An dage tattaunawa ta hudu da aka shirya gudanarwa tsakanin Iran da Amurka
Published: 1st, May 2025 GMT
Iran ta sanar da cewa an dage tattauanwa ta karo na hudu da aka shirya gudanarwa tsakaninta Washington a ranar Asabar mai zuwa.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ne ya sanar da manema labarai da hakan a yammacin yau Alhamis yana mai cewa an sauya ranar da za a gudanar da tattaunawar ta gaba tsakanin Iran da Amurka da aka shirya gudanarwa a ranar Asabar 3 ga watan Mayu a birnin Rome na kasar Italiya.
Esmail Baghai ya bayyana cewa, an dauki wannan matakin ne bisa bukatar ministan harkokin wajen kasar Oman, kuma Za a sanar da sabon lokaci nan gaba.
Baghaei ya jaddada aniyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran na yin amfani da hanyar diflomasiyya wajen kare muradun al’ummar Iran da kuma kawo karshen takunkumi da matsin tattalin arziki da ke shafar hakkokin bil’adama da jin dadin al’ummar Iran.
Ya kuma ba da tabbacin cewa, Iran za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka a cikin wadannan shawarwari.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Amurka ta sake kai Hari a yankunan Saada da Hudaidah na Yemen
Jiragen yakin Amurka sun sake kai hare-hare da dama kan lardunan Saada da Hudaidah na kasar Yemen yau Alhamis.
Wata majiyar tsaro a Yemen ta kara da cewa, an kai wasu hare-hare uku a yankin Kataf da ke lardin Saada, yayin da wani kuma ya afkawa gundumar al-Houk da ke lardin Hudaidah a gabar tekun yammacin Yeman, lamarin da ya janyo hasarar kayayyaki na fararen hula.
Dama a cewar kafar yada labaran kasar Yemen Al-Masirah, jiragen yakin Amurka sun kai hari a gundumar al-Sayl da ke lardin al-Jawf a arewacin kasar Yemen ranar Laraba.
Tun a ranar 15 ga watan Maris da ya gabata ne, kawencen Amurka da Birtaniya ke kai hare-hare ta sama kan kasar Yamen, domin nuna goyon baya ga gwamnatin Isra’ila.
Kafin hakan a ranar Litinin, 28 ga watan Afrilu, Amurka ta kai wani mummunan hari ta sama a birnin Sanaa, inda ta kashe mutane akalla 12 tare da jikkata wasu hudu.
A cikin wata sanarwa da ma’aikatar lafiya ta kasar Yemen ta fitar ta ce an kashe ‘yan kasar Yemen 12 da suka hada da kananan yara, yayin da wasu hudu suka jikkata sakamakon harin da Amurka ta kai kan wasu gidajen zama a yankin Thaqban na birnin Sanaa.
A safiyar litinin jiragen yakin Amurka sun kai harin bam a daya daga cikin wuraren da ake tsare da bakin haure ‘yan Afirka da ke yankin Saada, inda suka kashe mutane 68 tare da jikkata 47.