Aminiya:
2025-10-13@13:37:50 GMT

Soja ya kashe matarsa, ya hallaka kansa a Jihar Neja

Published: 13th, October 2025 GMT

Wani soja mai muƙamin Las Kofur ya ɗirka wa matarsa harbi har lahira sannan ya kashe kansa a Jihar Neja.

Las Kofur Akenleye Femi da ke aiki a Bataliya ta 221, ya yi wannan aika-aika ne a Barikin Sojoji na Wawa da ke Ƙaramar Hukumar Borgu a Jihar Neja.

Muƙaddashin Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Soja ta 22 da ke Ilorin, Kyaftin Stephen Nwankwo, ne ya tabbatar da lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce abin ya faru ne a ranar 11 ga Oktoba, 2025.

Ya ce mutuwar sojan da matarsa ta haifar da tashin hankali a cikin sansanin soja, inda mazauna wurin suka shiga ɗimuwa da mamaki kan abin da zai iya jawo irin wannan lamari.

Yaƙin Gaza: Hamas da Isra’ila sun fara sakin fursunoni Zaɓen Kamaru: Tchiroma Bakary na da kwarin gwiwa a yayin da ake jiran sakamako

“An gano gawar Last Kofur Femi da matarsa ne a cikin dakinsu da ke Block 15, Room 24 na Corporals and Below Quarters a Wawa Cantonment,” in ji Kyaftin Nwankwo.

Ya ce binciken farko ya nuna cewa sojan yana kan aiki a cikin sansanin kafin ya nemi izinin zuwa gida domin wasu bukatun kansa, sai daga bisani aka gano gawarsu a gida.

Kyaftin Nwankwo ya ce an ajiye gawar mamatan domin ci gaba da bincike, kuma rundunar sojan na aiki tukuru don gano musabbabin lamarin.

Rundunar Soja ta Najeriya ta bayyana matuƙar baƙin cikinta kan wannan abin takaici, tare da miƙa ta’aziyya ga iyalai, abokai da abokan aikin mamatan.

Kwamandan Rundunar, Birgediya Janar Ezra Barkins, ya sha alwashin gudanar da cikakken bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru, tare da ɗaukar matakan da za su hana faruwar irin haka a nan gaba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: harbi

এছাড়াও পড়ুন:

Za A Yi Wa Masu Lalurar Ido Aiki Kyauta A Jihar Jigawa

Wata kungiya mai zaman kanta ta tantance mutane 60 wadanda za’a yiwa aikin ido kyauta a wasu kananan hukumomi 2 dake jihar Jigawa.

Shugaban kungiyar mai zaman kanta, Alhaji Umar Saidu Yelleman Jambola ya bayyana cewar za’a gudanar da aikin ne kyauta ga mutane 60 a kananan hukumomin Malam madori da kaugama.

A cewar sa wadanda za su ci moriyar aikin an zabi su ne daga dukkanin mazabu da ke kananan hukumomin.

Sa’idu Yalleman ya kara da cewa yara da manya ne za su amfana da aikin idon kyauta wanda kungiyar ta dau nauyi.

Da yake jawabi ga manema labarai, Dr Abubakar Adamu yace wadanda aka tantance kuma suke da yanar ido za’a kai su asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano dake birnin Kano don yi masu aikin.

Wakilan shirin na kananan hukumomin Malam Madori and Kaugama,  Malam Bashari Suleiman da Dan-Alhaji sun ce a mako mai zuwa ne za’a gudanar da aikin ga wadanda aka tantance.

Da yake jawabi a madadin wadanda zasu ci moriyar aikin, wakilan mazabun Garun-Gabas da Mairakumi, Mustapha Bala da Suraja Garba sun yabawa kokarin Alhaji Umar Jambola.

A nasu jawaban, Shugabannin kananan hukumomin Kaugama da Malam madori, Alhaji Salisu Sani Garun-Gabas da Alhaji Masaki Usman Dansule sun yaba da hobbasan Umar Jambola na taimakawa masu karamin karfi a kananan hukumominsu.

Usman Mohammed Zaria

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Falasdinawa Sun Gano Gawakin Wadanda HKI Ta Kashe A gaza  Fiye Da 320 Cikin Kwanaki Biyu Kacal
  • Kungiyar ‘Yan Dako Ta Kasa Ta Nada Sabon Sakatare A Jigawa
  • Sojoji Sun Kashe Kwamandan IPOB ‘Alhaji’, Da Wasu 26, Sun Kama 22
  • Za A Yi Wa Masu Lalurar Ido Aiki Kyauta A Jihar Jigawa
  • Wasu Daga Cikin Muhimman Alamomin Ciwon Kansa
  • Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda 5 a Borno
  • Mutane 2 sun rasu a rikicin manoma da makiyaya a Kebbi
  • Guguwar Ritaya Na Barazana Ga Ayyukan Hukumar Kwastam Yayin Da Jami’ai 825 Za Su Yi Ritaya
  • Haramcin Haƙar Ma’adanai: Majalisa Za Ta Kawo Ƙarshen Asarar Dala Biliyan 9 Duk Shekara