Leadership News Hausa:
2025-11-27@21:13:46 GMT

Tsokaci A Kan Mata Masu Tsananin Kishi

Published: 12th, October 2025 GMT

Tsokaci A Kan Mata Masu Tsananin Kishi

Kishi halak ne kuma so ne yake kawo kishin. Masu irin wannan kishin karshensu nadama ce. Kishi wani abu ne da ake jinsa a cikin rai, kuma kishi ba sai akan aure ake yin sa ba.Hanyoyin da ya kamata abi wajen magance irin wannan shi ne; muna tuna komai yayi farko to yana da karshe, sannan ba kanta farau ba kuma ba kanta karau ba.

Muna saka hakuri da tawakkali mu yi kiyayya ba mai zurfi ba, sannan mu yi soyayya ba mai zurfi ba, a karshe sai abin ya zo mana da sauki. Allah ya sa mu dace, amin.

 

Sunana Comr, Nr. Ibrahim Lawan Stk:

Abubuwa da dama na haifar da kishi amma mafi lura shi ne rashin godiya a wajen Allah subahanahu wata’ala da kuma son zuciya tare da son rai irin na mata. Kishi shi ne son kasancewa da namiji a matsayin abokin tarayya ko zamantakewar Aure ba tare da wata ta ji ra’ayin hakan ba ko kuma ta nuna bukata tare da ra’ayin akan namijin da wata ke rayuwa da shi ba. Hanyoyin da za a bi domin magance matsalolin kishi musamman a lokacin da miji zai karo abokiyar zama sun hada da hakuri, danne zuciya, tare da juriya hadi da biyayya ga duk wani umarni daga wajen miji don kuma kaucewa sabawa umarnin Allah da Manzon sa (S.A.W).

 

Sunana Nabila Dikko, Argungun Jihar Kebbi:

To mafi akasarin dalilai da ke sa mata irin wannan kishi shi ne; karancin fahimta da rashin hakuri, da son mallaki namiji su kadai, da son zuciya, kuma hakan na kawo rashin zaman lafiya da rikici da lalacewar dangantaka. Kishi wani abu ne da ke sa zuciya ta dinga son mallakar wani abu ita kadai ko abin da kake da shi ko tsoron rasa shi. A musulinci, kishi halas ne idan bai kauce wa ka’ida ba. Domin magance kishi dole sai mace ta dogara ga addu’a, ta daidaita tunaninta, ta rungumi gaskiyar cewa mijinta yana iya kara aure, sannan ta mayar da hankali wajen kyautatawa maigidanta ba tare da yin abubuwan da ba su dace ba. Shawarata ga mata su kasance masu natsuwa, su guji haddasa rigima. Sai maza ku kasance masu adalci, ku bayyana gaskiya, ku kiyaye hakkin kowace mata, a daidaita adalci ku daina haddasa tsananin kishi a tsakanin matanku.

 

Sunana Aminu Adamu, Malam Maduri A Jihar Jigawa:

To, da farko dai akwai jahilci domin shi ke jawo mutum ya kashe kan sa, don indai mutum yana da ilimi ya san illar kashe kai. Sai na biyu kuma rashin rungumar kaddarar da Allah ya kaddarawa mutum domin ita kaddara bata canjawa. To, kishi wani abu ne da Allah yake halittar mutane da shi maza da mata to a lokuta da dama maza su kan yi kokari wajen sarrafa nasu sabanin wasu daga cikin mata da kishin yake sa su aikata aikin da-na-sani ko ma su hallaka kan su.

 

Sunana Hafsat Sa’eed, daga Neja:

Kishi yana cikin addinin musulunci amma kuma akwai kishin hauka irin wanda mace za ta je ta hallaka ‘yar’uwarta ko abin da ‘yar’uwarta ta yi sai ta yi. Mutum yana da wahala ya daukowa kansa babban aiki. Idan namiji zai karo aure ya kamata ka bashi goyan baya, ka yi masa fatan alkhairi, haka idan ta shigo ka samu ku zauna lafiya dole akwai abin da zai sa ka yi kishi sai ka yi daidai misali ba wanda ya haura ka’ida ba.

 

Sunana Hassana Yahaya Iyayi, daga Jihar Kano:

Babbar magana ai wadanan dai sun hada kansu da wahala da kuma da-na-sani dan kishi dai babu komai a cikinsa sai wahala. To, shashanci ne da rashin sanin ciwon kai. Kishi dai wani halitta ne wani kuwa dorawa kaine, kishiya babu dadi amma ayi hakuri a kau da kai. Sun yi hakuri su kara hakuri.

 

Sunana Abba Abubakar Yakubu, daga Jos, a Jihar Filato:

Babu shakka kishi na zama guba a wajen easy matan, musamman a lokacin da mazajen su za su kara aure. Wasu kan nemi jefa kansu ga fushin ubangiji ta hanyar kokarin tilastawa mazajen su jingine bukatar su, ta kara aure, amma kuma su kawar da kai daga halayyar sa ta neman mata a waje. Sannan su a karan kansu, idan ma ba su sha guba sun hallaka kansu ba, suna shiga malamai, matsafa, da ‘yan tsibbu, wadanda ke aikata shirka, don neman biyan bukatun su. Akwai wadanda sanadiyyar kishi suke gamuwa da ciwon hawan jini da ciwon zuciya, ko matsalar kwakwalwa.

 

Sunana Princess Fatima Mazadu, Goben Nijeriya:

Kishi kam masifa ce babba, soyayya da kauna ke janyo wa wasu kishi, wasu kuma kwadayin dukiya da kyle-kyelen duniya. Danganta kansu ga mutuwa a kowani lokaci namiji bai zamo lallai ya rigata mutuwa ba, sannan mace ta sani lallai kishi halitta ce, amma bai halarta akan auren wata har ya zamo kin iya kashe kanki ba ko saboda abun duniya. Shawarata a nan su rage mummunan kishi, su nemi na kansu, su zamo masu godiya da kulawa a rayuwa wasu matan ko auren ma babu bare kwadayin dukiya da kishi.

 

Sunana Muktari Sabo Jahun A Jihar Jigawa:

Tabbas ana samun mata masu kishin da ya wuce hankali saboda son zuciya kuma gaskiya makomarsu bata kyau. Kishi dabi’ace da Allah ya halicci mata akai har ma wasu mazan ya kamata su nuna kishinsu ta hanya mafi kyau lokacin da mijinsu zai kara aure kuma su sani da ba a auren da suma ba a aurosu ba. Shawara a nan ita ce kowa ya ji tsoron Allah akan hakan.

 

Sunana Hauwa Abubakar Sarki, daga Suleja Jihar Neja:

Kishiya halitta ce sai dai kowa da yadda yake sarrafa nasa kalar kishin, har kullum muna kira ga matan da suke da tsanani kishi da kar su bari kishi ya rufe masu ido har ya kai ga sun aikata abun da za su zo suna da-na-sani. Biyewa Zuciya, kuma sannan a dabi’ar dan namiji baya son macen da ta cika tsanani kishi. Kishi wata aba ce da ubangiji ke halittar bawa da shi ba tare da ya sani ba. Tsananta addu’a da mika al’amura ga ubangiji a yayin da mijinki ya zo maki da zancen kara aure, dole za ki ji babu dadi a ranki amma in ki ka dage da addu’a sai komai ya zo cikin sauki. Shawara ta kada mu bari zukatanmu ya zamana ita ke sarrafa mu ba mu ke sarrafa ta.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Taskira Illolin Da Ke Tattare Da Mallaka Wa Kananan Yara Wayar Hannu October 4, 2025 Taskira Bukatar Mutane Su Kula Da Warin Jikinsu September 27, 2025 Taskira Amfani Da Rashin Amfanin Auren Jari August 23, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

ECOWAS ta yi Allah wadai da juyin mulki a Guinea Bissau

Kungiyar raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta yi Allah wadai da juyin mulkin da ya faru a ranar Alhamis a kasar Guniea Bissau, kwanaki uku bayan zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu, inda ta kira shi da “barazana kai tsaye ga zaman lafiyar kasar da yankin.”

Wannan “juyin mulkin soja” ya zama “mummunan keta tsarin mulki” kuma “barazana kai tsaye ne ga zaman lafiyar kasar da yankin baki daya,” in ji ECOWAS a cikin wata sanarwa da ta fitar.

Dama kafin hakan Shugabannin tawagar masu sa ido kan zaben na Guinea Bissau na kungiyar Tarayyar Afirka da ECOWAS, sun bayyana ” matukar damuwa game da sanarwar da sojoji suka yi na yin juyin mulki a kasar.”

A wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar, shugabannin sun ce gabanin sanarwar, kasar na cikin shirin sauraron sakamakon zaben da aka yi, wanda suka ce ya gudana lami lafiya.

A halin da ake ciki dai Sojojin da suka kwace mulki a Guinea-Bissau sun rantsar da Horta N’Tam a matsayin sabon shugaban riko na tsawon shekara daya.

Janar N’Tam ya sha rantsuwa ne yau alhamis a hedikwatar sojojin da ke babban birnin kasar Bissau, bayan da suka hambarar da shugaban kasar Umaro Sissoco Embalo a jiya Laraba.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana bin diddigin lamarin da “matukar damuwa,” tana kira da a girmama bin doka.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Faransa, Jamus, Italiya, da Burtaniya sun yi tir da “karuwar rikici” a yammacin kogon jodan November 27, 2025 Rasha A Shirye Take Ta Taimaka Wa Najeriya A Fada Da Ta’addanci November 27, 2025 Palasdinawa Sun Karbi Gawawwakin Shahidai 15 Daga ‘Yan Mamaya November 27, 2025 Makaman Iran Masu Linzami Ne Kandagarkon  Dake Takawa Makiya Birki November 27, 2025 Najeriya: Allah Ya Yi Wa Babban Malamin Addini Shehu Dahiru Bauchi Rasuwa November 27, 2025 An Zabi Iran A Cikin Majalisar Zartarwa Ta Hukumar Yaki Da Makamai Masu Guba Ta Duniya CWC November 27, 2025 HKI Tana Amfani Da Tsagaita Wuta A Gaza Don Sake Shata Kan Iyakokin Yankin November 27, 2025 Yawan Falasdinawa Da Suka Yi Shahada Na Karuwa Saboka Keta Yarjeniyar Tsagaita Wuta November 27, 2025 An Rutsa Da Tsohon shugaban Kasar Najeriya A Guine Bissau Bayan Juyin Mulki November 27, 2025 Iraki: An Dakatar Da Tura Iskar Gas Zuwa Injunan Bada Wutan Lantarki A Yankin Kurdistan November 27, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Wata mata ta kashe ’yar shekara 7 a Ribas
  • ECOWAS ta yi Allah wadai da juyin mulki a Guinea Bissau
  • Makaman Iran Masu Linzami Ne Kandagarkon  Dake Takawa Makiya Birki
  • Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa
  • Ma’aikatar Harkokin Wajen Falasdinu Ta Sanar Cewa Akalla Yan Mata 33000 Ne Isra’ila Ta Kashe A Gaza
  • ’Yan sanda sun kama masu laifi 34 a Kaduna
  • ’Yan sanda sun kama masu laifi da 34 a Kaduna
  • An ceto ’yan mata 24 d aka yi garkuwa da su a makaranta a Kebbi
  • Amarya ta yi wa angonta yankan rago bayan kwana 3 da aurensu a Katsina
  • NAJERIYA A YAU: Irin Radadin Da Masu Cutar Amosanin Jini Ke Fuskanta