ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Ana Gudanar Da Taron Masu Mukamin Magajin Gari Na Kasa Da Kasa A Birnin Dunhuang Na Sin October 13, 2025 Daga Birnin Sin Barazanar Amurka Ta Kara Haraji Game Da Batun Ma’adanan Farin Karfe Ba Hanya Ce Mai Bullewa Ba October 13, 2025 Daga Birnin Sin Hada-Hadar Cinikayyar Waje Ta Sin Ta Karu Da Kaso 4% Cikin Watanni Tara Na Farkon Bana October 13, 2025

.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Jigawa Za Ta Yi Wa Yara Miliyan 1.5 Rigakafin Cutar Shan Inna

Daga Usman Muhammad Zaria

Gwamnatin Jihar Jigawa ta kammala shirye-shiryen yi wa  yara sama da miliyan daya da rabi ‘yan ƙasa da shekaru biyar allurar rigakafin shan inna zuwa karshen watan  Nuwamba a jihar.

Shugaban  Hukumar Kula  Lafiya a Matakin Farko ta Jihar (JSPHCDA), Dakta Shehu Sambo, ya bayyana haka a taron tattaunawa da manema labarai na yini guda da aka shirya,  tare da hadin gwiwar Hukumar Kula da Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, a Dutse, babban birnin jihar.

Dakta Sambo, wanda Mataimakin Mai wayar da kan jama’a na hukumar, Malam Nura Ado ya wakilta, ya ce ana sa ran adadin yara 1,516,244 ne za a yi wa rigakafin a wannan watan.

Ya ƙara da cewa rigakafin watan Nuwamba za a gudanar da shi ne tare da Makon Lafiyar Uwa, Jariri da Yara (MNCH), inda ake ba mata masu juna biyu kulawar lafiya.

Dakta Sambo ya roƙi goyon bayan kafafen yada labarai domin isar da sako da kuma wayar da jama’a.

A nasa jawabin, Shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Mohammed Rahama Farah, ya yaba wa jihar Jigawa bisa rage yawaitar cutar ta shan inna da kashi 58 bisa dari a shekarar 2024.

Sai dai ya yi gargadin ccewahar yanzu cutar na barazana a Najeriya , domin an samu lamura 72 a jihohi 14 a shekarar 2025, don haka akwai buƙatar ƙara faɗaɗa rigakafi.

Rahama Farah ya yi kira shugabannin kananan hukumomi da su sa ido sosai kan yadda ake gudanar da aikin domin tabbatar da nasara, tare da bukar kafofin watsa labarai su ƙara wayar da kai ga iyaye.

Ya kuma yi kira da a ɗauki aikin a matsayin na kowa da kowa domin kawo ƙarshen yaduwar cutar shan inna a Jigawa da sauran jihohin ƙasar nan.

Ita ma da yake jawabi a madadin Hukumar Kula da Lafiyar Farko ta Ƙasa (NPHCDA), Hajiya Firdaus Aminu ta yaba wa jihar bisa kyawawan shirye-shirye game da shirin yaki da cutar.

Za a gudanar da rigakafin shan innan na watan Nuwamba daga 27 ga watan Nuwamba zuwa 3 ga watan Disamba, 2025.

Aikin, tare da makon MNCH, za su gudana ne ta hanyar ƙungiyoyi 2,015 na ma’aikatan wucin-gadi a fadin kananan hukumomi 27 na jihar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Kashe Sama da Naira Miliyan 5 Don Tallafawa Shirin AGILE
  • Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban Amurka
  • Gwamna Radda Ya Sanya Hannu Kan Kasafin 2026 Ya Zama Doka
  • Andrea Thompson ta zama mace mafi ƙarfi a duniya
  • Shugaba Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta-baci Kan Harkar Tsaro Tare da Bada Umurnin Daukar Sabbin Jami’ai
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Yi Wa Yara Miliyan 1.5 Rigakafin Cutar Shan Inna
  • An haramta cin naman Kare da Kyanwa a Indonesia
  • Bincike : Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa Akalla 100,000 a Gaza
  • An Gudanar Da Jana’izar Shahidai 300 A Dai-Dai Ranar Shahadar Zahra (s) A Jiya Litinin
  • Amurka Da HKI Sun Kawo Karshen Hukumar GHF Mai Raba Abinci A Gaza