Gwamnatin Tarayya Za Ta Kammala Aikin Titin Abuja–Kaduna–Kano Shekara Mai Zuwa
Published: 14th, October 2025 GMT
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta kammala aikin titin Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano kafin ƙarshen shekara mai zuwa.
Ministan Kasa a Ma’aikatar Ayyuka, Barista Bello Muhammad Goronyo, ne ya bayyana haka bayan ya kai ziyara domin duba yadda aikin ke tafiya a ranar Talata.
Barista Goronyo ya ce Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya ba da umarni cewa a tabbatar da kammala aikin cikin lokaci, ganin muhimmancin hanyar wajen haɗa Arewa da Kudancin ƙasar da kuma babban birnin tarayya Abuja.
Ya bukaci kamfanin da ke gudanar da aikin da ya hanzarta kammalawa kafin wa’adin da aka tsara, tare da gyara ramukan da ke hanyar domin sauƙaƙa zirga-zirgar jama’a.
Ministan ya kuma nuna damuwarsa kan halin da masu amfani da hanyar ke ciki, inda ya jaddada bukatar gaggauta cike ramuka da gyaran sassan da ke da matsala domin inganta sufuri da tsaron fasinjoji.
Rel/Ibrahim Idris K/Namoda
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Wata mata ta kashe ’yar shekara 7 a Ribas
Ana fargabar cewa wata mata mai suna Success ta kashe wata yarinya mai shekaru bakwai, Alicia Olajumoke, a unguwar Rumueme da ke birnin Fatakwal na Jihar Ribas.
Mazauna yankin sun shaida wa Aminiya cewa matar da ake zargin tana da kusanci da dangin mahaifiyar yarinyar, wacce ita kaɗai ce a wurin iyayenta.
El-Rufai ya koma jami’yyar haɗaka ta ADC An janye ’yan sanda 11,566 daga gadin manyan mutane a faɗin NijeriyaBayanai sun ce ita ma matar ta caka wa kanta wuƙa a wuya bayan kashe yarinyar, kuma bayan an garzaya da duk su biyun asibiti, likitoci suka tabbatar da cewa sun riga mu gidan gaskiya.
Lamarin wanda ya faru a ranar Talata ya ɗimauta mazauna yankin, la’akari da zargin cewa matar ta kashe yarinyar ce a gidanta bayan ta je har makarantarsu ta ɗauko ta ba tare da izinin mahaifiyarta ba.
Jami’ar hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Jihar Ribas, SP Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis, inda ta ce an kai gawar yarinyar ɗakin ajiye gawa domin bai wa likitoci damar kammala bincikensu na kimiyya gabanin soma nasu binciken.
“Mun ziyarci wurin da abin ya faru, mun ɗauki hotuna, kuma an garzaya da su asibiti inda aka tabbatar da mutuwarsu.”