’Yan bindiga sun tarwatsa ƙauyuka sama da 10 a Katsina
Published: 30th, July 2025 GMT
’Yan bindiga sun tarwatsa kauyaku sama da 10 da ke zagaye da ƙaramar hukumar Bakori ta jihar Katsina.
Maharan dai sun rika kashe mazauna kauyukan sannan su sace wasu su yi garkuwa da su domin karɓan kuɗin fansa.
Bayanai na cewa a ’yan kwanakin nan, ’yan bindigar na cin karensu babu babbaka a inda suka tarwatsa kauyuka kamar su Guga da Kandarawa da Kakumi da kuma Monono.
Har ila yau lamarin ya shafi ƙauyukan anguwar ’Yar Dabaru da anguwar Ɗan Marka, da Sabon Gida da ƙauyan Doma da dai sauran su.
Hakan dai ya haifar da kauracewa ƙauyukan ga mazaunansu da suke da sauran numfashi inda a yanzu haka ake da ’yan gudun hijira sama da 3,500 da ke neman mafaka a cikin garin Bakori.
Kazalika, rahotanni sun kuma ce akwai wasu sama da 2,500 da ke garin Guga don neman mafaka.
’Yan gudun hijirar wadanda akasarinsu mata ne da ƙananan yara sun watsu a wurare daban daban.
Aminiya ta zagaya unguwan Kafaɗi da unguwar Ma’aru da ke Sabuwar Abuja a cikin garin na Bakori, inda wakilinmu ya tarar da cincirindon mata da ƙananan yara a rakuɓe, a gidajen ’yan uwa, wasu kuma a makarantun firamaren gwamnati da ke karamar hukumar ta Bakori.
A tattaunawar Wakilinmu da wasu daga cikin ’yan gudun hijira wadanda suka fito daga kauyaku daban-daban na jihar, sun nuna alhininsu game da yadda ’yan bindigar ke cin karensu ba babbaka a yankin.
Imrana Shafi’u wanda ’yan bindigar suka harbe shi a ƙafa har wuri biyu, wanda shi ya yi hijira ne daga kauyan Ɗan Marka, ya ce lamarin na da ban tsoro matuƙa.
A cewarsa, “Ni ma Allah ne ya sa zan rayu domin ’yan bindigan sun zaci na mutu ne.
“Domin da suka zo kanmu harbin kan mai uwa da wabi, suka yi ta yi, inda suka kashe mutane da dama.
“Ni ma dai Allah ne ya tsirar dani, domin duk wadanda nake tare da su duk an kashe su, ni kadai na tsira cikin ikon Allah,” in ji shi.
Ita kuwa Malama Marawiya wacce ta yi gudun hijira daga kauyan ’Yar Dabaru ta ce da rana tsaka ’yan bindiga suka keto cikin kauyan nasu, suka tarwatsasu sa’ilin da suka tasa ƙeyar mata sama da 10 kuma duk yawancinsu suna ɗauke da goyo suka yi cikin daji da su.
Marawiya ta kara da cewa kusan kwanakin matan 10 ke nan a hannun su kuma sun ce sai an biya kudin fansa har Naira miliyan daya da rabi kan kowanne mutum daya kafin a sake su.
Ta Kara da cewa “A da in suka dauki mutum bai wuce su ce a ba su Naira dubu ɗari biyar ba amma a wannan karon sai suka ce sai an biya har sama da naira miliyan daya da rabi ga kowanne mutum,” in ji ta.
Yusuf Usman, wanda suka yi sansani a wata makarantar Firamare ta Nadabo da ke cikin garin Bakori, ya ce kusan su ɗari uku ne suka yi gudun hijira daga kauyan Doma, cikinsu har da tsofaffi.
Ya kuma ce, “A haka muka tako da ƙafa muka yini muna tafiya tare da mata da yaran kanana har Allah ya kawo mu garin Bakori,” in ji shi.
Ya kara da cewa kusan shekara biyar kenan suna fama da wannan matsalar ta tsaro, kuma ba dare ba rana bare damina ko rani, haka ake shigowa kauyakun su ana kashe su sannan kuma a tasa ƙeyar su a tafi da su daji domin karɓan kuɗin fansa.
Shugaban kwamitin da ƙaramar hukumar Bakori ta kafa domin kula da ’yan gudun hijirar, Mallam Mamman Yaro Bakori, ya ce adadin ’yan gudun hijirar sun kai 3,500 a garin Bakori.
Ya Kara da cewa a garin Guga Kuma akwai akalla kimanin mutane 2,500 da suke gudun hijira a can.
Shugaban ya ce kuma kusan a kullum yawan su ƙaruwa yake yi, sannan suna warwatse ne a wurare daban daban a inda wasu suke zaune a gidajen ‘yan uwansu wasu kuma suna zaune ne a makarantar firamare ta Nadabo a cikin garin Bakori.
Sai dai ya ce tuni Shugaban ƙaramar hukumar Bakori, Abubakar Barde ya bayar da umurnin kai masu tallafin kayan abinci sau uku a rana tare da kudin cefane don saukaka masu rayuwar da suke ciki.
Wasu na bayyana cewa a ‘yan kwanakinnan ’yan bindigar na cin karensu babu babbaka a inda suka kafa sansaninsu a dajin Guga da Kandarawa da Kakumi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga yan gudun hijira yan bindigar garin Bakori cikin garin
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan sa-kai aƙalla 100 da jami’an tsaro 30 sun mutu a bakin aiki a Katsina —Gwamnati
Sama da mutum 100 daga cikin jami’an tsaron al’umma da Gwamnatin Katsina ta samar ne suka suka mutu a yayin aikin karaɗe ’yan bindiga da suka addabi al’ummomin jihar.
Wannan ƙari ne a kan sojoji da kuma aƙalla jami’an ’yan sanda 30 da suka rasu a yayin aikin tabbatar da tsaron rayuwa da duniyoyin al’umma, a cewar ma’aikatar tsaron jihar.
Kwamishinan tsaron jihar, Nasir Mua’zu ya sanar da haka ne a martaninsa kan wasu rahotanni da ke yawo a kafofin sada zumunta, waɗanda ya ce ana amfani da su domin tayar da hankalin jama’a.
Mu’azu ya ce Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Raɗɗa yana yin iya bakin koƙarinsa wajen shawo kan matsalar ’yan ta’adda kuma ana samun nasara a kansu.
Kwamishinan ya ce lokacin da Gwamna Raɗɗa ya karbi shugabancin Jihar Katsina, ƙananan hukumomi aƙalla 24 ne ke fama da matsalar ’yan bindiga, amma kuma sakamakon haɗin kai da jami’an tsaro da kuma ƙirƙiro ƙungiyar ’yan sa-kai ta jihar, an yi nasarar murƙushe su a ƙananan hukumomi 11.
Mu’azu ya ce, matsalar ta kuma yi sauƙi a wasu ƙananan hukumomi tara, in banda Faskari da Ƙankara da Safana da kuma Matazu, da ke ci gaba da dama da hare-hare.
Ya bayyana cewa hakan ba ya nufin cewa gwamnati ta gaza, domin jami’an tsaro na iya bakin ƙoƙarinsu wajen tabbatar da tsaron lafiya da duniyoyin al’umma a wuraren.
A cewarsa, duk da hatsarin da gwamnan ya yi kwanakin baya, bai daina tattaunawa da shugabannin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki a harkar tsaro ba da ke jihar, domin shawo kan matsalar.
Don haka ya buƙaci haɗin kai daga kowanne ɓangare, musamman ganin yadda jami’an tsaron ke sadaukar da rayukansu wajen kare lafiya.