Sojoji Sun Kashe Kwamandan IPOB ‘Alhaji’, Da Wasu 26, Sun Kama 22
Published: 12th, October 2025 GMT
Sojojin Nijeriya sun kashe wani kwamandan ƙungiyar ƴan ta’adda IPOB/ESN da ake nema ruwa a jallo, mai suna ‘Alhaji’, tare da wasu mutane 26 a jerin hare-haren da suka kai a sassan ƙasar tsakanin 8 zuwa 11 ga Oktoba, 2025. Rundunar Sojin ta ce an kuma ceto mutane biyar da aka yi garkuwa da su, tare da kwace makamai, da harsasai, da kuɗaɗe.
A kudu maso gabas, Sojojin Operation UDO KA sun kai farmaki a Izzi, jihar Ebonyi, inda suka kashe ‘Alhaji’ bayan ya yi yunƙurin kwace bindiga daga hannun wani Soja lokacin kama shi. Haka kuma, a jihar Imo, an rusa wata maboyar IPOB/ESN da ake amfani da shi wajen horar da mambobi.
Sojoji Sun Cafke Babban Kwamandan IPOB Sojoji Sun Kama Ƙasurgumin Ɗan Bindiga, Sun Kashe Shugaban IPOBA Arewa maso gabas, Sojojin Operation Haɗin Kai sun kashe ‘yan ta’adda tara a Magumeri da Gajiram a jihar Borno, inda suka ceto fararen hula biyu tare da ƙwato fiye da Naira ₦4.3 miliyan. A wasu hare-haren sama a jihar Sokoto, an hallaka shugabannin ‘yan ta’adda da dama, yayin da aka kama masu safarar miyagun ƙwayoyi daga Legas zuwa Zamfara.
A Arewa ta Tsakiya da Kudu maso Kudu, Sojojin Operation Whirl Stroke da Operation DELTA SAFE sun kama masu garkuwa da mutane, sun kashe ‘yan ƙungiyar asiri biyu, kuma sun ƙwato makamai da babura. Rundunar Sojin ta ce gaba ɗaya an kashe ‘yan ta’adda 26, an kama mutum 22, kuma an ceto mutane biyar da aka yi garkuwa da su.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Musulmin da Aka Kashe A Zamfara, Katsina Da Sokoto Sun Ninka Na Kiristoci A Tsakiyar Najeriya: MACBAN
Ngelzarma ya kuma ce mutanen da suka mutu a Zamfara, da Katsina da Sokoto sun ninka na tsakiya Nijeriya, kuma mafi yawansu Musulmi ne. Ya buƙaci a kalli matsalar tsaron Nijeriya da idon basira da fahimtar bangarori da dama, yana mai cewa idan za a yi hukunci kan rikicin, ya kamata a kira shi da kisa bil’adama gaba ɗaya, ba kisan addini guda ɗaya ba.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA