An Gudanar Da Taron Hadin Kai Na Raya Albarkatun Kasa Tsakanin Sin Da Mozambique
Published: 11th, October 2025 GMT
A nasa tsokaci kuwa, sakataren gwamnatin Mozambique mai kula da ma’adinai Jorge Daudo, cewa ya yi lardin Shandong yana daya daga cikin larduna masu kwazo da ci gaban masana’antu a Sin, kuma yana da karfi a fannonin hakar ma’adinai, da sarrafa karafa da masana’antu. Sabo da haka, Mozambique na fatan kara yin hadin gwiwa da lardin na Shandong.
এছাড়াও পড়ুন:
Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban Amurka
An kulle Fadar Shugaban Kasar Amurka ta White House tare da wasu gine-ginen gwamnati da dama, sakamakon harbin ɗan bindigar da ya raunata sojoji biyu a kusa da fadar.
A yayin, an harbe masu tsaron fadar biyu har lahira.
Gwamna Patrick Morrisey da farko ya ce an kashe sojojin, amma daga baya ya ce yana samun “rahotanni masu karo da juna” game da halin da suke ciki, yana mai da cewa za a fitar da ƙarin bayani idan an tabbatar.
A cikin wani rubutu a shafin X, ya ce, “Yanzu muna samun rahotanni masu cin karo da juna game da halin sojojin biyu, kuma za mu bayar da ƙarin bayani idan mun samu cikakken rahoto.
“Addu’o’inmu suna tare da waɗannan jarumai, iyalansu, da dukan al’ummar Amurka.”
A cewar rahotanni, Shugaba Donald Trump yana gidansa na hutu a Mar-a-Lago da ke Palm Beach, Florida, a lokacin da lamarin ya faru.
Mai magana da yawun Fadar White House, Karoline Leavitt, ta ce cikin wata sanarwa: “Fadar White House ta san da wannan mummunan lamari kuma tana bin diddigi. Shugaban kasa ya samu cikakken bayani.”
’Yan sandan birnin Washington DC sun ce an kama wanda ake zargi da harbin.
Sojojin National Guard sun kasance a Washington DC tsawon watanni a matsayin wani bangare na matakin Trump na yaki da laifuka a babban birnin ƙasar.
A cikin wani rubutu a dandalinsa na Truth Social, Trump ya ce: “Dabban da ya harbi mambobin National Guard biyu, wanda dukkansu suka ji rauni mai tsanani kuma yanzu suna a asibitoci daban-daban, shi ma ya ji rauni sosai, amma duk da haka, zai ɗanɗana kuɗarsa.”