Maryam Sanda na cikin waɗanda Tinubu ya yi wa afuwa
Published: 11th, October 2025 GMT
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa Maryam Sanda afuwa, wadda aka yanke wa hukuncin kisa a shekarar 2020 bisa laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello, ɗan tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Alhaji Haliru Bello.
Maryam,’ mai shekara 37, ta shafe shekaru shida da watanni takwas a gidan yarin Suleja kafin yi mata afuwa.
Rahotanni sun nuna cewar an yi mata afuwar ne bayan yin nadama da aikata kyakkyawan halaye.
Iyayen Maryam sun roƙi gwamnati da ta sake ta saboda ’ya’yanta biyu da ta ke da alhakin kula da su, tare da alƙawarin sauya halayenta.
Shugaba Tinubu, ya kuma yi wa wasu mutane afuwa da suka haɗa da Manjo Janar Mamman Vatsa, Ken Saro-Wiwa, da kuma Sir Herbert Macaulay.
Gaba ɗaya mutane 175 ne shugaban ya yi musu afuwa, ciki har da masu manyan laifuka, tsoffin fursunoni, da waɗanda suka yi kyakkyawan tuba.
Wannan shi ne karon farko da Shugaba Tinubu ya yi amfani da ikon yafe laifi don tausaya wa waɗanda suka aikata laifuka tun bayan hawansa mulki.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Afuwa Gidan Yari Maryam Sanda
এছাড়াও পড়ুন:
Amarya ta yi wa angonta yankan rago bayan kwana 3 da aurensu a Katsina
Ana zargin wata amarya da yi wa angonta yankan rago kwana uku bayan ɗaurin aurensu a Jihar Katsina.
Angon mai suna Abubakar Abdulkarim da aka fi sani da Dan Gaske, ana zargin ya rasa ransa bayan da amaryar ta yi amfani da wuƙa wajen halaka shi.
Shaidu sun ce ta yi masa mummunan rauni a wuya wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa.
Angon da amaryarsa suka daura aure ne a ranar Alhamis, 18 ga Nuwamba, 2025, amma farin cikin aure ya rikide zuwa makoki a ranar Lahadi da rana lokacin da lamarin ya faru.
Gobarar tankar mai ta ƙone gidaje a Jihar Neja NAJERIYA A YAU: Irin Radadin Da Masu Cutar Amosanin Jini Ke FuskantaWani ɗan uwansa mai suna Aminu Danladi ya ce cewa sun yi taro da marigayin da safiyar ranar, suna shirya ziyarar ’yan uwansu da za a kai da yamma.
Ya ce daga baya ango ya koma gida domin shiri, sai kuma aka ji labarin an same shi kwance a cikin jini babu rai.
Aminu ya kuma ƙaryata jita-jitar da ake yaɗawa cewa auren dole ne aka yi wa ma’auratan, inda ya tabbatar da cewa dangantakarsu ta kasance lafiya kafin aure.
Majiyoyi sun ce matar, ’yar asalin Katsina, ta taɓa yin aure a baya, abin da ake zargin dangin mijin ba su sani ba.
An ce bayan faruwar lamarin amaryar ta ruɗe inda ta je gidan maƙwabta tana neman abinci. Wannan hali ya sa tsofaffin mata zargin akwai matsala, suka bi ta gida inda suka tarar da gawar mijin, suka kuma sanar da jami’an tsaro.
Rundunar ’Yan Sanda ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce ta fara gudanar da bincike a kai.
Kakakin ’yan sanda na jihar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya ce an kama mutum ɗaya da ake zargi da hannu a lamarin, kuma bincike na ci gaba.
Kwamishinan ’Yan Sanda na Katsina, CP Bello Shehu, ya tabbatar da cewa za a gudanar da bincike mai zurfi, tare da kira ga jama’a da su bayar da bayanai masu amfani.