Sin Ta Samarwa Sassan Kasa Da Kasa Damar Shigowa Ba Tare Da Bukatar Biza Ba
Published: 1st, August 2025 GMT
A kwanakin baya, an bude tashar jirgin ruwa ta fasinja ta kasa da kasa ta kasar Sin ta farko, wato tashar jirgin ruwa ta Shekou dake birnin Shenzhen. ’Yan kasuwa daga Argentina, da Chile, da Brazil sun shiga kasar Sin ta tashar bisa sabuwar manufar shiga kasar Sin ba tare da biza ba, inda aka rage lokacin daidaita aikin canza jirgi daga awoyi biyu da rabi zuwa kasa da rabin awa.
Wannan batu ya kasance wani misali, bayan da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar shiga kasar Sin ba tare da biza ba. A cikin shekaru 5 da suka gabata, wato cikin wa’adin aiwatar da shirin shekaru biyar-biyar na raya kasar Sin na 14, gwamnatin kasar ta kara kyautata manufofin shiga kasar ba tare da biza ba a fannoni daban daban, don sa kaimi ga yin mu’amala tare da sauran sassan kasa da kasa.
A halin yanzu, kasar Sin ta bada damar shiga kasar ba tare da biza ba ga kasashe 75, inda yawan kasashen da suke da izinin ratsa kasar Sin ba tare da biza ba ya karu zuwa 55, kana yawan tasoshin bincike dake kan iyakar kasar Sin da sauran kasashe makwabta, inda ake iya shiga kasar Sin ba tare da biza ba ya karu zuwa 60, kana tsawon lokacin da ake iya yada zango cikin kasar ya karu zuwa awoyi 240, wanda hakan ya kawo sauki ga al’ummun kasashen waje, dake zuwa kasar Sin don yawon shakatawa, da yin ciniki da kuma yin ziyara.
Manufofin shiga kasar Sin ba tare da samun biza ba sun shaida cewa, Sinawa suna son baki tun a da can, kuma gwamnatin kasar Sin ta yi imani da fadada bude kofa ga kasashen waje. A shekaru 5 masu zuwa, Sin tana maraba da karin al’ummun kasashen waje da za su shiga kasar Sin, da ganewa idanunsu yanayin kasar da kuma fahimtarta. Kazalika, hakan zai kara shaida cewa, bunkasar kasar Sin na da nasaba da duniya, kana wadatar duniya tana bukatar kasar Sin baki daya. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: shiga kasar Sin ba tare da biza ba kasashen waje kasar Sin ta
এছাড়াও পড়ুন:
CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka
Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin CMG, ya gabatar da labarin ganawar da aka yi jiya Alhamis tsakanin shugabannin Sin da Amurka a Busan na Korea ta Kudu, cikin harsuna 85. Kuma zuwa yau Juma’a, mutanen da suka karanta rahotanni masu alaka da ganawar ta hanyoyin watsa labarai na dandalin CMG sun kai miliyan 712. Haka kuma, kafafen watsa labarai na kasa da kasa 1678, sun wallafa tare da tura rahotanni da bidiyon labaran CMG na harsuna daban daban game da ganawar, har sau 4431.
Har ila yau a wannan rana, an gudanar taron tattaunawa na kasa da kasa kan bude kofa da kirkire kirkire da ci gaba na bai daya a kasar Uruguay, wanda CMG da hadin gwiwar ofishin jakadancin Sin dake kasar suka shirya a Montevideo babban birnin Uruguay. (Mai fassara: FMM)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA