Aminiya:
2025-11-28@12:17:10 GMT

Kamaru: Jam’iyyun adawa sun ayyana Bakary a matsayin wanda ya lashe zaɓe

Published: 14th, October 2025 GMT

Jam’iyyun adawa a ƙasar Jamhuriyar Kamaru sun ayyana Issa Bakary Tchiroma a matsayin wanda lashe zaɓen shugaban ƙasar da gagarumin rinjaye.

Gamayyar jam’iyyun adawa da ƙungiyoyin fararen hula na Union for Change ta ce sakamakon da suka tattara daga fadin ƙasar da ƙasashen waje ya nuna Bakary ya samu kashi 60 zuwa 80 cikin ɗari na ƙuri’u a rumfunan zaɓe da dama.

Sun buƙaci Shugaba Paul Biya, wanda ke neman wa’adin mulki na takwas a zaɓen da ya gaggauta miƙa saƙon taya murna ga Issa Bakary Tchiroma.

“Muna kira ga shugaban ƙasa mai barin gado da ya gaggauta taya sabon shugaban ƙasa murna,” in ji ƙungiyar,” in ji wata sanarwa da shugabannin ƙungiyar, Anicet Ekane da Djeukam Tchameni, suka fitar a birnin Douala.

Zaben Kamaru: Issa Tchiroma Bakary ya lashe yankunan da Biya ke da rinjaye Majalisar Shura ta fara ganawar sirri da Malam Triumph

“’Yan Kamaru sun yanke shawara. Sakamakon da muke karɓowa daga sassan ƙasar da ma ƙetare ya nuna a sarari cewa, ɗan takarar talakawa, Issa Tchiroma Bakary, ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 12 ga Oktoba 2025,” in ji sanarwar.

Ƙungiyar ta zargi jam’iyyar mai mulki ta CPDM da ƙoƙarin amfani da “tsohuwar hanyar maguɗi,” amma ta ce duk da haka Bakary ya yi mata “mummunar kaye mara misaltuwa,”

Union for Change 2025 ta kuma roƙi hukumomin gwamnati da jami’an tsaro da su mutunta zabin al’umma da zaman lafiya, tare da kira ga ’yan ƙasa da su ci gaba da kasancewa cikin shiri domin kare zaɓinsu.”

Bakary, wanda tsohon minista ne a gwamnatin shugaba Paul Biya, an zaɓe shi a watan Satumba a matsayin “ɗan takarar haɗin kai na jama’a.”

Ƙungiyar, wadda rahotanni ke cewa ta ƙunshi fiye da ƙungiyoyi 50 na siyasa da na fararen hula, ta ce manufarta ita ce haɗa ɓangarorin adawa domin yin aiki tare wajen sauyin siyasa da sake gina ƙasa.

“Ƙungiyar Talakawa ce, wadda take buɗe ƙoa ga kowa — ɗan ƙasa ko ƙungiya, ciki har da waɗanda ’yan takararsu aka hana shiga zaɓen shugaban ƙasa ba bisa ƙa’ida ba,” in ji sanarwar.

Ƙungiyar ta bayyana kanta a matsayin sabuwar ƙarfi na farfaɗo da dimokuraɗiyya, tana mai alƙawarin sake gina Kamaru a cikin lokacin canji na shekaru uku zuwa biyar.

A lokacin da ake rubuta wannan rahoto, Hukumar Ƙoli ta Ƙasar ba ta fitar da sakamakon hukuma ba, lamarin da ake ganin zai iya ƙara ɗaga zullumin siyasa a kwanaki masu zuwa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Bakary Tchiroma Issa Bakary Tchiroma Kamaru Paul Biya Zaɓe

এছাড়াও পড়ুন:

Sojoji sun yi juyin mulki a Guinea-Bissau

Sojoji a Guinea-Bissau sun ce sun yi juyin mulki tare da karɓe ragamar mulkin ƙasar.

Sun kuma sanar da dakatar da zaɓukan ƙasar tare da rufe iyakokinta nan take.

’Yan sanda sun kama masu laifi 34 a Kaduna Tukur Mamu ya karbi N50m daga kuɗin fansar harin jirgin kasan Kaduna – DSS

Wannan na zuwa ne kwana uku bayan ƙasar ta gudanar da zaɓen ’yan majalisa da na shugaban ƙasa.

A yau ne aka wayi gari ana ji. harbe-harbe a kusa da fadar shugaban ƙasa, lamarin da ya tashi hankalin mutane.

Daga bisani kuma dakarun soji suka rufe babban titin da ke zuwa fadar shugaban ƙasar.

A cewar majiyar AFP, sojojin sun karanta sanarwar ƙwace mulkin ƙasar a hedikwatar rundunar da ke babban birnin ƙasar, Bissau.

 

Cikakken rahoto na tafe…

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hamɓararren Shugaban Guinea-Bissau ya gudu Senegal
  • An gano gawawwakin mata uku ’yan Kamaru da aka sace a Anambra
  • Juyin mulki ya rutsa da Jonathan a Guinea-Bissau
  • Shugaba Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta-baci Kan Harkar Tsaro Tare da Bada Umurnin Daukar Sabbin Jami’ai
  • Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro
  • Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan harkar tsaro
  • Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan tsaro
  • Sojoji sun yi juyin mulki a Guinea-Bissau
  • Tabarbarewar Tsaro na Barazana ga Siyasar Ƙasar Nan Gabanin Zaɓen 2027-Ado Doguwa
  • Uganda: An Kama Fiye Da ‘Yan Hamayyar Siyasa 300 A Lokacin Yakin Neman Zabe