Cibiyar Lafiya Ta Nasser Ta Ce: Yaran Gaza 5,500 Suna Bukatar Agajin Gaggawa A Kasashen Waje
Published: 13th, October 2025 GMT
Cibiyar kula da lafiya ta Nasser Medical Complex da ke Gaza ya bayyana cewa: Yara 5,500 ne ke bukatar agajin gaggawa a kasashen waje
Daraktan cibiyar kula da lafiya ta Al-Shifa da ke Gaza ya ce: Babu wani agajin jinya da ya shiga zirin Gaza duk da cewa an shafe sa’o’i 72 tsagaita bude wuta.
Ya kara da cewa: Mutane 170,000 marasa lafiya da kuma wadanda suka jikkata na bukatar tafiya cikin gaggawa zuwa wajen Gaza domin neman magani.
Al-Nasser Medical Complex ya kuma ce: Yara 5,500 na bukatar magani a wajen Gaza. Daraktan asibitin yara na Nasser Medical Complex, Dr. Ahmed Al-Farra, ya bayyana cewa, akwai yara 5,500 a zirin Gaza da ke bukatar agajin gaggawa a wajen yankin saboda tsananin karancin magunguna da kuma ci gaba da tabarbarewar yanayin kiwon lafiya.
A nata bangaren, Nour Al-Saqa, mai kula da harkokin yada labarai na kungiyar likitocin da ke yankin zirin Gaza, ta ce sama da mutane 170,000 da suka jikkata a zirin Gaza na bukatar kulawar gaggawa.
Yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta fara aiki tun ranar Juma’a. A matakin farko, yarjejeniyar ta tanadi shigar da kusan tireloli 600 na kayan agajin gaggawa a kowace rana. Sai dai wasu kananan motoci ne kawai aka ba su izinin shiga, kuma har yanzu ba a kai agajin jinya a zirin Gaza ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Shugaban Amurka Ya Yi Barazanar Aikewa Ukraine Makamai Masu Linzami Kirar Tomahawk October 13, 2025 Trump, da Al’Sisi za su jagoranci taron zaman lafiya kan Gaza October 12, 2025 ‘Yan Kamaru na kada kuri’a a zaben shugaban kasar October 12, 2025 Wata Kotu a Faransa ta yi watsi da rufe wata makarantar musulmi a birnin Nice October 12, 2025 Gwamnatin Cuba ta yi watsi da zargin da Amurka ke yi na hannu a yakin Ukraine October 12, 2025 Arachi: HKI Ba Abar Amincewa Ba Ce, Falasdinawa Su Yi Hattara October 12, 2025 Iran Ta Yi Allawadai Da HKI Kan Hare-Haren Da Take Kaiwa Kudancin Lebanon October 12, 2025 An Gudanar Da Taron ‘Farkawar Musulmi’ A Nan Tahren Inda Aka Tattauna Batun Falasdinu October 12, 2025 Amurka Da Masar Ne Zasu Jagoranci Taron Rattaba Hannu Tsakanin HKI Da Falasdin A Sharm Sheikh October 12, 2025 China Ta Sha Alwashin Maida Martani Kan Harajin Trump A Kanta Na 100% October 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: agajin gaggawa a
এছাড়াও পড়ুন:
An ceto ’yan mata 24 d aka yi garkuwa da su a makaranta a Kebbi
An ceto ’yan matan nan 24 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Makarantar sakandaren Gwamnati ta GGCSS da ke yankin Maga da ke Jihar Kebbi.
Gwamnan jihar Kebbi Nasiru Idiris a taron manema labarai a ranar Talata fadar gwamnatin jihar ya tabbatar da an karɓo ɗalibban da aka sace a farkon makon nan.
Ya ce “an karɓo ɗiyanmu ’yan makaranta waɗanda aka yi garkuwa da su a Maga. Shugaban ƙasa ya baiwa jami’an tsaro umarni a tafi a gano inda yaran suke kuma a karɓo su muna tabbatar wa uwayen yara da al’ummar Kebbi yara sun dawo.
“Muna godiya ga shugaban ƙasa da jami’an tsaro musamman sojoji da ’yan sanda da Sibil difens da sauransu da suka tsaya aka karɓo yaran nan cikin ƙoshin lafiya.
“Mu gwamnatin Kebbi ba mu biya kuɗin fansa don a saki yaran ba, a binciken da muka yi ba wanda ya biya kuɗin fansar yaran, mu ba mu ba da ko kwabo ba,” a cewar Gwamnan Idiris.