MDD ta yi gargadi game da mummunar matsalar da yunwa ka iya haifarwa ga al’ummar Gaza
Published: 4th, August 2025 GMT
Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da wani kakkausar gargadi kan matsalar ruwan sha da ke kara kamari a zirin Gaza, inda ta bayyana cewa yunwa na ci gaba da rataya a kan al’ummar da ke kara hana samun tsaftataccen ruwan sha da tsaftar muhalli.
A cikin wani sabon rahoto, MDD ta ce kashi 96% na iyalai a Gaza na fuskantar matsalar rashin ruwa, yayin da kashi 90% na al’ummar kasar ba su da tsaftataccen ruwan sha.
Tun da farko, ofishin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya ya sanar da cewa Falasdinawa 1,373 ne suka yi shahada yayin da suke neman abinci tun lokacin da aka kaddamar da aikin agaji na Gaza a ranar 27 ga watan Mayu.
Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya tabbatar da cewa Falasdinawa a Gaza na fuskantar wani mummunan bala’i na jin kai, sakamakon yakin yunwa da Isra’ila ta kakaba mata a yakin da take yi na kisan kare dangi a yankin.
Babban Kwamishinan UNRWA Philippe Lazzarini ya yi tsokaci kan karar da babban jami’in na Majalisar Dinkin Duniya ya yi, yana mai bayyana cewa, yanayin yunwa mafi muni ya riga ya faru a Gaza, kuma bala’in “da mutum ya yi.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Rasha da China sun fara wani gagarumin atisayen soji na hadin gwiwa a tekun Japan August 4, 2025 Araqchi Ya Bayyana Makomar Sinadarin Uranium Da Iran Ta Inganta A Lokacin Yaki August 3, 2025 Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci Sun Bayyana Cewa: Masu Shirin Halaka Gaza Suna Son Mamaye Duniyar Musulmi Ne August 3, 2025 Iran Ta Jaddada Cewa: Karfin Makamai Masu Linzami Da Jiragen Sama Marasa Matuka Ciki Suna Nan Cikin Shiri August 3, 2025 Gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Tana Kokarin Boye Barnarta A Zirin Gaza August 3, 2025 Tsohon Shugaban Amurka Joe Biden Ya Caccaki Trump Kan Rusa Kundin Tsarin Mulkin Kasar August 3, 2025 IRGC Tace Bata Amince Da Kasashen Biyu A Kan Kasar Falasdinu Ba August 3, 2025 Iran Da Japan Suna Iya Jagorantar Duniya Don Rabata Da Makamai Kare Dangi August 3, 2025 Kungiyar Hamas Ta Bayyana Cewa Ba za ta Ajiye Makamanta ba Sai Bayan samar Da Kasar falasdinu August 3, 2025 Kungiyar Hamas Ta Wallafa Hotunan bidiyo Na Fursinan HKI tsare A Gaza August 3, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Majalisar Dinkin Duniya
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Slovenia Da Haramta Tura Makamai Zuwa Haramtacciyar Kasar Isra’ila
Slovenia ta kasance Ƙasar Turai ta farko da ta ba da sanarwar hana tura makamai zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila
Kasar Slovenia ta sanar da haramta musayar zirga-zirgan kayayyakin kasuwanci tsakaninta da haramtacciyar kasar Isra’ila musamman safarar makamai da kayan aikin soji zuwa Isra’ila, inda ta zama kasa ta farko ta Turai da ta dauki wannan matakin. Fira Minista Robert Gollub ne ya kaddamar da wannan matakin domin nuna adawa da mummunan bala’in jin kai a Gaza.
Wata sanarwa da ofishin fira ministan ya fitar ta tabbatar da hakan yayin wani taron majalisar ministocin da aka gudanar a farkon alhamis.
A karkashin sabon kuduri, duk makamai da kayan aikin soja an hana aikewa da su daga Slovenia zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila, ko shigo da su daga haramtacciyar kasar Isra’ila, ko kuma jigilar su ta yankin Slovenia.
Wannan matakin dai ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da sukar matsalar jin kai a Gaza da kuma gazawar Tarayyar Turai wajen daukar kwararan matakai dangane da gwamnatin yahudawan sahayoniyya.
Sanarwar ta kara da cewa: Sakamakon rashin jituwar cikin gida da kuma rarrabuwar kawuna, a halin yanzu kungiyar Tarayyar Turai ba ta iya gudanar da wannan aiki na ladabtar da Isra’ila.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kasar Spain Ta Bayyana Abin Da Ke Faruwa A Gaza A Matsayin Abin Kunya Ga Bil’Adama August 1, 2025 Iran ta yi watsi da zargin gwamnatocin turai na yunkurin kashe wasu mutane a kasashensu August 1, 2025 Mali da Rasha sun tattauna kan hadin gwiwar makamashi August 1, 2025 Afirka ta Kudu na shirin daukar matakan kauce wa tasirin harajin Amurka August 1, 2025 Haaretz: Sojojin Isra’ila 7 ne suka kashe kansu a watan Yuli August 1, 2025 Gaza: Mutane Da Dama Sun Yi Shahada A Yau Wasu Kuma Sun Jikkata August 1, 2025 Kungiyar AU Ta Yi Watsi Da Kafa Gwamnatin Adawa Da Kungiyar RSF Ta Yi A Sudan August 1, 2025 Shugaban Kasar Iran Zai Ziyarci Pakistan A Gobe Asabar August 1, 2025 Habasha Ta Kaddamar Da Shirin Shuka Bishiyoyi Miliyan 700 A Rana Daya August 1, 2025 Sayyid Abdulmalik Husi: Taimakon Da Ake Jefawa Gaza Ta Sama Yaudara Ce August 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci