Mutune 70 da aka yi garkuwa da su sun samu ƴanci a Jihar Katsina, bayan yarjejeniyar sulhu da aka ƙulla da fitaccen shugaban ƴan bindiga, Isiya Kwashen Garwa. A wani faifan bidiyo da ya bayyana, Garwa ya saki mutane 40 a ƙaramar hukumar Faskari, kwanaki biyu bayan ya fara sakin wasu 30, wanda hakan ya kai adadin zuwa 70 gaba ɗaya.

Rahotanni daga mazauna yankin sun ce sakin na baya-bayan nan ya biyo bayan tattaunawa tsakanin shugabannin al’umma da sansanin Garwa, a wani mataki da ake ganin zai rage tashin hankali da hare-hare a yankin. Duk da haka, Garwa ya nuna rashin jin daɗi kan abin da ya kira sumamen Sojoji a unguwar Ruwan Godiya a lokacin Sallar Juma’a, inda ya yi zargin cewa wasu Hausawa da Fulani sun samu raunuka. Ya gargaɗi cewa irin waɗannan hare-hare na iya rusa sulhun da aka ƙulla.

Abubuwan Da Ba A Faɗa Ba Game Sulhu Da Ƴan Bindiga A Katsina An Cafke Wani Magidanci Da Lafin Sojan Gona A Katsina

Hukumomin jihar ba su fitar da wata sanarwa ba kan sumamen da ake zargin ba, sai dai majiyoyin tsaro sun ce an kai hare-haren ne kan maboyar ƴan ta’adda tare da nufin kare rayukan jama’a. Mutanen da aka sako, galibinsu manoma ne da aka sace daga ƙauyukan karkara a Faskari, suna cikin kulawar likitoci da kuma binciken tsaro kafin a mayar da su wurin iyalansu.

Gwamnatin jihar ta ce tattaunawa tana daga cikin dabarun tsaro da ake amfani da su, amma ta jaddada cewa dole ne ƴan bindiga su miƙa makamansu gaba ɗaya tare da fuskantar hukunci kan laifuffukan da suka aikata.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Faskari Tsaro

এছাড়াও পড়ুন:

Sanata Natasha ta koma Majalisar Dattawa

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar Kogi ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, ta koma ofishinta da ke harabar majalisar bayan ƙarewar wa’adin dakatarwar watanni shida da aka yi mata.

A wani bidiyon komawarta ofis da ya karaɗe shafukan sada zumunta, ’yar majalisar ta zargi Shugaban Majalisar Dattawan, Sanata Godswill Akpabio da ɗaukarta a matsayin baiwarsa.

Yarima Salman ya jagoranci jana’izar babban mai ba da fatawa na Saudiyya Kotu ta hana NUPENG rufe Matatar Ɗangote

A cewarta, kamar yadda Akpabio ke matsayin sanata haka ita ma sanata ce.

Sanata Natasha ta ce duk da cewa an dakatar da ita ba bisa ƙa’ida ba, ta riƙa sauke nauyin al’ummar mazaɓarta na Kogi ta Tsakiya, saboda a cewarta ba ta son al’ummarta su ji kamar an yi watsi da su.

Tun da safiyar yau ce rahotanni suka bayyana cewa an buɗe ofishin sanatar da ke Suite 2.05 a cikin ginin Majalisar Dattawan.

Gabanin komawarta, ’yan sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa domin tarwatsa magoya waɗanda suka raka ta zuwa Majalisar Dattawa daga Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.

Bayanai sun ce magoya bayan sun yi tattaki ne domin raka sanatar zuwa majalisar domin komawa bakin aikinta.

Ana iya tuna cewa mako gabanin komawarta ne Sanata Natasha ta rubuta wa Majalisar Dattawan wasiƙa, wadda ta bayyana a niyyarta ta dawowa aiki bayan dakatarwa na tsawon wata shida, amma majalisar ta ce ta ɗan jira tukuna.

A watan Fabrairu ne dai tankiya ta ɓarke a zauren Majalisar Dattawa tsakanin shugaban majalisar da Sanata Natasha, lamarin dai ya kai ga har Akpabio ya umarci ɗaya daga cikin masu yi wa sandan majalisar hidima da ya fitar da ita daga zauren majalisar, kuma daga bisani aka dakatar da ita na tsawon wata shida.

Wannan lamarin ya kai ga har Sanata Natasha ta yi kira ga Majalisar Ɗinkin Duniya da ta hukunta Majalisar Dattawan Najeriya game da dakatarwar da aka yi mata.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gavi Zai Yi Jinyar Watanni 5 Bayan Yi Masa Tiyata
  • Sanata Natasha ta koma Majalisar Dattawa
  • An gudanar da bikin ɗaga tutar Falasɗinu a Birtaniya
  • Jariri ya mutu a bayan uwarsa yayin tsere wa ’yan bindiga a Neja
  • Bayan Mutuwar Wani Matashi, An Kafa Dokar Ta Baci A Yauri
  • Karin ƙananan hukumomi 2 sun yi sulhu da ’yan bindiga a Katsina
  • Bayan Nesanta Kanta, Jami’ar European American Ta Yi Wa Rarara Tayin Digiri
  • Lokaci Yayi Da Shugabannin Arewa Za Su Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Yankin –  ACI
  • An Cafke Wani Magidanci Da Lafin Sojan Gona A Katsina