Gwamnan Kabawa Ya Tabbatarwa Ma’aikatan Gwamnati Ingantacciyar Walwala
Published: 2nd, May 2025 GMT
Gwamnatin jihar Kebbi, ta baiwa ma’aikatan jihar tabbacin ci gaba da jajircewa wajen kyautata jin dadin su da kuma kare hakkokinsu.
Gwamna Nasir Idris wanda ya ba da wannan tabbacin a lokacin da yake jawabi ga ma’aikata domin bikin ranar watan Mayu a Birnin Kebbi, ya jaddada cewa ma’aikata aminai ne masu kima wajen ci gaban jihar Kebbi, kuma su kasance masu ruwa da tsaki da ba za a yi watsi da su ba.
Gwamna Idris, wanda ya bayyana bikin ranar Mayu a matsayin wani muhimmin lokaci, ya yabawa ma’aikatan bisa jajircewarsu da irin gagarumar gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban jihar.
“Kwazonku da jajircewarku sune kashin bayan tattalin arzikinmu. Ina yaba muku kan kokarinku na jajircewa”.
Gwamna Idris, ya kuma amince da kalubalen da ma’aikatan jihar ke fuskanta tare da ba su tabbacin gwamnatinsa ta kudiri aniyar magance wadannan matsalolin.
A yayin da yake taya kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da TUC murnar zagayowar ranar ma’aikata, Gwamna Idris ya nuna jin dadinsa ga kungiyar ‘yan kasuwa bisa jajircewar da suke yi na kyautata jin dadin ma’aikata sannan ya bukaci ma’aikata da su ci gaba da jajircewa wajen gudanar da ayyukansu tare da ci gaba da ciyar da jihar gaba.
Tun da farko a nasa jawabin, shugaban kungiyar kwadago ta kasa (NLC) na jihar, Kwamared Murtala Usman, ya bayyana jin dadinsa a madadin kungiyoyin NLC da TUC bisa yadda Gwamnan ya ba da kulawar da yake yi wajen kyautata jin dadin ma’aikata da ci gaban su.
Kwamared Usman ya yaba da irin goyon bayan da Gwamnan ke ci gaba da baiwa ma’aikata, inda ya bayyana halartan taron bikin ranar Mayun 2025 kamar yadda aka zata duba da tarihinsa a matsayinsa na tsohon dan kungiyar kwadago da kuma tsohon shugaban kwadago.
Muhimman abubuwan da suka wakana a wajen taron sun hada da fareti da ma’aikata suka yi, da bayar da lambar yabo ga gwamna Idris da kungiyar dalibai ta kasa (NANS) reshen jihar Kebbi da kungiyar ma’aikatan jinya ta kasa suka yi.
Shugabannin kungiyar NLC na jihar sun kuma mika kyautuka ga wasu fitattun mutane bisa gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban jihar Kebbi.
COV/ Abdullahi Tukur
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Gwamna Idris jihar Kebbi
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnan Sokoto Ya Amince Da Sauya Wa Manyan Sakatarori 25 Ma’aikatu A Jihar
Gwamnatin jihar ta ce, matakin na daya daga cikin kokarin gwamnati mai ci na inganta ayyukanta domin samar da romon dimokuraɗiyya ga al’ummar jihar Sokoto.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp