Al’ummar yankin sun bayyana cewar matsalar tsaron ta gurgunta tattalin arzikin yankin musamman ayyukan noma wanda ya sa ɗaruruwan mutane da dama neman mafaka a sansanin gudun hijira a Sakkwato da makwabtan jihohi.

 

Dasuki ya bayyana cewar a ranar 12 ga Augusta 2025, ‘yan ta’adda sun shiga mazaɓar Fakku a karamar hukumar Kebbe tare da kashe mutane biyar da garkuwa da mutane 28 da satar shanu 37.

 

“Haka ma a ranar 15 ga Agusta, ‘yan bindigar  sun kai farmaki mazaɓar Sangi tare da tilastawa jama’a neman mafaka a Kuchi da Koko a jihar Kebbi. Bugu da kari a ranar 18 ga Agusta ‘yan ta’adda sun afkawa mazabar Ungushi tare da kisan mutane biyu da garkuwa da mutane bakwai tare da asarar dabbobi.”

 

Dasuki ya kuma bayyana cewar, mazaɓun Jabo a karamar hukumar Tambuwal da Tambuwal/Shimfiri suna fuskantar kalubalen tsaro da ke bukatar agajin gaggawa.

 

Dan majalisar ya bayyana halin kuncin da al’ummar yankin ke ciki, ya ce munanan hare- haren sun tarwatsa kwanciyar hankalin al’umma, jama’a sun kauracewa garuruwa, haka ma yara sun daina zuwa makaranta, a yayin da manoma sun dakatar da zuwa gona a bisa ga tsoron ta’addancin.

 

A bisa ga amincewa da kudirin, majalisar ta bukaci rundunar sojin Nijeriya da rundunar ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro da su gaggauta tura jami’an tsaro domin karfafa kai hare- hare a yankin Kuchi a karamar hukumar Kebbe da yankunan karamar hukumar Tambuwal domin kare rayuka, dukiyoyi da gonaki.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Rashin Tsaro A Nijeriya Ba Zai Ƙare Ba Matuƙar Ba A Samar da Ayyukan Yi Da Mulki Na Adalci Ba – Amaechi October 14, 2025 Manyan Labarai Amnesty International Ta Soki Tinubu Kan Yi Wa Masu Laifin Take Haƙƙin Ɗan Adam Afuwa October 14, 2025 Manyan Labarai Zaman Gidan Yari Ya Nuna Min Mutanen Da Ya Kamata Na Yi Hulɗar Siyasa Da Su — Faruk Lawan October 14, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: karamar hukumar

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu Ya Isa Birnin Rome Don  Halartar Taron Tsaro Na Aqaba

 

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai An Sauya Kwamishinan Ƴansandan Abuja Saboda Rashin Tsaro October 12, 2025 Manyan Labarai Trump Da Al-Sisi Za Su Jagoranci Taron Zaman Lafiya Dawwamammiya Ta Gaza A Masar October 12, 2025 Manyan Labarai Yaƙi Da Boko Haram: An Kashe Sojoji 2,700 A Shekara 12 – Janar Irabor October 12, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ’Yan bindiga sun kai hari a Kankia
  • Rasha ta kai wa tawagar kayan agajin MDD hari a Ukraine
  • Hukumar Kwastam Ta Tara Naira Biliyan ₦658.6 A Watan Satumba — DG Na NOA
  • Dan Majalisar Tarayyar Kaduna ya bar Jam’iyyar PDP
  • Rikicin kabilanci: Mutane 2 sun mutu, wasu 7 sun jikkata a Jigawa
  • Ahmed Musa Ya Nemi Afuwar Ƙungiyar 3SC Akan Abinda Ya Faru Da ‘Yan Wasansu A Kano
  • Cibiyar Lafiya Ta Nasser Ta Ce: Yaran Gaza 5,500 Suna Bukatar Agajin Gaggawa A Kasashen Waje
  • Tinubu Ya Isa Birnin Rome Don  Halartar Taron Tsaro Na Aqaba
  • Tinubu ya tafi Rome don halartar taro kan sha’anin tsaro