Tinubu ya tafi Rome don halartar taro kan sha’anin tsaro
Published: 12th, October 2025 GMT
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya tafi birnin Rome na Ƙasar Italiya, domin halartar taron shugabannin ƙasashe kan sha’anin tsaro.
Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin labarai, Bayo Onanuga, ya ce za a fara taron ne a ranar 14 ga watan Oktoba, kuma zai mayar da hankali kan matsalar tsaro da ke addabar yankin Yammacin Afirka.
Taron na ‘Aqaba Process’ an kafa shi ne a shekarar 2015 ta hannun Sarki Abdullah II na Ƙasar Jordan, kuma ana gudanar da shi tare da haɗin gwiwar Jordan da ƙasar Italiya.
Taron na nufin tattauna hanyoyin yaƙi da ta’addanci da kuma magance matsalolin tsaro da ke adabbar ƙasashe daban-daban, musamman a yankin Yammacin Afirka.
Taron zai haɗa shugabannin ƙasashe na Afirka, jami’an leƙen asiri da na tsaro, da wakilan ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da na ƙungiyoyin fararen hula, domin tattauna yadda za a magance matsalolin tsaro da ke addabar yankin.
Za a tattauna kan yadda ƙungiyoyin ta’addanci ke yaɗuwa a Yammacin Afirka, alaƙa tsakanin masu laifi da ’yan ta’adda, da kuma alaƙar da ke tsakanin ta’addanci a yankin Sahel.
Hakazalika, za a tattauna yadda za a daƙile yaɗuwar aƙidar ta’addanci a Intanet da kuma lalata hanyoyin sadarwar da ’yan ta’adda ke amfani da su wajen yaɗa ra’ayoyinsu da ɗaukar sababbin mabiya.
Shugaba Tinubu zai kuma tattauna da wasu shugabannin ƙasashe don neman hanyoyin daƙile matsalar tsaro da ke addabar yankin.
Tinubu ya samu rakiyar Ministan Harkokin Waje, Ambasada Bianca Odumegwu–Ojukwu; Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar.
Sauran sun haɗa daMai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu; Darakta-Janar na Hukumar Leƙen Asiri ta Ƙasa (NIA), Ambasada Mohammed Mohammed; da wasu manyan jami’an gwamnati.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Afrika Ta Yamma matsalar tsaro taro tsaro da ke
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan tsaro
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro da ta addabi dukkan sassa a Nijeriya.
Cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin wannan Larabar mai ɗauke da sa hannunsa, Tinubu ya bayyana cewa dole ne a ɗauki matakan gaggawa da suka dace domin fuskantar barazanar tsaro da ke ƙaruwa ƙasar nan.
Shugaban ya bayar da umarnin ɗaukar ƙarin jami’an tsaro da suka haɗa da jami’an ’yan sanda 20,000, lamarin da zai ƙara adadin jami’an zuwa 50,000.
Haka kuma, Tinubu ya bai wa rundunar sojin ƙasa da sauran hukumomin tsaro umarnin ɗaukar ƙarin jami’ai.
Sanarwar ta ce za a yi amfani da sansanonin masu yi wa ƙasa hidima NYSC a matsayin wuraren horas da sabbin ’yan sandan.
Ƙarin bayani na tafe…