Ana Gudanar Da Taron Masu Mukamin Magajin Gari Na Kasa Da Kasa A Birnin Dunhuang Na Sin
Published: 13th, October 2025 GMT
A matsayin birnin dake karbar bakuncin taron, Dunhuang mazauni ne ga wurare 3 dake cikin jerin wuraren gargajiya na hukumar UNESCO da kuma wuraren kayayyakin gargajiya sama da 260, wanda kuma ke nuna hadaddun dabarun da aka dauka a shekarun baya-bayan nan da nufin kare al’adun gargajiya yayin da ake bunkasa birnin.
এছাড়াও পড়ুন:
Mutuwar Sheikh Dahiru Bauchi Babban Rashi Ne Ga Kasa Baki Daya
Daga Bello Wakili
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya karɓi labarin rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi cikin alhini da jimami.
Fitaccen malamin da ke Bauchi ya rasu ne a ranar Alhamis 27 ga watan Nuwamban 2026, yana da shekaru 101.
Shugaban Ƙasan ya yi jimamin rasuwar jagoran Darikar Tijjaniyya, yana bayyana shi a matsayin ginshiƙin ɗabi’a wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa da wa’azi.
Shugaba Tinubu ya ce rashinsa babban rashi ne ba ga iyalansa da dimbin mabiyansa kaɗai ba, har ma ga ƙasa baki ɗaya.
Shugaban Ƙasa ya tuna da albarka da goyon bayan da ya samu daga marigayi Sheikh Dahiru Bauchi a lokacin yakin zaɓen 2023.
“Sheikh Dahiru Bauchi malami ne, uba, mai cike da natsuwa da hikima. A matsayinaa na mai wa’azi kuma masani kan tafsirin Alƙur’ani Mai Girma, yana da’awar zaman lafiya da tsoron Allah. Rasuwarsa ta bar babban gibi,” in ji Shugaban Ƙasa.
Shugaba Tinubu ya yi ta’aziyya ga mabiyan Shehun a ci da wajen ƙasa bisa wannan babban rashi.
Haka kuma ya ja hankalinsu da su girmama sunansa ta hanyar bin koyarwarsa ta zaman lafiya, ƙarfafa dangantakarsu da Allah, da kuma kasancewa masu taushin zuciya ga jama’a.