Aminiya:
2025-11-14@20:59:39 GMT

Cirar kudin kwastoma: Majalisa ta gayyaci CBN da bankuna

Published: 14th, October 2025 GMT

Majalisar Wakilai ta gayyaci Babban Bankin Najeriya (CBN) da bankunan kasuwanci domin amsa tambayoyi kan yadda suke cirar cajin kudade barkatai daga asusun masu ajiya.

Majalisar ta gayyace su ne bayan kudurin da Honorabul Tolani Shagaya ya gabatar kan abin da ta kira ‘cirar cajin kudade barkatai babu bayani ba,’ da bankuna suke yi daga asusun masu ajiya, sabanin dokokin CBN.

Honorabul Shagaya ya ce kodayake bankuna da gudanar da hidima ne da ake biya, amma yawancin ’yan Najeriya suna kuka kan yadda suke yawan ciyar kudade — kamar na tura sakon tses, kula da katin ajiya, kula da asusun ajiya, tura kudi, hrajin kan sarki da wasu da ba su san da ake fiye da sau daya.

Ya ce bankuna na ci gaba da cirar irin wadannan kudade daga asusun jama’a duk kuwa da dokar CBN da ke kula da haraji, amma bankunan ba su bi.

Dan Majalisar ya ce, “Wannan mummunar dabi’a tana shafar kasuwanci da masu karamin karfi da dalibai da sauran masu rauni da suke cikin halin kakanika yi.

“Idan ba a gaggaunta yin bincike da kuma magance wannan matsalar za ta ci gaba da kawo rashin yardar jama’a da tsarin banki tare da tafiya ba tare da wasu rukuni na al’ummar kasa ba, gami da zagon kasa ga muradun bankin CBN,” a cawersa.

Bayan sauraron kudurin ne Majisar ta umarci CBN ya wallafa cikakken jerin cajin kudaden da ya amince da su cikin kalamai masu saukin ganewa, kuma ta hukunta bankuna masu kunnen kashi.

Daga nan Majalisar ta bukaci CBN ya samar da kafar tuntuba mai saukin samu domin gabatar da korafin kwastomomi kan irin wadannan caji.

Mambobin Majalisar sun kuma bukaci hukumar kare hakkin kwastomomi (FCCPC) da dangoginsa da wayar da kan al’umma kan hakkokin da suka danganci cajin da bankuna ke cira daga asusun masu ajiya.

Daga nan zauren Majalisar ya umarci Kwamitin Majalisar kan Harkokin Cibiyoyin Hadahadar Kudade su bayyana a gabansa domin amsa tambayoyi kan wadannan korafe-korafe sannan ya mika rahotonsa cikin makonni hudu domin daukar matakin da ya dace.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Injiniya Sagir Ibrahim Ƙoƙi Ya Fice Daga Jam’iyyar NNPP

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Majalisar Wakilai Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Wa Tawagar Ɗan Majalisar Neja November 7, 2025 Siyasa Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha November 4, 2025 Labarai “Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan  Trump November 3, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dalilin Asusun NADF Na Yin Hadaka Da Gwamnatin Jihar Jigawa
  • Majalisar Wakilai ta dage lokacin fara yin jarabawar WAEC a kwamfuta zuwa 2030
  •   Janar Ali Fadwi: Muna Aiki Tukuru Domin Sabunta Nisan Makamanmu Masu Linzami
  • Sojoji Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Dillalin Makamai A Taraba
  • Majalisa ta amince da buƙatar Tinubu na karɓo rancen N1.15bn
  • Majalisar Dattawa Ta Amince da Karbo Rancen Naira Tiriliyan 1.15 Domin Cike Gibin Kasafin Kudi
  • Injiniya Sagir Ibrahim Ƙoƙi Ya Fice Daga Jam’iyyar NNPP
  • Ɗan Majalisar Wakilai daga Kano Sagir Ƙoƙi ya fice daga NNPP
  • An Bayyana Ranar Karshe Ta Biyan Kudin Aikin Hajji Mai Zuwa
  • Yadda muka daƙile yunƙurin tsige Akpabio daga shugabancin Majalisa – Orji Kalu