Aminiya:
2025-10-13@13:33:06 GMT

ASUU za ta fara yajin aikin mako 2 daga ranar Litinin

Published: 12th, October 2025 GMT

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), ta sanar da fara yajin aikin gargaɗi na tsawon mako biyu a dukkanin jami’o’in gwamnati da ke Najeriya.

Shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna ne, ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Jami’ar Abuja.

Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaro

Ya ce yajin aikin zai fara ne da tsakar daren ranar Litinin, 13 ga watan Oktoba, 2025.

ASUU, ta riga ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki 14 wanda ya ƙare a ranar 28 ga watan Satumba, 2025.

A cewar Farfesa Piwuna, babu wani abu da aka yi don dakatar da yajin aikin, don haka dukkanin malamai za su daina aiki a lokacin yajin aiki.

Wannan yajin aikin na zuwa ne duk da cewa har yanzu gwamnati da ASUU na ci gaba da tattaunawa don warware matsalolin da suka daɗe suna fama da su.

Wasu daga cikin matsalolinsu sun shafi batun albashi, kuɗaɗen alawus-alawus, da kuma yarjejeniyar da aka cimma tun shekarar 2009 tsakanin ɓangarorin biyu.

Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, ya bayyana a ranar Laraba cewa gwamnati na matakin ƙarshe na tattaunawa da ASUU da sauran ƙungiyoyi don warware matsalolinsu.

Ya kuma ce gwamnati ta riga ta fitar da Naira biliyan 50 don biyan haƙƙoƙin malaman da suka cancanta, yayin da aka sake sakin wasu Naira biliyan 150 a kasafin kudin 2025 domin biyan buƙatun jami’o’i.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yajin aiki yarjejeniya yajin aikin

এছাড়াও পড়ুন:

Za A Yi Wa Masu Lalurar Ido Aiki Kyauta A Jihar Jigawa

Wata kungiya mai zaman kanta ta tantance mutane 60 wadanda za’a yiwa aikin ido kyauta a wasu kananan hukumomi 2 dake jihar Jigawa.

Shugaban kungiyar mai zaman kanta, Alhaji Umar Saidu Yelleman Jambola ya bayyana cewar za’a gudanar da aikin ne kyauta ga mutane 60 a kananan hukumomin Malam madori da kaugama.

A cewar sa wadanda za su ci moriyar aikin an zabi su ne daga dukkanin mazabu da ke kananan hukumomin.

Sa’idu Yalleman ya kara da cewa yara da manya ne za su amfana da aikin idon kyauta wanda kungiyar ta dau nauyi.

Da yake jawabi ga manema labarai, Dr Abubakar Adamu yace wadanda aka tantance kuma suke da yanar ido za’a kai su asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano dake birnin Kano don yi masu aikin.

Wakilan shirin na kananan hukumomin Malam Madori and Kaugama,  Malam Bashari Suleiman da Dan-Alhaji sun ce a mako mai zuwa ne za’a gudanar da aikin ga wadanda aka tantance.

Da yake jawabi a madadin wadanda zasu ci moriyar aikin, wakilan mazabun Garun-Gabas da Mairakumi, Mustapha Bala da Suraja Garba sun yabawa kokarin Alhaji Umar Jambola.

A nasu jawaban, Shugabannin kananan hukumomin Kaugama da Malam madori, Alhaji Salisu Sani Garun-Gabas da Alhaji Masaki Usman Dansule sun yaba da hobbasan Umar Jambola na taimakawa masu karamin karfi a kananan hukumominsu.

Usman Mohammed Zaria

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ASUU ta tsunduma yajin aikin mako 2
  • Gwamnatin Tarayya Ta Gargaɗi ASUU Kan Yajin Aiki, Ta Ce “Babu Aiki, Babu Albashi”
  • Yajin Aikin ASUU:  Ba za mu biya duk wanda bai yi aiki ba — Gwamnatin Tarayya
  • Trump, da Al’Sisi za su jagoranci taron zaman lafiya kan Gaza a Masar ranar Litinin  
  • Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU ta Shiga Yajin Aiki
  • Yanzu-Yanzu: ASUU Ta Tsunduma Yajin Aiki Na Tsawon Mako Biyu
  • Za A Yi Wa Masu Lalurar Ido Aiki Kyauta A Jihar Jigawa
  • Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Kulawa Ke Sa Malamai Barin Aiki
  • Guguwar Ritaya Na Barazana Ga Ayyukan Hukumar Kwastam Yayin Da Jami’ai 825 Za Su Yi Ritaya