Aminiya:
2025-09-18@00:34:43 GMT

’Yan daba sun tarwatsa taron neman zaman lafiya na dattawan Katsina

Published: 3rd, September 2025 GMT

Wasu matasa da ake zargin ’yan daba ne sun tarwatsa wani taro da dattawan Katsina suka shirya a kan zaman lafiya a jihar jim kadan da fara shi ranar Talata.

Hakan na zuwa ne ’yan kwanaki kadan bayan an kai irin makamantan irin wadannan hare-haren a kan tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i da tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami.

Wata kungiya mai rajin tabbatar da zaman lafiya a jihar mai suna Katsina Security Community Initiative ce ta shirya taron na ranar Talata da nufin lalubo bakin zaren kan matsalar tsaron da ta addabi jihar.

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Juma’a a matsayin ranar hutun Mauludi Tinubu ya dawo da shugaban NTA da ya sauke

Katsina dai ta shafe tsawon shekaru tana fama da matsalolin tsaro na ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa, lamarin da ya yi sanadin kisan mutane da dama tare da rasa dukiyoyi na miliyoyin Naira.

Sai dai an kai harin ne a daidai lokacin da Gwamnan jihar, Dikko Umar Radda ya jagoranci tawagar dattawan jihar zuwa Fadar Shugaban Kasa Bola Tinubu, inda suka sa labule kan matsalar tsaron jihar.

Shi dai taron na Katsina ya tattara kwararru da dama, cikinsu har da tsofaffin sojoji da ’yan sanda da malamai da kuma sauran shugabannin al’umma.

To sai dai an fara samun matsala a taron ne lokacin da wanda ya shirya shi, Dr Bashir Kurfi, ya fara jawabi a kan matsalar tsaron jihar.

A cikin jawabin nasa dai, ya yi zargin cewa kananan hukumomin jihar da dama yanzu sun kusa zama kufai, yayin da harkokin tattalin arziki da noma da kiwo da ma harkokin karatu suka durkushe saboda hare-haren ’yan bindigar.

Amma yana cikin jawabi ne sai wani ya tashi ya katse shi, inda ya ce gwamnatin jihar na niya bakinta wajen magance matsalar, amma su ba sag ani, don haka ba za su bar shi ya ci gaba da magana ba.

Sun kuma zargi Dr Kurfi da cewa dan adawa ne saboda a zamanin gwamnatin da ta gabata bai yi irin wadannan maganganun ba, inda suka kira shi da makiyin gwamnati mai ci.

Da aka bukaci mai maganar da ya jira lokacin yin tsokaci kafin ya yi bayani, sai wasu takwarorinsa ma suka mike, nan take wajen kuma ya yamutse.

A nan ne suka fara jifa da kujeru har suna kai wa wasu daga cikin ’yan jaridar da ke daukar rahoto a wajen hari.

Bayanai sun nuna an girke ’yan dabar a ciki da wajen wurin tarom, yayin da wasu daga cikinsu suka rika nuna wukake suna barazanar caka wa duk wanda suke gani a matsayin makiyin gwamnatin jihar.

Sai dai duk da harin da ya tarwatsa taron, wanda ya shirya shi ya ce ba za su saduda ba.

Ya kuma zargi gwamnatin jihar da daukar nauyin ’yan dabar, inda ya ce dukkansu suna da alaka da gwamnatin, domin da bakinsu ma sun fadi hakan.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: yan daba Taron zaman lafiya

এছাড়াও পড়ুন:

Jihar Jigawa Ta Amince Da Karin Kasafin Kuɗi Na Naira Biliyan 75 Na Shekarar 2025

Gwamnatin Jihar Jigawa  ta amince da ƙarin kasafin kuɗi na Naira Biliyan 75 na shekarar 2025, ga gwamnatin jiha da kuma ƙananan hukumomi 27.

Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan zaman majalisar da aka gudanar a gidan gwamnati dake Dutse, babban birnin jihar.

Ya bayyana cewa, wannan ƙarin kasafin kuɗi ya samo asali ne daga ƙarin kuɗaɗen shiga domin biyan buƙatun kuɗaɗen da suka taso, da kuma ƙarfafa manyan fannoni da za su kawo ci gaba mai ɗorewa a faɗin jihar.

Alhaji Sagir Musa Ahmed ya ce, majalisar ta amince da Naira Biliyan 58 ga gwamnatin jiha da kuma Naira Biliyan 17 ga Kananan Hukumomi 27, wanda ya shafi kashe-kashen kudade na yau da kullum da kuma manyan ayyuka.

Ya ce, wannan ƙarin kasafin kuɗin zai inganta ayyuka da tsare-tsare da ake gudanarwa a muhimman fannoni irin su ilimi, kiwon lafiya, ababen more rayuwa, noma da sauran muhimman ayyukan ci gaba.

Sagir ya ƙara da cewa, za a mika ƙarin kasafin kuɗin ga Majalisar Dokokin Jihar domin tattaunawa da amincewa da shi, kamar yadda kundin tsarin mulki da ka’idojin kasafi suka tanada.

Kwamishinan ya ƙara jaddada cewa, wannan mataki ya nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen gudanar da mulki bisa gaskiya da adalci, da kula da kuɗaɗen jama’a yadda ya dace, da kuma tabbatar da samar da ingantattun ayyuka ga al’ummar jihar baki ɗaya.

 

Usman Muhammad Zaria

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • UNICEF Ya Ba Da Tallafin Kayayyakin Aiki Ga Cibiyoyin Lafiya A Kirikasamma
  • Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Sabon Tsarin Kula Da Lafiyar Mata Masu Juna Biyu Da Kananan Yara
  • Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a Ribas
  • Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
  • Jihar Jigawa Ta Amince Da Karin Kasafin Kuɗi Na Naira Biliyan 75 Na Shekarar 2025
  • ALGON ta karrama Gwamna Buni da lambar yabo kan kawo ci gaba a Yobe
  • Baqa’i: Kowace Kasa A Duniya Tana Da Hakkin Mallakar Makamashin Nukiliya Na Zaman Lafiya
  • ’Yan bindiga sun kai wa sojoji hari a ranar da ake zaman sulhu
  • Sabunta Cinikin Ba Da Hidima, Masu Zuba Jari Na Waje Suna Ganin “Damar Da Kowa Ke Bukata A Kowane Lungu Na Sin”
  • Gwamnatin Neja Ta Musanta Rahoton Hana Da’awa A Jihar