Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wasu ma’aurata da wasu mutane biyar bisa zarginsu da gudanar da ɗaurin aure ba tare da izinin iyayensu ba ko kuma bin tsarin addinin Musulunci a unguwar Nasarawa da ke cikin birnin Kano. Wadanda ake zargin sun hada da ango mai suna Aminu mai shekaru 23 da amaryarsa Sadiya mai shekaru 22.

Sauran wadanda aka kama su ne Umar mai shekaru 24 wanda ya kasance wakilin ango; Abubakar, mai shekaru 23, wanda ya kasance waliyyin amarya; Usaina, mai shekaru 21; da kuma wasu ‘yan mata guda biyu wadanda suka kasance shaidu a yayin ɗaurin auren. Ahmed Musa Ya Nemi Afuwar Ƙungiyar 3SC Akan Abinda Ya Faru Da ‘Yan Wasansu A Kano Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 236 A Jihohi 27 Da Birnin Tarayya Rahotanni sun bayyana cewa, an ɗaura auren ne akan sadaki Naira 10,000, ba tare da amincewar iyayen ma’auratan ba. Da yake tabbatar da faruwar lamarin, mataimakin babban kwamandan hukumar ta Hisbah, Dr. Mujaheeddeen Aminuddeen, ya ce an kama wadanda ake zargin ne biyo bayan korafe-korafen da ‘yan unguwar suka kai wa hukumar. Ya bayyana cewa, matakin da wadanda ake zargin suka ɗauka ya saɓawa koyarwar addinin Musulunci da kuma dokokin aure na jihar, yana mai jaddada cewa, hukumar ta Hisbah ba za ta amince da duk wani abu da ya saɓawa tsarin addini da na shari’a a jihar Kano ba. Dr. Aminudeen ya kara da cewa, a halin yanzu wadanda aka kama suna hannun Hisbah domin ci gaba da bincike. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Ra'ayi Riga Labarin Xinjiang A Zane: Aikin Yawon Shakatawa Na Kara Samar Da Arziki Ga Al’ummar Xinjiang October 13, 2025 Labarai Ba Gudu Ba Ja-da-baya Kan Ci Gaba Da Kwaskwarima Ga Tsarin Haƙar Ma’adanai – Minista October 13, 2025 Manyan Labarai Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 236 A Jihohi 27 Da Birnin Tarayya October 13, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: mai shekaru

এছাড়াও পড়ুন:

Shugaba Tinubu Ya Yi Wa Maryam Sanda Afuwa Bayan Shafe Shekaru 6 A Gidan Yari

Baya ga Maryam Sanda, Shugaba Tinubu ya kuma yafe wa wasu mutane da dama, ciki har da Janar Mamman Vatsa, Herbert Macaulay, da Faruku Lawan, wanda tsohon ɗan majalisar tarayya ne daga Jihar Kano.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sanatan Bauchi Ta Arewa Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP October 11, 2025 Manyan Labarai Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano October 10, 2025 Manyan Labarai Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Karyata Batun Yi Wa Kiristoci Kisan Ƙare Dangi October 10, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Rundunar Ƴansanda Ta Kama Gaggan Ƴan Fashi 9 A Kano
  • Rikicin kabilanci: Mutane 2 sun mutu, wasu 7 sun jikkata a Jigawa
  • Ahmed Musa Ya Nemi Afuwar Ƙungiyar 3SC Akan Abinda Ya Faru Da ‘Yan Wasansu A Kano
  • Sojoji Sun Kashe Kwamandan IPOB ‘Alhaji’, Da Wasu 26, Sun Kama 22
  • Shugaba Tinubu Ya Yi Wa Maryam Sanda Afuwa Bayan Shafe Shekaru 6 A Gidan Yari
  • ’Yan ta’adda sun kashe sojoji 4 a wani sabon hari a Borno
  • Matasa 2 Sun Mutu Bayan Nutsewa A Rafi A Kano
  • Yadda Haɗa Jinsin Shanu A Zamance Zai Ƙara Samar Da Madara
  • Sibil Difens ta cafke mutum 3 kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi a Kano