Sashen masana’antun samar da sabbin makamashi na kasar Sin ya samu ci gaba cikin sauri a shekarun baya bayan nan, a gabar da ake ta aiwatar da managartan matakai na bunkasa tattalin arziki ba tare da fitar da iskar Carbon mai dumama yanayi ba.

 

Tun daga shekarar 2013, adadin kayayyakin samar da lantarki daga karfin iska da aka kafa a Sin sun ninka har sau 6, yayin da na samar da lantarki daga karfin rana suka ninka sama da sau 180.

Ya zuwa yanzu, sabbin kayayyakin samar da lantarki ta wannan hanya da ake kafawa duk shekara a kasar Sin, sun kai kaso sama da 40 bisa dari kan na daukacin kasashen duniya, adadin da ya yi matukar ba da gudummawa ga bunkasa duniya ta hanyar kaucewa gurbata yanayi. (Saminu Alhassan)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

‘Yansanda Sun Fara Bincike Kan Rasuwar Wani Dan NYSC A Bauchi

Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga LEADERSHIP a ranar Talata, Kakakin Rundunar ’Yansandan Jihar Bauchi, CSP Ahmed Wakil, ya ce rundunar ‘yansandan ta samu kiran waya da misalin karfe 9:20 na safe daga CLO, inda ya ce Chukwuebuka mai lambar jiha BA/25A/2069 bai farka ba daga barcinsa, yayin da sauran ’yan uwansa Kiristocin ke shirin tafiya wurin bauta a ranar Lahadi.

 

“CLO ya je don ya tayar da shi daga barci amma sai ya gano cewa, ba ya numfashi, nan take ya kai rahoton lamarin ga hedikwatar ‘yansanda ta Dambam,” in ji Wakil.

 

Biyo bayan umarnin kwamishinan ‘yansandan jihar Bauchi, CP Sani Omolori-Aliyu, jami’in ‘yansanda na sashen ya jagoranci tawagarsa zuwa wurin.

 

An garzaya da Chukwuebuka zuwa wani asibiti da ke kusa, inda wani likita ya tabbatar da mutuwarsa.

 

Daga bisani, aka akai gawarsa zuwa Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Azare, kamar yadda doka ta tanada.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tsarin Samar Da Kayayyaki Na Masana’antar Lantarki Ya Ci Gaba Da Samun Karfin Juriya A Kasar Sin
  • Rashin Lantarki: Babu wanda za mu zaɓa a 2027 — Jama’ar Talasse
  • Gyaruwar Alakar Kasuwancin Sin Da Amurka Ta Zarce Bukatun Kasashen Biyu
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 128
  • Sashen Tattalin Arzikin Teku Na Sin Ya Bunkasa A Rabin Farko Na Bana
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 124
  • Majalisar Kano Ta Dakatar Da Shugaban Karamar Hukuma Bisa Zargin Kara Farashin Takin Gwamnati
  • ‘Yansanda Sun Fara Bincike Kan Rasuwar Wani Dan NYSC A Bauchi
  • Ilimin Fasahar Zamani Dama Ce Ta Samun Kyakkyawar Makoma A Afrika
  • Ronaldo Zai Daura Aurensa Na Farko A Rayuwa Tare Da Budurwarsa Georgina