Hukumar Hasashen Yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta yi gargaɗin cewa za a yi ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da tsawa na kwaki uku a faɗin ƙasar daga ranar Litinin.

NiMet ta fitar da wannan hasashen ne ranar Lahadi a Abuja, lamarin da ke ƙara barazanar ambaliya a wasu jihohin ƙasar.

Shirin kashe N712bn kan gyaran filin jirgin Legas ya tayar da ƙura Najeriya na hasashen samun N300bn a shekara daga noman dabino

Hasashen na zuwa ne bayan ruwan sama ya lalata gidaje kimanin 50 da gonaki da wuraren ibada a Jihar Filato.

Hukumar ta yi hasashen cewa za a yi tsawa da ruwan sama a jihohin arewacin ƙasar da suka haɗa da Adamawa da Taraba da Sakkwato da Kebbi da Zamfara da Jigawa da Kano da kuma Katsina ranar Litinin, kuma lamarin zai yi ƙamari zuwa yammacin ranar.

“Akwai yiwuwar samun ambaliya a wasu sassan jihohin Adamawa da Taraba da kuma Bauchi a wannan lokacin da aka yi hasashen,” kamar yadda NiMet ta bayyana a sanarwar.

A tsakiyar Nijeriya, ana sa ran saukar ruwan sama kaɗan da safiya a jihohin Binuwai da Neja da Kogi da Nasarawa da Kuma Birnin Tarayya Abuja.

Kuma zuwa rana da yamma, ana sa ran ruwan saman zai kai jihohin Filato da Kwara da kuma sauran jihohi maƙwabta.

A yawancin jihohin kudancin ƙasar dai hasashen hadari ake yi, inda ake ganin yiwuwar samun ruwan sama kaɗan a jihohin Ebonyi da Enugu da Imo da Anambra da Abia da Ogun da Edo da Delta da Legos da Ribas da Cross Rivers da Akwa Ibom da kuma Bayelsa da sanyina safiya.

Amma daga baya ana sa rai za a yi ruwa mai yawa, inda NiMet ke gargaɗin cewa za a iya samun ambaliya a jihohin Oyo da Ogun da Edo da kuma Delta.

Ranar Talata, hukumar tana hasashen cewa za a ci gaba da samun ruwan sama mai yawa da tsawa a yankin arewacin ƙasar musamman a jihohin Taraba da Katsina da Kebbi da Sokoto da Kaduna da kuma Zamfara.

“Ana tsammanin matsakaicin ruwan sama da tsawa a faɗin yankin daga baya a ranar,” in ji hukumar.

Jihohin tsakiyar ƙasar ciki har da Abuja, na tsammanin ruwan sama mai ɗaukewa da dawowa, yayin da jihohin kudancin ƙasar daga Legas zuwa birnin Calabar za su iya fuskantar ruwan sama babu ƙaƙƙautawa.

NiMet ta ja hankalin mazauna jihohin Anambra da Delta da Bayelsa da Cross River da kuma Akwa Ibom su shirya wa yiwuwar ambaliya.

Zuwa ranar Laraba, ana sa ran ruwan sama da tsawa zai karaɗe jihohin Taraba da Kaduna cikin sanyin safiya, inda kuma za a samu guguwa da ruwan sama daga baya a jihohin Borno da Bauchi da Gombe da Jigawa da kuma Kano.

Yankin tsakiyar ƙasar kuma zai sake ganin yayyafi da safiya, kuma da rana za a yi ruwan sama mai yawa.

A kudanci kuwa, ana hasashen za a yi ruwan sama mai ɗaukewa da dawowa a jihohin Legas da Ribas da Bayelsa da Cross River. Jihar Bayelsa ta fi fuskantar barazanar ambaliya a tsakiyar mako, in ji hukumar

Hukumar ta yi kira ga mazauna jihohin su ɗauki matakan kauce wa barazanar ambaliyar.

“[Ku] kaurace wa tuƙi a cikin ruwan sama mai ƙarfi, kuma jihohin da ke da yiwuwar samun ambaliya su yi tsare-tsarensu na ba da agajin gaggawa nan-take,” in ji hasashen.

NiMet ta kuma shawarci magidanta su ɗaure ababen da ka iya faɗuwa kuma su sanya rigunan sanyi tare da cire kayan laturoni daga lantarki a lokacin guguwa.

Hukumar ta kuma shawarci kamfanonin jiragen sama su nemi shawarwari na yanayi wajen shirya jadawalin jigilar matafiyansu.

NiMet ta buƙaci ‘yan Nijeriya su bibiyi shafinta na intanet don samun ƙarin bayani kan yanayi.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ambaliyar ruwa Hasashen Yanayi ruwan sama ruwan sama mai

এছাড়াও পড়ুন:

Haɗarin tirela ya yi sanadin asarar awaki sama da 100 a Zariya

A daren Juma’a ne dab da wayewar gari wata motar tirela ɗauke da awaki da kaji wadda ta taso daga Gwauron Dutse a Jihar Kano ta yi haɗari.

Motar tirelar wadda take ɗauke da dakon awaki da kuma kwandunan kaji mai yawa a samanta baya ga mutane da ta ɗauko ta yi haɗarin a kusa da kasuwar Ɗan Magaji saman gadar da ke kan hanyar  Zariya zuwa Kaduna.

Martani: Har yanzu muna ci gaba da yajin aiki — Ma’aikatan jinya   An ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su a Kebbi

Awaki kusan sama da 100  suka mutu da kuma kaji kusan ɗari 500 ne aka ƙeyasta sun mutu.

Sai dai ba a sami asarar rai ko ɗaya ba, sai dai akasarin mutanen da suke motar sun sami raunuka cikinsu har da direban motar, kuma  an garzaya da su zuwa Asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika Zariya don samun kulawar likitoci.

Wasu daga cikin matasan da suka kai ɗauki wurin sun kwashe matattun awakin da kajin inda suka watsa cikin wani kududdufi da ake kiwon kifi a kusa da inda  motar ta yi hatsarin dan gudun kada wasu  bɓata gari su kwashe dan sayarwa al’umma da mushen matattaun dabbobin.

Wani ganau da ke zaune a wurin da hatsarin ya faru ya ce yana zaton kamar barci ne ya kama direban motar.

A cewar ganau ɗin an tafka asarar sosai na dukiya a hatsarin motar sai dai shugabannin mazauna wurin sun sa ido domin ganin cewa ba a kwashi matattaun dabbobin ayi wani wuri da su ba.

An yi ƙokarin tuntuɓar mai magana da yawu hukumar kula da haɗɗura ta ƙasa reshen Zariya tare da tura masa saƙon kar ta kwana domin jin dalilin faruwar lamarin, amma har zuwa lokacin haɗa rahoton bai ɗauki waya ba.

Wasu daga cikin kajin da suka mutu

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Najeriya na hasashen samun N300bn a shekara daga noman dabino
  • Gwamnatin Jigawa Ta Dauki Manyan Matakan Kare Jihar Daga Ambaliyar Ruwa
  • Amurka Ta Gargaɗi Ƴan Nijeriya Kan Zuwa Ƙasarta Domin Haihuwa
  • Ambaliya: Mutum 165 sun mutu a Nijeriya a bana — NEMA
  • Fim Na Kisan Kiyashin Nanjing Ya Mamaye Kasuwar Fina-Finan Sin Bisa Samun Kudin Shiga Yuan Biliyan Daya
  • Manyan Ƙalubale Takwas Da Ke Shafar Farashin Tumatir
  • 2027: APC Da ADC Na Gwagwarmayar Neman Samun Goyon Bayan Mutanen Arewa
  • Hanyar Da Matasa Za Su Bi Don Ceto Dimokuraɗiyyar Nijeriya Daga Rugujewa
  • Haɗarin tirela ya yi sanadin asarar awaki sama da 100 a Zariya