Tsohon Dan Majalisar Taraba Usman Ya Fice Daga APC
Published: 4th, August 2025 GMT
Tsohon dan majalisa mai wakiltar mazabar tarayya ta Wukari/Ibi ta jihar Taraba a majalisar wakilai, Hon. Shiddi Danjuma Usman ya fice daga jam’iyyar APC. Usman ya bayyana rikicin cikin gida na jam’iyyar da rashin bin ka’idojin dimokuradiyya a matsayin dalilinsa na ficewa daga jam’iyyar. ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Da Dama A Kauyukan Zamfara Gwamnatin Kano Za Ta Mayar Da Gidan Gyaran Hali Na Kurmawa Gidan Tarihi Shiddi, wanda ya wakilci mazabarsa a majalisar wakilai ta 8 da ta 9, ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da manema labarai a ranar Lahadi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Guterres: Jerin Shawarwarin Da Sin Ta Gabatar Sun Cika Ka’idar Kundin Tsarin Majalisar Dinkin Duniya
Babban sakataren MDD António Guterres, ya bayyana a jiya Talata cewa, jerin shawarwarin da Sin ta gabatar wato shawarar raya duniya, shawarar tabbatar da tsaron duniya, shawarar raya wayewar kan al’ummun duniya, da kuma jagorantar harkokin duniya, sun dace da ka’idar kundin tsarin MDD.
Guterres ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida a wani taron manema labarai da aka yi a ranar. Ya ce shawarwarin da Sin ta gabatar sun mutunta manufar kasancewar bangarori da dama, kuma sun goyi bayan MDD a matsayin cibiyar hadin gwiwar kasa da kasa, tare da dukufa kan inganta hadin gwiwa tsakanin kasashe daban daban da warware rikice-rikice cikin lumana.
Guterres ya kara da cewa, yanzu ana fuskantar rarrabuwar kawuna a fagen siyasa ta duniya da kuma karuwar yaduwar rikice-rikice, da ma rashin hukunta masu laifi. Bugu da kari, sabbin fasahohi suna ci gaba da bullowa “ba tare da bin wani tsari ba”, yayin da rashin daidaito ke kara tsananta. A wannan yanayi, babban taro karo na 80 na MDD mai tsawon mako guda da za a fara a mako mai zuwa, zai ba da duk wata dama ga tattaunawa da shiga tsakani.(Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp