Aminiya:
2025-11-28@13:11:57 GMT

Shugaban Hukumar Zaɓen Yobe Jihar Yobe ya rasu

Published: 14th, October 2025 GMT

Allah Ya yi wa Shugaban hukumar Zavbe ta Jihar Yobe (SIEC) Dakta Mamman Mohammed rasuwa sakamakon gajeriyar jinya.

Marigayi Dokta Mohammed, likita ne kuma ƙwararren ma’aikacin gwamnati. Ya rasu ne a Asibitin Koyarwa na Jihar Yobe da ke Damaturu a ranar Litinin.

Za a yi Sallar Jana’izarsa a yau talata 14 ga Oktoba, 2025, a Fadar Sarkin Fika da ke garin Potiskum.

Dakta Mohammed ya shahara wajen sadaukar da kai da sadaukarwa wajen inganta dimokuradiyya da shugabanci na gari a Jihar Yobe, in ji waɗanda suka san shi.

Za a yi Sallar Jana’izarsa a yau talata 14 ga Oktoba, 2025, a fadar mai martaba sarkin Fika da ke garin Potiskum.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Zaɓe

এছাড়াও পড়ুন:

Zulum ya ba kowanne ɗalibin Borno da ke karatu a Indiya tallafin N500,000

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a ranar Litinin ya ziyarci ɗaliban jihar da ke karatu a ƙasar Indiya, inda ya ba kowannen su tallafin Naira 500,000.

Gwamnan, wanda ke ziyarar aiki a Indiya, ya fara ganawa da waɗanda suka ci gajiyar shirin tallafin karatu na jihar a Jami’ar Sharda da ke Noida.

Ko sisi ba a biya ’yan bindiga ba kafin su saki ɗaliban da suka sace – Gwamnan Kebbi Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Oyo saboda aikata kisan kai

Ya tabbatar musu da jajircewar gwamnatinsa wajen kula da walwalarsu domin samun nasarar karatunsu, sannan ya gargade su da su mai da hankali kan karatun nasu.

Ya ce, “Na zo nan yau saboda dalili ɗaya, don tunatar da ku cewa gwamnatin Jihar Borno na alfahari da ku, wadda kan haka take saka hannun jari a kan makomarku.

“Kuna da muhimmanci ga ci gaba da sake gina jiharmu. Ilimin da ƙwarewar da kuke samu a nan zai amfani, ga jama’arku da kuma kannenku masu zuwa,” in ji Zulum.

Gwamna Zulum ya bayar da tallafin kuɗi na Naira 500,000 ga kowane ɗalibi, abin da ya jawo farin ciki matuƙa ga ɗaliban.

Daga nan, gwamnan ya tafi zuwa yankin Lucknow a ƙasar Indiya, inda ya yi irin wannan taimako ga ɗaliban Jihar Borno a Jami’ar Integral.

Ya kuma ba da umarni a bai wa waɗanda suka ci gajiyar tallafin karatu na Jihar Borno da ke karatu a ƙasar Malesiya irin wannan tallafin kuɗi, yana mai jaddada alkawarin yin adalci ga dukkan ɗaliban da ke amfana da shirin tallafin karatu.

Ɗaliban sun yaba wa gwamnan saboda ziyarar, inda bayyana shi a matsayin shugaba mai tausayi da kulawa.

A cikin tawagar gwamnan akwai Babban Sakataren Fadar Gwamnatin Borno, Barista Mustapha Busuguma da Babban Sakataren Hukumar BOGIS, Injiniya Adam Bukar Bababe.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Kashe Sama da Naira Miliyan 5 Don Tallafawa Shirin AGILE
  • Gwamnan Bauchi ya yi ta’aziyyar rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi
  • An Zabi JMI A Cikin Majalisar Zartarwan Ta Hukumar Yaki Da Makaman Guba Ta Duniya CWC
  • Juyin mulki ya rutsa da Jonathan a Guinea-Bissau
  • Jihar Jigawa Za Ta Rufe Karbar Kudaden Aikin Hajjin 2026 Ranar 24 Ga Watan Disamba
  • Shugaba Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta-baci Kan Harkar Tsaro Tare da Bada Umurnin Daukar Sabbin Jami’ai
  • Tabarbarewar Tsaro na Barazana ga Siyasar Ƙasar Nan Gabanin Zaɓen 2027-Ado Doguwa
  • Jami’an tsaro sun ƙaddamar da shirin murƙushe ’yan bindiga a Kaduna
  • Zulum ya ba kowanne ɗalibin Borno da ke karatu a Indiya tallafin N500,000
  • An buɗe wasu makarantu domin ci gaba da jarawaba a Katsina