Iran Ta Gabatar Da Shawarar Kulla Yarjejeniyar Tausayawa A Tsakanin Matan Duniya
Published: 14th, October 2025 GMT
Mai bai wa shugaban kasar Iran shawarar akan harkokin mata da iyali Malama Zahra Beruz Azar ta gabatar da shawarar a kulla wata yarjejeniya ta tausayawa a tsakanin matan duniya domin samar da damar gina rayuwa ta jin kai da ‘yan’adamtaka mai dorewa.
Malama Zahra Behruz Azar ta gabatar da wannan shawarar ne dai a yayin taron kasa da kasa na mata da aka bude a kasar China.
Haka nan ta kuma bayyana cewa; A wannan lokacin muna rayuwa ne a cikin karnin da ci gaba da fasahar kere-kere su ka sauya salon rayuwa, ta yadda kirkirarriyar fasaha ta zama mai matukar tasiri a cikin matakan da ake dauka, kamar kuma yadda Sakandami ( Robot) ya maye gurbin bil’adama a cikin wasu fagage.”
Mai bai wa shugaban kasar Iran din shawara akan harkokin mata da iyali ta ci gaba da cewa; Tare da gagarumin ci gaban da ake da shi a fagen kere-kere sai dai kuma bai zama mai hada zukata ba, da hakan ya sa tazara mai yawa ta karu a tsakanin masu shi da marasa shi,kuma mutane suna kara zama cikin kadaici.
Haka nan kuma ta yi ishara da yadda ake kasuwanci da yake-yake da wasa da kwakwalen mutane da yadda kiyayya da gaba a cikin fagagen sadarwa na jama’a.
Zahra Behruz Azar ta ce jin kai da tausayawa su ne abubuwan da za su dawo da ruhin ‘yan’adamtaka a cikin duniyar da tashe-tashen hankula su ka ci dununta.
Dangane da rawar da mata suke takawa a Iran, Malama Zahra Behruz ta ce; Matan da suke cikin jami’oi a Iran sune kaso 60%, yayin da fagen kirkire-kirkire su ka kai kaso 24%. Lokitocin da ake da su a fadin Iran kuwa, mata ne kaso 40%, sai kuma masu bayar da shawar akan harkar kiwon lafiya da sun kai 30%.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Larijani: Gagarumar Tarbar Da Aka Yi Wa Fursunonin Falasdinawa Ta Nuna Hakikanin Wanda Ya Sami Nasara October 14, 2025 Hamas Ta Mika Yahudawa 7 Daga Cikin 20 Da ke Hannunta Ga Kungiyar Red Cross October 13, 2025 Iran: Kakabawa Kasa Mai Makwabta 16 Takunkumi Ba Abu Ne Mai Sauki Ba. October 13, 2025 An Gano Gawarwaki 323 Karkashin Burabutsai Bayan Dakatar Da Bude Wuta A Gaza October 13, 2025 Tehran Ta yi Gargadi Game Da Barazanar Yaduwar Fadan Iyakar Afghanisatan Da Pakistan. October 13, 2025 Kungiyar (ASUU) Ta Sanar Da Shiga Yajin Aikin Gargadi A Kasa Baki Daya . October 13, 2025 Aragchi: HKI Ba Zata Mutunta Tsaida Wuta A Gaza Ba October 13, 2025 Iran Ta Ki Zuwa Masar Saboda Bata Son Haduwa Da Azzaluman Da Suka Kashe Falasdinwa A Gaza October 13, 2025 Shugaban Kasar Amurka Donal Trump Ya Isa HKI Kafin Taron Sharm Sheikh October 13, 2025 An Fara Musayar Fursinoni Tsakanun Hamas Da HKI A Safiyar Yau Litini October 13, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Makaman Iran Masu Linzami Ne Kandagarkon Dake Takawa Makiya Birki
Kwamandan rundunar soja ta “Sayyidush-shuhada” dake Tehran Janar Qurbani Muhammad Wali Zadeh ya bayyana cewa; makamai masu linzami da Iran take da su ne, da kuma jiragen sama marasa matuki suke takawa makiya birki.”
Janar Qurbani Muhammad Wali Zadeh ya kuma ce; Albarkacin sadaukar da jinanai da shahidai su ka yi ne da kuma kwazon kwararrun masana, su ka sa Iran samun wannan karfin da take da shi.
Wali Zadeh wanda ya halarci taron girmama rundunar sa-kai ta Basiji da kudancin birnin Tehran, ya kara da cewa, Iran ta samu matsayin da take da shi ne a wannan lokacin daga jihadin shahidai da tsayin dakar al’ummar Iran, sannan kuma ya kara da cewa; A halin yanzu karfin Iran a fagen makamai masu linzami ya kai kolin da makiya suka kwana da sanin cewa duk wata barazana ta kawo wa jamhuriyar musulunci hari, zai fuskanci martani mai tsanani.
Haka nan kuma ya ce; Al’ummar Iran ba ta taba zama mai tsokana da fara kai hari ba a cikin kowane fada, amma kuma ba ta ja da baya a gaban barazanar makiya.
Janar din sojan na Iran ya yi Ishara da martanin da Iran din ta mayar bayan shahadar Janar Shahid Kassim Sulaimani da ya tabbatar da karfinta na kare kai. Wannan karfin ne yake hana abokan gaba tarbar aradu da ka, su kawo wa Iran din hari.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Najeriya: Allah Ya Yi Wa Babban Malamin Addini Shehu Dahiru Bauchi Rasuwa November 27, 2025 An Zabi JMI A Cikin Majalisar Zartarwan Ta Hukumar Yaki Da Makaman Guba Ta Duniya CWC November 27, 2025 HKI Tana Amfani Da Tsagaita Wuta A Gaza Don Sake Shata Kan Iyakokin Yankin November 27, 2025 Yawan Falasdinawa Da Suka Yi Shahada Na Karuwa Saboka Keta Yarjeniyar Tsagaita Wuta November 27, 2025 An Rutsa Da Tsohon shugaban Kasar Najeriya A Guine Bissau Bayan Juyin Mulki November 27, 2025 Iraki: An Dakatar Da Tura Iskar Gas Zuwa Injunan Bada Wutan Lantarki A Yankin Kurdistan November 27, 2025 Ma’aikatar Harkokin Wajen Falasdinu Ta Sanar Cewa Akalla Yan Mata 33000 Ne Isra’ila Ta Kashe A Gaza November 26, 2025 Mataimakin Shugaban Nijeriya Ya Dawo Gida Bayan Kammala Taron G20 A Afrika Ta Kudu. November 26, 2025 Aljeriya Tayi Kira Da A Dakatar Da Israila Game Da Hare-haren Da Take Kaiwa November 26, 2025 Sojoji Sun Sanar Da Kwace Mulki A Kasar Guinea Bissau November 26, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci