2025-07-08@02:23:36 GMT
إجمالي نتائج البحث: 932
«Tafawa Balewa»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Yayin da dokar haramtawa hukumar kula da ‘yan gudun hijirar Palasdinu ta MDD (UNRWA) yin aiki a Isra’ila ke gab da fara aiki, kwamitin sulhu na majalisar ya kira wata budaddiyar muhawara dongane da batun, inda wakilin Sin da wakilan sauran kasashe suka sake bayyana goyon bayansu ga hukumar. Wakilin Sin na dindindin a MDD Fu Cong, ya yi kira ga Isra’ila da ta daina dakatarwa da kai wa hukumar hari, kana ta dakatar da zartar da dokoki masu ruwa da tsaki, yana mai kira ga kasashen duniya su ci gaba da goyon bayan hukumar wajen gudanar da ayyukanta da marawa MDD da kwamitin sulhun baya, wajen daukar matakan gaggawa domin tabbatar da hukumar ta gudanar da ayyukanta. Yankin Gabashin...
Assalamu alaikum masu sauraro, sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da rashin amincewar kasashen masar da Jordan kan maida Falasdnawa cikin kasashensu wanda ni tahir amin zan karanta. A makon da ya gabata ne shugaban kasar Amurka Donal Trump ya fadawa kafafen yada labarai a lokacinda yake cikin jirgin fadar shugaban kasa ko ‘Air Force 1, kan cewa yana duba yiyuwar kwasar Falasnidawa a Gaza zuwa kasar Masar sannan sauran falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan da kuma sauran wurare a kasar Falasdinu da aka mamaye zuwa kasar Jordan. Wannan zancen dai ba sabuwa bace, a rikicin gabas ta tsakiya, shuwagabanin Amurka a baya, sun yi wannan maganar amma bata yuba. A halin yanzun babu wata kasa, ya...
Jaridar “Le Monde” ta kasar Faransa ta dauki labarin da yake cewa iyalai masu yawa sun fice daga HKI baki daya zuwa kasashen Portugal,Cyprus, da kuma Girka. Rahoton ya ci gaba da cewa; Dalilan yin hijirar daga HKI zuwa kasashen waje sun kunshi yaki, rashin tsaro da kuma siyasar gwamnatin Benjemine Netanyahu. Har ila yau, jaridar ta kasar Faransa ta ce, dubban ‘yan share wuri zauna ne suke ficewa daga Falasdinu dake karkashin mamaya a wasu lokutan iyalai ne kaco kau suke ficewa. Kwanaki kadan da su ka gabata wasu iyalai da suke kunshe da mutane 20 da su ka hada iyaye, kakanni da jikoki sun yi hijira zuwa Cyprus domin su rayu a can. A cikin kafafen sadarwa na...
A yau Laraba ne dai sojojin Sudan su ka sanar da shimfida ikonsu a garin ‘Khartum-al-Bahri. Majiyar sojan kasar ta Sudan ta kuma bayyana cewa, a halin yanzu suna aiki tare da bangarorin da suke dace, domin ganin fararen hula mazauna garin sun koma gidajensu a cikin lokaci mafi kusa. A cikin kwanaki kadan da su ka gabata sojojin na kasar Sudan sun sami nasarar kwace yankuna da dama a kewayen Khartum-al-Bahri da su ka hada da gabashin tekun maliya. Wannan cigaban da sojojin na Sudan su ka samu, ya biyo bayan korar dakarun rundunar kai daukin gaggawa ne daga babbar shalkwatar soja dake tsakiyar birnin Khartum, haka nan kuma cibiyar sojan ta sadarwa, da babbar cibiyar leken asiri ta...
Wani jirgin kamfanin Max Air ya tsallake rijiya da baya yayin sauka a filin jirgin Malam Aminu Kano (MAKIA) a ranar Talata da daddare. Jirgin wanda yake ɗauke da fasinjoji 53 da ma’aikata shida yana dawowa daga Jihar Legas ne lokacin da haɗarin ya faru. Me kuka sani game da ficewar Mali, Nijar, da Burkina Faso daga ECOWAS? Mun kama mutum 46 da miyagun ƙwayoyi a Yobe — NDLEA Wani fasinja ya bayyana cewa jirgin ya rasa tayar gabansa yayin sauka a filin jirgin. Fasinjan ya yi karin bayani da cewa cewa tayar jigin ta fashe sannan ta kama da wuta a daidai lokacin da ya sauka cikin filin da misalin karfe 10:19 na dare. “Daidai lokacin da tayar ta...
Babban kwamishinan hukumar kula da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya “UNRWA” ya bayyana wa kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya cewa: Aiwatar da dokokin Isra’ila kan hukumar UNRWA zai zama bala’i Babban Kwamishinan Hukumar Kula da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA), Philippe Lazzarini, ya ce: Aiwatar da cikakken dokar Majalisar Dokokin Haramtacciyar kasar Isra’ila ta Knesset kan hukumar UNRWA zai zama masifa, yana mai gargadin cewa: Rage ayyukan hukumar ta “UNRWA” a wajen tsarin siyasa, kuma a daidai lokacin da kwarin gwiwa daga kasashen duniya ya yi kadan, wanda hakan zai kawo cikas ga yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza. Shafin watsa labaran Falasdinu na “Wafa” ya bayar da rahoton cewa: A jawabin da...
Iran ta mayar da martani game da shirin shugaban kasar Amurka Donald Trump na tilastawa Falasdinawan Gaza komawa kasashen Jordan da kuma Masar. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmaeil Baghaei ya yi watsi da shirin na Trump a wani sako a kan shafinsa na X. Baghaei ya ce, kisan kiyashin da gwamnatin Isra’ila ta kwashe watanni 15 tana yi, ya kasa kawar da Falasdinawa daga tushensu, don haka ba wani abunda zai iya tilasta musu ficewa daga yankinsu. “Wannan ita ce kasarsu ta asali kuma sun sadaukar da komi don su ci gaba da zama a can kuma su ci gaba da gwagwarmayar neman yancin kai,” a cewar kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran. Wannan kiran na...
Da yake jawabi a taron manema labarai ranar Talata a Yola a madadin Masarautar Fufore, Alkasum Abba, ya ce kafa sabbin Masarautu abu ne wanda sam bai da ce ba kuma an aiwatar da tsarin ba bisa ka’ida ba. Ya yi ikirarin cewa, sun yi iyakacin kokarinsu na neman tattaunawa da sulhu a kan lamarin da gwamnan jihar amma abin ya ci tura.
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka CAF, ta fitar da jadawalin ƙasashen da za su fafata a Gasar Kofin Nahiyyar Afirka AFCON wadda Morocco za ta karɓi baƙunci a watan Disamba na bana. An gudanar da bikin fitar da jadawalin ranar Litinin a Cibiyar Taro ta Ƙasa ta Mohammed V National da ke birnin Rabat a Morocco. A soma duba watan Sha’aban ranar Laraba — Sarkin Musulmi Nijeriya na da arzikin da za ta riƙa ɗaukar nauyin tafiye-tafiyen Tinubu — Minista Tawagogi biyu mafi ƙwazo a kowanne rukuni ne za su tsallaka kai tsaye zuwa mataki na gaba, sai kuma tawagogi huɗu mafi ƙwazo da suka zo a mataki na uku a duk cikin rukunan. Morocco wadda wannan shi ne karo...

Dan Majalisar Dattijan Amurka Ya Mayar Da Martani Kan Kalaman Trump Na Tilastawa Falasdinawa Gudun Hijira
Dan Majalisar Dattawan Amurka ya bayyana kiran da shugaban Amurka ya yi tilastawa Falasdinawa gudun hijira Falasdinawa da cewa kokari ne na shafe wata al’umma daga kan doron kasa Dan Majalisar Dattawan kasar Amurka Sanata Bernie Sanders a jiya Litinin ya fara mayar da martani ga shugaban Amurka Donald Trump inda ya bayyana kiran da Trump ya yi na korar Falasdinawa daga Zirin Gaza zuwa kasashen da ke makwabtaka da su a matsayin kokarin “Shafe wata al’umma ce daga kan doron kasa kuma laifin yaki ne” inda ya bukaci dukkan Amurkawa da su yi Allah wadai da wannan furuci. A ranar Asabar da ta gabata ce shugaban Amurka Donald Trump ya ba da shawarar mayar da Falasdinawa daga zirin Gaza...
Kalaman shugaban Amurka na cewa zai tsarkake Zirin Gaza na Falasdinu ta ruda kawayen kasarsa na Larabawa tare da hargitsa su Wani mai sharhi na jaridar Washington Post David Ignatius ya ce kalaman shugaban Amurka Donald Trump na tsarkake Gaza da mika Falasdinawa zuwa Masar da Jordan ya sanya kasashen Larabawa da suke kawancen da Amurka cikin halin fargaba da dardar. Shafin watsa labaran Al-Quds Al-Arabi, ta yi nuni da cewa Trump ya gabatar da tunaninsa domin hanyar gabatar da shawarwari da tunani tana da dama tare da sabani da siyasa a aikace. Ta ce Trump na fuskantar daukan matakin yin kasadar da zai lalata kyawawan ra’ayinsa da bayyana munanan tunaninsa. Jaridar ta kara da cewa: shugaban na Amurka zai...
Dan Majalisar Dattawan Amurka ya bayyana kiran da shugaban Amurka ya yi tilastawa Falasdinawa gudun hijira Falasdinawa da cewa kokari ne na shafe wata al’umma daga kan doron kasa Dan Majalisar Dattawan kasar Amurka Sanata Bernie Sanders a jiya Litinin ya fara mayar da martani ga shugaban Amurka Donald Trump inda ya bayyana kiran da Trump ya yi na korar Falasdinawa daga Zirin Gaza zuwa kasashen da ke makwabtaka da su a matsayin kokarin “Shafe wata al’umma ce daga kan doron kasa kuma laifin yaki ne” inda ya bukaci dukkan Amurkawa da su yi Allah wadai da wannan furuci. A ranar Asabar da ta gabata ce shugaban Amurka Donald Trump ya ba da shawarar mayar da Falasdinawa daga zirin Gaza...
Runduna daya ta sojojin Najeriya ta gudanar da bikin jana’izar marigayi Mascot, Sajan Dalet Danfari Akawala, a shalkwatar rundunar dake jihar Kaduna. Wanda dokin sojojin ne. A wata sanarwa da mukaddashin Daraktan hulda da jama’a na rundunar soji ta daya, Laftanar Kanar Musa Yahaya ya fitar, ya ce Kanar Akabike ne ya jagoranci jana’izar, wanda ya wakilci babban hafsan rundunar, Manjo Janar Mayirenso Lander David Saraso. A cewar sa, Marigayi Sajan Dalet Danfari Akawala ya yi hidimar sashen sadaukarwa da aminci, tare da nuna jajircewa da juriya a gidan Soja. “Bikin shi ne hanyar mu na girmamawa ta ƙarshe ga wani wanda ya kawo sauyi da farin ciki da aiki tukuru da kuma daukaka sashen da yayi...
A cim ma burin Gwamna Umar Namadi na ci gaban bil’adama a cikin ajandar mai dauke da abubuwa 12, majalisar zartaswar jihar Jigawa ta kafa wani kwamiti mai mambobi 10 domin samar da hanyoyin da za a bi wajen nemo masu hazaka domin karfafa kirkire-kirkire a tsakanin matasa masu tasowa a jihar. Kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da al’adu na jiha Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bayyana haka bayan taron majalisar da aka gudanar a Dutse. Ya ce, kwamitin ya kunshi kwamishinonin lafiya, muhalli, kananan hukumomi yayin da kwamishinan ilimi mai zurfi zai zama shugaba. Sauran mambobin sun hada da masu ba da shawara kan fasaha, ICT da tattalin arziki na dijital, ilimi mai zurfi, aikin gona,...
Hamas ta bayyana komawar Falasɗinawa a matsayin nasara, tana mai cewa hakan ya karya yunƙurin da aka yi na tilasta wa mutanen barin gidajensu.
Ofishin yada labarai na gwamnati a zirin Gaza ya sanar da cewa Falasdinawa kusan 300,000 da suka rasa matsugunansu ne suka koma gida a gabar tekun a ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma da kungiyar Hamas. “Wannan ya zo ne bayan kwanaki 470 na kisan kiyashi da sojojin mamaya na Isra’ila suka yi,” in ji sanarwar, wanda ya yi sanadin shahadar Falasdinawa akalla 47,000 tare da lalata wargaza yankin Falasdinawan. An bayyana cewa sama da kashi 90%, yankin ya lalace sakamakon hare haren Isra’ila. An ruguza duk wasu wurare da cibiyoyi masu matukar mahimmanci kama daga asibitoci, makarantu, gidajen jama’a wuraren samar da ruwan sha da wutar lantarki. A yanzu Falasdinawan dake komawa wannan yankin...
Kwamitin zaman lafiya da tsaro na Tarayyar Afirka ya sanar da cewa zai gudanar da zaman gaggawa yau Talata kan halin da ake ciki a gabashin Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango (DRC). Kwamitin na (PSC) zai gudanar da wani zaman gaggawa a yau Talata kan halin da ake ciki a yankin, wanda ke fama da yakin da ake yi tsakanin dakarun Kongo da mayakan M23″ in ji Paschal Chem-Langhee, mai magana da yawun kwamitin, yayin da al’amura ke kazanta a Goma, babban birnin gabashin DRC. Kafin nan daruruwan ma’aikatan MDD da fararen hula a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kongo sun tsere zuwa makociyar kasar, Rwanda, yayin da gomman sojojin Kongo din suka “mika wuya” ga jami’an tsaron Rwanda a ranar Litinin, bayan ‘yan...

An Kammala Gwaje-Gwajen Wasan Kwaikwayo Na Shirye-Shiryen Bikin Sabuwar Shekarar Sinawa Na CMG Na 2025
An gudanar da gwajin wasan kwaikwayo karo na biyar na shirye-shiryen bikin sabuwar shekarar Sinawa na CMG na 2025 jiya Lahadi. Ya zuwa yanzu, an kammala dukkanin ayyukan share fagen shirye-shiryen bikin sabuwar shekarar Sinawa na CMG na 2025. (Safiyah Ma)
A yau Litinin ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da katin murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, a matsayin martani ga abokai a jihar Iowa ta kasar Amurka, inda ya ce, Sin da Amurka na da manyan muradun bai daya, da damar yin hadin gwiwa, kuma suna iya zama abokan hulda da aminai. Ya yi fatan jama’ar kasashen biyu za su kara cudanya da juna, da kara yin mu’amala da juna, da yin aiki tare wajen rubuta labarin abokantaka a tsakanin jama’ar kasashen biyu, da ba da sabbin gudummawa ga ci gaban dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka. (Mohammed Yahaya)
A Yau Litinin ne dai da safe dubban Falasdinawa su ka fara komawa Arewacin Lebanon bayan gushewar watanni 15 na yaki. Dubban Falasdinawan ne dai suke tafiya a kafa, yayin da wasu suke tafiya a cikin manyan motoci suna bi ta titin Salahuddin. Tun da fari tashar talabijin din 12: ta HKI, ta watsa labarin cewa; sojoji sun janye daga mashigar Natsarim, da su ka kafa domin yin bincike tun ranar 27 ga watan Oktoba 2023. Da dama daga cikin Falasdinawan sun kwana a wannan mashigar bayan da sojojin HKI su ka hana su wucewa a jiya Lahadi. Barin Falasdinawan su koma arewacin Gaza, yana a karkashin yarjejeniyar da aka cimmawa a tsakaninsu da Hamas,dangane da fursunonin yaki. A jiya...
Dubban daruruwan Falasdinawa da suka rasa matsugunansu sun fara komawa yankin arewacin zirin Gaza da yaki ya daidaita bayan da aka cimma matsaya tsakanin Hamas da Isra’ila. Tuni kungiyar Hamas ta yaba da komawar Falasdinawan zuwa arewacin Gaza wanda ta danganta a abun tarihi. An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas bayan shafe watanni 15 ana gwabza kazamin yaki a Gaza. An fara aiwatar da kashin farko na yarjejeniyar a ranar 19 ga watan Janairu, kuma ana sa ran za’a saki Falasdinawa sama da 1,890 da ‘yan Isra’ila 33, wadanda ke cikin 240 da kungiyoyin Hamas ta yi garkuwa dasu a harin ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023. Tun lokacin yakin ya lakume rayukan Falasdinawa akalla 47,306,...
An tsawaita yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Isra’ila da Lebanon na tsawon kimanin makonni uku bayan da gwamnatin kasar ta ki janye dakarunta kamar yadda aka kulla da farko. An bayyana cewa yarjejeniyar tsakanin kasashen biyu za ta ci gaba da aiki har zuwa ranar 18 ga Fabrairu, 2025. Shi ma firaministan kasar Labanon Najib Mikati ya tabbatar da tsawaita wa’adin, yana mai kara da cewa Lebanon za ta mutunta hakan. Bisa yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka sanar tsakanin Isra’ila da Hizbullah a watan Nuwamba, a jiya ne ya kamata sojojin Isra’ila su fice daga kudancin Lebanon. “Gwamnatin Lebanon ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta har zuwa ranar 18 ga Fabrairu, 2025,”...
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, ya yaba da irin gudunmawar da darikar Tijjaniyya ke bayarwa wajen samar da hadin kai a tsakanin al’ummar musulmin kasar nan. Mataimakin shugaban kasar ya yi wannan yabon ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron Mauludin bana 2025 na marigayi Sheikh Ibrahim Nyass, jagoran darikar Tijjaniyya a filin wasa na Sani Abacha dake Kano. Mataimakin wanda ya samu wakilcin Alhaji Babagana Fannami, Ya yabawa kungiyar musulmi bisa tsayin daka a tsawon karnukan da suka gabata akan koyarwar addinin musulunci na gaskiya. Shettima wanda shi ne babban bako na musamman a wajen taron, ya yaba da tsarin jagoranci na darikar ‘Sufi’ ga bil’adama. Babban bako na musamman ya jaddada...
Bikin Bazara Na Kasar Sin Na Samun Karbuwa Daga Masu Yawon Shakatawa Na Duniya
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi rangadi a rundunar arewaci ta rundunar sojin ’yantar da al’ummar Sinawa wato PLA, gabanin Bikin Bazara. Xi Jinping wanda shi ne sakatare janar na kwamitin kolin JKS kuma shugaban hukumar koli mai kula da ayyukan soji (CMC), a madadin kwamitin kolin da hukumar CMC, ya mika gaisuwar sabuwar shekara ga dukkan jami’an rundunar soji ta PLA, da sojoji ’yan sanda, da fararen hula dake aiki a rundunar soja, da mambobin kungiyoyin sa kai da ma jam’an tsaro da aka kebe domin bukatar gaggawa. A bana, Bikin Bazara na sabuwar shekarar al’ummar Sinawa ya fado ne a ranar 29 ga watan nan na Janairu. (Fa’iza Mustapha)
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bukaci masu tsara manufofi a fannin ilimi a Najeriya da su dauki kwararan matakai don magance gibin da ke tattare da zamantakewa da al’adu da ababen more rayuwa da manufofin da ke haifar da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a kasar. Shugabar ofishin UNICEF na Kano, Rahama Rihood Farah, ne ya yi wannan kiran a wani taron manema labarai na bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025. Ya yi nuni da cewa, Jihohin Kano, da Jigawa da Katsina suna da adadin yara miliyandaya da dubu dari takwas da sittin da uku, da dari biyu da bakwai (1,863,207) da ba sa zuwa makaranta a matakin firamare, da...
Daga cikin yara ‘yan makaranta miliyan 242 da matsanancin yanayi ya raba da muhallansu a kasashe 85 a shekarar 2024, dalibai miliyan 2 da dubu 200 ne a Najeriya suka rabu da muhallansu, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin ilimi a shekarar. Rahoton wanda Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fitar a daidai lokacin da duniya ke bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025, ya nuna cewa a Najeriya baki daya dalibai miliyan 2,200,200 ne suka daina makaranta sakamakon ambaliyar ruwa. Da take gabatar da jawabi kan tasirin da sauyin yanayi ke da shi ga ilimin yara, shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah ya bayyana cewa, ambaliyar ruwa da ta...
Kungiyar kwamishinonin kudi ta kasa ta jinjinawa kokarin gwamnatin jihar Jigawa na bunkasa Ilmin ya’ya mata. Shugaban kungiyar kuma kwamishinan kudi na jihar Ekiti, Mr Akim Oyebode ya bayyana hakan a lokacin da suka ziyarci Gwamna Umar Namadi a gidan gwamnati dake Dutse. Mr Akim Oyebode ya ce kungiyar tana alfahari da ayyukan raya kasa da Gwamna Umar Namadi ya aiwatar tun hawansa karagar mulki, a sassan jihar ta Jigawan. Yana mai cewar sun ziyarci jihar Jigawa ne domin yi wa Gwamnan ta’aziyyar rashin da aka masa. A nasa jawabin, Gwamna Umar Namadi ya yaba musu bisa wannan ziyara tare da fatan za su koma jihohinsu lafiya. Usman Mohammed Zaria
Gwamnatin Jihar Jigawa ta yaba da kokarin ‘yan Nigeria mazauna kasar Saudiyya bisa gudunmawar da suke bayarwa ga harkokin kiwon lafiyar al’ummar jihar. Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan a lokacin rangadin duba aikin idanu da ‘yan Nigeria mazauna kasar Saudiyya da hadin gwiwar gwamnatin jihar ke gudanarwa a babban asibitin Dutse. Gwamnan wanda ya zagaya wuraren da aka kwantar da wadanda aka yi wa aikin idanun, ya nuna jin dadinsa da gamsuwa da yawan mutanen da aka yi wa aikin. Daga cikin wadanda suka amfana da aikin sun hada da masu matsalar ido su 500 da aka yi wa tiyata, sai kuma mutane 300 da aka baiwa gilashi. Kazalika, mutane 400 kuma suka...
Majalisar dokokin jihar Jigawa ta jaddada aniyar ta na hada kai da ofishin kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF domin samun nasarar aiwatar da tsare-tsare da za su inganta rayuwar yara da marasa galihu a jihar. Mataimakin kakakin majalisar, Alhaji Sani Isyaku Abubakar, ya bada wannan tabbacin lokacin da ya karbi bakuncin tawagar ofishin UNICEF na Kano karkashin jagorancin Hajiya Fatima Adamu. Ya lura cewa irin wannan haɗin gwiwa tsakanin majalisa, Action Against Hunger da Save the Children International sun haifar da sakamako mai kyau ta hanyar tallafawa matakan majalisa ta hanyar fasaha da ba da shawara don tsara manufofin da sauran tsare-tsaren a Jigawa. Alhaji Sani Isyaku Abubakar ya bada tabbacin ci gaba...

Falasdinawa Sun Gudanar Da Bukukuwan Tarbar Fursunonin Falasdinawa 114 Da Aka Sako Daga Gidan Yarin Isra’ila
Falasdinawa sun gudanar da wata gagarumar liyafar tarbar fursunonin Falasdinawa 114 a Ramallah da aka sako daga gidan yarin ‘Yan sahayoniyya Daruruwan jama’a a birnin Ramallah da ke gabar yammacin kogin Jordan sun gudanar bikin tarbar fursunoni 114 da aka sako daga gidan yarin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a wani bangare na biyu na yarjejeniyar musayar fursunoni tsakanin ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa da gwamnatin yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya, yayin da wasu fursunoni 16 daga cikinsu suka isa birnin Zirin Gaza. Jama’ar garin Ramallah sun dauki fursunonin da aka sako a kafadarsu a matsayin alamar nasara. Fursunonin sun bayyana godiyarsu ga ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa kan jajurcewar da suka yi a Gaza, kuma har ta kai ga kulla yarjejeniyar musayar. A yayin bikin,...
Shugaban Amurka Donald Trump ya zayyana wani ra’ayi mai manufar tsarkake zirin Gaza. Trump na mai cewa yana son aikewa da Falasdinawa daga yankin zuwa kasashen Masar da Jordan “na dan lokaci” ko kuma “a cikin dogon lokaci”. don samun zaman lafiya. Ana dai ganin tamakar Trump na kwatanta yankin Falasdinu da “wurin rushewa nan gaba” bayan watanni 15 na yakin da Isra’ila ta kadamar kan Gaza.