2025-10-16@16:53:50 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1313
«Tafawa Balewa»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Miliyoyin Iraniyawa a ranar 8 ga watan muharram sun fito sanye da bakaken kaya da tunawa a bubuwan da suka faru a ranar kwanakin Asoora inda aka kashe Imam Hussain (a) jikan manzon All… Banda wannan raya kwanakin Ashoora ci gaba ne da nuna turjiya da kuma saukar da kai kan azzaluman shuwagabanni ko da ba tare da samun nasara a zahiri ba kuma nan kusa ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa an gudanar da taturrukan Ashoora a duk fadin Iran, kuma a yau Tasoo’a za’a ci gaba da fitowa har zuwa gobe a Ashoora randa Imam Hussain (a) tare da sahabbansa 72 suka yi shahada a hannun sojojin yazeed a Karbala a ranar 10...
Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza na kasar Falasdinu da aka mamaye, ta bada sanarwan cewa da ita da sauran kungiyoyi da suke gwagwarmaya da HKI kimani shekaru biyu da suka gabata, sun amince da batun tattaunawa da kuma tsagaiuta budewa juna wuta wanda masu shiga tsakani suka gabatar. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa, shugaban kasar Amurka Donal Trump ya ce, wai HKI ta amince da shawarar budewa juna wuta da ya gabatar, amma kuma har yanzun ba’a bayyana dalla-dalla menen a cikin yarjeniyar ta kunsa ba. Har’ila yau gwamnatin kasar Masar ta ce tana kokarin ganin an samar da tsagaita budewa juna wuta na kwanaki 60.

Sojojin HKI Kimani 40 Ne Suka Halaka Ko Suka Jikata A Jiya Jumma’a A Yankin Shuja’iyya Na Birnin Gaza
Kungiyar Falasdinawa ta Jihadul Islami a Gaza, ta bada sanarwan halaka ko jikatar sojojin yahudawan Sahyoniyya 40 a gaza a wani tarko mai sarkakiyan da suka dana masu. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar Saraya Qudus” reshen soje na kungiyar Jihadul Islamim yana fadar haka a jiya Jumma’a. Daya daga cikin kwamnadojin dakarun ya bayyana cewa da farko halakar yahudawan ta faru ne a garin Gaza a kuma unguwar shuja’iyya. Inda da farko suka halaka sojojin yahudawa kimani 10 a cikin wani ginin da suka shiga cikinsa tare da amfani da makamai mai linzami, sannan a wani gidan Sannan waso sojojin kimani 20 sun halaka ko sun ji rauni a lokacin dakarun suka yi am,fani da...

Shugaban Kasar Iran Ya Gabatar Da Jawabio A Taron Kolin Kungiyar ECO Musamman Kan Harin Da Kasarsa Ta Fuskanta
Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Sojojin kasarsa sun koya wa ‘yan sahayoniyya masu wuce gona da iri babban darasi Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, a jawabin da ya gabatar a taron kolin kungiyar Hadin Gwiwar Tattalin Arziki ta ECO da aka gudanar a kasar Azarbaijan a yau Juma’a, ya jaddada cewa: Sojojin kasar Iran bisa doka mai lamba 51 na yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya sun kare al’ummar Iran da mutuncin kasar da cikakken ikonta a yakin da aka yi a baya-bayan nan, kuma sun koyar da masu wuce gona da iri darasi mai girma da kuma dakile yaduwar yaki a wannan yanki. A yayin taron koli karo na 17 na kungiyar hadin kan tattalin arziki ta ECO da aka...
Sojojin mamayar Isra’ila sun mayar da cibiyoyin bada agaji zuwa filin yakin kashe Falasdinawa a Zirin Gaza Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da mayar da cibiyoyin bayar da agajin jin kai zuwa wani mummunan tarko na aiwatar da kisan kiyashi kan Falasdinawa, wanda hare-haren baya-bayan nan da suka kai kan fararen hula sunka yi sanadiyar hasarar rayuka da dama tare da jikkata wasu masu yawa. Wannan mummunan al’amari ya janyo gargadin Majalisar Dinkin Duniya cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana kai wa masu fama da yunwa hari. Jiragen yakin gwamnatin mamayar Isra’ila da kuma amfaniu da manyan bindigogi suna barin wuta kan mai uwa da wabi kan Falasdinawa da suka taru domin karbar kayan jin kai. Gwamnatin mamayar Isra’ila...
Wani mummunan lamari na kisan gilla ya afku a ƙauyen Galadanchi da ke Ƙaramar hukumar Dutse a Jihar Jigawa. Rundunar ’yan sandan jihar ta kama wani tsoho mai shekara 70 bisa zargin kashe ƙanwarsa saboda rikici kan filin gado. Gwamnan Bauchi ya ƙaddamar da kwamitin ƙirƙiro da sabbin masarautu An gano wasu bama-bamai 56 da ISWAP suka binne a Borno Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar y’an sandan jihar, SP Lawan Adam Shi’isu ya fitar ya ce tsohon mai suna Adamu Yakubu – ɗan asalin ƙauyen Galadanchi ne wanda ya samu saɓani da ƙanwarsa mai suna Hannatu Hashimu, mai shekara 45, kan rabon gadon wata gona da suka gada. Bayanan binciken farko da ’yan sanda suka fitar, ya nuna cewa...
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce Sin ba ta goyon bayan wani bangare a rikicin Ukraine. Mao, wadda ta bayyana hakan yau Juma’a yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, ta ce har kullum matsayar Sin ita ce karfafa gwiwar komawa ga tattaunawar wanzar da zaman lafiya. Jami’ar ta kara da cewa, Sin ta yi rawar gani wajen ingiza bukatar tsagaita bude wuta, da kawo karshen yaki. Kazalika, a cewarta dukkanin sassan kasa da kasa sun kwana da sanin matsayar adalci, da hangen nesa ta kasar Sin, cewa tsawaitar rikicin Ukraine ba zai haifar da ‘da mai ido ga kowa ba. Har ila yau, a cewar jami’ar, Sin na goyon bayan gaggauta...
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta umarci Majalisar Dattawa da ta mayar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya. A watan Maris, Majalisar Dattawa ta dakatar da Natasha na tsawon watanni shida, bayan wata taƙaddama da ta ɓarke tsakaninta da Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio. Kotu ta ci tarar Natasha N5m saboda kin bin umarninta ’Ya’yana na da ’yancin mallakar filaye a Abuja – Wike Taƙaddamar ta samo asali ne kan yadda aka canja tsarin zama a zauren majalisar. Bayan dakatarwar, Natasha ta zargi Akpabio da yunƙurin cin zarafinta, inda ta kai ƙara Majalisar Ɗinkin Duniya kan lamarin. A ranar Juma’a, Mai shari’a Binta Nyako ta yanke hukunci cewa dakatarwar watanni shida da aka yi wa Natasha...
Gwamnatin kasar Amurka ta dorawa JMI sabbin takunkuman tattalin arziki ta bangaren man fetur a jiya Alhamis, a dai-dai lokacinda take maganar sake farfado tattaunawa da ita. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Scott Bessent sakataren kudi na Amurka yana fadar haka ‘Amurka zata ci gaba da gurgunta tattalin arzikin JMI da dukkan hanyoyin samun kudadenta, har sai ta dawo kan muradunta. Wannan dai yana daga cikin shirin Amurka na takurawa tattalin arzikin kasar Iran har zuwa lokacinda mutanen kasar zasu kasa hakuri su kuma tashi su kifar da gwamnatin JMI daga cikin gida. Wannan ne takunkuman tattalin arziki na farko wanda gwamnatin Amurkan ta dorawa JMI bayan yakin kwanaki 12 da ita da HKI suka dorawa...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya yi watsi da labarin da ministan harkokin wajen kasar Jamus ya watsa dangane da shirin Nukliyar kasarsa ya kuma kara da cewa labarin jabu ne. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a shafinsa na X . Ya kuma yi watsi da zancen ministan harkokin wajen kasar Jamus wanda yake cewa, jinginar da aiki tare da hukumar makamashin nukliya ta duniya wato IAEA wanda JMI ta yi, ya na nuna cewa ba wanda zai bincika ayyukanta na makamashin nukliya ba, kuma ta rufe kofar tattaunawa Kenan. Aragchi ya bayyana cewa wannan ba haka bane, saboda shirin nukliyar kasar Iran a halin yanzu ya na karkashin majalisar...
Babban magatakardar MDD Antonio Gutress ta sanar da kaduwarsa da kuma jin haushin yadda wahalhalun Falasdinawa a Gaza suke karuwa, yana mai cewa: Sauran abinda ya rage da zai rike rayuwa a Gaza, ya kusa karewa saboda rufe hanyoyin da suke shiga Gaza da HKI ta yi. Kakakin babban magatakardar na MDD Stephen Dujarric, ne ya ambato maigidan nasa yana fadin haka akan yanayin da zirin Gaza yake ciki, tare da kuma da cewa; MDD tana son ganin an bai wa fararen hula kariya da kuma biya musu bukatunsu. Antonio Guterres ya kuma bayyana firgitarsa a lokaci daya kuma da bacin ransa akan yadda Falasdinawan Gaza su ka cikin mawuyacin hali, yana mai kara da cewa da akwai adadi mai...
Wasu ’yan bindiga sun kai hari kan masu dawowa daga binne gawa a kauyen Rim na jihar Filato, inda suka datse wa daya daga cikin matasan da ke wurin hannu daya. Bayanai sun nuna cewa mutanen na kan hanyarsu ce ta dawowa daga bikin binne wani mutum ne a kauyen Bachit da ke da makwabtaka da su inda suka yi arba da maharan wadanda suka tare su suka bude musu wuta, sannan suka datse wa daya daga cikin mutanen hannu daya. Rasha ta amince da gwamnatin Taliban a Afghanistan Ambaliya da iska sun rushe gidaje 171 a watanni biyu a Gombe – SEMA Wani Hadimin Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, mai suna Timothy Dantong, wanda yake cikin mutanen da suke dawowa...
Kwamatin Harkokin Kananan Hukumomi na Majalisar Dokokin jihar Jigawa ya fara rangadin kwanaki biyu a karamar hukumar Roni a ci gaba da rangadin kananan hukumomin jihar 27 da kwamatin ya kaddamar. A jawabin sa a sakatariyar karamar hukumar Roni, Shugaban kwamatin Alhaji Aminu Zakari, ya ce tsarin mulkin kasa ya bai wa majalisa ikon dubawa da kuma tantance yadda bangaren zartaswa ke aiwatar da manufofi da shirye shiryen gwamnati. Ya ce ziyarar za ta mayar da hankali ga dubawa da kuma tantance kundin bayanan sha’anin mulki da na harkokin kudi da suka hada da kundin kasafin kudi na shekarar 2024 zuwa 2025 da Asusun kula da matsalolin muhalli da kundin bayanan kwamitocin karamar hukumar da takardun biyan kudade wato Voucher...
Sojojin mamayar Isra’ila sun kai munanan hare-hare kan Falasdinawa da suka rasa gidajensu da fama da masifar yunwa, lamarin da ya yi sanadiyar shahadan mutane da dama Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana ci gaba da aiwatar da kisan kiyashi kan ‘yan gudun hijira da kuma wadanda ke jiran agaji a zirin Gaza, inda a daren jiya zuwa safiyar Alhamis, hare-haren wuce gona da irinsu suka yi sanadiyar shahadan Falasdinawa da dama, tare da jikkata wasu baya ga bacewar wai adadi mai yaw ana mutane a karkashin baraguzan gine-gine. Asibitin Al-Shifa ya sanar da shahadan fararen hula 11 da suka hada da yara da mata a wani sabon kisan kiyashi da sojojin mamayar Isra’ila suka aikata ta hanyar kai hare-haren bama-bamai...
Sanarwar ta ƙara da cewa, a yayin taron an sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin gwamnatin jihar Zamfara da Hukumar Samar da Wutar Lantarki ta Yankunan Karkara, sannan aka tattauna da masu ruwa da tsaki, tambayoyi da amsoshi, ra’ayoyi, da kuma alƙawura. A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya ce ya gaji matalauciyar gwamnatin a bangaten lantarki. Ya ci gaba da cewa, “An katse ƙananan hukumomi da yawa daga babban lantarkin ƙasa. An sace wayoyin lantarki da dama, wasu kuma sun lalace, wasu muhimman ababen more rayuwa sun durƙushe a cikin shekaru saboda watsi da su, sannan masana’antu da kasuwancinmu sun gurgunta saboda rashin ingantaccen wutar lantarki. “Duk da haka, mun zaɓi kada mu shiga wasan zargi,...
Dubabban falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan ne gwamnatin HKI ta kora daga gidajensu tun bayan ta fara wani shiri wanda ta kira Katangan karfe a farkon wannan shekarar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kungiyar Doctors without Borders wato MSF a takaice tana fadar haka a jiya Laraba. Rahoton ya kara da cewa HKI tana son korar dukkan falasdinawa da suke rayuwa a yankin yamma da kogin Jordan ne don samun damar kafa kasar Yahudawa zallah kamar yadda suke fata. Rahoton ka kara da cewa falasdinawa a garuruwan Tulkaram Jenin da kuma Nurushamne al-amarin ya fi shafa inda yahudawan suka kore falasdinawa akalla dubu 40,000 daga farkon wannan shekara ta 2025 sun kuma rusa gidajen...
Ministan tsaron cikin gida na HKI Itamar Ben-Gvir ya yi kira ga babban murya kan cewa dole ne HKI ta mamaye dukka zirin gaza ta kuma kori falasdinawa da suke cikinsa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalato Ben Gafir yana fadar haka a jiya ya kuma kara da cewa mamaye gaza da kuma yankin yamma da kogin Jordan da kuma shi ne kawai zai sa a samar da kasar yahudawan zalla inda babu ba falasdine ko guda a yankunan guda biyu. Kiran nasa dai ya gamu da maida martani daga yan siyasa a ciki da wajen HKI. Tun shekara ta 2023 ne gwamnatin HKI take son mamyar zirin gaza ta kuma kori Falasdiwa a yankin. Bayan yaklin...
Tsangayar Kwalejin koyar da aikin Jinya ta Jihar Jigawa dake garin Birnin kudu ta gudanar da bikin kaddamar da sabbin dalibai 116 da za su yi karatun difloma ta kasa da babbar difloma ta kasa karon farko na shekarar karatu ta 2024 zuwa 2025. A jawabinsa wajen taron kaddamar da daliban, kwamishinan ma’aikatar lafiya na jihar Jigawa Dr. Muhammad Abdullahi Kainuwa, ya ce aikin sa na farko daga samun wannan mukami shi ne batun kafa hukumar Gudanarwar Kwalejin da sake fasalin Kwalejin, wanda hakan ya bada damar tantancewa da kuma samun amincewar Cibiyar kula da makarantun aikin Jinya ta Najeriya. Yana mai cewar, daukar wannan mataki ya bada damar kara yawan dalibai da Kwalejin take dauka daga 120 zuwa 240,...
Falasdinawa da dama ne suka yi shahada yayin da wasu suka jikkata sakamakon wani sabon harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wasu yankuna na Gaza Fararen hula Falasdinawa da dama ne suka yi shahada tare da jikkata wasu masu yawa sakamakon kazamin harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wasu yankuna a zirin Gaza tun da sanyin safiyar Laraba. Shaidun gani da ido sun bayyana cewa: Akalla fararen hula 6 ne suka yi shahada yayin da wasu kuma suka jikkata a lokacin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai harin bama-bamai a kan tantunan mutanen da suka rasa matsugunansu a yankin Al-Mawasi da ke Khan Yunis. Sannan wasu Fararen hula 10 da suka hada da kananan yara suka...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa shirin makamashin nukliya na kasar Iran kuma na zaman lafiya ya zama abin alfakhari ga mutanen kasar da daukaka. Don haka gwamnati mutanen kasar ba zasu taba yarda a barshi ba. Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da yake hira da tashar talabijin ta CBS news na kasar Amurka dangane da hare-haren da HKI da kuma Amurka suka kaiwa kasar a cikin watan yuni da ya gabata. Hare-haren da aka kaiwa kasar a dai-dai lokacinda take tattaunawa da Amurka. A wani bangare a maganars Aragchi ya bayyana cewa baya ganin Iran zata farfado da tattaunawa da kasar Amurka nan kusa. Ya ce: Idan har zamu sake shiga tattaunawa da...
Gwamnatin shugaban Donal Trump na Amurka ta bada sanarwan rage yawan wasu makaman da take aikawa kasar Ukraine. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran na nakalto majiyar Fadar Majiyar fadar white House na bayyana cewa pentagon ko ma’aikatar tsaron kasar ta bada rahoton cewa rumbun ajiyar makaman kasar yayi kasa sosai don haka akwai bukatar a dakatar da aikawa kasar Ukraine wasu makaman, kamar garkuwan kare sararin samaniya da kuma makamai masu taimaka mata wajen kare kanta. Labarin ya nakalto Anna Kelly kakakin fadar white house na cewa an dauki wannan matakin en don sanya Amurka a gaba, duk da cewa ba zata dakatar da bawa kawayenta taimakon da ya dace ba.
Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta cafke wani matashi mai shekaru 30 da ake zargin ya kashe mahaifiyarsa a Karamar Hukumar Gumel ta Jihar Jigawa. Kakakin ’yan sandan Jigawa, SP Lawan Shi’isu, ya ce matashin mai suna Hussaini Abubakar ana zargin ya kashe mahaifiyarsa, Dahara Mu’azu mai shekaru 75 da misalin karfe 8 na yammacin ranar 29 ga watan Yunin 2025. Za mu shige gaba idan aka dawo da tattauna shirin nukiliyar Iran — EU HOTUNA: An yi jana’izar Dantata a Madina SP Shiisu ya ce matashin ya jikkata mahaifiyarsa da bulon ƙasa, kuma bayan an garzaya da ita asibiti ta mutu washegari. Ya ce wannan lamari ya sanya rundunar ta gaggauta tura tawagar jami’ai kuma aka cafke matashi da a...
Cikin tawagar akwai Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Ƙasa, Yarima Lateef Fagbemi, SAN; a Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris; da Ƙaramin Ministan Harkokin Gidaje da Cigaban Birane, Hon. Yusuf Abdullahi Ata; da kuma Hassan Abdullahi, Daraktan Tsaro na Cikin Gida a ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (NSA), wanda ya wakilci NSA. Wasu fitattun malamai na addinin Musulunci da suka kasance cikin tawagar sun haɗa da Dakta Bashir Aliyu Umar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, da Limamin Masallacin Ɗantata da ke Abuja, Khalifa Abdullahi Muhammad. Jami’an Ofishin Jakadancin Nijeriya da ke Jiddah sun haɗu da tawagar, ƙarƙashin jagorancin Ambasada Ibrahim Modibbo, tare da Ambasada Mu’azzam Ibrahim Nayaya, da Manjo Janar Adamu Hassan,...
A yayin zaman, ana sa ran tattauna batutuwa da dama da suka haɗa da ’yancin ƙananan hukumomi, ƙirƙiro hukumar zaɓe ta ƙasa don kula da zaɓen ƙananan hukumomi, kafa ƴansanda na jihohi, da ƙara yawan kujerun mata a majalisun dokoki domin samun wakiltar jinsin mata. Haka kuma, za a duba ƙuduri guda shida da suka shafi inganta gaskiya da rikon amana a harkokin kuɗi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Ba za a iya kawar da fasahar nukiliya ta hanyar harin bam ba Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arakchi ya jaddada cewa: Ba za a iya kawar da fasaha da kimiyyar da ake bukata don inganta sinadarin Uranium ta hanyar kai hare-haren bama-bamai ba. A wata hira da ya yi da tashar talabijin ta CBS, Araqchi ya yi tsokaci kan ikirarin shugaban Amurka Donald Trump na cewa ana iya komawa tattaunawa da Iran a cikin wannan mako: Araqchi yana mai mayar da martini da cewa: “Ba ya jin za a dawo da tattaunawar cikin gaggawa.” Ya kara da cewa: “Kafin yanke shawarar komawa kan tattaunawar, dole ne Iran ta fara tabbatar da...
Tawagar likitocin kasar Sin ta 24 wadda ke jamhuriyar Nijer, ta ba da horon fasahar likitancin gargajiya ta Sin a babban asibitin Nijar dake birnin Yamai, wanda ya jawo hankulan mahalarta kusan 50, ciki har da manyan ma’aikatan kiwon lafiya na asibitin, da dalibai daga kwalejin likitanci ta jami’ar Yamai da kuma masu sha’awar likitancin gargajiya na Sin. Zheng Zhida, shugaban tawagar likitoci ta Sin, ya bayyana a bikin kaddamar da horon cewa, tun bayan kafa cibiyar likitancin gargajiya na Sin dake babban asibitin Nijar, duban-dubatar marasa lafiya sun amfana da ita. Ya ce horon na wannan karo ba darasi ne kawai dake bada fasahohin likitanci ba, wani aiki ne na mu’ammalar al’adu. A nasa bangare, farfesa Mamane Daou, daraktan...
Kakakin gwamnatin JMI ta bayyana cewa a dai-dai lokacinda Amurka ta kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin nukliyar kasar , babu wata tattaunawa da Amurka nan kusa, duk tare da cewa Amurkawan sun bayyana cewa za’a ci gaba da shi. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kakakin gwamnatin kasar Iran Malama Fatimah Muhajirani tana fadar haka a jiya Talata, ta kuma kara da cewa, babu wata rana da aka sanya na tattaunawa da Amurka kuma mai yuwa babu wata tattaunawa da ita nan kusa. Fatima tana maida martani ne ga wata sanarwan da gwamnatin kasar Amurka ta bayara na, na cewa nan kusa zasu sake farfado da tattaunawa da JMI. Tehran dai ta bayyana cewa bata bukatar wani...
Daya daga cikin manya manyan sojojin kasar Iran ya bayyana cewa wargajewar HKI da kuma halakar Firai ministan kasar tabbas ne babu makawa. Ya kuma gargadi makiyan JMI kan cewa duk wani kuskuren da zasu tabka sai ya sanya dukkan sansanoninsu na soje a yankin cikinbabban barazana na lalatasu. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto , Major General Yahya Rahim Safavi yana fadar haka a taron addu’a da kuma girmma marigayi Manji Janar Muhammad Baqiri babban hafsan hafsoshin kasar wanda yayi shahada a ranar Jumma’a 13 ga watan Yunin da ya gabata. Ya kuma kara da cewa babban shaitan da kuma karamin shaitan duk zasu halaka sun kasa kaiwa ga bukatunsu a yankin kwanaki 12 da suka...
Dakatar da ayyukan wuce gona da iri kan Iran wani sharadi ne na ci gaba da tattaunawar makamashin nukiliya Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin siyasa Majid Takht-e Ravanchi ya bayyana cewa: Sharadin ci gaba da gudanar da zaman shawarwarin makamashin nukiliyar Iran shi ne dakatar da duk wani matakin wuce gona da iri kan Iran, kuma har yanzu Amurka ba ta dauki wani mataki ba kan wannan batu. A wata hira da tashar BBC game da batun tattaunawar makamashin nukiliyar Iran da Amurka: Takht-e Ravanchi ya ce: “Sun ji daga Amurka cewa a shirye take ta ci gaba da tattaunawar, amma har yanzu ba a tsayar da ranar ba, kuma Iran ba ta amince da...
A bisa jagorancin Alhaji Mustapha Junaid, iyalan mamacin, da suka haɗa da matan sa da ‘ya’ya da jikokin sa, sun tarbi tawagar, kuma sun yi masu godiya. Minista Badaru ya miƙa saƙon ta’aziyya daga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana cewa, “Rasuwar Baba Aminu ta taɓa Shugaba Tinubu matuƙa. Yana addu’ar Allah ya yi masa sakayya da gidan Aljannar Firdausi, kuma yana ba dukkan iyalan sa haƙurin su yi jimirin jure wannan babban rashi.” Jakaden Nijeriya a Saudi Arebiya, Ambasada Ibrahim Modibbo, da Babban Jagoran Aikin Jakadanci, Ambasada Mu’azam Ibrahim Nayaya, da Jami’in Kula da Tsaro a Ofishin Jakadanci, Manjo Janar Adamu Hassan, duk suna cikin tawagar. Malaman da aka je da su kuma duk sun yi addu’o’i ga marigayi...
Kasar Sin ta kawo karshen aikin bayar da agajin gaggawa mafi girma a gundumar Rongjiang da ke lardin Guizhou, a yankin kudu maso yammacin kasar da misalin karfe 10 na safiyar ranar Lahadi, yayin da aka kammala ruwan saman da aka tafka kamar da bakin kwarya kamar yadda mahukuntan yankin suka bayyana. Lardin Guizhou da wasu larduna masu iyaka da shi da ke kudu maso yammacin kasar Sin sun fuskanci mamakon ruwan sama tun daga ranar 18 ga watan Yuni, lamarin da ya haifar da mummunar ambaliyar ruwa, inda lamarin ya fi muni a yankin Rongjiang. Mahukuntan yankin sun raba yankin zuwa kashi bakwai a matsayin wadanda ambaliyar ta fi shafa tare da kwashe mazauna zuwa wasu manyan wurare masu...
Ya ce a tare da shi a cikin tawagar, akwai Ministan shari’a, Antoni-janar na tarayya, Yarima Lateef Fagbemi, SAN; Ministan yaɗa labarai, Alhaji Mohammed Idris, da ƙaramin Minista a ma’aikatar gidaje, Hon. Yusuf Abdullahi Ata. Tawagar ta kuma haɗa da wasu manyan Malamai, waɗanda suka ƙunshi, Dr Bashir Aliyu Umar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da Limamin masallacin Ɗantata da ke Abuja, Khalifa Abdullahi Muhammad. Daga nan ma’aikatan ofishin Jakadancin Nijeriya da ke Jidda, ƙarƙashin Jakada Mu’azzim Ibrahim Nayaya, wanda da ma shi ke kai-kawo wajen shirya yadda jana’iazar za ta gudana, duk sun haɗu da tawagar don gudanar da ita a yau Litini. Alhaji Ɗantata dai ya rasu ne a Abu Dhabi ta Haɗaɗɗiyar Ɗaular Larabawa...
Tawagar Sarki Muhammadu Sanui II da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da Gwamnan Jigawa Umar Namadi sun sauka a Madina domin halartar jana’izar Alhaji Aminu Dantata.
Sojojin HKI sun kai falasdinawa akalla 72 ga shahada a safiyar yau Litinin, daga cikinsu har da yara kanana da kuma wadanda suke jiraran a basu taimakon abinci a cibiyoyinsu a cikin Gazzar. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a yau litinin a Gaza sojojin HKI sun kashe Falasdinawa a wurare da dama a gaza. Labarin ya kara da cewa an garzaya da wadanda suka ji ciwo zuwa asbitin Al-Ahli. Bayan haka yahudawan kai kai hare-hare a yankin Zaitun da kuma kasuwar zawiyya. Labarin ya kara da cewa baba gadaje a Asbitin don haka zaka ga wadanda suka ji ciwon kwance a kasa. Har’ila yau labaran sun bayyana cewa mafi yawan wadanda sojojin yahudawa suka kashe...
Da yake jawabi jim kadan kafin tashinsa a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, Gwamna Yusuf ya bayyana marigayi Dantata a matsayin uba ga mutane da yawa, wanda karamcinsa da sadaukarwarsa ya wuce iyaka. Gwamnan ya jaddada cewa, zuwan tawagar a Madina shaida ce ta matukar mutuntawa da jama’a da gwamnatin jihar Kano suke yi masa na gadon alkairai da ya bari kuma a matsayinsa na dattijon jihar. Ana sa ran jana’izar da za a yi a birnin Madina, za ta samu halartar wakilan jiha da na tarayya, da ‘yan uwa, ‘yan kasuwa, malaman addinin Islama, da masoya daga sassan duniya baki daya, tare da yin addu’ar Allah ya jikansa. Daga kanmu, magana ta ƙare....
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wannan ne ma dalilin da yasa wasu ke ganin hadakar za ta iya yin karfi kwarai da gaske, kasancewar ta samu wakilci a sassa daban-daban na wannan kasa. Dalili kuwa shi ne, ‘yansiyasa ne da a baya suka samu damar rike manya-mnyan mukamai, sannan kuma har zuwa yanzu yana da tasiri a fagen siyasar kasar yadda ya kamata. Manya-manyan jiga-jigan da ake gani a cikin wannan sabuwar tafiya ta hadakar jam’iyyar sun hada da: Jagoran adawa a kasar, wanda a baya ya sha yin takarar shugabancin kasa, sannan kuma ko a shekarar 2023 shi ne ya zo na biyu bayan da ya samu kuri’a kusan miliyan bakwai. Alhaji Atiku Abubakar, wanda a yanzu dan jam’iyyar PDP ne; ya kasance guda...
Jagoran wannan sabuwar tafiya kuma tsohon sakataren gwamnatin Jihar Katsina, Mustapha Inuwa ne ya bayyana haka a lokacin da tsaffin ‘yan takarar suka je ofishinsa domin jadadda goyon bayansu kan sabuwar tafiya. Shi ma da yake magana a madadin sauran ‘yan takarar majalisar dokokin jiha a zaben 2023, Hon. Jamilu Yahaya ya bayyana cewa sun fice daga jam’iyyar PDP ne saboda yadda aka nisantar da su daga al’umma wanda su ne ke yin zabe. A nashi bangaren, shugaban ‘yan takarar shugabancin kananan hukumomi, Hon. Yasir Ibrahim ya ce sun shiga wannan hadaka ne saboda irin yaudarar shugabanci da aka yi masu a tsohuwar jam’iyyar PDP da ke fama da rikice-rikice. Da yake nasa tsokaci, shugaban tsaffin ‘yan takarar kansiloli na...
Masu bincike sun gano cewa sojojin HKI sun kashe Falasdinawa akalla 100,000 tun bayan fara yakin tufanul Aksa a ranar 7 ga watan Octoban shekara 2023. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kan cewa farfesa Michael Spagat da kuma Khalil Shikaki Bafalasdine masanin masanin fasahar siyasa a Jami’ar London na kasar Burtania suka jagoranci bincike wanda ya kai ga fitar da wannan sakamakon. Labarin ya kara da cewa masu binciken sun kiyasta mutane a gidaje 2000 a birnin Gaza kadai wanda falasdinawa kimani 10,000 suke rayuwa, sannan suka yi lissafi suka kaim ga wannan sakamakon. Bincike ya kara da cewa daga watan jenerun shekara ta 2025 falasdinawa 75,200 sojojin yahudawan suka kashe da makamai, sannan wasu kimani...
Wasu daga cikin jami’an sojojin HKI sun yi furuci da cewa, an ba su umarni ne da su rika bude wuta akan Fararen hula Falasdinawa da suke zuwa cibiyoyin karbar kayan agaji, suna jaddada cewa, wadanda su ka kashe din ba su yin wata barazna a gare su. Jaridar “Haarezt” ta ‘yan sahayoniya ta buga rahoton da ya kunshi furucin sojojin nasu da su ka tabbatar da cewa; An ba su umarni ne da su rika harbin duk wanda su ka gani a kusa da cibiyoyin raba kayan abinci. Jaridar ta kuma ce; Sojojin sun yi amfani da kowadanne irin bindigogi da su ka hada da manya wajen harbin fararen hula Falasdinawa. Yawan Falasdinawan da su ka yi shahada a...
Tashar talabijin din Aljazira ta bayar da rahoton da yake cewa; Rashin abinci mai gina jiki da karewar madarar jarirai a yankin Gaza, ya sa jarirai biyu sun yi shahada. Majiyar asibitin Nasar ta a birnin Khan –Yunus dake kudancin Gaza, ta ambaci cewa jariran biyu sun rasa ransu ne saboda rashin abinci mai gina jiki da kuma madarar jarirai.
Hukumar samar da bunkasa da hadin gwiwar kasa da kasa ta kasar Sin ta gabatar da taron manema labarai a yau Juma’a, inda aka yi karin haske game da yadda Sin take baiwa kasashen Afirka tallafi da samun bunkasa tare da su cikin hadin gwiwa. An ce, ya zuwa yanzu, Sin tana taimakawa kasashen Afirka fiye da 21 a bangaren kimiyyar aikin gona, inda ta tura musu kwararrun aikin gona fiye da 200. Kazalika, bangarorin biyu suna hadin gwiwa wajen gudanar da ayyukan dake da nasaba da na’urorin wutar lantarki da horar da kwararru da habaka da karfinsu da sauran bangarori. Kana suna kaddamar da ayyukan samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, ciki har da samar da...
“Wannan ya nuna dalibai, 96,838 zasu rubuta jarabawa a fadin Nijeriya gaba daya duk ta wannan shekarar ce, 2025,a cibiyoyin rubuta jarabawa,183,yayin da wasu kuma za su jira.” Hakanan ma Hukumar tace tana nan tana bankado cibiyoyin rubuta jarabawa da ake yin cuwa- cuwa, da kuma wadanda basu cancanta, ace n arubuta jarabawar a wuraren ba, saboda rashin ingancin abubuwan da ake amfani da su lokacin jarabawar. Akwai wuraren/ cibiyoyin rubuta jarabawa wadanda aka tantance hakan kuwa ya biyo baya binciken kwakwaf da aka yi lokacin da aka yi jarabawar ta gwaji, jarabawar ta sosai,da wadda aka sake rubutawa.Kamar yadda aka bayyana, kuma kamar yadda sakamakon bincike-binciken da aka yi, akwai cibiyoyin rubuta jarabawa,113 wadanda yanzu an dakatar da amfani...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Cristiano Ronaldo ya sanya hannu kan yarjejeniyar tsawaita kwatiraginsa da shekara biyu a ƙungiyar Al Nassr da ke buga gasar Saudi Pro League. Wannan dai na nufin kyaftin din na tawagar Portugal zai ci gaba da zama a ƙungiyar har 2027, lokacin da zai kai shekara 42 a duniya. Sheikh Dahiru Bauchi ya cika shekara 101 a duniya Gwamnatin Katsina ta amince da ƙidayar almajirai, makarantun Islamiyya Al-Nassr ta bai wa Ronaldo kwantiragi mafi tsada a tarihin wasanni, inda ya rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniyar fam miliyan 24.5 ($33.7m), lamarin da zai ba shi damar samun albashin da zai rika karbar sama da fam miliyan a duk kwana biyu. Ɗan wasan mai shekara 40 ya je Al Nassr ne a...
Ban da haka kuma, wani babban dalilin da ya sa kasar Sin ke kokarin tallafa wa sauran kasashe a fannin aikin likitanci, shi ne akidarta ta “kafa al’ummar duniya mai kyakkyawar makoma ta bai-daya”. A cikin gidan kasar, an yi nasarar kawar da talauci, da kokarin neman wadatar da dukkan al’ummun kasar, lamarin da ya sa ake samun jituwa a tsakanin al’umma, da ci gaban tattalin arziki mai dorewa. Saboda haka, kasar Sin na ganin cewa, kamata ya yi, a yi kokarin tabbatar da ci gaban tattalin arzikin kasashe daban daban na bai-daya, inda za a dinga rage gibin dake tsakanin kasashe, da na zaman rayuwar al’ummu daban daban, ta yadda za a iya daidaita matsalolin da dan Adam ke...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Benuwe, sun kama mutum biyar da ake zargi da hannu a kisan wasu matasa biyu ’yan asalin Jihar Kano. Waɗanda aka kashe sun haɗa da Jamilu Ahmad da Barhama Suleiman, kuma an kai musu hari ne cikin daren ranar Litinin a unguwar Agan, kusa da ƙofar shiga Makurdi. Gwamnatin Neja ta rufe Jami’ar IBB bayan ɓarkewar rikici 2027: Zan karɓi kowane irin muƙami da Tinubu zai ba ni — Sanata Barau An yi jana’izarsu a ranar Talata a Babban Masallacin Abuja, inda manyan jami’ai suka halarta, ciki har da Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro, Malam Nuhu Ribadu, da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf. An birne su a maƙabtar Gudu, inda Ribadu da Gwamna...
Dan wasan mai shekaru 40 ya zura kwallaye 93 sannan ya taimaka wajen zura 19 a wasanni 105 da ya buga a dukkanin wasannin da ya buga a kungiyar ta Saudiyya, amma har yanzu bai samu nasarar lashe kofi a gasar ba, a kakar wasan da aka kammala kwanan nan, Al Nassr ta kare a matsayi na uku a teburin, inda ta rasa gurbi a gasar cin kofin zakarun yankin Asia na shekara mai zuwa kuma a maimakon haka za ta buga gasar AFC Champions League 2. Bugu da kari, Al Nassr a halin yanzu ba ta da koci tun bayan da ta raba gari da babban kocinta Stefano Pioli a ranar Laraba, wanda ya zama koci na uku...

Gwamnan Jigawa Ya Kaddamar Da Rumbun Sauki Don Sayar Wa Ma’aikata Kayayyakin Abinci A Farashi Mai Rahusa A Sakkwato
Tun da farko, Gwamna Aliyu ya ce, gwamnatinsa ta bullo da shirin ne domin ta saukaka farashi da kashi 20 ta hanyar saukar da farashin kayan abinci kasa warwas. Gwamnan ya ce, an tsara shrin ne domin saukakawa ma’aikatan jiha, na kananan hukumomi da masu karbar fansho ta hanyar samar da nau’ukan kayan abinci kamar shinkafa, gero, alkama, masara, dawa, man girki da taliya a cikin farashi mafi sauki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce wakilan ƙasarsa za su gana da na Iran domin ci gaba da tattaunawa kan makaman nukiliyarta a mako mai zuwa. “Za mu tattauna da Iran a mako mai zuwa, ƙila mu ƙulla yarjejeniya ko kuma akasin haka, ba na ce ba,” in ji shi yayin jawabinsa a taron ƙasashe na ƙungiyar ƙawancen tsaro ta NATO da ake yi a ƙasar Netherlands. ’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 2, sun kama wasu a Kaduna An ɗaure mutum 6 shekaru 120 kan satar yara a Kano “Ba su daɗe da gama yaƙi ba, yanzu za su ci gaba da harkokinsu. Ban damu dole sai na ƙulla wata yarjejeniya da su ba,” a cewarsa. A jiya Talata...
Sanarwar ta ƙara da cewa, aikin Sahara ba wai kawai aikin jaridar bogi ba ne; ya samo asali ne zuwa da suna ‘Gonzo’, wanda ke da alaƙa da ƙarairayi wajen bayar da rahoto. Sanarwar ta ci gaba da cewa: “An ja hankalinmu kan labaran ƙarya da Sahara Reporters ke yaɗawa, shafin da ya shahara wajen yaɗa labaran ƙarya domin tayar da ƙura a intanet. “A yayin tattaunawa da manema labarai kai tsaye a makon da ya gabata, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana ƙudirinsa na ɗaukar nauyin kasafin kuɗi, inda ya tabbatar da cewa bai karbi lamuni na cikin gida ko na ƙasashen waje ba tsawon shekaru biyu da ya yi yana mulki. “Amma abin ya ba mu...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya bayyana matukar damuwar da Sin ke da ita dangane yanayin da yankin Gabas ta Tsakiya ke ciki, tare da bayyana fatan ganin an tsagaita bude wuta tsakanin Isra’ila da Iran nan bada jimawa ba. Guo Jiakun ya bayyana haka ne yayin taron manema labarai na yau Talata, lokacin da yake tsokaci game da rahotannin dake cewa shugaban Amurka Donald Trump, ya sanar da cewa an cimma cikakkiyar yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Isra’ila da Iran. Kakakin ya kuma nanata cewa shaidu sun riga sun nuna cewa, matakan soji ba za su kawo zaman lafiya mai dorewa ba, kuma yarjejeniya da tattaunawa su ne kadai hanyoyin warware rikice-rikice. Ya kara da cewa,...
Mataimakin shugaban majalisar dattijai, Jibrin Barau, ne ya sanar da kudirin bayan amincewa da rahoton kwamitin majalisar dattawa kan samar da kayayyaki. Adeola ya ce, karin wa’adin ya zama dole domin baiwa gwamnatin tarayya damar kammala wasu manyan ayyuka da suka samu jinkiri sakamakon karancin kudaden shiga. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Iyalan mafarauta 16 ’yan Jihar Kano da aka yi wa kisan gilla a garin Uromi da ke Jihar Edo sun yi zargin cewa gwamnati ta yi watsi da su. Wasu daga cikin waɗanda suka tsallake rijiya da baya a harin da kuma iyalan waɗanda aka kashe, sun bayyana cewa alƙawarin kuɗin magani da tallafi da kuma diyya fa gwamnatocin jihohin Edo da Kano suka yi musu bai wuce fatar baki ba. Ayarin farautan sun baro garin Fatakwal na Nijar Ribas ne, a hanyarsu ta komawa gida domin bikin Ƙaramar Sallah, amma wasu ’yan banga a Uromi suka tare su, suka yi musu kisan gilla. Akasarin mafarautan sun fito ne daga yankin Toronkawa da ke Ƙaramar Hukumar Bunkure ta Jihar Kano,...
2. Gyaran zaɓe da shari’o’in zaɓe 3. Ƙirƙirar sabbin jihohi 4. Samar da Ƴansandan jihohi 5. Haɗa kai don gudanar da mulki Daga cikin muhimman shawarwari, akwai na kafa hukumar zaɓen ƙananan hukumomi (NALGEC), ƙara kujeru ga mata a majalisu, da ba wa ‘yan Nijeriya dake ƙasashen waje damar yin zaɓe. Hakanan, akwai shawarwarin sauya wasu abubuwa daga jerin abubuwan da majalisar tarayya ke da ikon yi zuwa na majalisun jihohi, da kuma ƙirƙirar Majalisar Sarakuna ta ƙasa. Kwamitin ya yi kira ga duk ‘yan ƙasa da su halarci tarurrukan sauraron ra’ayin jama’a da za a gudanar a: – Lagos (Kudu maso Yamma) – Enugu (Kudu maso Gabas) – Ikot Ekpene (Kudu maso Kudu) – Jos (Arewa Tsakiya) – Maiduguri...
Ya nanata cewa nasarar da aka samu ya zuwa yanzu ta samo asali ne sakamakon kyawawan tsare-tsare, ingantaccen jagoranci, da kuma kula da albarkatu. Gwamnan ya bayyana cewa an samu ci gaba sosai a harkar tsaro a jihar idan aka kwatanta da abin da ya gada a shekarar 2023. A cewar sa, inganta haɗin gwiwa da jami’an tsaro ya taka muhimmiyar rawa wajen rage yawaitar ayyukan ‘yan bindiga da sauran miyagun ayyuka a Zamfara. Dangane da ababen more rayuwa kuwa, Gwamna Lawal ya ba da misali da ayyukan da ake ci gaba da aiwatarwa da kuma waɗanda aka kammala a ƙarƙashin shirin “Renewal Project,” wanda ya haɗa da gine-gine da gyaran hanyoyi, makarantu, da cibiyoyin kiwon lafiya...
Aƙalla mutum biyar ne aka tabbatar da rasuwarsu, yayin da wasu 15 suka jikkata sakamakon fashewar wani bam a Jihar Kano. Aminiya ta gano yadda fashewar bam ɗin ya haddasa firgici a yankin da lamarin ya faru, inda jami’an tsaro da na agajin gaggawa suka garzaya wajen don kai ɗauki. An yi wa ma’aikatan ƙananan hukumomin Gombe ƙarin albashin N5,000 Mahara sun kashe ’yan ɗaurin aure 12 daga Zariya a Filato Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya ce fashewar na iya kasancewa bam ɗin da sojoji suke yin jigilar ne wanda aka yi sakaci ya fashe. “Na samu kiran gaggawa cewa wani abu mai tayar da hankali ya faru. Da na isa wajen, sai na ga abin...
Idris, wanda shi ne ya jagoranci zaman, ya bayyana irin nasarorin da aka samu a ƙarƙashin jagorancin Babban Hafsan Tsaro da sauran Hafsoshin Sojin a matsayin mai tabbataccen tasiri da gamsasshen sakamako. Ya ce: “Abin da muka gani ba wai kawai daƙile waɗannan barazanar ba ne, sai dai ma sake karɓe sararin ƙasar mu, da tunanin jama’a, da kuma a matakin aiki. Yanzu ‘yan Nijeriya za su iya tabbatar da cewa manyan hanyoyin mu sun fi samun tsaro ƙwarai idan aka kwatanta da ‘yan shekarun baya.” Ya lissafa nasarorin da rundunonin sojin Nijeriya suka samu a sassa daban-daban na ƙasar nan, ciki har da yankin Arewa-maso-gabas da gaɓar teku. “Daga nasarar ragargaza sansanonin Boko Haram da ISWAP...

Jakadan Sin Dake Amurka Ya Yi Jawabi A Gun Liyafar Da Kwamitin Kasa Mai Lura Da Kasuwancin Amurka Da Sin Ya Shirya
Kwamitin kasa mai lura da kasuwancin Amurka da Sin ko USCBC, ya gudanar da liyafar murna ta shekarar 2025, a ranar Laraba 18 ga wata a birnin Washington na Amurka, liyafar da jakadan kasar Sin a Amurka Xie Feng ya halarta tare da gabatar da jawabi. Cikin jawabin nasa jakada Xie ya ce cimma moriya da nasara tare, muhimman ginshikai ne na ci gaba mai dorewa na hadin-gwiwar Sin da Amurka ta fuskar raya tattalin arziki da kasuwanci, inda dukkan bangarorin biyu gami da duniya ke cin gajiya. A halin yanzu, habakar tattalin arzikin duniya na tafiyar hawainiya, kuma kara hada kai ita ce mafita daya tilo ta shawo kan hakan. Ya ce ci gaban kasar Sin zarafi ne ga...
Gwamnatin Jihar Sakkwato ta ce ba gazawa ba ce ta sa ta yanke shawarar tattaunawa da ’yan bindigar da suka yanke hukuncin ajiye makamansu ba. Ta ce wannan hanya ce mafi kyau da za ta kawo zaman lafiya mai ɗorewa a jihar. Katolika ta horar da shugabannin al’umma da na addini kan zaman lafiya Kotu ta daure mutumin da yake yada bidiyon tsiraici shekara 76 a kurkuku Wani mai amfani da kafar sada zumunta, Basharu Altine Guyawa, ya soki wannan mataki na gwamnatin. Amma Mai Bai Wa Gwamnan Jihar Shawara kan Tsaro, Kanal Ahmed Usman (mai ritaya), ya ce manufar gwamnati ita ce ta kawo zaman lafiya, ba don ta kasa ba. Ya ce, “Mun san kowa na da ‘yancin...
Barcelona ta amince da yarjejeniyar ɗaukar ɗan wasan gaba na ƙungiyar Athletic Bilbao Nico Williams, amma kuma har yanzu akwai ƙalubalen da zasu fuskanta kafin ɗan wasan ya samu damar rattaba hannu a ƙungiyar ta Catalonia, ɗan wasan na ƙasar Sifaniya Williams, wanda ya zura ƙwallaye 31 a wasanni 167 da ya buga wa Bilbao, ya janyo hankalin ƙungiyoyin Arsenal da Bayern Munich a bana. Amma ɗan wasan mai shekaru 22 ya amince da kwantiragin shekaru shida a Barcelona, wanda hakan zai sa ya hadu da abokinsa kuma abokin wasansa a matakin ƙasa Lamine Yamal a Nou Camp, Williams ya buƙaci Yamal da ya taimaka masa wajen zuwa Barcelona, bayan kakar da ya yi a Bilbao inda ya taimaka musu...
Brig.-Gen. Abu-Mawashi ya kara da cewa an kama ‘yan ta’adda 14,138 da sauran masu aikata laifuka yayin da aka ceto mutane 5,365 a cikin wannan lokaci. Abu-Mawashi ya ci gaba da cewa, sojojin sun kwato daruruwan makamai da kuma harsashi da yawa duk acikin wannan lokaci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ce matsalar da ke addabar jam’iyyar PDP ba ta tsaya kan Atiku Abubakar kaɗai ba, face tana da nasaba da girman kai tsakanin shugabannin jam’iyyar. Da yake magana da manema labarai a ranar Laraba, Gwamna Lawal ya ce: “Kowa yana da nasa matsalar; ba kan Atiku Abubakar kawai ba ne; ta wuce hakan.” An ɗaure mutum 7 kan yi wa ɗan sanda rauni a Kano ’Yan bindiga sun kashe manoma 24 a Katsina “Matsala ce daga cikin gida… Na ga matsalar tana da alaƙa da girman kai, ba a bar kowa a baya ba.” Da aka tambaye shi ko yana daga cikin masu haddasa matsala a cikin jam’iyyar, ya amsa cewa yana ciki. Gwamna...
Ya ce duk da cewa akwai damuwa kan yadda za a aiwatar da hakan, Gwamnatin Tarayya na da damar tsara ƙa’idoji da dokoki na musamman ga kowace jiha don hana amfani da ‘yansandan wajen cin zarafi. A halin yanzu, gwamnonin jihohi daga faɗin Nijeriya na gudanar da wani taron gaggawa a Babban Birnin Tarayya, wanda ke gudana a sakatariyar Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF). Taron ya samu halartar gwamnonin jihohi da mataimakansu daga dukkanin jihohi 36 na ƙasar. Koda yake ba a bayyana cikakken ajandar taron ba, kasancewar mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, da Ministan Tsaro, Mohammed Badaru, na cikin mahalarta taron, ya nuna cewa batutuwan tsaro ne ke kan gaba a tattaunawar. Taron na...
A yayin ƙaddamar da asibitin ƙwararrun, tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya buƙaci gwamna Lawal da ya ci gaba da gudanar da ayyukan ceto har sai Zamfara ta kasance ɗaya daga cikin manyan jihohin Nijeriya. Tsohon shugaban ƙasar ya ce: “A yau ina jihar Zamfara ne domin na ga ingantacciya, wadda ta ci gaba, mai ci gaba kuma sabuwar Zamfara a ƙarƙashin jagorancin ka. “Ga mu nan. Abubuwa biyu sun ba ni mamaki: Kwamishinan lafiya ya bayyana cewa kun samar da na’urorin CT scan da MRI Machine, na san wasu asibitocin koyarwa ba su da CT scan da MRI, wasu kuma suna da shi amma ba sa aiki. Ku ga na ku, yana aiki ga al’umma. “Na...
Alhazai 442 sun tsallake rijiya da baya, bayan jirgin da ya ɗauko su bayan sun kammala aikin Hajjin bana ya samu sakon cewa an dasa bom a cikinsa a yayin da yake sararin samaniya a ƙasa Indonesiya. A ranar Talata ne jirgin, mallakin kamfanin Saudia Air, ya yi saukar gaggawa a birnin Jakarta babban birnin ƙasar Indonesiya, bayan da ya ɗauko alhazan da daga birnin Jidda na ƙasar Saudiyya. ’Yan sanda ƙasar Indonesiya sun ce an yi nasarar fitar da ɗauƙacin fasinjojin jirgin su 442 a filin jirgi da ke lardin Sumatra ta Arewa. Ma’aikatar Sufuri ta ƙasar Indonesiya ta ce jirgin ya yi saukar gaggawa ne bayan samun wani saƙon imel cewa an sanya bom a jirgi. Sarki ya...
Shugaban Ƙasar Amurka, Donald Trump ya ce yana neman ganin an kawo karshen rikicin nukiliyar ƙasar Iran gaba ɗaya, a yayin da aka shiga kwana na biyar a yaƙin da ya ɓarke tsakanin Iran da Isra’ila. Trump ya bayyana shirinsa na tura manyan jami’an ƙasarsa zuwa birnin Tehran domin tattaunawa da hukumomin Iran a game da lamarin. Ya bayyana haka ne a yayin da yake hawa jirgi domin barin ƙasar Kanada, inda ya halarci taron ƙasashen G7. A yayin taron, shugabannin ƙasahen sun bayyana Iran a matsayin barazana, da bai kamata a bari ta mallaki makaman nukiliya ba. A ɗaya bangaren kuma sun bayyana ’yancin Isra’ila na kare kanta. Matatar man Isra’ila ta daina aiki bayan harin Iran Sarki ya...
Ministan harkokin wajen kasar Rwanda Olivier Nduhungirehe ya bayyana cewa, kwakkwaran zumunci da ake sadawa a aikace a tsakanin Rwanda da kasar Sin na yin tasiri mai kyau ga al’ummar Rwanda. A cikin wata hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, yayin bikin baje kolin tattalin arziki da cinikayya na Sin da Afirka karo na hudu (CAETE) da aka gudanar daga ranar 12 zuwa 15 ga watan Yuni a birnin Changsha, babban birnin lardin Hunan na tsakiyar kasar Sin, Nduhungirehe ya kara da cewa, “Muna da kyakkyawar alaka da kasar Sin.” Ya yi karin haske game da hadin gwiwa mai fadin gaske a tsakanin kasashen biyu a fannonin kiwon lafiya, ilimi, aikin gona, fasaha da makamashi. Yana mai cewar, “Muna...
“A yankin Arewa ta Tsakiya, ana sa ran za a yi tsawa da sanyin safiya a sassan jihohin Benuwe, Filato, Neja, Babban Birnin Tarayya, da Jihar Nasarawa. “A washegari, ana hasashen tsawa da ruwan sama a wasu sassan babban birnin tarayya, Neja, Nasarawa, Benuwe, Kwara, Kogi, da Filato. “A yankin Kudu, ana sa ran samun hadari tare da yiwuwar samun ruwan sama a sassan jihohin Enugu, Ebonyi, Cross River, Legas, Akwa Ibom, Ribas, da Bayelsa,” in ji NiMet. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...

Iran Ta Sanar Da Dakatar Da Tattaunawa Da Amurka A Wannan Lokaci Da Take Fuskantar Yaki Daga Isra’ila
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewa: Babu wata tattaunawa da zata yi da Amurka a halin da take ciki na kare kanta A yayin da haramtacciyar kasar Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare kan yankunan kasar Iran, a hukumance Iran ta bayyana rashin yiwuwar ci gaba da zaman tattaunawa da Amurka kan batun shirinta na makamshin nukuliya, tare da dora wa Amurka alhakin abin da ke faruwa kai tsaye. Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Akwai hadin kai tsakanin haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka wajen kai hare-hare kan kasar Iran domin rusa zaman tattaunawar nukiliya da haka ke bayyana kawar da duk wata magana ta hakikanin aniyar Amurka na samar da hanyar warware takaddamar Shirin Iran...
Ministan harkokin wajen Omani Badr Albusaidi ya sanar da cewa, ba za a gudanar da zagaye na shida na tattaunawar nukiliya tsakanin Iran da Amurka ba. Yau Lahadi ne aka shirya gudanar da zagaye na gaba na shawarwari a Muscat babban birnin kasar Oman. A cikin wani sakon da ya wallafa a kan X (tsohon Twitter), Albusaidi ya tabbatar da sokewar, yayin da ya jaddada cewa “diflomasiyya da tattaunawa sun kasance hanya daya tilo ta samun zaman lafiya mai dorewa.” “Tattaunawar Iran da Amurka, wadda aka shirya gudanar da ita a birnin Muscat ranar Lahadin nan, ba za ta gudana a yanzu ba. Tattaunawar diflomasiyyar da aka faro kan shirin nukiliyar Iran, a watan Afrilu a shiga tsakanin masarautar Oman,...
A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta fitar, ta yi tir da harin na Isra’ila akan Iran tare da bayyana cewa, ya haifar da rikici a tsakanin bangarorin biyu da kuma musayar harba makamai masu linzami. Gwamnatin ta Najeriya ta nuna bakin cikinta akan abinda ya faru, tare da kuma da yin kiran a tsagaita wutar yaki da gaggawa, da kai zuciya nesa. Har ila yau, sanarwar ma’aikatar harkokin wajen ta Nigeria wacce kakakinta Kimiebi Imomotimi Ebienfa ya rattabawa hannu a yau Asabar,14 ga watan Yuni 2025, ta jaddada cewa; yaki ba zai maye gurbin tattaunawa ba, kuma hanyar diplomasiyya ce za ta kai ga samar da zaman lafiya mai dorewa, girmama juna da aiki da dokokin kasa...
Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakci wanda ya tattauna ta wayar tarho da jami’ar harkokin waje ta tarayyar turai ya bayyana cewa, ci gaba da tattaunawa a tsakanin Iran da Amurka ba shi da wata ma’ana, kamata ya yi jami’an tarayyar turai din su yi Allawadai da wuce gona da irin HKI akan Iran. Da safiyar yau Asabar ne dai jami’ar diplomasiyyar ta turai Kaja Kallas ta kira yi minsitan harkokin wajen jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakci inda su ka tattauna halin da ake ciki a yammacin Asiya da ya hada da harin da HKI ta kawo wa Iran. Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana harin na HKI da cewa, wuce gona da iri ne da...
Ba tare da saninmu ba, yawancin al’ummar Afirka musamman ma naYammacin Afirka suna fama da abinda ake kira da suna irin hali ko yanayin da aka shiga sanadiyar lamarin cinikin Bayi.Bayan shekara 100 da aka yi daga shekarar 1801 zuwa 1901, an yi wani kokarin da ake yi ma kallon tamkar wani takune na yadda za’a kubuta daga irin cin fuskar da ake yi kowace rana. Kafin dai a tsunduma sosai cikin lamarin cinikin Bayi, yana da matukar kyau a fara yin bayani kan yadda abin ya fara:Lamarin cinikin Bayi ba manufa bace ta Yammacin Turai.Duk lamarin ya zarce wani hasashen da za’a iya yi ko wani rubutun,da aka yi aka aje.Idan kuma aka duba ta bangaren nahiyar Afirka ita...
Jami’in kungiyar Hamas ya bayyana cewa: Kakkausan martanin da Iran ta mayar ya tabbatar da cewa babu mai girman kai da ba zai fuskanci mayar da martani ba Izzat al-Rishq mamba na ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya jaddada cewa: Kakkausan martanin da Iraniyawa suka mayar ya tabbatar da cewa; babu mai girman kai da ba zai fuskanci mayar da martani kan zaluncinsa ba, kuma babu wuce gona da iri ba tare da hukunci ba. Izzat al-Rishq ya yi nuni da cewa: Tabbas makamai masu linzami da jiragen saman yaki marasa matuka ciki na Iran sun yi nasarar kai wa cikin tsakiyar haramtacciyar kasar Isra’ila, duk kuwa da kace-nacen da ake yi na girke na’urorin kakkabo makamai...
Bayan hakan, Pogba ya kunce kwantiraginsa da Juventus a watan Nuwamban 2024, kuma tun watan Maris da ya gabata ya samu damar komawa fili domin shirya dawowarsa. Yanzu haka yana ci gaba da atisaye tare da fatan ƙulla sabuwar yarjejeniya da Monaco domin ci gaba da taka leda a ƙasarsa ta haihuwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kwanaki takwas bayan wata mummunar ambaliyar ruwa da ta mamaye garin Mokwa, hedikwatar Ƙaramar hukumar Mokwa a Jihar Neja, an gano gawar mutum ɗaya daga cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su. Mazauna garin sun shaida wa Daily Trust cewa, an tsinci gawar ne a ranar Alhamis a wata gona da ke kan hanyar wucewa kusa da wani wuri da aka fi sani da ‘dam’. Ambaliya: Gwamnatin Kano ta fara tsaftace magudanan ruwa Abin da muke da shi a Najeriya ba cikakkiyar dimokuraɗiyya ba ce — Fayemi A cewar shaidun gani da ido, an kasa tantance wanda abin ya shafa saboda gawar ta lalace. An binne shi ne a inda aka gano gawarsa. Wata mazauniyar yankin mai suna Tswata Mai...
A cewar Bawa, gwamnatocin da a karkashinsu aka wawashe dukiyar kasa, su ne na Mulkin Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo (daga 1999 zuwa 2006), sai Marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’Adua (daga 2007 zuwa 2009), kazalika a mulkin Shugaba Goodluck Jonathan daga (2010 zuwa 2014), sai kuma mulkin Muhammadu Buhari (daga 2015 zuwa 2023). Wadannan bayanai na kunshe cikin littafin, ‘The Shadow Of Loot and Loss – Uncobering Nigeria’s Petrol Subsidy Fraud,’ wanda tsohon sarkin yaki da cin hanci da rashawa ya rubuta. Alkaluman da Bawa ya bayyana daga cikin gwamnatocin hudu, shugaba Buhari ne ke kan gaba wajen biyan tallafin da ake ta cece-kuce akai na Naira tiriliyan 11, sai kuma na Jonathan wanda ya kashe Naira tiriliyan 3.9. Gwamnatin...
An sanar da tashin shi daga City kafin karshen kakar wasa ta bana, kuma De Bruyne ya yi bankwana da magoya baya a filin wasa na Etihad bayan wasansa na karshe a gida da suka buga da Bournemouth a watan Mayu, City ta yi kokarin cike gibin da De Bruyne ya bari, yayinda ta dauki yan wasan tsakiya Tijjani Reijnders daga AC Milan da Rayan Cherki daga Lyon. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A yayin da ake tsaka da bikin Ranar Dimokradiyya a Najeriya, al’ummar jihar Gombe sun wayi gari da sabuwar dokar takaita zirga-zirgar babura daga ƙarfe 7:00 na yamma zuwa ƙarfe 6:00 na safe a duk faɗin jihar. Sanarwar da ta fito ne daga hannun Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’Yan Sanda ta jihar, DSP Buhari Abdullahi, ranar Alhamis, a madadin kwamishinan ’yan sandan jihar Bello Yahaya. Sanarwar ta ce an kafa dokar ne don rage ayyukan ta’addanci a fadin jihar. Guguwa ta hallaka mutum 6, ta jikkata 30 a Taraba An kashe mutum 41 cikin mako ɗaya a Filato Kafa dokar na zuwa ne kwana uku bayan wasu matasa da ba a tantance su wane ne ba suka kashe...
Haka kuma, ya zargi Matawalle da karɓar Naira miliyan 300 daga tsohon gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari, don a sako ɗaliban, amma ya bai wa ‘yan bindiga miliyan 30 kacal. APC ta ƙaryata wannan zargi. Ta kuma bayyana cewa zargin Kaura yana shafar wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar kamar tsohon Gwamna Abdulaziz Yari, wanda yanzu ke wakiltar Zamfara ta Yamma a Majalisar Dattawa. Jam’iyyar APC ta ƙalubalanci Kaura da ya kawo hujjoji kan wannan zargi da kuma wasu mutane da aka sace a jihar, kamar satar ɗalibai mata 270 daga makarantar Government Girls Secondary School da ke Jangebe a ranar 26 ga watan Fabrairun 2021, da kuma satar ɗaliban Kwalejin Noma da Kiwo da ke Bakura. APC ta jaddada cewa gwamnatin...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Inganta sinadarin Uranium da ɗage takunkumai na iya sa tattaunawar ta yi amfani Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya rubuta cewa: A bayyane yake cewa cimma yarjejeniyar da za ta tabbatar da zaman lafiya na dindindin na shirin makamashin nukiliyar Iran abu ne mai yiyuwa, kuma ana iya cimma shi cikin sauri. Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya rubuta a shafinsa na Twitter game da sabon zagayen tattaunawa tsakanin Iran da Amurka da kuma matsayin Iran a kansu yana mai cewa: Shugaba Trump ya bayyana a lokacin da ya shiga fadar White House cewa ba lallai ne Iran ta mallaki makamin nukiliya ba, wannan matsayi ya yi daidai da akidar Iran...

He Lifeng Ya Bukaci Amurka Da Ta Warware Takaddamar Cinikayya Da Sin Ta Hanyar Tattaunawa Da Hadin Gwiwa
Mataimakin firaministan Sin He Lifeng, ya bukaci Amurka da ta warware takaddamar cinikayya da Sin ta hanyar tattaunawa, da hadin gwiwa da zai iya haifar da moriyar bai daya. He, ya ce Sin na jaddada burin ganin Amurka ta yi aiki da bangaren Sin, ta yadda za a martaba alkawura da matakai da aka amince, da nuna sahihanci wajen yin aiki tukuru, da aiwatar da gaskiya da kwazo wajen aiwatar da matsayar da aka cimma, ta yadda za a kai ga kare nasarorin da aka cimma ta hanyar shawarwari. He, ya yi tsokacin ne yayin taron farko na shawarwari game da harkokin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka, wanda ya gudana a ranakun Litinin da Talata a birnin...
Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, zai yi wa ’yan Najeriya jawabi da misalin ƙarfe 7 na safiyar ranar Alhamis, domin bikin ranar dimokuraɗiyya na 2025. A cewar wata sanarwa daga kwamitin shirya bikin, shugaban ƙasa zai kuma je zaman haɗin gwiwa da ’yan majalisar dokoki da rana. Na shirya yin haɗaka don ƙalubalantar Tinubu a 2027 – Amaechi Majalisar Dokokin Kuros Riba ta dakatar da shugabar ƙaramar hukuma na wata 3 Sanarwar ta kuma bayyana cewa ba za a yi faretin bikin a bana ba. A maimakon haka, za a yi muhawara da jama’a a fadar shugaban ƙasa da misalin ƙarfe 4 na yamma. Bikin bana na zuwa ne yayin da Najeriya ke cika shekara 26 a gwadaben mulkin dimokuraɗiyya...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sojojin HKI sun kai hari akan Falasdinawan da su ka yi cincirindo domin karbar abinci da hakan ya yi sanadiyyar shahadar da dama daga cikinsu. Tun da safiyar yau Laraba ne dai sojojin HKI su ka rika kai hare-hare akan cibiyoyin cibiyoyin raba agaji wadanda dama suna a karkashin kulawar su kansu ‘yan sahayoniyar da kuma Amurka. Har ila yau hare-haren sun shafi gidajen fararen hula a cikin wasu unguwanni na zirin Gaza. Majiyar Asibitin “Audah” ta sanar da cewa an kai shahida 4 da kuma wadanda su ka jikkata sanadiyyar hare-haren na sojojin mamaya a wurin raba kayan agaji dake kan titin “Salahuddin” a tsakiyar zirin Gaza. A arewacin yankin Gaza kuwa wasu samarin Falasdinawa 4 sun yi shahada...
Sai dai wasu daga cikin dillalan man fetur a Nijeriya na ganin ya kamata matatar ta riƙa sayar da lita ɗaya ƙasa da Naira 800, la’akari da cewa ana sayar mata da ɗanyen mai a kuɗin Naira maimakon Dala. Dangote dai ya nuna ƙwarin guiwar cewa kamfaninsa zai taka rawar gani wajen samar da isasshen mai ga ‘yan Nijeriya tare da sauƙaƙa matsin da mutane ke ciki sakamakon hauhawar farashin fetur a ƙasar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A cewarsa, shuwagabancin Tinubu ya gina tubalin ci gaba mai ɗorewa ta hanyar yanke hukunci masu wahala amma masu amfani. Dangane da sauyin jam’iyyun siyasa da ke faruwa, Namadi ya ce yawaitar sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC alama ce da ke nuna yadda jama’a ke ƙara amincewa da shugabancin Tinubu da kuma burin da yake shi ga ƙasar nan. Ya ce masu barin jam’iyyunsu suna haka ne domin suna ganin makoma mai kyau a ƙarƙashin jagorancinsa. Har ila yau, Namadi ya bayyana cewa ziyarar aikin da ya kai Indiya kwanan nan ta samar da muhimman yarjejeniyoyi da masu saka jari da ƙwararru don bunƙasa harkar noma a Jihar Jigawa. Ya ce an cimma matsaya a fannoni irin su kiwon shanu,...
Gwamnatin kasar Burtaniya ta bada sanarwan kakabawa ministocin HKI guda biyu takunkuman tattalin arziki saboda ra’yinsu na wuce gona da Iri wanda zai bata duk wani shirin da kasashen duniya suke da shin a tabbatar da zaman lafiya a yanking abas ta tsakiya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kira-kirayen ministocin na kara mamaya da kuma korar falasdina daga yankin yamma da kogin Jordan ne yasa burtaniya ta nuki wannan batakin. Bezalel Smotrich dai , wanda shi ne ministan kudi na HKI ya ce HKI zama kara mamayar yankin yamma da kogin Jordan, kafin zaben shekara ta 2026, sannan ya rantse kan cewa za’a share falasdinawa a gaza, kuma zasu wargaza kungiyar Hamas a cikin...
Tawagar fursinonin yaki na kasar Rasha daga kasar Ukrain sun koma gida, saboda yarjeniyar da kasashen biyu suka cimma a birnin Istambul na kasar Turkiyya. Kamfanin dillancin labaran Spunik na kasar Rasha ya bayyana cewa a taro na biyu tsakanin jami’an gwamnatocin kasashen biyu a birnin Istambul na kasar Turkiya wato ranar 2 ga watan yunin da muke ciki ce suka cimma yarjeniyar musayar fursinonin a karo na biyu. Labarin ya nakalto ministan tsaron kasar Rasha yana cewa fursinonin Rasha da suke hannun Ukraine sun isa kasar Rasha a jiya talata. Haka ma bangaren Rasha ta mikawa gwamnatin Ukraine wasu daga cikin fursinonin da suke hannunta. Ministan ya kara da cewa a halin yanzu firsinonin suna kasar Belerus inda aka...

Jami’in Makamashin Nukiyar Iran Ya Ce; Zarge-Zargen Da Ake Yi Kan Shirin Makmashin Nukiliyar Iran Siyasa Ce Kawai
Jami’in makamashin nukiliyar Iran ya jaddada cewa: Zarge-zargen da ake yi wa Iran kan shirinta na makamashin nukiliya, siyasa ne tsantsa Kakakin Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran Behrouz Kamalvandi, ya ce: Zargin da ake yi wa Iran game da batun Shirin makamashin nukiliya na zaman lafiya, tsagwaron siyasa ne, ba bisa ka’ida ko na fasaha ba. Kakakin Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran ya kara da cewa: Kudurorin da suka biyo baya da kuma kara matsin lamba a kan Iran suna share fagen fuskantar al’amura a nan gaba. Yayin da yake ishara da cikas iri-iri da ke kawo sarkakiya ga ci gaban shirin makamashin nukiliyar Iran, Behrouz Kamalvandi ya bayyana cewa: Wadannan kalubalen da suka kara ta’azzara a cikin ‘yan shekarun...
Tsohon gwamanan Jihar Zamfara kuma Karamin Ministan Tsaro, Bello Muhammed Matawalle ya bayyana cewa, kofar Jam’iyyar APC abude take idan gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal na Jamiyyar PDP na bukatar shigowa Jamiyyar. Ministan ya bayyana haka ne a Mahaifarsa Maradun a lokacin ziyar Sallah da magoya bayan Jam’iyyar APC na Kananan Hukumomi 14 suka kai masa a gidansa da ke Maradun cikin Jihar Zamfara. Matawalle ya bayyana cewa, muna jin rade-radin cewa , gwamna Dauda zai dawo Jam’iyyar APC sakamakon Jam’iyyar su ta PDP na fama da matsalar rikice-rikice. Domin yanzu haka da Sallar nan daya daga cikin gwamnonin PDP ya dawo APC A Legas. Don haka, Kofarmu a bude take ga gwamna Dauda Lawal, zuwansa APC dan bamu kyama,...
Mutane tara ne suka rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a kauyen Kyaramma da ke karamar hukumar Ringim a jihar JIgawa. A cewar rundunar ‘yansandan jihar Jigawa, hatsarin wanda ya afku a ranar Asabar da ta gabata da misalin karfe 2 na rana, ya rutsa da wasu motoci kirar Golf 3 saloon guda biyu tare da jikkata wasu da dama. Gwamnatin Gombe Ta Yi Albishir Ɗin Gina Babban Zangon Noma Da Kiwo Ɗauke Da Kasuwar Duniya A Jihar Ndume Ya Gargaɗi Tinubu Kan 2027: “An Taɓa Yi Wa Jonathan Irin Wannan” A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, Shiisu Adam ya fitar, ya bayyana cewa daya daga cikin motocin mai lamba...
Wani rahoto na gungun kwararru da aka fitar a Lahadin nan, ya nuna yadda kasar Sin ke ta kokarin samar da kyakkyawan yanayin zaman lafiya, da kawance, da hadin gwiwa a yankunan tekun kudancin kasar. Rahoton na kwararrun cibiyar Xinhua, mai alaka da kamfanin dillancin labarai na kasar Sin wato Xinhua, na da lakabin “Mayar da tekun kudancin Sin wuri mai cike da zaman lafiya, kawance da hadin gwiwa: matakan da Sin ke dauka”, ya ce har kullum Sin na nacewa matakan wanzar da zaman lafiya, da daidaito a yankunan tekun kudancin kasar, kuma nasarar hakan na da alaka da matakan hadin gwiwa da ake aiwatarwa tsakanin Sin da kasashe mambobin kungiyar ASEAN. Rahoton ya kara da cewa, ta hanyar...
Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya buƙaci Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, da ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki. Matawalle ya yi wannan kira ne a ranar Asabar, a garinsu Maradun, yayin da dubban magoya bayansa suka kai ziyarar gaisuwar Sallah. Sallah: Gwamnatin Sakkwato ta bai wa kowane Alhaji kyautar N450,000 Gwamnatin Tarayya na shirin farfaɗo da kamfanin ƙarafa na Ajaokuta Matawalle, wanda shi ne tsohon gwamnan Jihar Zamfara, ya ce APC jam’iyya ce ta mutanen kirki da masu kishin ƙasa. Ya ce maimakon a ci gaba da takun-saka tsakanin gwamnati da ’yan adawa, zai fi kyau Gwamna Dauda ya fito fili ya rungumi jam’iyyar da ke da madafun iko domin ci gaban jihar da ƙasar gaba ɗaya....
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Aƙalla mutum tara ne suka rasu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a ƙauyen Kyaramma da ke Ƙaramar Hukumar Ringim ta Jihar Jigawa. Rundunar ’yan sandan jihar, ta ce hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2 na ranar Asabar, inda motoci biyu ƙirar Golf 3 suka yi taho-mu-gama, kuma mutane da dama sun jikkata. Edgar Lungu: Za a yi zaman makokin kwana 7 a Zambiya Gobara ta tashi a otal ɗin da ke ɗauke da Alhazan Najeriya 480 a Makkah Ɗaya daga cikin motocin, mai lambar Kaduna MKA 687 AY, ana ɗauke da ita ne daga Abuja zuwa garin Gujungu, kuma direban motar mai suna Adamu Sunusi, mai shekaru 35 daga Ƙaramar Hukumar Hadeja. Rahoton ’yan sanda...
Daya daga cikin shuwagabannin Falasdinawa ya yi shahada sanadiyyar hare-haren da sojojin HKI suka kai kan zirin gaza. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa Asa’d Abu Sharia shi ne baban sakataren kungiyar ‘Dakarun Palastinewa”. Wacce aka kafa a shekara ta 2001 M. Kungiyar kanta ta tabbatar da wannan labarin ta kuma bayyana cewa ya dade yana shugabantar wannan kungiyar sannan a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 ya shiga cikin yakin da aka fara kan HKI kuma dakarunsa sun kama yahudawa da dama suka shigo da su su gaza. Banda haka shi ne yake jagorantar bangaren soje na kungiyarsa. Sau da dama ya jagoranci Falasdinawa a yaki da yahudawan a Gaza. Sannan kungiyar tana...
Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya nanata matsayin Taiwan da jaddada manufar Sin daya tak a duniya yayin tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Faransa Jean-Noel Barrot a jiya Jumma’a. Ya kuma bayyana adawar Sin da shigar kungiyar tsaro ta NATO cikin harkokin yankin Asiya da Pasifik. Wang Yi wanda mamba ne na ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS ya nanata cewa, batun da ya shafi Taiwan, batu ne na cikin gidan Sin da ya shafi ’yancin kasar da iko kan yankunanta, wanda ya bambanta da batun kasar Ukraine. Ya ce Sin na daukar amincewa da manufar kasar daya tak da Faransa ta yi da muhimmanci, kuma tana fatan ganin hakan a aikace. Bugu da kari, ministan ya...

Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Na Ganin Tattaunawa Da Hadin Gwiwa A Matsayin Hanyar Warware Takaddamar Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka
CGTN ta wallafa nazarin ne a dandamalinta na harsunan Ingilishi da Spaniyanci da Faransanci da Larabci da Rashanci. Kuma mutane 5610 ne suka kada kuri’a tare da bayyana ra’ayoyinsu cikin sa’o’i 12. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp