Hanoun wani karin mataki ne da ‘yan gwagawarmaya suka dauka na raunana makiya tare da rusa martabar sojojin mamayar Isra’ila. Yana...
Wannan matakin ya biyo bayan shawarar Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na ASUU wanda ya amince da tsarin “Ba Albashi, Ba Aiki” saboda yawan jinkirin biyan albashi da suke fuskanta. ASUU ta ɗora laifin hakan kan Ofishin Akanta-Janar na Tarayya. Shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa Chris Piwuna, ya bayyana a ranar Litinin cewa gwamnatin na nuna halin ko-in-kula kan batun. Ya ce duk da yawan ganawa da jami’an gwamnati, malamai na fuskantar jinkirin albashi ba tare da wani dalili ba. “Muna so mu yi aiki, amma ba za mu iya ba saboda ba su ba mu damar yin haka ba. Wannan aiki ne da aka yi da gangan. Matsalar ba daga wajen tsarin biyan albashi ba ne, matsalar tana wajen...
Shugaban Kungiyar Harka Islamia a tarayyar Najeriya Sheikh Irahim Zakzaky ya taya mutanen kasar murna saboda nasarar da suka samu kan HKI da kuma Amurka a yakin kwanaki 12 a cikin watan da ya gabata. Ya ce wannan nasarar bata takaita da mutanen kasar Iran kadai ba , hada har da al-ummar Musulmi da kuma da kuma masu sun yenci a ko ina suke. Ya kuma yaba da yadda gikuwan nmalamai na kasar Iran suka sami nasarar kare kasar daga mafi yawan hare-haren HKI a kan kasar. Ya bayyana cewa Iran ta sami nasara a kan kasashen yamma da makamai wadanda suka fi nasu karfi da inganci, har’ila yau sun sami nasara a kan ma;aikatan yahudawan da suke taimaka masu...
Kasar China ta maida martani ga takunkuman tattalin arziki na wasu kayakin kiwon lafiya wadanda tarayyar Turai da dorta maya. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto majiyar kasar ta Chaina na fadar haka ta kuma kara da cewa gwargwadon takunkuman da suka dorawa kasar gwargwadon maida martanin kasar ta China. Labarin ya kara da cewa wannan haramcin ba zai shafi kamfanonin turai da suke samar da kayakin aikin kiwo lafiya a cikin kasar China ba. A cikin watan Yunin da ya gabata ne kungiyarn EU ta hana gwamnatocin kasashe kungiyar sayan kayakin aikin likita fiye da dalar Amurka miliyon 5 tare da bukatar kasar china ta daina nuna bambanci a cikin ahrkokin kasuwanci da ke tsakaninsu.
Kungiyar Kananan Hukumomin Nijeriya (ALGON) reshen Jihar Kaduna, ta mika sakon taya murna ga Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, bisa lambar karramawa ta CON da shugaban kasa ya yi masa ado da ita, wacce ke matsayin wata alamar girmamawa a Jamhuriyyar Nijeriya ta Hudu. Wannan karramawar, wata alama ce a sarari ga sadaukarwar mai girma gwamna, da gagarumin nasarorin da ya samu a hukumance, da kuma jagoranci mai tsari da yake kai domin ci gaba da tsara tafiyar dimokuradiyyar kasa. Dalilin Kwararru Na Bukatar Kafa Cibiyoyin Bincike Kan Nau’ikan Dabbobi A Nijeriya Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (8) Wannan na kunshe ne a cikin wata takarda dauke da sa hannun sakataren yada labarai...
“Wannan aiki ne, wanda za a iya cewa; tamkar a yanzu ne muka fara dora damba a kansa”, a cewar shugaban. Haka zalika, shugaban ya kuma sanar da wadanda suka halaccin taron kaddamar da shirin tabbacin cewa; wadannan ayyuka na noman zamani, za su kara taimakawa wajen kara samar da ayyuka a fannin aikin noma sama da 2,000. Ya ci gaba da cewa, kayan za su kuma taimaka wajen kara ayyukan masana’antun kasar da samar da damar gudanar da yin bita da kuma kwararrun kayan aikin noma 9,000. Shugaban ya jaddada muhimmancin yin amfani da kayan aikin noma na zamani, wanda hakan zai taimaka wa manoman wannan kasa. Har ila yau, ya kuma yi nuni da cewa; kaddamar da wannan...
An fara tuhumar tsohon ɗan ƙwallon Arsenal, Thomas Partey da laifuka biyar da suka haɗa da fyaɗe da kuma cin zarafi, an bayar da rahoton cewa ya aikata laifukan ne a tsakanin shekarar 2021-2022, cewar ‘yansandan Birtaniyya. Daga cikin laifukan akwai fyaɗe akan wasu mata uku waɗanda ake tuhumarsa da cin zarafinsu ta hanyar tursasawa kan mace ta farko da ta biyu sai kuma laifin lalata da mace ta uku. ‘Yansanda a ƙasar Birtaniya sun ce ya kamata Thomas ya bayyana a Kotun Majistare ta Westminster a ranar 5 ga watan Agusta, tuhumar ta biyo bayan binciken da jami’an tsaro suka gudanar, wanda ya fara a watan Fabrairun 2022 bayan da ‘yansanda sun samu rahoton fyaɗen. Partey dai ya bar...
Wasu ’yan bindiga sun kai hari kan masu dawowa daga binne gawa a kauyen Rim na jihar Filato, inda suka datse wa daya daga cikin matasan da ke wurin hannu daya. Bayanai sun nuna cewa mutanen na kan hanyarsu ce ta dawowa daga bikin binne wani mutum ne a kauyen Bachit da ke da makwabtaka da su inda suka yi arba da maharan wadanda suka tare su suka bude musu wuta, sannan suka datse wa daya daga cikin mutanen hannu daya. Rasha ta amince da gwamnatin Taliban a Afghanistan Ambaliya da iska sun rushe gidaje 171 a watanni biyu a Gombe – SEMA Wani Hadimin Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, mai suna Timothy Dantong, wanda yake cikin mutanen da suke dawowa...
Yayin taron manema labarai na yau Alhamis, kakakin ma’aikatar cinikayyar kasar Sin He Yongqian, ta ce ba su da wata masaniya, game da cewa shugaban Amurka na shirin jagorantar wata tawagar ‘yan kasuwa zuwa kasar Sin. Sai dai kuma duk da hakan, a cewarta har kullum matsayar Sin a bayyane take, cewa tana fatan ita da Amurka za su bi turba guda, kuma karkashin jagorancin yarjejeniyoyin da shugabannin kasashen biyu suka amince da su, za su rungumi ka’idojin mutunta juna, da zama cikin lumana, da gudanar da hadin gwiwar cimma moriyar juna, ta yadda za a ci gaba da cimma matsaya guda. Har ila yau, sassan biyu za su kai ga rage sabani, da karfafa hadin gwiwarsu, da bunkasa alakar...
Ministan tsaron cikin gida na HKI Itamar Ben-Gvir ya yi kira ga babban murya kan cewa dole ne HKI ta mamaye dukka zirin gaza ta kuma kori falasdinawa da suke cikinsa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalato Ben Gafir yana fadar haka a jiya ya kuma kara da cewa mamaye gaza da kuma yankin yamma da kogin Jordan da kuma shi ne kawai zai sa a samar da kasar yahudawan zalla inda babu ba falasdine ko guda a yankunan guda biyu. Kiran nasa dai ya gamu da maida martani daga yan siyasa a ciki da wajen HKI. Tun shekara ta 2023 ne gwamnatin HKI take son mamyar zirin gaza ta kuma kori Falasdiwa a yankin. Bayan yaklin...
Iran ta nuna makamai masu linzami wadanda suka bude kofofin jahannama kan ‘yan sahayoniyya A martanin da gwamnatin yahudawan sahayoniyya suka kai wa Iran, sojojin Iran da dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar sun nuna karfinsu na soji a matsayin wani bangare na “Alkawarin Gaskiya na 3”, inda suka harba daruruwan makamai masu linzami na ballistic da hypersonic. A wani bangare na wannan harin na ramuwar gayya, Iran ta kai jerin hare-hare na hadin gwiwa, wanda kaso mafi tsoka na makamai masu linzami kamar Emad, Ghadr, Fattah 1, Sejjil da Khaybar. A halin yanzu rahotonni da hotuna daga haramtacciyar kasar Isra’ila suna kara fitowa kan yadda makamai masu linzamin Iran suka tarwatsa wurare masu muhimmanci na gwamnatin haramtacciyar...
Lokaci bai kura wa sauran kasashe na koyi da Sin ba. Sun gwada aron tsare-tsaren kasashen yamma, kuma babu inda hakan ya kai su. Don haka za su iya tsara irin dabarun da ya dace da yanayinsu domin kyautata makomar kasashensu da al’ummominsu. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hedikwatar Tsaron Nijeriya (DHQ) ta ce dakarun tsaro na rundunar “Operation Hadin kai” sun kashe mayaƙan Boko Haram 10 yayin wata arangama a yankin Rann zuwa Gamboru Ngala da ke Jihar Borno. Daraktan watsa labarai na hedikwatar tsaron, Manjo Janar Markus Kangye ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin. Gwamnan Bauchi zai ƙirƙiro sabbin masarautu Sai bayan Magariba za a yi wa Dantata jana’iza a Madina Manjo Janar Markus Kangye ya ce aikin kawar da ‘yan ta’addan da aka aiwatar ranar Litinin ya faru ne bayan rundunar ta lashi takobin kawar da sauran ‘yan Boko Haram/ISWAP da ke ɓuya a yankin Tafkin Chadi. “Arangamar ta faru ne a lokacin wani aiki na haɗaka wanda aka...
Tsohon Gwamnan Anambra, Peter Obi ya ce zai yi takarar shugabancin Nijeriya a 2027 domin ba zai shiga duk wata yarjejeniyar haɗakar takara da kowa ba. Obi wanda ya yi takarar shugabancin Nijeriya a Zaben 2023 a karkashin inuwar jam’iyyar Labour (LP), ya tabbatar wa magoya bayansa cewa babu gudu babu ja da baya dangane da takararsa a babban zaɓen kasar na gaba. An sanya dokar hana fita a Kaduna An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata zuwa Talata Sai dai ya ce idan har akwai wata yarjejeniya da zai kulla, ba za ta wuce wacce za ta ba shi damar zama shugaban ƙasa na wa’adi daya ba, sannan ya miƙa wa shugaba na gaba mulki a ranar 28 ga watan Mayun...
Masu bincike sun gano cewa sojojin HKI sun kashe Falasdinawa akalla 100,000 tun bayan fara yakin tufanul Aksa a ranar 7 ga watan Octoban shekara 2023. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kan cewa farfesa Michael Spagat da kuma Khalil Shikaki Bafalasdine masanin masanin fasahar siyasa a Jami’ar London na kasar Burtania suka jagoranci bincike wanda ya kai ga fitar da wannan sakamakon. Labarin ya kara da cewa masu binciken sun kiyasta mutane a gidaje 2000 a birnin Gaza kadai wanda falasdinawa kimani 10,000 suke rayuwa, sannan suka yi lissafi suka kaim ga wannan sakamakon. Bincike ya kara da cewa daga watan jenerun shekara ta 2025 falasdinawa 75,200 sojojin yahudawan suka kashe da makamai, sannan wasu kimani...
Alhaji Ahmad Manga ya ce, “an ɗauki matakin ne da haɗin gwiwar gwamnatin jiha da gwamnatin tarayya”. Jami’an CPG na Zamfara sun kuma samu goyon bayan dakarun Civilian JTF na jihar Borno, inda suka ƙaddamar da harin a-yi-ta-ta-ƙare na bazata ga maɓoyar ta Bello Turji. Gwamnatin jihar Zamfara ta ce artabun na ranar Litinin da haɗin gwiwar jami’an tsaro suka fara da ɗan fashin dajin tamkar buɗe sabuwar ƙofar ci gaba da yaƙarsa ne. “Alhamdulillahi an tarar da shi har gida nai inda ba a taɓa zuwa ba, kuma ya ga cewa ana iyawa, kuma an isko shi,” inji Ahmad Manga. Ya ƙara da cewa “an kuma buga wuta, an yi nasarori da dama inda aka...
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Monaco ta ƙulla yarjejeniyar kaka biyu da tsohon ɗan wasan Manchester United da kuma Juventus, Paul Pogba. Pogba mai shekara 32 ya koma a matakin wanda bai da kwantiragi tun daga watan Nuwamba, bayan da Juventus ta soke yarjejeniyar da ke tsakaninsu. Nijeriya ce kasa ta 12 mafi talauci a duniya — IMF Yadda na hannun daman ’Yar’Adua ya yi tuggun hana ni zama shugaban ƙasa — Jonathan A watan Maris ɗin bara ne aka dakatar da Pogba shekara huɗu, sakamakon zargin shan abubuwan ƙara kuzarin jiki. Amma yanzu zai koma taka leda bayan da aka rage hukuncin zuwa wata, sakamakon ɗaukaka kara a watan Oktoba. Ya fara taka leda a Manchester United daga nan ya...
Wani mummunan hatsari ya afku a Masar inda ‘yan mata 18 suka mutu sakamakon fashewar wata motar dakon mai Wani mummunan hatsarin mota ya afku a kasar Masar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar wasu mata 18 da direban bas a kan hanyarsu ta zuwa gonar inabin domin girbin inabin. Hatsarin ya afku ne a ranar Juma’a a kan hanyar yankin da ke gundumar Menoufia, bayan wata babbar mota ta yi karo da motar bas din da ke dauke da ‘yan matan 18. Dukkansu sun fito ne daga kauye daya, Kafr El-Sanabseh, a gundumar Menoufia, kuma dukkansu ‘yan kasa da shekara 21 ne. Hotunan wannan mummunan hatsarin da aka yi ta yawo da su a shafukan sada zumunta, sun nuna...
Masana da jami’ai a Nijeriya, sun yaba wa ci gaba na a-zo-a-gani da karin kuzarin da ake samu a hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Nijeriya, suna masu bayyana kokarin da aka yi zuwa yanzu a hadin gwiwar bangarorin biyu a tafarkin zamanantar da kansu. Masanan sun bayyana haka ne yayin taro na biyu na bayan taron FOCAC da aka yi ranar Alhamis a Abuja, babban birnin kasar. Cibiyar nazarin dangantakar Sin da Afrika dake Nijeriya ce ta shirya taron mai taken “Hada Hannu Wajen Zamanantar da Sin da Afrika da cimma shirye-shirye 10 na Hadin Gwiwa a Cikin Al’ummar Sin da Afrika mai Makoma ta Bai Daya a Ko da Yaushe.” Da yake jawabi, daraktan cibiyar nazarin Sheriff Ghali...

Jiniyoyin Gargadi Sun Tashi A HKI A Lokacinda Mayakan Ansarallah Suka Cilla Makamai Masu Linzami Kan Kasar
An ji karar jiniyoyin gargadi a wurare da dama a HKI suna tashi bayan sun hango malamai masu linzami wadanda sojojin Yemen suka cilla daga kasar zuwa haramtacciyar kasar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kafafen yana labaran yahudawan na cewa sun yi shirin kakkabo makaman kafin su isa. Amma basu bada rahoton yawan barnan da makamai suka yi ba bayan shigowarsu haramtacciyar kasar. Yahudawan sun bayyana cewa an ji karar jiniyar gargadi a yankunan Beersheba, Dimona da kuma garuruwan da suke kewaye da su a safiyar yau Asabar. Majiyar sojojin kasar Yemen sun bayyana cewa sun cilla makaman kan haramtacciyar kasar Isra’ila ne saboda ci gaba da kissan kiyashin da take a zirin gaza.
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Doctor Zainab Muhammad na daya daga cikin mata a Arewacin Najeriya da ta jajirce tare da kudirin cika burinta na karantar kimiyya duk da kalubalen da wasu matan dake yankin Arewa suke bayyanawa suna fuskanta wurin karantar fannin. Doctor Zainab ba kimiyya kawai ta karanta ba, ta karanci daya daga cikin kimiyyoyin da ake ganin sun fi kowanne wahala wanda a mafi yawan lokuta ba mata kadai ba har da mazan ma na kauracewa wannan karatun. Zainab Kwararriyar likita ce wacce ta shahara wurin kula da marasa lafiya a asibitoci. NAJERIYA A YAU: Yadda ‘Yan Najeriya Za Su Kula Da Lafiyar Jikin Su DAGA LARABA: Ko Najeriya Na Da Kudin Renon Sabbin Jihohi?...
Yawan gawarwakin da aka tsinta bayan harin duk na mabiyansa ne. Ɗaya daga cikin su, Bashari Maniya, wanda tsohon ɗan bindiga ne da ya ce ya tuba kuma ya fara taimaka wa jami’an tsaro, shi ma ya mutu bayan motar da yake ciki ta faɗa rami mai zurfi. Manga ya bayyana cewa ba da bindiga aka kashe Maniya ba, saɓanin jita-jitar da ke yawo. “Sabuwar mota ce, kuma ba su san dajin sosai ba. Yayin da suke gudu a cikin daji, sai suka faɗa cikin wani rami mai zurfi. Motar ta kife, kuma an kasa ciro ta cikin sauƙi,” in ji shi. Ya ce lokacin da aka zo taimaka musu, an same su a cikin motar a sume. Motar ba...

Gwamnan Jigawa Ya Kaddamar Da Rumbun Sauki Don Sayar Wa Ma’aikata Kayayyakin Abinci A Farashi Mai Rahusa A Sakkwato
Tun da farko, Gwamna Aliyu ya ce, gwamnatinsa ta bullo da shirin ne domin ta saukaka farashi da kashi 20 ta hanyar saukar da farashin kayan abinci kasa warwas. Gwamnan ya ce, an tsara shrin ne domin saukakawa ma’aikatan jiha, na kananan hukumomi da masu karbar fansho ta hanyar samar da nau’ukan kayan abinci kamar shinkafa, gero, alkama, masara, dawa, man girki da taliya a cikin farashi mafi sauki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban Amurka Donald Trump ya soki Isra’ila da Iran, bayan zargin ƙasashen biyu da karya yarjejeniyar tsagaita wuta da aka ƙulla. Lamarin na zuwa ne bayan ɓullar rahoton kai wa juna hari daga dukkan ƙasashen biyu, duk da ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta ’yan sa’o’in da suka gabata. Sarkin Musulmi ya ba da umarnin fara duban watan Muharram An tura ’yan China 6 kurkuku kan laifin ta’addanci a Nijeriya Trump ya ce ƙasashen sun daɗe suna faɗa da juna, kuma a wannan mataki ana iya cewa ba su ma san abin da suke yi ba. Ya ce: “Ba abin da muke so ke nan ba, ina tabbatar muku cewa ina fushi da abin da suka aikata.” Shugaba Trump ne mutum na...
Fadar Shugaban Kasa ta ce shugaba Bola Tinubu zai zabi wanda zai yi masa takarar mataimaki a zaben 2027 a hukumance ne kawai bayan a kammala babban taron jam’iyyar APC a 2026. Kakakin shugaban, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawarsa da jaridar Daily Trust a ranar Alhamis. Da yake martani kan dalilin da ya sa fadar shugaban ta yi shiru kan zargin cewa Tinubu na son canza mataimaki a 2027 musamman la’akari da yadda ’yan jam’iyyar ke ta nuna goyon bayansu ga shugaban shi kadai, Onanuga ya ce hakan ba gaskiya ba ne. Nan da mako biyu za mu yanke shawara kan shigar wa Isra’ila yaƙi — Trump Muna shawartar Trump kada ya shiga yaƙin Iran da...
A ci gaba da ƙoƙarinta na tabbatar da kyawawan halaye da kuma samar da zaman lafiya a tsakanin al’umma, Hukumar Hisbah ta Jihar Yobe ta lalata katan 243 na barasa da galan 100 na barasa da aka haɗa a gida, da aka fi sani da sukudaye. A wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na Hukumar, Adamu Muhammad ya sanya wa hannu, ta ce an lalata barasa a Damaturu, a wani mataki na aiwatar da dokar hana sha da kayan rarraba barasa a jihar. Guguwar ruwan sama ta yi ɓarna a Kwalejin Kimiyya da Fasaha a Kogi Tinubu na ƙaddamar da wasu ayyuka a Jihar Kaduna Shugaban Hukumar Hisbah na jihar, Dokta Yahuza Hamza Abubakar ne ya bayyana cewa aikin ya...
Kafin wannan, yana riƙe da sarautar Walin Gaya, wanda aka ba shi lokacin da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta ƙirƙiri sabbin masarautu. Masarautar ta ce an ɗauki wannan matakin ne domin kare mutunci da ƙimar sarautun gargajiya bisa tsarin da aka gada. Sai dai matakin ya zo ne mako guda bayan Alhaji Usman ya soki gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf, kan zarginta da karɓar bashi na dala miliyan 6.6. Gwamnatin Kano ta musanta zarge-zargen, tana mai cewa ba gaskiya ba ne face tsantsar siyasa. Ko da yake masarautar ba ta danganta ƙwace sarautar da wannan suka da Alhaji Usman ya yi ba, lokacin da aka ɗauki matakin ya haifar da zargi da cece-kuce a tsakanin jama’a. Daga kanmu, magana...
Ta hanyar inganta manufar yafe harajin kwastam a kai a kai, kasar Sin ta samar da yanayin kasuwanci mai karko a kasashen Afirka. Bugu da kari, kasar Sin tana kallon manufofinta na rangwame a matsayin matakan tabbatar da burin samun ci gaba, inda take kokarin kyautata tsarin cinikayyar waje na kasashen Afirka, da kuma ba da goyon baya wajen raya masana’antu, da habaka tsare-tsaren tattalin arziki a Afirka. Dalilin da ya sa kasar Sin ke kokarin tabbatar da ci gabanta da kasashen Afirka na bai daya, shi ne domin ra’ayinta game da dangantakar dake tsakaninta da Afirka, wato al’ummar Sin da Afirka suna da makomar bai daya a nan gaba. A ganin kasar Sin, ita da Afirka suna da tarihi...
Borussia Dortmund ta soma buɗe wasanninta na gasar FIFA Club World Cup da canjaras a karon-battar da ta yi da kungiyar Fluminense ta Brazil a ranar Talata. Ana dai ganin babbar kungiyar da ta zama gagarabadau a Rio de Janeiro Fluminense a matsayin mafi hatsari a rukunin F wanda ya kunshi har da kungiyar Ulsan HD ta Koriya ta Kudu. Buni ya bai wa manoma 1,000 tallafin aikin gona Amurka na iya kashe jagoran addini na Iran don mun san inda yake — Trump An dai rika kai wa juna hari a yayin wasan da suka barje gumi a filin wasa na Metlife da ke East Rutherford a wajen birnin New York, sai dai mai tsaron ragar Dortmund, Gregor Kobel...
Alhazai 442 sun tsallake rijiya da baya, bayan jirgin da ya ɗauko su bayan sun kammala aikin Hajjin bana ya samu sakon cewa an dasa bom a cikinsa a yayin da yake sararin samaniya a ƙasa Indonesiya. A ranar Talata ne jirgin, mallakin kamfanin Saudia Air, ya yi saukar gaggawa a birnin Jakarta babban birnin ƙasar Indonesiya, bayan da ya ɗauko alhazan da daga birnin Jidda na ƙasar Saudiyya. ’Yan sanda ƙasar Indonesiya sun ce an yi nasarar fitar da ɗauƙacin fasinjojin jirgin su 442 a filin jirgi da ke lardin Sumatra ta Arewa. Ma’aikatar Sufuri ta ƙasar Indonesiya ta ce jirgin ya yi saukar gaggawa ne bayan samun wani saƙon imel cewa an sanya bom a jirgi. Sarki ya...
“Na ce Shettima ɗanmu ne, kuma muna alfahari da shi. Na kuma gode wa Tinubu bisa yadda ya bai wa ‘yan Arewa maso Gabas muƙamai masu gwaɓi kafin na nemi a mara masa baya,” in ji Salihu. A lokacin taron, wasu matasa sun kusan kai masa hari, amma ya ce hakan ya faru ne saboda wasu ba su fahimci abin da ya yi ba. Ya kuma jaddada cewa a tsarin jam’iyya, mutum ɗaya ne kawai ake zaɓa a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a lokacin zaɓen fidda gwani, kuma shi ne ke da ‘yancin zaɓar mataimakinsa. “Ba a daidaita tikitin shugaba da mataimaki a zaɓen fidda gwani. Ɗan takara kawai ake zaɓa, kuma yana da ‘yancin zaɓar wanda zai mara...
Sarkin yankin Oke Agbe a Jihar Ondo ya ci Musulmi tara, tare da barazanar koran su da kuma haramta yin addinin Musulunci a garinsa bayan da wasu dodanni suka kai hari a wani masallaci da gidan limami. Aminiya ta samu rahoto cewa, wasu dodanni sun kai hari a masallaci da gidan wani limami, suka lakaɗa wa matansa da ’ya’yansa duka a yankin Oke Agbe, da ke shiyyar Akoko a Ƙaramar Hukumar Akoko ta Arewa a Jihar Ondo Jihar Ondo. Ƙungiyar Kare Haƙƙin Musulmi (MURIC), ta bayyana cewa, “Basaraken yankin ya yi Musulmin tara da aka ci zalinsu tara, saboda sun yi ihu tare da zagin dodannin, maimakon su riƙa yin kuka suna roƙon dodannin. “Basaraken ya umarci matan limamin su...
Jam’iyyar APC a Yankin Sanatan Kaduna ta Arewa (Zone 1) ta bayyana goyon bayanta ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Gwamnan Jihar Kaduna Uba Sani, da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, don sake tsayawa takara a wa’adin mulki na biyu. An yanke wannan shawara ne a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Jami’ar Tarayya ta Ilimi da ke Zaria, inda tsoffin gwamnoni, ministoci, ‘yan majalisa, da kwamishinoni da shugabannin hukumomi na tarayya da jiha suka halarta. EFCC Ta Kama Mutane 11 Kan Zargi Aikata Damfara A Intanet A Kaduna An Karrama Dalibar Kaduna Da Ta Zo Ta Biyu A Gasar Karatun Alkur’ani Ta Duniya Masu ruwa da tsakin sun jero nasarorin da gwamnati mai ci ƙarƙashin APC...
Wasu Hare-haren da gwamnatin Isra’ila ta kai ya haddasa gobara a wasu matatun mai a lardin Bushehr da ke kudancin kasar Iran. Gobarar ta tashi ne a wurin a ranar Asabar bayan da wasu kananan jiragen yakin Isra’ila guda biyu suka kai hare-hare a kan kayayyakin sarrafa iskar gas da ke yankin kudancin Pars. Hare-haren sun yi haddassa fashe fashe a matatar iskar gas ta Fajr-e Jam, daya daga cikin mafi girma a Iran, da kuma wata karamar matatar mai a mataki na 14 na tashar iskar gas ta Kudu Pars. Har yanzu ba a fitar da kiyasin barnar a hukumance ba. Bayan gobarar, ma’aikatar mai ta Iran ta fitar da wata sanarwa inda ta tabbatar da harin. Sanarwar ta...
Farashin Man Fetur ya tashi a kasuwar duniya bayan harin da Isra’ila ta kai wa Iran, lamarin da ya tayar da hankalin masu zuba jari. Ana fargabar cewa rikicin da ke ƙara taɓarɓarewa tsakanin ƙasashen biyu zai iya kawo tangarɗa wajen samar da man fetur daga yankin Gabas ta Tsakiya. An kashe masu garkuwa da mutane da kuɓutar da wasu Ambaliyar Mokwa: An sake gano gawar mutum bayan kwanaki 8 Wani muhimmin wurin da ake safarar man fetur na duniya, wato mashigar Hormuz da ke kusa da Iran na da matuƙar tasiri, domin kashi ɗaya cikin biyar na dukkanin man da ake fitarwa daga nan ne ake bi da shi. Amma duk da haka, kasuwannin hannun jari sun fuskanci faɗuwar...
Kwanaki takwas bayan wata mummunar ambaliyar ruwa da ta mamaye garin Mokwa, hedikwatar Ƙaramar hukumar Mokwa a Jihar Neja, an gano gawar mutum ɗaya daga cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su. Mazauna garin sun shaida wa Daily Trust cewa, an tsinci gawar ne a ranar Alhamis a wata gona da ke kan hanyar wucewa kusa da wani wuri da aka fi sani da ‘dam’. Ambaliya: Gwamnatin Kano ta fara tsaftace magudanan ruwa Abin da muke da shi a Najeriya ba cikakkiyar dimokuraɗiyya ba ce — Fayemi A cewar shaidun gani da ido, an kasa tantance wanda abin ya shafa saboda gawar ta lalace. An binne shi ne a inda aka gano gawarsa. Wata mazauniyar yankin mai suna Tswata Mai...
Kwanaki takwas bayan wata mummunar ambaliyar ruwa da ta mamaye garin Mokwa, hedikwatar Ƙaramar hukumar Mokwa a Jihar Neja, an gano gawar mutum ɗaya daga cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su. Mazauna garin sun shaida wa Daily Trust cewa, an tsinci gawar ne a ranar Alhamis a wata gona da ke kan hanyar wucewa kusa da wani wuri da aka fi sani da ‘dam’. Ambaliya: Gwamnatin Kano ta fara tsaftace magudanan ruwa Abin da muke da shi a Najeriya ba cikakkiyar dimokuraɗiyya ba ce — Fayemi A cewar shaidun gani da ido, an kasa tantance wanda abin ya shafa saboda gawar ta lalace. An binne shi ne a inda aka gano gawarsa. Wata mazauniyar yankin mai suna Tswata Mai...
Ya ce Jihar Kurus Ribas ita ce ta farko a yankin kudu da ta shiga a dama da ita a harkar noman alkama, lamarin da ke nuni da gayar nasara wajen samar da abinci a kowani sassa na kasar nan. Kyari ya kara da cewa shirin rabar da takin zamani ya taimaka wajen bunkasa samar da shinkafa zuwa tan 58,000, lamarin da ya bai wa gwamnatin tarayya sanya tallafi a bangaren rabar da shinkafa ga jihohin da ambaliyar ruwa ta shafa. Ministan ya ce akwai bukatar kare masu amfani da kuma kayan da ake nomawa, “kaso 80 cikin 100 na abincinmu manoman cikin gida ne suka samar da su.” A daidai gabar da ake hasashen adadin ‘yan Nijeriya zai kai...
Kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran Manjo Janar Hussain Salami ya fada a yau Alhamis cewa; Abokan gaba suna yi mana barazana da yaki, sannan ya tabbatar da cewa a shirye suke su fuskanci duk abinda zai faru. Manjo janar Salami wanda ya gabatar da jawabi ga taron dakarun sa-kai na “Basiji a nan Tehran ya kuma kara da cewa; Babu wani wuri komai zurfi da nisansa a HKI da ba mu tsinkayowa, idan kuwa aka ba mu umarni to za su yi nasara, mu Sanya abokin gaba ya yi nadama. A gefe daya ministan tsaron Iran ya bayyana cewa; Duk wani hari da ake tunanin kawo wa Iran, to kuwa zai fuskanci mayar da martani mai...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ma’aikatar leken asiri ta kasar Iran ta fidda farkon bayanan sirra wanda ta samo daga HKI wadanda kuma suke tabbatar da dangantakar da hukumar IAEA take da shi da HKI da kuma sauran kasashen yamma da hukumomin tsaronsu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran tace a cikin bayanan da ma’aikatar ta wallafa ya zuwa yanzu ya nuna irin yadda hukumar IAEA take mika bayanan da ta samu daga cibiyoyin Nukliya na kasar Iran ga HKI. Wanda ya kaiga kissan masana da kwararrun a fasahar makamacin Nukliya a baya. Bayanan sun bayyana yadda hukumar ta IAEA take mikawa dukkan takardun sirri na shirin makamashin nukliya na kasar Iran ga makiyanta don su yi aiki a kai. Banda HKI wadannan bayanan...
Gwamnan Kebbi, Dakta Nasir Idris (Ƙauran Gwandu) ya jajanta wa al’ummar kasuwar katako ta bayan kara da ke Birnin Kebbi bisa ibtila’in gobara da ta auka musu. Mataimakin Gwamnan, Sanata Umar Abubakar Tafida ne ya wakilci gwamnan a yayin ziyarar jaje da ya kai wa ’yan kasuwar da abin ya shafa. A saurari sauyin da za mu yi wa ɓangaren man fetur a Nijeriya — Dangote NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Magance Matsalar Kwacen Waya A lokacin da ya zagaya domin duba irin ɓarnar da wutar ta yi a kasuwar, Mataimakin Gwamna ya yi kira da su mayar da lamarin ga Allah da kuma ɗaukar wannan ibtila’in a matsayin jarabawa daga gare Shi. Haka kuma, ya miƙa wa ’yan kasuwar gudumawar...
Majalisar koli ta tsaron kasar Iran ta bayyana cewa jerin wuraren da zata kaiwa hare hare a HKI a duk wani yakin da zata taso tsakanin kasshen biyu, suna hannu. Daga ciki har da ciboyoyin Nukliyar kasar wadanda ta boye su. Tashar talabjin ta Presstv a nann Tehran ta nakalto majalisar ta na fadar haka a jiya Litinin, ta kuma kara da cewa ta kara samun bayanai masu muhimmanci a wannan fagen, bayan bayanan leken asirin da ta samu a cikin yan kwanakin da sukka gabata. Labarin ya kara da cewa a halin yanzu sojojin JMI suna cikin shiri fiye da na ko wani lokaci, don maida martani ga makiya. Tace a halin yanzu jerin wuraren da sojojin Iran zasu...
Alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar a yau Litinin 9 ga wata sun nuna cewa, a watan Mayun bana, ma’aunin farashin kayayyakin masarufi, watau CPI na kasar, ya ragu da kaso 0.1 bisa dari, bisa na makamancin lokacin bara, kuma farashin makamashi ya zama babban dalilin da ya haifar da raguwar. Kana, ma’aunin farashin sarrafa kaya na cikin gida, watau PPI shi ma ya ragu da kaso 3.3 bisa dari, bisa na makamancin lokacin bara, kuma adadin ya ragu da kaso 0.4 bisa dari, idan aka kwatanta da na watan Afrilun bana. Duk da cewa ma’aunin CPI na watan Mayu ya ragu kadan, amma farashin kayayyaki a wasu bangarori ya canza, al’amarin da ya shaida rawar da...

Ministan Harkokin Kiwon Lafiya Na Iran Ya Bukaci A Yawaita Sayar Da Kayakin Likita Zuwa Kasashen Waje
Minitan kiwon lafiya na kasar Iran ya bukaci kamfanonin da suke kera kayalin kiwon lafiya da kuma aikin likita so kara yawan kayakin da ake sayarwa zuwa kasashen waje. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Mohammad Reza Zafarkhan yana wannan kiran a jawabin da ya gabatar a taron bude kasuwar baje koli na kayalin aikin likita da kuma kiwon lafiya a nan Tehran. Ministan ya kara da ce wa duk tare da mummunan takunkuman tattalin arzikin da kasashen yamma musamman Amurka ta dorawa kasar wannan bai hana ta ci gaba a fannonin ilmi masu yaw aba. Wanda ya kaita kasa da wasu manya-manyan kasashen duniya a wasu fagagen. Ministan ya bukaci kamfanonin kera kayakin likita da kiwon...
Minitan kiwon lafiya na kasar Iran ya bukaci kamfanonin da suke kera kayalin kiwon lafiya da kuma aikin likita so kara yawan kayakin da ake sayarwa zuwa kasashen waje. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Mohammad Reza Zafarkhan yana wannan kiran a jawabin da ya gabatar a taron bude kasuwar baje koli na kayalin aikin likita da kuma kiwon lafiya a nan Tehran. Ministan ya kara da ce wa duk tare da mummunan takunkuman tattalin arzikin da kasashen yamma musamman Amurka ta dorawa kasar wannan bai hana ta ci gaba a fannonin ilmi masu yaw aba. Wanda ya kaita kasa da wasu manya-manyan kasashen duniya a wasu fagagen. Ministan ya bukaci kamfanonin kera kayakin likita da kiwon...
Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya nanata matsayin Taiwan da jaddada manufar Sin daya tak a duniya yayin tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Faransa Jean-Noel Barrot a jiya Jumma’a. Ya kuma bayyana adawar Sin da shigar kungiyar tsaro ta NATO cikin harkokin yankin Asiya da Pasifik. Wang Yi wanda mamba ne na ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS ya nanata cewa, batun da ya shafi Taiwan, batu ne na cikin gidan Sin da ya shafi ’yancin kasar da iko kan yankunanta, wanda ya bambanta da batun kasar Ukraine. Ya ce Sin na daukar amincewa da manufar kasar daya tak da Faransa ta yi da muhimmanci, kuma tana fatan ganin hakan a aikace. Bugu da kari, ministan ya...
Yanzu mun yi hakan a kananan Hukumomi takwas,zuwa Lahadi mai zuwa,zamu je ta tare. Zamu ci gaba da yin hakan har zuwa watan Nuwamba wanda hakan zai sa mu kammala da kananan Hukumomi 27. Zuwa yanzu ana ganin amfanin abinda aka yi,a duk kananan Hukumomi da muka ziyarta. Ina ganin mun yi rawar gani kan muradai 12,amma kamar yadda na ce al’ummar Jigawa sune wadanda ya dace su yi bayani kan irin ayyukan alkhairi da ci gaban da muka yi a matsayinmu na gwamnati. Da aka yi ma shi maganar ya ware kashi 30 cikin 100 saboda bangaren ilimi,cewa ya yi ai Jigawa Jiha ce da take da manoma. Domin kuwa kusan kashi 85 zuwa 90 na yawan al’ummar...

Adadin ‘Yan Jaridar Falasdinu Da Suka Yi Shahada Sun Karu Zuwa 226 Tun Bayan Fara Kisan Kare Dangi A Gaza
Adadin ‘yan jarida wadanda suka yi shahada a Gaza ya karu zuwa 226 tun bayan fara kisan kare dangi kan yankin Ofishin yada labarai na gwamnati a Gaza ya tabbatar a yau Juma’a cewa: Adadin ‘yan jaridun da suka yi shahada ya karu zuwa 226, bayan sanar da shahadar dan jarida Ahmed Qaljah. Ofishin ya bayyana cewa: Yawan ‘yan jaridan da suka yi shahada ya karu zuwa 226 tun farkon yakin kisan kare dangi kan zirin Gaza, bayan sanar da shahadar daya daga cikin ‘yan jaridan Falasdinawa: Ahmed Qaljah, wanda ya yi aiki a matsayin mai daukar hoto na gidan talabijin na Al-Arabiya. Ofishin ya yi Allah-wadai da kakkausar murya kan yadda gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke kai hare-haren wuce...
Abdullahi ya ce, an dauko wanda ya fadan a sume amma daga baya aka tabbatar da mutuwarsa. Ya kara da cewa, an mika gawar marigayin ga Hakimin Kawon Arewa, Alhaji Hamisu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hakika abin da suke yi shi ne kokarin cika alkawarin da gwamnatin kasar Sin ta sanya, na taimakon yankunan karkara na kasashen Afirka wajen samun hakikanin ci gaba, inda za a kyautata muhallin rayuwar mutane, da fitar da su daga kangin talauci, maimakon samar da karuwar adadin tattalin arziki kawai. Kana a bayan manufar ta kasar Sin akwai wani tunani mai muhimmanci da kasar ta rike, wato na “Gina al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai daya”. A ganin kasar Sin, dukkan al’ummun kasashe daban daban suna zama a duniya daya, don haka suna da makomar bai daya. Saboda haka ya kamata a lura da bukatun sauran kasashe, da tabbatar da ci gaban mabambantan kasashe na bai daya, yayin da...
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da gwamnan Jihar Ribas da aka dakatar, Siminalayi Fubara, a gidansa da ke Legas. Wannan ganawar na cikin ƙoƙarin warware rikicin siyasa da ya addabi jihar. Jami’an DSS sun kashe ’yan bindiga 45 a Neja ’Yan sanda sun sake hana hawan Sallah a Kano Fubara, ya samu saɓani da ubangidansa na siyasa, Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, bayan hauwansa mulki. Saɓani kan ikon mallakar kuɗin jihar da naɗin muƙamai ya janyo rarrabuwar kawuna a cikin gwamnatin jihar da kuma majalisar dokokin jihar. A watan Maris 2025, Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Ribas tare da dakatar da Gwamna Fubara, mataimakiyarsa, da kuma ‘yan majalisar dokokin jihar baki ɗaya. Ya naɗa...
ROOSC Ta Kaddamar Da Rabon Kayan Koyon Karatu a Karamar Hukumar Kaduna Sout Shirin Dawo da Yara Makaranta na Gwamnatin Jihar Kaduna Mai suna ROOSC ya kaddamar da rabon kayan koyon karatu ga dalibai a Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu, Jihar Kaduna. An gudanar da bikin kaddamarwar ne a Makarantar Firamare ta LEA da ke Unguwar Mu’azu, inda manyan masu ruwa da tsaki kan harkar ilimi, musamman shugabannin addini da na al’umma, suka halarta. Da yake jawabi a wajen taron, Ko’odinetan ROOSC a Jihar Kaduna, Mr. Ezra Angai, ya bayyana cewa wannan shiri hadin gwiwa ne tsakanin Gwamnatin Jihar Kaduna da abokan ci gaba da kuma kungiyoyin aiwatar da shirin, domin inganta samun ilimi mai nagarta ga yaran da ba...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yayin da sallah ya gabato, mutane da dama kan yi fadi tashi don biyan wasu bukatun su na bukukuwan sallah, kuma kamar yadda aka saba, a irin wannan lokaci ne iyalai da dama kan maida hankulan su don ganin sun biya wasu daga cikin bukatun su musamman wadanda suka jibanci bikin sallah. Siyayyan kayan kayan abinci na daya daga cikin wadannan hidindimu, sai dai kayan miya da suka zama dole ayi amfani dasu yayin bikin sallah sun yi tashin gwauron zabo inda alumma da dama ke ta bayyana damuwar su kan wannan batu. NAJERIYA A YAU: Hanyoyin kauce wa ɓarnar ambaliyar ruwa DAGA LARABA: “Sai Na Tara Kudin Cin Abinci Na Nake...
Sanarwar tafiyar tasa ta biyo bayan ganawar da Inzaghi ya yi da jami’an Inter a ranar Talata, sanarwar da Inter Milan ta fitar ta ce Kulob din da Simone Inzaghi sun yanke shawarar rabuwa, “Wannan shi ne shawarar da aka dauka bisa yarjejeniyar juna”, shugaban Inter Giuseppe Marotta ya kara da cewa “Ina so in gode wa Simone Inzaghi saboda aikin da ya yi, ya matukar taka rawar gani a shekaru 4 da muka shafe muna aiki tare, don haka Inter Milan na yi mashi fatan alheri a duk inda zai samu kanshi a nan gaba”. Inzaghi ya lashe gasar Seria A daya, Coppa Italia biyu da kuma Supercoppa Italia sau uku a lokacin da ya ke San Siro,...

Karuwar Darajar Sana’ar Samar Da Kayan Laturoni Da Dangoginsu a Sin Cikin Watanni 4 Na Farkon Bana Ya Karu Da 11.3%
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ya ce yanzu lokaci ne da Arewa za ta nuna adalci ta hanyar barin shugaba daga Kudu ya kammala wa’adin mulkinsa. Ya ƙara da cewa, “Idan za a fitar da wani ɗan takarar shugaban ƙasa daga ‘yan adawa a nan gaba, to ya dace ya fito daga Kudu maso Yamma. Wannan ne dai-daito da adalci.” Sanatan ya kuma soki gwamnatin baya da cewa ko da yake kusan dukkan shugabannin tsaro sun fito ne daga Arewa, amma hakan bai dakatar da ta’addanci a yankin ba, kuma bai hana hare-hare da kashe-kashe a jihohin Filato, Binuwai da sauran jihohin Arewa ta Tsakiya ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na...