HausaTv:
2025-11-28@14:37:49 GMT

 MDD: Mutane 300,000 Su Ka Gudu Daga Sudan Ta Kudu A 2025

Published: 14th, October 2025 GMT

 MDD ta bayyana cewa; saboda fadan da ake yi a tsakanin magoya bayan shugaban kasa Silvaa Kiir da mataimakinsa Riek Machar ya tilastawa mutane kusan 300,000 su ka yi hijira.

Shi dai mataimakin shugaban kasar ta Sudan Ta Kudu, Riek Machar ana yi masa shari’a bisa zarginsa da aikata laifuka akan bil’adama.

Hukumar kare hakkin bil’adama ta fitar da bayanin da yake cewa: Ana ci gaba da yin fadace-fadace a cikin yankuna da yawa, ba tare da an daina ba, tun daga rattaba hannu akan yarjejeniyar sulhu a 2017, tare da kara da cewa; A cikin wannan shekarar ta 2025 kadai mutane 300,000 ne su ka fice daga cikin kasar.

A tsakanin wannan adadin da akwai mutane 148,000 da su ka isa kasar Sudan, sai kuma wasu 50,000 da su ka shiga kasar Habasha. Har ila yau, wani adadin na mutane 50,000 sun isa Uganda, yayin da wasu 30,000 suka shiga kasar DRC, sai kuma 25,000 a kasar Kenya.

A cikin gida kuwa adadin mutanen da sun kai rabin miliyan ne su ka fice daga gidajensu zuwa inda za su sami tsaro.

A wani rahoto na MDD a karshen watan Yuli, ta bayyana cewa; yakin basasar kasar ta Sudan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 1800 a tsakanin watan Janairu na wannan shekara zuwa Satumba da ya shude.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Ta Gabatar Da Shawarar Kulla Yarjejeniyar Tausayawa A Tsakanin Matan Duniya October 14, 2025 Larijani:  Gagarumar Tarbar Da Aka Yi Wa  Fursunonin Falasdinawa Ta Nuna Hakikanin Wanda Ya Sami Nasara October 14, 2025 Hamas Ta Mika Yahudawa 7 Daga Cikin 20 Da ke Hannunta  Ga Kungiyar Red Cross October 13, 2025 Iran: Kakabawa Kasa Mai Makwabta 16 Takunkumi Ba Abu Ne Mai Sauki Ba. October 13, 2025 An Gano Gawarwaki 323 Karkashin Burabutsai Bayan Dakatar Da Bude Wuta A Gaza October 13, 2025 Tehran Ta yi Gargadi Game Da  Barazanar Yaduwar Fadan Iyakar Afghanisatan Da Pakistan. October 13, 2025 Kungiyar (ASUU) Ta Sanar Da Shiga Yajin Aikin  Gargadi A Kasa Baki Daya . October 13, 2025 Aragchi: HKI Ba Zata Mutunta Tsaida Wuta A Gaza Ba October 13, 2025 Iran Ta Ki Zuwa Masar Saboda Bata Son Haduwa Da Azzaluman Da Suka Kashe Falasdinwa A Gaza October 13, 2025 Shugaban Kasar Amurka Donal Trump Ya Isa HKI Kafin Taron Sharm Sheikh October 13, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Matsalolin Tsaro A Yankunan Bakin Ruwa A Kasar Siriya Ya Kai Ga Zanga-Zangar Lumana

Jami’an tsaro na kasar Siriya karkashin gwamnatin rikon kwarya ta HKI sun budewa masu zanga zangar lumana wuta a yankunan bakin ruwa na kasar.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a jiya Talata ce, a garuruwan Tartus, Lazikiyya da lardin Lantakiya mutane suka fito zanga zanga ta lumana inda suke neman adlci ga Alawiyawa da sauran kananan addinin da mazhabobi a yankin. Har’ila yau da sakin wadanda gwamnati take tsare da su.

Amma jawabin gwamnatin Jolani ga masu zanga-zangar shi ne aman wutan bindigogi da hayaki mai sa hawaye a kama masu zanga-zangar da dukan wasu daga cikinsu.

Labarin ya kara da cewa matsalolin tsaro sun tarbarbare a yankin bakin ruwa na kasar Siriya sosai, tare da sace mutane da kashe su da kuma kama su a tafi da su inda ba wanda ya sani.  Wannan ya sa a dole mutanen yankin suka fito suna neman sauyi da kuma kawo karshen wannan musibar.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Al-Houthi ya yi ta’aziyyar shahadar babban kwamanda na Hizbullah November 26, 2025 UNIFIL: Isra’ila tana sabawa wa kudurorin MDD a cikin  Lebanon November 26, 2025 Aljeriya Ta Bukaci Kasashen Duniya Su Dauki Mataki Don Kawo Karshen Ta’asan HKI A Yankin Asiya Ta Kudu November 26, 2025 Shugaban Majalisar Koli Ta Taron Kasa Iran Ya Yawaba Pakistan Saboda Goyon Bayanta November 26, 2025 EU da AU na taro kan diyya ga laifukan mulkin mallaka da cinikin bayi November 25, 2025 Hizbullah: Isra’ila na kure idan ta na tunanin kashe-kashe zai kawo karshen kungiyarmu November 25, 2025 Tashar Press TV ta kaddamar da sashen harshen Hebrew November 25, 2025 Bincike : Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa Akalla 100,000 a Gaza November 25, 2025 Kasar Gambia Ta Bai Wa Jagoran ‘Yan Hamayyar Siyasar Kasar Kamaru  Mafaka Ta Wucin Gadi November 25, 2025 China Ta Yi Tir Da Yadda Kasar Japan Ta Girke Makamai Masu Linzami A Kusa Da Yankin Taiwan November 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Isra’ila Ta Kashe Mutane 10 A Wani Hari Da Ta Kai A Birinin Damaskas Na Kasar Siriya
  • Jagoran : Amurka Tasha Kashi A Yakin Kwanaki 12 Duk Da Manyan Makamai Na Zaman Da Take Da Su.
  • An Rantsar Da Sabon Shugaban Mulkin Soja Na kasar Guinea-Bissau
  • ECOWAS ta yi Allah wadai da juyin mulki a Guinea Bissau
  • An Rutsa Da Tsohon shugaban Kasar Najeriya A Guine Bissau Bayan Juyin Mulki
  • Mataimakin Shugaban Nijeriya Ya Dawo Gida Bayan Kammala Taron G20 A Afrika Ta Kudu.
  • Sojojin Sun Sanar Da Kwace Mulki A Kasar  Guinea Bissau
  • Matsalolin Tsaro A Yankunan Bakin Ruwa A Kasar Siriya Ya Kai Ga Zanga-Zangar Lumana
  • Aljeriya Ta Bukaci Kasashen Duniya Su Dauki Mataki Don Kawo Karshen Ta’asan HKI A Yankin Asiya Ta Kudu
  • DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane?