’Yan sanda sun ceto mutum 10 daga hannun ’yan bindiga a Kaduna
Published: 11th, October 2025 GMT
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta samu nasarar ceto mutum 10 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su tsawon watanni huɗu da suka gabata a Ƙaramar Hukumar Kagarko.
A cikin sanarwar da kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan, ya fitar, ya bayyana cewa daga cikin waɗanda aka ceto har da yara masu shekaru ɗaya, uku da kuma 13.
DSP Mansir, ya ce ’yan bindigar sun kai farmaki ƙauyen Kushe Makaranta, inda suka sace mutanen daga gidajensu sannan suka kai su dajin da ke kusa da Rijana.
Rundunar, ta ce aikin ceto mutanen ya samu ne ta haɗin gwiwar ’yan sanda, jami’an DSS, da kuma sojoji.
Wani mazaunin yankin ya shaida cewa suna matuƙar farin ciki da wannan nasara, musamman ganin cewa mutanen sun kwashe watanni a hannun ’yan bindiga cikin tsananin wahala.
Hukumomin tsaro sun ce ana ci gaba da bincike domin kamo sauran ‘yan bindigar da suka tsere, tare da inganta matakan tsaro a yankin don kauce wa sake faruwar irin wannan lamarin.
“Za mu ci gaba da aiki tare da sauran hukumomi don tabbatar da cewa babu wata ƙungiyar ‘yan ta’adda da za ta samu mafaka a Kaduna,” in ji DSP Mansir Hassan.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Yan Sanda Garkuwa
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan bindiga sun kashe sojoji 3 a Kebbi
’Yan bindiga sun kashe sojojin Nigeriya guda uku a wani kwanton ɓauna da suka yi masu a lokacin da suke ƙoƙarin hana yin garkuwa da wasu mutane a ƙauyukan ƙananan hukumomin Sakaba da Danko-Wasagu a Jihar Kebbi.
Sojojin da aka kashe an yi masu sutura a babban barikin sojoji da ke garin Zuru, hedikwatar ƙaramar hukumar Zuru.
Mai Martaba Sarkin Zuru Alhaji Sanusi Mika’ilu Sami, ya halarci janazar domin tausayawa da jinjina wa marigayin kan sadaukarwar da suka yi a wurin kare mutanen ƙasa.
Majiyar da ta shaida wa Aminiya ta ce sojojin sun kai ɗauki ne a lokacin da suka samu labarin ’yan ta’addan sun kai farmaki tare da ƙoƙarin yin garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa.
Rashin wutar lantarki ta kassara kasuwanci a Kaduna, Kano da Katsina ’Yan Najeriya miliyan 60 na fama da taɓin hankali — LikitaSai dai ana jiran bayani daga rundunar soja ta kasa kan wadannan jami’ai nata da aka kashe a fagen daga a yakin jihar Kebbi.