Zuwa Kofin Duniya: Za A Yi Ta Ta Kare A Nahiyar Afirka
Published: 12th, October 2025 GMT
Kasashe hudu da suka fi kokari a cikin wadanda suka kare a mataki na hudu za su fafata wasannin raba-gardama, sai wadanda suka samu nasara su sake raba-gardama da wasu kasashen na waje.
A yanzu daI manyan kasashen nahiyar ta Afirka irin su Kamaru da Nijeriya suke fuskantar barazanar rasa gurbi, duk da haka suna da wasu damarmakin da idan suka yi sa’a za su iya tsintar kansu a gasar a badi.
Kasar Masar ta wuce Burkina Faso da maki biyar, sannan idan ta samu nasara a kan Djibouti shikenan ta samu tikiti. Ita kuma kasar Djibouti tana can karshen teburi ne, domin maki daya tak take da shi a wasa takwas da ta buga.
Idan ma Masar ta yi rashin nasara a wasan, za ta fatata da Guinea-Bissau a ranar Lahadi. Burkina Faso kuma wadda take kokarin zuwa ta biyu za ta buga wasa ne da kasar Saliyo, sai kuma kasar Habasha, amma tana bukatar samun nasara a wasannin kafin samun gurbin buga wasannin raba-gardama.
A rukunin (B) kuwa nasarar da Senegal ta samu a kan DR Congo ce ta ba ta damar darewa teburin rukunin, inda yanzu ta ba da tazarar maki daya. Tawagar ta Teranga Lions za ta je wasa da Sudan ta Kudu wadda ke karshen teburi, sai ta buga wasan karshe da Mauritania, inda take bukatar nasara biyu domin samun shiga gasar.
DR Congo dai na fatan Senegla ta yi rashin nasara, ita kuma ta samu nasara a wasannin biyu a gidan Togo da kuma Sudan a gida. Sudan na bukatar nasara a duka wasanninta, sannan Senegal ta yi rashin nasara wasanninta biyu domin samun gurbin zama ta daya a teburi, amma tana da damar zuwa ta biyu idan ta doke Congo.
A wannan rukunin kuma bayan hukuncin da FIFA ta dauka a kan kasar Afirka ta Kudu na cire mata maki uku saboda sanya dan wasan da bai cancanta ba a wasanta da kasar Lesotho.
Yanzu Benin ce kan gaba a rukunin, inda take saman Afirka ta Kudu da bambancin kwallaye, sai Nijeriya da Rwanda suke da maki da na hudu, amma duk suna da damar samun gurbi.
Benin na da wasa a gidan Rwanda da Nijeriya, sai tawagar Afirka ta Kudu za ta buga da Zimbabwe, sai Rwanda a gidanta. Nijeriya tana da wasa a gidan Lesotho sai Benin, kuma dole ne ta ci wasanninta guda biyu, amma ko da ta lashe wasannin, sai yadda ta wakana a sauran wasannin kafin sanin matsayarsa.
Nasarar da Cape Berde ta samu a kan Kamaru da ci daya mai ban haushi a watan jiya ta sa kasar ta kama hanyar kafa tarihin zuwa gasar cin Kofin Duniya na farko a tarihinta.
Yanzu kasar na bukatar nasara daya kacal a wasanta da Libya ko kuma a wasanta a gida da kasar da ke karshen teburi, wato tawagar ‘yan wasan kasar Eswatini. Kamaru za ta iya samun nasara da bambancin zura kwallaye idan ta doke Mauritus da Angola, ita kuma Cape Berde ta yi canjara a wasannin biyu, ko kuma idan Kamaru ta samu maki hudu a wasannin biyu,
ita kuma Cape Berde ta yi rashin nasara. Sai kuma Libya ce ta uku, kuma maki uku ne tsakaninta da Kamaru, kuma za ta iya bayar da mamaki.
Kasar Morocco ta riga ta samu gurbin shiga gasar cin kofin duniyar.
A cikin rukuni na E kuma kasashen Tanzania da Nijar da Zambia ne sauran kasashen da ke rukunin, kuma yanzu suna ta fafatawa ne domin samun gurbi na biyu wanda zai iya buga wasan raba-gardama.
A cikin rukuni na (F) kuwa, Ibory Coast na gaba da Gabon da maki daya bayan canjaras da ta yi da kasar Gabon a Francebille a watan Satumba. Kasar za ta je gidan Seychelles a ranar Juma’a, sai kuma ta fafata da Kenya a ranar Talata. Gabon za ta je gidan Gambia, sai kuma Burundi ta bakunce ta.
A cikin rukuni na G kuwa Algeria ita ma ta ba da tazarar maki hudu a saman teburi, kuma tana bukatar maki uku ne a wasanta da kasar Somalia wadda ta riga ta fita ko kuma ta biyu Uganda zai ta ba gurbi. Uganda ta zarce Mozambikue ne kawai da bambancin zura kwallo a matakin na biyu.
Can kuwa a cikin rukuni na H, Tunisia ta riga ta tsallake bayan samun gurbi duk da cewa akwai sauran wasaNNI biyu da za ta buga, inda ita kuma Namibia ta dage wajen neman zama ta biyu a rukunin. Namibia za ta je gidan Liberia a ranar Alhamis kafin ta karkare a birnin Tunis.
Daga rukuni na I kuma kasashe uku ne ke fafutikar samun gurbin na kai-tsaye, amma Ghana ce a sama da tazarar maki uku a saman Madagascar da Comoros. Ghana za ta samu gurbi idan ta yi nasara sannan Madagascar ta gaza samun maki uku. Wasan karshe na Ghana shi ne a gida da Comoros, ita kuma Madagacar za ta je gidan Mali a wasan na karshe.
Kamar yadda FIFA ta tsara, kasashe hudu da suka fi maki a cikin kasashen da suka kare a na biyu daga rukunoni tara din ne za su fafata wasannin raba-gardama a watan Nuwamba.
Zuwa yanzu dai kasashen Gabon da Madagascar da DR Congo da Burkina Faso ne a gaba a cikin tawagogi na biyu. Sakamakon za su iya canjawa bayan wasanni biyu na karshe, sannan kuma ba a riga an sanar da tsarin wasannin na raba-gardama ba.
Amma kasashen da suka samu nasara a wasannin na raba-gardama ne za su sake fafatawa a wasanin na raba-gardama da wasu kasashen na duniya kafin samun gurbi a gasar ta duniya.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAকীওয়ার্ড: ta yi rashin nasara nasara a wasan raba gardama samu nasara
এছাড়াও পড়ুন:
Ammar Hakim Ya Gargadi Kasashen Yamma Da su Kiyayi Tsoma Baki A Harkokin Cikin Gidan Kasar.
Rahotannu sun bayyana cewa sayyid Ammar Hakim shugaban kungiyar wisdom movement na kasar Iraqi ya kaddama da yakin neman zabe inda yayi kira da hadin kai tsakanin alummar kasar kuma ya gargadi kasashe waje da su guji tsoma baka a cikin alamuran kasar.
Wadannan bayanai suna zuwa ne adaidai lokacin da kasar Amurka take matsin lamb akan kasar Iraqi na ta rusa kungiyar Hashdu shaabi, musamman bayan abubuwa da suka faru a kasashen siriya da kuma kasar Labanon.
An kafa kungiary ta Hshadushaabi ne karkashin umarnin babban malamin Addini na kasar Ayatullah Sisitani domin tunkarar kungiyar ta’adda ta da’aesh
Daga karshe Hakim ya jaddada cewa alummar iraki ne kawai suke da hakkin yanke hukumci ba tare da ingizasu ba, duk da matsain lambar da take fuskanta daga kasashen waje. Yace muna son iraki madaidaiciya mai mututunta akidar alummar da suka fi rinjaye, saboda iraki ta kowa ce, babu wani mutum ko gunguni jama’a da zai yi abu shi daya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sarkin Morocco Ya yi Magana Tun Bayan Barkewar Zanga-zanga A Kasar . October 11, 2025 Wani Dan Majalisar Dokokin Kasar Iran Ya Ja Kunnen Amurka Kan Taba Jiragen Dakon Man Kasa October 11, 2025 Bayan Yakin Kwanaki 12, Kifar Da Gwamnatin JMI Ya Fita Daga Zabin Makiya: Aref October 11, 2025 Iran Ta Bukaci HKI Ta Aiwatar Da Yarjeniya Da Gaza Kamar Yadda Take October 11, 2025 HKI Ta Kashe Mutane 19 A Gaza Duk Tare Da Tsagaita Wuta October 11, 2025 Iran Tana Goyon Bayan Duk Wani Shirin Zaman Lafiya Da Ya Hada Da Kawo Karshen Kisan Kiyashi A Gaza October 11, 2025 Faransa Da Jamus Da Kuma Birtaniya Sun Bayyana Aniyarsu Ta Ganin An Farfado Da Tattauna Da Iran October 11, 2025 Kungiyoyin Falasdinawa Sun Fitar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Kan Tsagaita Bude Wuta A Gaza October 11, 2025 Venezuala Ta Bukaci Kwamitin Sulhun M.D.D Da Ya Tabbatar Da Cewa: Amurka Tana Barazana Ga Zaman Lafiya October 11, 2025 Pakistan Ta Kai Hari Kan Kasar Afganistan, Inda Ake Rade-Radin Kashe Shugaban Taliban Na Kasarta October 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci