Sarah Mullally ta Kafa Tarihi a Matsayin Shugabar Mace ta Farko na Cocin Ingila
Published: 3rd, October 2025 GMT
Sarah Mullally ta zama sabuwar Shugabar Cocin Ingila, wato Archbishop ta Canterbury, inda ta kasance mace ta farko da za ta jagoranci Cocin Ingila inda wannan muƙamin ya samo asali tun zamanin Daular Romawa da kuma al’ummar Anglican na duniya.
Sarki Charles III ya amince da naɗin Mullaly bayan kwamitin da aka dora wa alhakin nemo wanda zai maye gurbin Justin Welby, wanda ya yi murabus a farkon wannan shekarar saboda wani zargi na cin zarafi, kamar yadda gwamnatin Birtaniya ta sanar a ranar Jumma’a.
Cocin Ingila ita ce ta haifi ɗarikar Anglican a duniya. Mullally, mai shekaru 63, ta zama Archbishop ta Canterbury ta 106.
A cikin wata sanarwa, tsohuwar ma’aikaciyar jinya ta bayyana cewa ta fahimci “babban nauyi” da ke tattare da sabon aikinta, amma ta ce tana jin “nutsuwa da amincewa ga Allah don ya taimake ni.”
Firaminista Keir Starmer ya yi maraba da nadin mace ta farko da za ta rike wannan mukami. “Cocin Ingila tana da matukar muhimmanci ga wannan kasa. Coci-cocinta da majami’unta, makarantu, da kungiyoyin agaji suna cikin tsarin al’ummominmu,” in ji shi a wata sanarwa, yana mai cewa sabuwar Archbishop za ta “taka rawar gani a rayuwar kasa.”
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Farko Sarah Mullally Tarihi
এছাড়াও পড়ুন:
Kakakin Majalisar Taraba Da Ƴan Majalisa 15 Sun Fice Daga PDP Zuwa APC
Bonzena ya ƙara da cewa duk da cewa kafin yanzu APC ce ke da rashin rinjaye a majalisar, an ci gaba da aiki cikin zaman lafiya, amma yanzu yana farin cikin ganin cewa dukkan mambobin majalisar sun haɗe ƙarƙashin tsari daya da ya yi daidai da hangen shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA