Juyin mulki: Shugaba Rajeolina ya tsere daga ya rushe majalisa
Published: 14th, October 2025 GMT
Shugaban Madagascar, Andry Rajoelina, ya rusa majalisar dokoki ta ƙasar a yayin da rikicin soja ke ƙara ƙamari tare da neman hambarar da gwamnatinsa.
A ranar Talata ya sanar da rushe majalisar Dokoki ta Ƙasar, a daidai lokacin da ake fama da tarzomar soja da ta tilasta masa tserewa daga ƙasar.
A cewar wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta wallafa a shafinta na Facebook, Rajoelina ya fitar da wata doka da ke umartar rushe majalisar dokoki nan take.
Wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da wasu dakarun soja na musamman suka goyi bayan zanga-zangar matasa da ke neman sauya gwamnati, lamarin da ya haifar da ƙoƙarin juyin mulki.
Cirar kudin kwastoma: Majalisa ta gayyaci CBN da bankuna Gwamnan Enugu da kwamishinoninsa sun koma APCShugaban ya bayyana a wani jawabi da aka yaɗa ta kafafen sada zumunta a daren Litinin cewa ya fice daga ƙasar ne saboda tsoron rasa rayuwarsa.
Majalisar dokoki dai ta kasance cikin wani zama na musamman don tattauna yiwuwar tsige Rajoelina daga shugabancin ƙasa, amma rushewar da ya yi wa majalisar ya daƙile wannan yunƙuri gaba ɗaya.
Wannan doka da Rajoelina mai shekaru 51 ya fitar ta ƙara dagula siyasar Madagascar, mai yawan jama’a kimanin miliyan 31 a gabar tekun gabashin Afirka.
Tun wasu makonni da suka gabata, Rajoelina na fuskantar matsin lamba daga gungun matasa ’yan Gen Z da ke jagorantar zanga-zangar neman sauya gwamnati.
Aminiya ta fahimta cewa har yanzu ba a san inda shugaban ke ba, yayin da halin rashin tabbas ke ci gaba da mamaye al’amuran siyasa a ƙasar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Andry Rajoelina Madagacar Rajoelina
এছাড়াও পড়ুন:
Soja ya kashe matarsa, ya hallaka kansa a Jihar Neja
Wani soja mai muƙamin Las Kofur ya ɗirka wa matarsa harbi har lahira sannan ya kashe kansa a Jihar Neja.
Las Kofur Akenleye Femi da ke aiki a Bataliya ta 221, ya yi wannan aika-aika ne a Barikin Sojoji na Wawa da ke Ƙaramar Hukumar Borgu a Jihar Neja.
Muƙaddashin Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Soja ta 22 da ke Ilorin, Kyaftin Stephen Nwankwo, ne ya tabbatar da lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce abin ya faru ne a ranar 11 ga Oktoba, 2025.
Ya ce mutuwar sojan da matarsa ta haifar da tashin hankali a cikin sansanin soja, inda mazauna wurin suka shiga ɗimuwa da mamaki kan abin da zai iya jawo irin wannan lamari.
Yaƙin Gaza: Hamas da Isra’ila sun fara sakin fursunoni Zaɓen Kamaru: Tchiroma Bakary na da kwarin gwiwa a yayin da ake jiran sakamako“An gano gawar Last Kofur Femi da matarsa ne a cikin dakinsu da ke Block 15, Room 24 na Corporals and Below Quarters a Wawa Cantonment,” in ji Kyaftin Nwankwo.
Ya ce binciken farko ya nuna cewa sojan yana kan aiki a cikin sansanin kafin ya nemi izinin zuwa gida domin wasu bukatun kansa, sai daga bisani aka gano gawarsu a gida.
Kyaftin Nwankwo ya ce an ajiye gawar mamatan domin ci gaba da bincike, kuma rundunar sojan na aiki tukuru don gano musabbabin lamarin.
Rundunar Soja ta Najeriya ta bayyana matuƙar baƙin cikinta kan wannan abin takaici, tare da miƙa ta’aziyya ga iyalai, abokai da abokan aikin mamatan.
Kwamandan Rundunar, Birgediya Janar Ezra Barkins, ya sha alwashin gudanar da cikakken bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru, tare da ɗaukar matakan da za su hana faruwar irin haka a nan gaba.