2025-08-16@00:27:48 GMT
إجمالي نتائج البحث: 120

«rijistar masu kaɗa»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Samar da dabino zai samu sauyi mai mahimmanci a Jihar Jigawa bayan da wani kamfani daga kasar Saudiyya mai samar da dabino da gwamnatin jihar suka ƙulla yarjejeniya domin ƙara yawan amfanin gona. Ta wannan haɗin gwiwa za a kawo sababbin fasahohin zamani da irin dabino masu yawa don shigar da su cikin tsarin noma. Sanata Natasha na neman diyyar N100bn wurin Akpabio Ƙungiya ta rage farashin kayan marmari saboda Azumin Ramadan A cewar bayanai daga Hukumar Abinci da Aikin Noma ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO), Saudiyya ita ce ƙasa ta biyu mafi girma wajen samar da dabino na duniya, inda take samar da tan miliyan 1.61 na dabino. Masar ita ce ƙasa mafi girma wajen samar da dabino, inda...
    Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya buƙaci manyan ‘yan siyasa daga yankin Arewa da Kudu Maso Kudu su haɗa kai gabanin zaɓen 2027. El-Rufai, ya yi wannan kira ne yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi dattijo kuma jagoran yankin Neja Delta, Edwin Clark. Babu ɗan Arewa mai hankali da zai yi tallan APC a 2027 – Jigo a PDP Fasinjoji 4 sun rasu yayin da bas ta kama da wuta a Jigawa A cewarsa, Najeriya tana cikin matsala mai tsanani kuma tana buƙatar ɗauki cikin gaggawa. “A shekarun baya, Arewa da Kudu Maso Kudu sun kasance abokan siyasa,” in ji El-Rufai. “Kada mu manta da hakan. Mu koma kam wannan haɗin kai. Mu ceci wannan ƙasa...
    Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya buƙaci manyan ‘yan siyasa daga yankin Arewa da Kudu Maso Kudu su haɗa kai gabanin zaɓen 2027. El-Rufai, ya yi wannan kira ne yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi dattijo kuma jagoran yankin Neja Delta, Edwin Clark. Babu ɗan Arewa mai hankali da zai yi tallan APC a 2027 – Jigo a PDP Fasinjoji 4 sun rasu yayin da bas ta kama da wuta a Jigawa A cewarsa, Najeriya tana cikin matsala mai tsanani kuma tana buƙatar ɗauki cikin gaggawa. “A shekarun baya, Arewa da Kudu Maso Kudu sun kasance abokan siyasa,” in ji El-Rufai. “Kada mu manta da hakan. Mu koma kam wannan haɗin kai. Mu ceci wannan ƙasa...
    Mutane huɗu sun rasa rayukansu, wasu 10 kuma sun samu raunuka bayan wata motar bas ƙirar Hummer ta kama da wuta a garin Gwaram da ke Jihar Jigawa. Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 4 na yammacin ranar Asabar, a kusa da makarantar sakandaren gwamnati ta Government Girls Unity Secondary School da ke Gwaram. Gobara ta ƙone gidaje, amfanin gona da dabbobi a Borno  Za a kafa ƙarin makarantu a Zariya — Abbas Tajudeen Kakakin ’yan sandan Jihar Jigawa, SP Lawan Adam, ya tabbatar da faruwar hatsarin cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi. Ya ce motar ta taso daga Ƙaramar Hukumar Zaki daga Jihar Bauchi zuwa ƙauyen Ribadi da ke Ƙaramar Hukumar Gwaram. Sanarwar ta bayyana cewa...
    Gwamnan Jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke, ya kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a faɗin jihar a ranar Asabar. Gwamnan ya isa rumfar zaɓensa da ke Sagba/Abogunde, Ƙaramar Hukumar Ede, inda aka tantance shi kafin ya kaɗa kuri’arsa. Zaɓen, wanda ake gudanarwa don zaɓen sabbin shugabanni a ƙananan hukumomi 30 na jihar, ya samu fitowar masu zaɓe sosai tare da ingantaccen tsaro. Gwamna Adeleke ya yaba da yadda zaɓen ke tafiya cikin lumana, inda ya buƙaci al’umma su ci gaba da kaɗa ƙuri’a ba tare da tsoro ko matsin lamba ba. Gwamnan Shekarar 2024: Sanata Ademola Jackson Nurudeen Adeleke An Yanke Wa Mutane 5 Hukuncin Kisa Bayan Sun Kashe Wani Bafullatani A Jihar Osun Da yake jawabi...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yanayin tattalin arziki da ma wasu dalilai kan tilasta wa mutane da dama, ciki har da masu karɓar albashi a karshen wata, neman wata hanya ta daban dake kawo Karin kudade. Shin mene ne yake kawo hakan, kuma mene ne tasirinsa a kan rayuwar masu buga-bugar da ma al’umma? NAJERIYA A YAU: Ci-gaban Da Hukumomin Raya Shiyyoyi Za Su Samar DAGA LARABA: Dalilan Da Al’adar Zanen Fuska Ke Neman Gushewa A Kasar Hausa Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne a kan irin buga-bugar da ’yan Najeriya suke yi don sama wa kansu mafita. Domin sauke shirin, latsa nan
    Shirin Trump Na Gaza Rubio ya bayyana cewa shirin Trump shi ne kaɗai mafita a yanzu, duk da cewa ƙasashen Larabawa da na duniya suna goyon bayan kafa ƙasar Falasdinu tare da Isra’ila. A nasa bangaren, Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi ya ce kafa ƙasar Falasdinu ce kaɗai hanya ta samar da zaman lafiya a yankin.
    “A binciken da ake yi, an gano dukkan kayayyakin da aka sace bayan an sayar da su kan kudi naira 80,000, kuma wadanda ake zargin sun amsa laifin aikata laifin.” PPRO ya kara da cewa, ‘yansanda na ci gaba da neman mutum na uku da ake zargi mai suna Ibrahim Danmariya, wanda ake kyautata zaton shi ne mai karbar kayan da aka sace. Abdullahi ya bukaci mazauna yankin da su lura kuma su kai rahoto ga ofishin ‘yansanda mafi kusa. “Muna kira ga jama’a da su bayar da bayanai masu amfani da za su kai ga kama wanda ake zargi da gudu. “Muna tabbatar wa jama’a cewa za a yi amfani da duk bayanan cikin sirri,” in ji Abdullahi.
    Hukumar Zaɓe Mai ta Ƙasa (INEC) ta ce ofishinta na Ƙaramar hukumar Gwadabawa da ke Jihar Sakkwato ya ƙone ƙurmus, inda  gobarar ta lalata akwatunan zaɓe da sauran kayayyaki. Mista Sam Olumekun, kwamishinan Hukumar INEC kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a wata sanarwa. Mutum 23 sun mutu da raunata wasu a haɗarin mota a gadar Kano Tinubu ya isa Ethiopia domin halartar taron AU A cewarsa, a taron Hukumar INEC na mako-mako da aka saba gudanarwa a ranar Alhamis, hukumar ta lura da wani mummunan lamari na tashin gobara a ofishin ƙaramar hukumar Gwadabawa da ke Jihar Sakkwato, kamar yadda sakatariyar gudanarwa mai kula da ofishin...
    Ana ci gaba da gudanar da zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi a Jihar Katsina, inda ake fuskantar ƙarancin masu kaɗa ƙuri’a, da kuma zargin sayen ƙuri’u a wasu rumfunan zabe. Jami’an tsaro, ciki har da ‘yansanda da NSCDC, sun sanya dokar taƙaita zirga-zirga tare da tura jami’ai wurare masu muhimmanci domin tabbatar da tsaro. A garin Tsani, rahotanni sun nuna cewa mutum biyu kacal aka gani a rumfar zabe, yayin da aka hango motar sintiri da APC na jami’an tsaro. Annobar Cutar Murar Tsuntsaye Ta Yadu A Jihohin Filato Da Katsina Ƴan Bindiga Sun Kai Hari A Katsina, Sun Sace Tsohon Daraktan NYSC, Janar Tsiga A rumfar Birchi ta Kudu, inda aka yi rajistar masu zabe 808, kaɗan daga cikinsu ne...
    Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce ofishinta na Ƙaramar hukumar Gwadabawa da ke Jihar Sakkwato ya ƙone ƙurmus, inda  gobarar ta lalata akwatunan zaɓe da sauran kayayyaki. Mista Sam Olumekun, kwamishinan Hukumar INEC kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a wata sanarwa. Mutum 23 sun mutu da raunata wasu a haɗarin mota a gadar Kano Tinubu ya isa Ethiopia domin halartar taron AU A cewarsa, a taron Hukumar INEC na mako-mako da aka saba gudanarwa a ranar Alhamis, hukumar ta lura da wani mummunan lamari na tashin gobara a ofishin ƙaramar hukumar Gwadabawa da ke Jihar Sakkwato, kamar yadda sakatariyar gudanarwa mai kula...
    A takardar, wadda mai ba shi shawara kan yaɗa labarai, Rabi’u Ibrahim, ya sa wa hannu, Idris ya ce: “Rediyo ko yaushe hanya ce ta samun ingantaccen bayani kuma abin dogaro ne ga al’umma, musamman a lokutan da ake fuskantar matsaloli.   “A ‘yan shekarun nan, rediyo ya taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan jama’a kan sauyin yanayi da tasirin sa ga duniyar mu. Tare da faɗin isar sa da sauƙin samun sa, rediyo yana da ikon ilimantarwa da ƙarfafa mutane su ɗauki matakan da suka dace don yaƙi da sauyin yanayi.”   Idris ya ambato jawabin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a taron COP29 na Majalisar Ɗinkin Duniya kan Sauyin Yanayi wanda aka gudanar a birnin Baku na...
    Gwamnatin Kano ta bayyana aniyarta na kafa Hukumar Kula da Masu Buƙata ta Musamman a wani mataki na tabbatar da adalci a tsakanin al’ummar jihar. Kwamishiniyar Mata da Yara masu bukata ta musamman, wacce Daraktar Jin Daɗi ta ma’aikatar, Binta Muhammad Yakasai, ta wakilta, ta bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa na yini guda da masu ruwa da tsaki kan kafa Hukumar Kula da Mutanen da ke da Bukatu na Musamman (PWDs) a Jihar Kano. Tana jaddada aniyar gwamnati na ƙarfafa PWDs, Yakasai ta ce, “Wannan taro ba kawai haɗuwar ra’ayoyi ba ne, amma wani mataki ne na tabbatar da adalci, haɗawa da ƙarfafa wani muhimmin ɓangare na al’ummarmu.” Ta bayyana manyan dalilai guda biyar da ke nuna bukatar kafa...
    Kamfanin Dangote na Peugeot Automobiles Nigeria Limited (DPAN), wanda ke kera wa da tallata motocin Peugeot a Nijeriya, ya fara tarawa da haɗa sabuwar Peugeot 3008 GT a masana’antarsa da ke Kaduna. Peugeot 3008 GT, mai injin 1.6-lita turbo mai ƙarfi, ya ƙara yawan jerin motocin da ake haɗawa a masana’antar DPAN, wanda ya ya ke samar da 301 sedan da Peugeot 5008 mai kujeru bakwai. Wannan sabon samfurin yana da Faisal kamar fitilun, da hasken rana mai iya buɗewa, da tayoyin 17-inch alloy. Matatar Dangote Ta Bai Wa Ɗalibai 473 Tallafin Karatu Zanga-zanga: Ku Kawo Ƙarshen Rashin Wutar Lantarki Da Ta Addabi Jihohi- Gwamnatin Kaduna  Hakanan, an samar da fasahar ABS don hana birki shanye wa, ESP don hana...
    Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya miƙa wa Majalisar Dokokin jihar sunayen zaɓaɓɓun kwamishinoni 16 domin tabbatarwa. Shugaban Majalisar, Danladi Jatau ne ya bayyana hakan yayin zaman majalisar da ya gudana ranar Litinin a birnin Lafiya. Atiku da Obasanjo suna ganawar sirri Ɗalibi ya kashe abokin karatunsu da gatari a Nasarawa Aminiya ta ruwaito cewa, daga cikin sabbin kwamishinonin da gwamnan ya zaɓa har da tsohon Shugaban Masu Rinjayen a majalisar dokokin jihar, Umar Tanko-Tunga da wani tsohon mamba a majalisar, Mohammed Agah-Muluku. Kakakin Majalisar ya buƙaci kowane ɗaya daga cikin zaɓaɓɓun kwamishinonin da su gabatar da kwafi 30 na duk bayanansu daga yanzu zuwa ranar Alhamis tare neman su hallara a gaban majalsiar a ranar Litinin ta makon...
    Gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa Umar Farouk Ibrahim a matsayin sabon Sakataren Gwamnatin Kano. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwar da Kakakin Gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a yammacin ranar Asabar. Shigo da hatsi daga ƙetare ya karya farashinsa a Neja Ya yi wa kansa keji don daina shan sigari Sanarwar ta ce naɗin sabon Sakataren Gwamnatin zai fara aiki ne a hukumance daga ranar Litinin mai zuwa 10, ga Fabarairun 2025. Sanarwar ta ce an naɗa sabon Sakataren Gwamnatin wanda ya shafe sama da shekaru talatin yana aikin gwamnati la’akari da ƙwarewar aiki da yake da ita a hukumomi da ma’aikatu daban-daban na wajen ganin an cimma muradin gwamnati mai ci na ciyar da Jihar...
    Majalisar wakilai ta umarci kwamitocin sadarwa da harkokin cikin gida da su binciki haɗa lambar shaidar zama ɗan ƙasa (NIN) da layukan waya ba tare da izini ba da kamfanonin sadarwa ke yi. Wannan mataki ya biyo bayan ƙudirin da ‘yan majalisa Patrick Umoh da Julius Ihonvbere suka gabatar, inda aka buƙaci hukumar NCC ta ɗauki mataki kan duk wani kamfanin sadarwa da aka samu da laifi, tare da NIMC ta tabbatar da sahihancin haɗa bayanan NIN. Ana Shirin Kiranye Ga Ɗan Majalisar Da Ya Bar Kwankwasiyya Trump Ya Hana Maza Masu Sauyin Jinsi Shiga Wasannin Mata Umoh ya ce wannan mataki na iya haifar da damuwa ga ‘yan ƙasa, tare da jefa su cikin hatsarin satar bayanai, da damfara,...
    Masarautar Fika da ke Jihar Yobe ta buɗe gasar ƙwallon ƙafa karo na uku a filin wasa na Dabo Aliyu da ke garin Potiskum. An buɗe gasar ƙarƙashin jagorancin mai Martaba Sarkin Fika, Alhaji Dr. Muhammad Ibn Abali Muhammad Idris wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Yobe. Ya je Maiduguri daga Legas a kan keke Rikicin rusau ya yi ajalin mutum 4 a Kano Gasar wacce aka fara a shekarar 2011 ta bunƙasa zuwa wani gagarumin taron wasanni a yankin, wadda ke haɗa ƙungiyoyi daga ƙananan hukumomi huɗu na yankin da suka haɗa da Fune, Potiskum, Fika, da Nangere. A shekarar 2017 aka gudanar da gasar karo  na biyu, lamarin da ya ƙara tabbatar da gasar a matsayin...
    Sanarwar ta kuma bayyana cewa, jami’an hukumar tsaron farin kaya daga jamhuriyar Nijar ne suka biyo wanda ake zargin ɗan bindigar ne a kan babbar hanyar Zurmi/Kauran Namoda a jihar Zamfara.   Da yake duba makaman da aka kama, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana kyakkyawar haɗin gwiwa tsakanin sojojin da gwamnatin jihar Zamfara wajen yaƙi da ‘yan bindiga.   “Dole ne in yaba wa sojoji, DSS, da ‘yan sanda, musamman ma Hukumar Tsaro Ta Farin Kaya, bisa nasarar aiwatar da wannan gagarumin kame.   “Ina so in jaddada cewa waɗannan nasarori da aka samu tare da wasu na daƙile ‘yan bindiga a jihar, sun samo asali ne daga haɗin kai da goyon bayan da gwamnatin jihar Zamfara ke baiwa ɗaukacin...
    Haka kuma, an naɗa Muhammad Yahaya Liman a matsayin sabon Daraktan Akanta. Ya samu ƙwarewa a fannonin rahoton kuɗi da sarrafa kuɗi, ana sa ran zai taimaka wajen ƙara ƙarfin tsarin kuɗi na jihar. An kuma naɗa Akibu Isa Murtala, wanda a baya ya kasance Mataimaki na Musamman a Ofishin Shugaban Ma’aikata, a matsayin Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Gudanarwa. Aikin sa shi ne kula da gudanar da ayyukan ma’aikatu. Injiniya Abubakar Sadiq kuma an naɗa a matsayin Mataimakin Manajan Darakta na Hukumar Samar da Ruwa da Tsabtace Muhalli a Ƙauyuka (RUWASA). An ɗora masa alhakin inganta samar da ruwa da tsabtace muhalli a yankunan karkara. Haka kuma, an kafa kwamiti na musamman domin farfaɗo da Hukumar Sufuri...