Afuwar Tinubu za ta buɗe hanyar ci gaba da aikata miyagun laifuka — Atiku
Published: 13th, October 2025 GMT
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya nuna damuwa kan yadda shugaba Bola Tinubu ya yi wa wasu mutane afuwa, ciki har da waɗanda suka aikata manyan laifuka.
A cikin saƙon da Atiku ya wallafa a shafinsa na X, ya ce ana yin afuwa ne ga waɗanda aka yi wa rashin adalci ko waɗanda suka nema gafara bayan sun shafe wani lokaci a gidan yari.
Ya ce a wannan karon an yi wa masu safarar ƙwayoyi, masu garkuwa da mutane, masu kisan kai, da kuma masu cin hanci da rashawa afuwa.
Atiku, ya ce abin mamaki ne yadda gwamnati ke yafewa irin waɗannan mutane, a daidai lokacin da ƙasar ke fama da matsalar tsaro da lalacewar tarbiyya, musamman tsakanin matasa masu shan miyagun ƙwayoyi.
Ya ce bincike ya nuna cewa kashi 29 na waɗanda aka yi wa afuwa suna da alaƙa da hakrar miyagun ƙwayoyi, yayin da Najeriya ke ƙoƙarin wanke sunanta a idon duniya kan yaƙi da miyagun ƙwayoyi.
Atiku, ya ce maimakon wannan afuwa ta zama darasi ga masu laifi, ta zama hanyar durƙusa da ɓangaren shari’a da jami’an tsaro da ke sadaukar da rayukansu wajen kamawa da hukunta masu aikata laifuka.
Ya ƙara da cewa idan gwamnati ta fara yafe wa masu laifi, hakan zai rage ƙimar shugabanci kuma ya ƙarfafa wa masu aikata laifuka su ci gaba da aikata su.
Atiku ya jaddada cewa Najeriya tana buƙatar shugabanci na gari wanda zai tabbatar da adalci a shari’a, ba tare da nuna bambanci ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Afuwa Miyagun ƙwayoyi Najeriya
এছাড়াও পড়ুন:
An janye ’yan sanda 11,566 daga gadin manyan mutane a faɗin Nijeriya
Sufeto Janar na ’Yan sandan Nijeriya, Olukayode Egbetokun, ya sanar da cewa sun aiwatar da umarnin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu na janye dakarunsu daga gadin ɗaiɗaikun mutane da ake kira VIP.
IG Egbetokun ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai a yau Alhamis, yana mai cewa zuwa yanzu sun janye dakaru 11,566 daga gadin manyan mutane a faɗin Nijeriya.
Mbappe ya ci ƙwallaye 4 rigis a wasan Madrid da Olympiacos An rantsar da sabon shugaban kasa a Guinea-Bissau bayan juyin mulkin sojoji“Wannan karon za mu aiwatar da umarnin da kyau saboda umarnin shugaban ƙasa ne,” in ji shi.
“Babu wani gwamna, ko minista, ko abokaina da za su kira su takura min saboda sun san cewa umarnin shugaban ƙasa ne. Ina kuma da tabbacin cewa ba za su uzzura wa kwamashinonin ’yan sanda ba ma.”
Ya ƙara da cewa za su tura jami’an da aka janye zuwa “wuraren da aka fi buƙatarsu, musamman a wannan lokaci mai muhimmanci.”
Aminiya ta ruwaito cewa, a bayan nan ne Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da aika ’yan sanda ga manyan mutane domin ba su tsaro na musamman, yana mai mayar da su zuwa aikin tsaro da ya shafi al’umma baki ɗaya.
Kazalila, a ranar Laraba, 26 ga watan Nuwamba ne Tinubun ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro a faɗin ƙasar, inda ya bayar da umarnin a ɗauki matakan gaggawa domin magance matsalolin tsaro da ƙasar ke fuskanta.
Shugaban ya ce a ɗauki sababbin ’yan sanda 20,000, ƙari a kan guda 30,000 da ya fara amincewa a ɗauk, wanda za a yi amfani da sansanonin horar da masu yi wa ƙasa hidima wajen horar da sababbin ’yan sandan da za a ɗauka.