Aminiya:
2025-09-18@20:18:37 GMT

An sace jariri sabuwar haihuwa a asibitin Ekiti

Published: 4th, August 2025 GMT

An nemi wani jariri sabuwar haihuwa an rasa a Cibiyar Lafiya ta Okeyinmi da ke Ado-Ekiti, babban birnin Jihar Ekiti, a ranar Litinin.

Wani ganau ya ce an gano ɓatan jaririn ne lokacin da ma’aikatan jinyar da ke bakin aiki suka je su duba lafiyarsa da safiyar wannan Litinin ɗin.

Za a samu ruwan sama kamar da bakin ƙwarya na kwanaki uku a faɗin Nijeriya — NiMet Shirin kashe N712bn kan gyaran filin jirgin Legas ya tayar da ƙura

Lamarin na ba-zato-ba-tsammani ya haifar da fargaba musamman yadda ɗimauta uwar jaririn da kuma wasu daga cikin mutanen da ke cikin harabar asibitin.

Tuni dai an garzaya da ma’aikatan da ke kula da ɗakin haihuwa da uwar jaririn da mai gadi da wasu da ake zargi zuwa ofishin ’yan sanda domin ci gaba da bincike.

Aminiya ta ruwaito cewa wasu masu neman na abinci a kusa da asibitin sun shiga ɗimuwa matuƙa dangane da faruwar lamarin.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sanda na jihar, SP Sunday Abutu, ya ce yanzu haka akwai mutum huɗu da ake zargi da suka shiga hannu, “kuma suna bayar da bayanai masu amfani da za su taimaka a binciken.”

Abutu ya ce Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Mista Joseph Eribo, ya umurci sashen bincike na musamman (CID) da su gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da dawo da jaririn cikin ƙoshin lafiya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Jariri

এছাড়াও পড়ুন:

Lakurawa Sun Hallaka Jami’in Kwastam A Jihar Kebbi

An garzaya da shi zuwa babban Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Kebbi, inda daga bisani likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.

An yi jana’izarsa a babban masallacin Sarkin Gwandu, sannan aka binne shi a makabartar Dukku da ke kan hanyar Makera zuwa Kangiwa.

Jana’izar ta samu halartar jami’an kwas5tan, ‘yan uwa, abokai da sauran mu5sulmi daga sassa daban-daban na jihar.

Har yanzu al’ummar garin Filgila da kewaye na cikin tashin hankali da fargaba, kasancewar hare-haren Lakurawa na jefa su cikin zulumi.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ’Yan sanda sun kama mutum 9 kan yin garkuwa da kansu
  • Yadda jariri ya rasu a bayan mahaifiyarsa yayin tsere wa harin ’yan bindiga a Neja
  • An kashe ’yan ta’addan IPOB da yawa a Imo — ’Yan Sanda
  • ‘Yansan Jigawa Sun Tabbatarwa Mafarauta Da ‘Yan Bulala Samun Horo
  • ’Yansanda Sun Kama Mutane 9 Kan Yin Ƙaryar Sace Su A Jihar Neja
  • Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ta Kammala Ziyarar Yini 3 A Ma’aikatar Kananan Hukumomin Jihar
  • Lakurawa Sun Hallaka Jami’in Kwastam A Jihar Kebbi
  • Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu Kano
  • DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya
  • NSCDC Za Ta Fara Sanyan Ido Kan Muhimman Abubuwan More Rayuwa A Jihar Kano