2025-11-18@17:10:47 GMT
إجمالي نتائج البحث: 496

«alawus alawus»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Gwamnatin Tarayya wajabta wa ɗaliban da suka kammala karatu mika kundin bincikensu na ƙarshe a matsayin sharaɗi kafin a tura su aikin yi wa kasa hidima (NYSC). Dokar za ta fara aiki ne daga ranar 6 ga Oktoba, 2025, kamar yadda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume ya sanar. Ya bayyana cewa dokar ta shafi duk ɗaliban ajin ƙarshe da suka cancanci zuwa NYSC ko da kuwa a ƙasashen waje suka kammala karatu. Wannan yana daga cikin sauye-sauyen da Gwamnatin Tarayya ta yi wanda ya alaƙanta aikin Yi wa Ƙasa Hidima (NYSC) da Tsarin Tattara Bayan Ilimi ma Kasa (NERD). Ranar Laraba jirgin ƙasan Abuja-Kaduna zai dawo aiki  Shekara 1 bayan rushewa, har yanzu ba gyara titin Kano–Maiduguri ba Bisa...
    Hukumar lura da jiragen ƙasa ta Nijeriya (NRC) ta tabbatar da cewa daga ranar Laraba, 1 ga Oktoba, 2025, za a dawo da zirga-zirgar jirgin ƙasa na fasinjoji a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna. Wannan na zuwa ne bayan dakatar da tafiye-tafiye a watan Agusta sakamakon hatsarin da ya rutsa da ɗaya daga cikin jiragen. A cikin sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Callistus Unyimadu, ya fitar, NRC ta ce matakin ya nuna jajircewarta wajen tabbatar da tsaro da kuma inganycin sufuri ga ’yan ƙasa. Hukumar ta bayyana cewa ranar Laraba za ta kasance rana ta Musamman domin yin gyara a kan layin jirgin don gujewa matsaloli a nan gaba. NRC Ta Dakatar Da Sufurin Jirgin Ƙasan Abuja-Kaduna...
    Gwamnatin Tarayya ta tabbatar wa da ƴan Nijeriya cewa za a ci gaba da samun isasshen man fetur duk da barazanar shiga yajin aiki da ƙungiyar PENGASSAN ta yi kan taƙaddama da matatar man Dangote. Wannan na zuwa ne bayan raɗe-raɗin cewa matatar ta dakatar da tsarin siyar da ɗanyen mai da ake biya sa da Naira. A wata sanarwa daga ma’aikatar kuɗi ta tarayya, daraktan hulɗa da jama’a Mohammed Manga ya bayyana cewa an gudanar da taron kwamitin kula da tsarin “buyqn Naira-don sayen ɗanyen mai” ƙarƙashin jagorancin Ministan Kuɗi, Wale Edun. Taron ya samu halartar Ministan tsare-tsare, da shugaban FIRS, da wakilai daga NNPC, CBN, NMDPRA da Afreximbank. Matatar Dangote Ta Dawo Sayar Da Man Fetur A Kuɗin...
    A ranar Laraba, 1 ga watan Oktoba, 2025, jirgin ƙasan da ke jigilar fasinja tsakanin Abuja zuwa Kaduna zai dawo aiki. Hukumar Sufurin Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC) ta ce jirgin farko a ranar zai baro tashar Idu da ke Abuja da ƙarfe 8.45 na safe, ya iso Kubwa 9.05 sannan ya sauka a tashar Rigasa da ke Kaduna da misalin 12.42 na rana. Daga Kaduna kuma jirgi zai baro Rigasa da misalin ƙarfe 2.30 na rana ya isa Kubwa da ƙarfe 8.40 na yamma. Sanarwar ta ƙara da cewa daga bisani za a ware kowace ranar Laraba domin aikin kula da lafiyar jiragen da ke aiki a layin na Abuja zuwa Kaduna. Shekara 1 bayan rushewa, har yanzu ba...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce kasarsa za ta gwammace ta fuskanci mayar da takunkumin da aka kakaba mata, maimakon ta mutunta bukatar Amurka da ke neman Iran din ta mika dukkanin tataccen Uranium da take da shi. Da yake zantawa da manema labarai kafin ya bar birnin New York zuwa birnin Tehran, Pezeshkian ya yi karin bayani kan kokarin diflomasiyya a lokacin babban taron Majalisar Dinkin Duniya, wanda ya hada da ganawa da shugabannin kasashen Faransa, da Finland, da Switzerland, da Norway, da Iraki, da Bolivia, da kuma majalisar kungiyar Tarayyar Turai. Yayin da yake nuni da cewa an cimma yarjejeniya da bangarorin Turai, ya nuna rashin jituwar da cewa duka daga bangaren  Amurka ne. “Mun cimma yarjejeniya...
    Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC) ta bayyana cewa jiragenta da ke jigilar fasinjoji daga Abuja zuwa Kaduna, za su koma aiki a mako mai zuwa. Mai magana da yawun NRC, Callistus Unyimadu, ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da hukumar ta fitar a jiya Asabar, duk da yake bai sanar da haƙiƙanin ranar da za a koma aikin ba. Tun daga shekarar 1899 Faransa take haddasa mana rikici — Nijar Ɗalibi ya kashe malaminsa har lahira a Kuros Riba Callistus, ya ƙara da cewa matakin ya biyo bayan nasarar kammala gyare-gyare da bincike a ɓangaren da aka samu matsala a baya-bayan nan. A cewarsa, hukumar na yin aiki ba tare da gajiyawa ba don...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Yawan ribar da manyan kamfanoni na kasar Sin suke samu ta karu da kashi 0.9 cikin 100 a mizanin shekara-shekara a cikin watanni takwas na farkon shekarar 2025, lamarin da ya farfado da raguwar da aka samu da kashi 1.7 cikin 100 a tsakanin watannin Janairu zuwa Yuli, kamar yadda alkaluman hukuma suka nuna a yau Asabar. Jimillar ribar da kamfanonin da ke samun makudan kudin shiga na kasuwanci a shekara na akalla yuan miliyan 20 (kimanin dalar Amurka miliyan 2.81) ta kai kusan yuan tiriliyan 4.7 a cikin watannin takwas, a cewar hukumar kididdiga ta kasar Sin. A cikin watan Agusta, ribar da manyan kamfanonin suka samu ta farfado sosai, inda ta karu da kashi 20.4 cikin 100 a...
    Yunkurin kasashen rasha da china na jirkinta dawowa da iran takunkumi har na tsawon wata 6 bai yi nasara ba a kwamitin tsaro na MDD saboda kasashe 4 ne suka nuna goyon bayansu da suka hada da kasashen China Rasha Pakistan da kuma Aljeriya, yayin da kasashe 9 kuma suka nuna rashin amincewa da shirin ciki harda mambobin kwamitin tsaro na mdd wato kasashen Birtaniya, Faransa da kuma Amurka. Kasar Rasha taki amincewa da wannan lamarin na dawo da takunkumin madd kan kasar iran , kamar yadda ita ma kasar china ta nuna rashin amincewarta afili da wannan mataki. Ana sa bangaren shugaban kasar iran Masud pezeshkiyaan ya bayyana cewa da sannuu Tehran za ta yi galaba akan wannan batun...
    Yayin da aka ce jam’iyyun siyasa a jamhuriya ta farko, sun fi karkata kan yanki, an yi yunkurin kafa jam’iyyun kasa a jamhuriya ta biyu da gangan. A wancan jamhuriyar (1979–1983), manyan jam’iyyun siyasar Nijeriya su ne GNPP, NPN, NAP,NPP, PRP, da kuma UPN. Duk da cewa, jam’iyyun sun banbanta a akida; amma ana ganin jam’iyyun UPN da PRP, a matsayin na masu fafutuka da kuma jajircewa, domin kuwa jam’iyyar UPN ta tsaya tsayin-daka wajen aiwatar da manufofinta. An gina tsarin jam’iyyar bisa manyan manufofi hudu kamar haka: ilimi kyauta tun daga makarantar reno har zuwa manyan makarantu, harkar kiwon lafiya kyauta, hadin gwiwar karkara da ci gabanta da kuma samar da cikakkun ayyukan yi masu dorewa. Wadannan alkawura, an...
    Sakataren Majalisar Koli ta Tsaron kasar Iran ya bayyana cewa, Tehran za ta katse yarjejeniyarta da take yi da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, tare da daina bada hadin kai ga binciken makamai na kasa da kasa, idan har aka aiwatar da tsarin “sake dawo mata da  takunkuman Majalisar Dinkin Duniya. Sakataren Majalisar ta Iran Ali Larijani ya sake nanata kudurin Iran na cewa ba da ta niyyar yin amfani da makamin nukiliya – ko dai a yanzu ko a nan gaba. Ya kuma ce ayyukan wuce gona da iri da Amurka da Isra’ila suka yi kan cibiyoyin nukiliyar Iran guda uku a watan Yuni ya sanya tattaunawar ta zama “bazara”. Yau Juma’a ne kwamitin sulhu na...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya yi kakkausar suka ga kasashen Turai uku da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar nukiliyar ta shekarar 2015, inda ya zarge su da yin “ba bisa ka’ida ba da kuma rashin da’a” ta hanyar neman mayar da takunkumin da kwamitin sulhu na MDD ya kakabawa Iran ta hanyar da ta dace. A wata tattaunawa da ta yi da sakatariyar harkokin wajen Birtaniya Yvette Cooper a ranar Alhamis, Araghchi ya bayyana cewa, kasashen Turai ba su da hujja kan kokarin da suke yi na maido da kudurorin da aka soke a baya. Araghchi “ya yi kakkausar suka kan matsayin kasashen Turai uku da cewa bai dace ba, ba bisa ka’ida ba kuma maras nauyi,” in...
    Kwararan bayanai na nuni da cewa tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya fara tattaunawa da Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, kan shirin komawa jam’iyyar. Majiyoyi daga cikin APC a Kano sun bayyana cewa Kwankwaso ya rubuta wasiƙa zuwa sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa a Abuja, yana sanar da aniyarsa ta komawa jam’iyyar. An rufe wurin haƙar zinare a Kebbi Sauya Sheƙa: Kwankwaso ya gindaya sharuɗa kafin sake komawa APC Sai dai Aminiya ba ta iya tabbatar da hakan ba ya zuwa lokacin hada wannan rahoton. Wata majiya daga sakatariyar APC ta ƙasa kuma ta tabbatar da cewa ana ci gaba da tattaunawa tsakanin Kwankwaso da Farfesa Nentawe kan sauya shekar, kuma maganar ta yi nisa...
    Har kullum Sin tana nacewa shawarwari, da tuntubar juna a matsayin muhimman matakan kyautata hadin gwiwa dake share fagen inganta cudanya. Tare da hakan, Sin na fatan Amurka za ta kaucewa kokarin dakile ci gabanta. Kuma duk wasu matakai na matsin lamba daga bangare guda kan kasar Sin, ba za su taba yin nasara ba, kamar dai yadda muka gani a baya. Don haka, a wannan gaba da ake ta samun karin sakamakon kyautata muamala da gudanar da shawarwari, kamata ya yi bangaren Amurka ya kauracewa kakaba shingen cinikayya, wanda ka iya gurgunta nasarorin da aka riga aka cimma. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na...
    Sabon kwantiragin ya nuna Arsenal na son kare shi daga ƙungiyoyi manya na ƙasashen Turai irin su Real Madrid da Manchester United. Arteta na fatan hakan zai taimaka wajen cika burinsa na lashe gasar Firimiya. Haka kuma, abokin Saliba a tsaron baya, Gabriel Magalhães, ya tsawaita kwantiraginsa har zuwa shekarar 2029. Arsenal za ta kara da Newcastle a filin St James’ Park a ranar Lahadi, inda ake sa ran haɗin Saliba da Gabriel zai ƙara ƙarfafa bayan ƙungiyar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban gwamnatin riƙon ƙwaryar Syria Ahmed al-Sharaa ya shaida wa babban taron Majalisar Dinkin Duniya cewa ƙasarsa ta sake ƙwato matsayinta a idon duniya. Wannan ne karon farko cikin kusan shekaru 60 da wani shugaban Syria ya yi jawabi a taron MDD. Siyasa ba ta yiwuwa da rowa — Gwamna Buni Za a gudanar da taron kiwon lafiya na farko a Gombe Al-Sharaa ya zama shugaban Siriya na farko da ya yi jawabi a Majalisar Dinkin Duniya tun bayan da Noureddine Attasi ya yi jawabi a shekara ta 1967, jim kaɗan bayan yaƙin Larabawa da Isra’ila, a lokacin da Damashka ta rasa iko da tuddan Golan wanda Isra’ila ta ƙwace a shekarar 1981. Al Sharaa ya ce yaƙin basasa ya...
    Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sake fitar da Naira biliyan 5 domin biyan bashin ’yan fansho da haƙƙoƙin ma’aikatan da suka yi ritaya, lamarin da ya kawo adadin kuɗaɗen da gwamnatinsa ta biya zuwa yanzu ya kai Naira biliyan 27 tun bayan hawansa mulki. A wannan karon, kimanin tsofaffin ma’aikata 1,026 ne suka samu haƙƙoƙinsu waɗanda aka tsayar da biya tun a shekarar 2017. Komawar Natasha majalisa ya nuna haɗin kai zai iya yaƙar rashin adalci — Atiku Darajar Naira ta ƙaru bayan CBN ya rage kuɗin ruwa Aminiya ta ruwaito cewa, wannan wani yunƙuri na gwamnatin domin rage bashin Naira biliyan 48 na tsofaffin ma’aikata a matsayin haƙƙoƙin fansho da giratuti. Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da...
    Majalisar Dokoki ta Kasa ta ɗage ranar dawowarta daga hutu zuwa 7 ga watan Oktoba, 2025. Karin bayani na tafe..
    Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya ayyana gobe Talata, a matsayin ranar ɗaya ga watan Rabi’ul Thani, 1447 bayan hijira, wanda ya kawo ƙarshen watan Rabi’ul Awwal, 1447, daidai da ranar 23 ga Satumba, 2025. Sanarwar ta fito ne a wata takarda da Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaid, wanda shi ne shugaban kwamitin da ke bai wa Majalisar Sarkin Musulmi shawara kan al’amuran addini, ya sanya wa hannu ya kuma raba wa manema labarai. A sanarwar, Sarkin Musulmi bai fayyace wuraren da aka ga sabon watan ba, sai dai ya bayyana cewa ya gamsu da sahihan rahotannin da aka gabatar, lamarin da ya sa ya ayyana ganin watan a hukumance. Ya yi addu’ar Allah Ya kawo zaman lafiya da...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Kasashen da ba su cika alkawuran da suka dauka ba suke zargin Iran da rashin mutunta yarjejeniyar makamashin nukiliya Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Kasashen da ba su cika alkawuran da suka dauka ba, a yanzu suke zargin Iran da kin mutunta yarjejeniyar makamashin nukiliyar. A cikin wata hira da gidan talabijin na CCTV na kasar China, Pezeshkian ya ce, “Suna sa ran za a aiwatar da yarjejeniyar manyan tsare-tsare na shekaru 25 da aka tsara a baya tsakanin Iran da China.” Pezeshkian ya yi ishara da gazawar Amurka da kasashen Turai wajen cika alkawuran da suka dauka karkashin yarjejeniyar makamashin nukiliya, yana mai cewa, a yau kasashen da ba su...
    Ya gargadi cewa, tarihi ba zai gafarta wa shugabannin Arewa ba idan suka kasa daukar matakin gaggawa wajen dakile kashe-kashe, garkuwa da mutane da rikice-rikicen da ke addabar yankin. Ya ce shiru da fifita wasu akan wasu daga cikin shugabanni suna kara ta’azzara matsalar tsaro a jihohin Zamfara, Kaduna, Katsina, Filato da Benuwe.   Ya bayyana cewa akwai damuwa matuka yayin da ‘yan bindiga ke ci gaba da addabar al’umma, wasu daga cikin manyan mutane na fifita shirya shagulgula masu tsada maimakon kiraye-kirayen tarurrukan neman mafita na gaske don kawo karshen wannan rikici.   “Lokacin yin shiru ya wuce, yanzu ne lokacin daukar mataki. Tarihi ba zai gafarta wa halin ko-in-kula ba a lokacin da ake bukatar mataki fiye da...
    Wanda zan iya tunawa za su kai goma haka. Ko akwai wani fim wanda bayan fitar sa ka samu ƙalubale daga dangi ko wajen masu kallo? Gaskiya a fim dai har yanzu ban samu wani ƙalubale ba, saboda duk abin da nake fitowa a rol na malunta ne. Kawai dai akwai wata waƙa da na yi bidiyonta a kanta ne gaskiya na fuskanci ƙalubale sosai, dan akwai wanda ya taɓa kira na yana hawaye ya ce min me ya ja min wannan harka haka har na fito ina rawa da jaruma?. To, sai na ji ban ji daɗi ba a lokacin, dan akwai gidajen TƁ da suka karɓa suke haskawa, nayi sauri na hana a haska ɗin. Sai kuma wani...
    Shugaban kasar Iran Masud pezishkiyan ya bayyana cewa Iran ba za ta mika wuya ga bukatun da suka wuce kima ba, kuma za ta iya shawo kan duk wani takunkumi da aka kakaba mata, Shugaban ya fadi haka ne a wajen bukin karrama yan kasar da suka samu lambobin yabo a gasar Olympic ta kimiyya ta duniya , bayan da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya kada kuriar amincewa da kudurin dawo da takunkumi dake da alaka da shirinta na nukiliya. Haka zalika shugaban kasar yace makiya suna iya kai hari kan sakamakon binciken fasaha da aka yi, amma kwararru da masana ilimin kimiya wadanda suka samar da wadannan naurorin su ne hakikanin gaskiyar dukiya ga kasarmu, don haka...
    Shugaba kuma Babban Jami’in Gudanarwa na Matatar Man Fetur na Kamfanin Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana cewa tun bayan fara samar da man fetur a shekara guda da ta gabata, matsalar dogon layin man fetur da ta shafe shekara 50 ana fama da ita ta zama tarihi. A lokacin wani taron bita da aka gudanar don murnar cika shekara ɗaya tun bayan ƙaddamar da samar da man fetur daga masana’antar dake samar da ganga 650,000 a kowace rana, Dangote ya jaddada cewa Ƴan Nijeriya sun sha fama da dogon layin mai tun daga 1975, amma wannan matsala ta fara zuwa karshe tun lokacin da masana’antar ta fara aiki a ranar 3 ga Satumba, 2024. Dangote ya yi nuni da kalubale...
    A baya, ƙasashe biyu kawai na Afirka ba sa shigo da man fetur, amma abin takaici, yanzu sun koma shigo da kaya. Wannan yana da illa ga Afirka,” in ji shi. Dangote ya bayyana cewa aikin masana’antar ya kasance mai haɗari sosai. Ya ce ya samu gargaɗi sau da dama daga masana harkokin mai, masu zuba jari, da jami’an gwamnati na cikin gida da waje, waɗanda suka yi jayayya cewa irin wannan aikin masana’antar mai girma manyan ƙasashe ne kaɗai ke iya yi, ya amince cewa da aikin ya gaza, zai rasa dukiyoyinsa ga masu ba da rance. “Yanke shawarar gina masana’antar ba abu ne mai sauƙi ba. Idan ya gaza, masu ba da rance za su daka wawa a...
    Kimiyyar sadarwa ta kawo sauƙin rayuwa a harkokin kasuwanci da mu’amalar kuɗi ta banki. Yawaitar amfani da wayar hannu wajen yin hada-hadar banki a Nijeriya ya sa mutane da dama ke tura kuɗi cikin sauƙi. A shekarar 2024 kaɗai, rahoton Hukumar Biyan Hada-hadar Banki ta Ƙasa (NIBSS) ya nuna cewa darajar kudin da aka tura ta hanyar waya ta kai Naira tiriliyan 41.5, lamarin da ya nuna ƙaruwar kaso 74 cikin 100 daga shekarar da ta gabata. Sai dai kuma hakan na iya kawo matsala, musamman idan aka yi kuskure aika kuɗi zuwa wani asusu daban. Wannan na faruwa sosai, musamman idan aka rubuta lambar asusu ko sunan mai asusu ba daidai ba. Shin me ya kamata mutum ya fara...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Zamanin kebe kai ya ƙare, Haɗin gwiwar Iran da Rasha ya cimma abin koyi mai nasara A yayin ganawarsa da ministan makamashin kasar Rasha Sergei Tyswell da tawagarsa, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Nasarar da aka samu na hadin gwiwa tsakanin kasashe masu cin gashin kai kamar Iran da Rasha, ya tabbatar da cewa zamanin kebe kai a duniya ya kare. Ya kuma jaddada cewa, wadannan kasashe suna iya samun ci gaba da bunkasa ba tare da bukatar ko dogaro da karfi mai amfani da bangare guda. Shugaban na Iran ya bayyana jin dadinsa da ci gaban hadin gwiwar kasashen biyu, musamman a fannin sufuri, makamashi, da ayyukan samar da wutar...
    Kafofin yada labaran Isra’ila sun rawaito cewa, an gudanar da wani dogon zaman tattaunawa a birnin London a yammacin jiya tsakanin ministan harkokin wajen Syria Asaad al-Sheibani da ministan kula da tsare-tsare na Isra’ila Ron Dermer, tare da halartar jakadan Amurka na musamman Tom Barak. Kafofin yada labaran Isra’ila sun bayyana cewa ganawar ta dauki tsawon sa’o’i biyar, inda bangaren Syria ya gabatar da martaninsa kan shawarar da Isra’ila ta gabatar na cimma yarjejeniyar tsaro, inda ta ce an samu ci gaba a tattaunawar. A baya dai bangarorin biyu sun gana a zagaye na biyu da aka sanar, ban da kuma tarukan sirri da suka gudanar a lokuta daban-daban wand aba a sanar ba, da nufin kulla alaka ta siyasa...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A yau ne Gwamna Siminalaye Fubara ke dawowa kujerarsa a matsayin gwamnan Jihar Ribas bayan dakatarwa da ayyana dokar ta baci na watanni shidda da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi a jihar.   Manazarta dai na hasashen wannan dawowar zata bude wani sabon babi a siyasar jihar Ribas. NAJERIYA A YAU: Matsayin Doka Kan Hawa Mumbari Ba Tare Da Izinin Gwamnati Ba DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya Yayin da wasu ke ganin gwamna Fubara zai koma bakin aiki ne ya cigaba da gudanar da mulkin jihar kamar yadda ya barta, wasu kuwa gani sukeyi akwai babban kalubale dake gaban gwamnan. Domin sauke shirin, latsa nan
      Wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Folasade Boriowo, ya fitar, ta ce a karon farko cikin shekaru da dama, daliban Nijeriya za su ci gaba da karatun tarihin Nijeriya tun daga Firamare 1 zuwa karamar Sakandare 3 yayin da daliban SSS 1 – 3 za su koyi sabon darasin da aka samar na ‘Civic and Heritage Studies’, wanda ya hada tarihin Nijeriya da Ilimin zamantakewar Jama’a. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce alkaluman baya bayan nan da aka fitar cikin Mujallar Economist, sun shaida yadda hada-hadar cinikayyar fitar da hajoji ta kasar Sin ke kara bunkasa cikin sauri a shekarar nan ta bana, inda fannin ke samun karuwar abokan hulda, da daidaiton matsayi cikin tsarin samar da hajojin masana’antu na kasa da kasa. Kakakin ya kara da cewa, kasashen duniya suna maraba da hajojin kasar Sin, kuma yakin ciniki da haraji ba su yi wani babban tasiri kan kasar Sin ba. A fannin hada-hadar cinikayya, sanya shinge ba alama ce ta karfin gwiwa ba, kuma katangar da Amurka ke ginawa kanta, daga karshe za ta illata karfinta ne. Lin Jian, wanda ya...
    Ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomin Jihar Yobe (ALGON) ta karrama Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, da lambar yabo ta karramawa bisa himmar ayyukan raya ƙasa da gwamnatinsa ke gudanarwa a faɗin jihar. Karramawar, wacce aka bayyana a matsayin irinta ta farko a tarihin Jihar Yobe, shugabannin ƙananan hukumomi 17 na jihar suka ba da ita ga gwamna. Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabala Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno Da yake jawabi, shugaban ƙungiyar ALGON a Jihar Yobe, kuma shugaban ƙaramar hukumar Damaturu, Alhaji Bukar Adamu, ya yaba da yadda Gwamna Buni yake gudanar da harkokin mulki na bai ɗaya. Ya ce nasarorin da aka samu sun haɗa da fannoni na...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rikicin kwamitin gudanarwa da malaman Kwalejin Fasaha ta Tarayya da ke Bida (Bida Poly), ya ƙara ƙamari bayan da makarantar ta dakatar da ayyukan Kungiyar Malamai (ASUP) sannan ta kawo sojoji domin kula da jarrabawa da dalibai ke gudanarwa. Ƙungiyar ASUP reshen kwalejin ta shiga yajin aiki mara wa’adi, domin neman a biya su alawus ɗin ƙarin aiki na watanni 18 da suka wuce. Ƙungiyar ta umarci mambobinsu da kada su gudanar da jarrabawar zangon da ta fara ranar Litinin, 15 ga Satumba, 2025. Wani ma’aikacin makarantar ya shaida wa wakilinmu cewa sojojin an gayyace su ne domin kare ɗalibai da wasu malamai daga shirin da ASUP ke yi na hana gudanar da jarrabawa. ’Yan bindiga sun kai wa sojoji...
      Shugabannin biyu sun yi nazari kan muhimman fannonin hadin gwiwa tsakanin Nijeriya da Faransa, inda suka amince da zurfafa hadin gwiwa don samun ci gaban juna da kwanciyar hankali a duniya.   LEADERSHIP ta ruwaito cewa ba a bayar da wani dalili na sauya wannan hutun ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Majalisar dattawa ta dakatar da Sanata Akpoti-Uduaghan a ranar 6 ga Maris, 2025, na tsawon watanni shida. Duk da cewa an kalubalanci lamarin a kotu, amma babbar kotun tarayya ba ta bayar da wani umarni na soke dakatarwar ba ko kuma tilasta sake dawo da ita bakin aiki.   A ranar 4 ga Satumba, 2025, Sanatar ta sanar da ofishin magatakarda akan aniyar ta na ci gaba da ayyukan majalisa, nan take, ofishin ya mika wasikar ga shugabannin majalisar dattawan. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
    Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) ya roƙi Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na KEDCO ya gaggauta dawo masa da wuta bayan rasuwar wasu marasa lafiya da ke samun kulawa ta ceton rayuwada na’ura. Wata sanarwa da kakakin asibitin, Hauwa Inuwa Dutse ta fitar ta nuna takaici bisa rasuwar marasa lafiyan, tana mai cewa mace-macen waɗanda za a iya kauce wa ne idan akwai tsayayyiyar wutar lantarki. Ta bayyana cewa Asibitin yana AKTH yakan biya kuɗin wuta akai-akai daga kuɗaɗen shigansa, kuma yana kashe kuɗaɗe wajen sanya mai a janareto domin amfani idan aka ɗauke wuta daga KEDCO. Don haka, “Hukumar gudanarwar Asibitin AKTH na roƙon Kamfanin KEDCO da ya taimaka wa ayyukan asibitin ta hanyar dawo da wutar a yayin...
    Kamar yadda Oche, wadda ‘ya’yan ‘yar’uwarta suke zuwa makarantar Reno ta Oluwami da Firmare , da take Abuja inda shekarun baya suke biyan wajen Naira 600,000 ko wane zangon karatu, saboda wasu haraje- harajen da aka haɗa da su ciki. “Maganar gaskiya kowace shekara idan za’a shiga sabon zangon karatu, makarantu su kan ƙara kuɗin makaranta, su ƙara wasu sabbin abubuwa, kamar su kuɗin ICT, wasanni tsaro. Sai dai ƙarin da akwai matuƙar matsala.” A makarantar( Prime School ) da ke, Karu,inda aka ƙiyasta ana biyan kusan Naira 300, 000, kowane zangon karatu,wani Malamin da baya son a ambaci sunansa ya ce, akwai ƙarin kuɗin makaranta waɗanda suna da alaƙa ne da lamarin daya shafi kayn zuwa makaranta, bunƙasar makaranta,...
    Babban sakatare tsaron kasa na Iran Ali Larijani ya fadi cewa ya zama wajibi kasashen musulmi su hada kai waje guda don tunkarar rashin hankalin Isra’ila da take yi kan alummar falasdinu. A cikin wani bayani da ya aike da shi a shafinsa na X ya ce wannan mataki zai tilastawa shugaban Amurka yin gaggawa wajen mika umarninsa ga gwamnatin Isra’ila bisa hujjar kawo zaman lafiya a duniya da kuma bada kyautar zaman lafiya ta Nobel. Kasar Qatar ta sanar da kiran zaman gagganawa na kasashen larabawa da na musulmi a ranar litinin mai zuwa domin tattaunawa game  da harin da Isra’ila ta kai domin kashe jagororin kungiyar Hamas a kasarta. Manyan jami’an hamas da suke tattaunawa kan batun bukatar...
    A cikin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 14, kasar Sin ta samu ci gaba a bangaren sufurin jiragen kasa na cikin birane, da motocin bas na zirga-zirgar yau da kullum, da zirga-zirga cikin aminci. A halin yanzu, akwai layukan dogo 331 a cikin birane 54 dake fadin kasar, inda jimilar tsawonsu ta kai kusan kilomita 11,000, wanda ke matsayi na farko a duniya. Babban rukunin gidajen rediyo da talabin na Sin wato CMG, ya samu wannan kididdiga ne daga ma’aikatar kula da sufuri da jigilar kayayyaki ta kasar a kwanan nan. A yanzu haka, sama da mutane miliyan 200 a kasar Sin sun zabi hanyoyin sufuri masu kiyaye muhalli a kowace rana, wadanda suka hada da miliyan 100 da suke hawa jiragen kasa masu inganci...
    Sanata Ibrahim Lamiɗo, mai wakiltar Sakkwato ta Gabas, ya nuna damuwarsa kan yadda matsalar tsaro ke ƙara tsananta a yankinsa, inda ya ce hare-hare da satar mutane sun zama ruwan dare. A hirarsa da manema labarai, Sanatan ya ce: “Gaskiya abin tsoro ne rayuwa a Gabashin Sakkwato. Kusan kowace rana sai an kai hari, an kashe mutane ko kuma an sace su. Muna cikin tashin hankali sosai.” ’Yan bindiga sun harbi fasinjoji 2, sun sace makiyaya a Neja Gwamna ya aike wa majalisa dokar haramta auren jinsi ɗaya a Kano Ya bayyana cewa duk da ƙoƙarin da yake yi wajen ganin an kawo gyara, wasu ’yan siyasa suna kawo cikas. Sai dai ya ce ba zai fasa jajircewa wajen ganin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Sanin Makamar Aiki ta Najeriya (NARD), ta bai wa Gwamnatin Tarayya sa’o’i 24 don ɗaukar mataki game da buƙatunsu, ko kuma su tsunduma yajin aiki. Wannan matakin ya biyo bayan cikar wa’adin gargaɗin kwanaki 10 da suka bayar a baya. Gwamnatin Tarayya za ta gurfanar da shugabannin Ansaru 2 a kotu Tinubu ya bayar da umarnin a sake karya farashin kayan abinci Tuni wasu likitoci a Abuja da Jihar Oyo suka tsunduma yajin aiki. Likitocin, waɗanda yawancinsu ke aiki a Asibitocin Koyarwa da na Ƙwararru, suna yawan tafiya yajin aiki saboda rashin biyan wasu haƙƙoƙinsu. A halin yanzu, suna neman a biya su kuɗin horon 2025 da bashin albashin da suka bi, sannan sun buƙaci a...
    A yau Laraba kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum, inda ya bayyana cewa, kasar Sin ta soki lamirin harin da aka kaddamar a birnin Doha, fadar mulkin kasar Qatar a jiya Talata, tana kuma adawa da matakin Isra’ila na cin zarafin ikon mulkin kasa da tsaron kasa na Qatar. Lin Jian ya ce kasar Sin na kira ga dukkan bangarorin da abin ya shafa, musamman Isra’ila, da su kara kokari wajen dakile rikicin, da sake fara tattaunawa maimakon akasin hakan. Dangane da sanarwar da Isra’ila ta gabatar wa Amurka kafin ta kaddamar da harin ta sama, Lin Jian ya bayyana cewa, matakin da Isra’ila ta dauka na da...
    A halin yanzu, sauye-sauyen da ba a taba ganin irinsu ba a cikin karni guda suna ci gaba da habaka cikin sauri, yayin da mulkin kama-karya, son kai, da kuma kariyar tattalin arziki suka kara yawaita. A wannan yanayi, a wajen taron yanar gizo na shugabannin kasashen BRICS da aka gudanar a ran 8 ga watan nan da muka ciki, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da shawarwari uku don karfafa “hadin kan kasashen BRICS” da kuma kafa kyakkyawar makomar bil’adama ta bai daya. Wato na farko nacewa ga kasancewar mabambantan bangarori a duniya. Bugu da kari, a kare adalcin duniya domin ci gaba da bude kasuwanci don samun nasara ga kowa, da kuma kiyaye tsarin tattalin arzikin duniya....
    138- Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane, Rastan na Aya. Shahid Murtada Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa na maulana jalaluddin Rumi. Ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ////…Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Hassan Al-mujtapa (a) jikan manzon All..(s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata, mun bayyana yadda aka fara yakin gama gari a Siffin tsakanin rundunar Amirulmumina Aliyu...
    Majalisar Dattawa ta sanar da cewa ba ta amince da buƙatar Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar Kogi ta Tsakiya kan komawa bakin aiki, saboda har yanzu ba a kammala shari’ar dakatar da ita ba. Tun dai a ranar 8 ga watan Agustan bana ne Sanata Natasha ta rubuta wa majalisar wasiƙa, inda ta sanar da ita shirinta na komawa bakin aiki a ranar 4 ga watan Satumba, tana mai kafa hujja da cikar wa’adin watanni shida da aka dakatar da ita. NAJERIYA A YAU: Tasirin Takaddamar NUPENG Da Dangote A Kan Tattalin Arzikin Najeriya Ana zargin jami’in sibil difens da harbe abokin aikinsa a Abuja Sanatar ta bayyana cewa kotun tarayya ta yanke hukunci a watan Yulin da ya gabata...
    Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da jami’an Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA), wakilan kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC, shuwagabannin kamfanin ‘MRS Holdings Limited’ da kuma kungiyar ‘yan kasuwa ta kasa (TUC).   Da yake bayyana bude taron, Minista Dingyadi ya jaddada aniyar gwamnati na sulhu a tsakanin kungiyar da masu gudanar da masana’antu. Ya bayyana bangaren mai da iskar gas a matsayin jigon tattalin arzikin Nijeriya, yana mai gargadin cewa tsawaita yajin aikin zai haifar da mummunan sakamako ga kasar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kungiyar Hamas ta jaddada cewa: Tana maraba da duk wani yunkuri da zai taimaka a fagen dakatar da ta’addanci kan al’ummar Falasdinu Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta jaddada hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a yammacin jiya Lahadin da ta gabata cewa, tana maraba da duk wani yunkuri da zai taimaka a fagen yunkurin da ake yi na dakatar da kai hare-hare kan al’ummar Falasdinu, tana mai bayanin cewa ta samu wasu ra’ayoyi daga bangaren Amurka ta hanyar masu shiga tsakani don cimma matsaya. A cikin wata sanarwa da kungiyar ta Hamas ta fitar ta ce: “Ta samu wasu ra’ayoyi daga bangaren Amurka ta hanyar masu shiga tsakani don cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta. A wannan...
    Yayin da makarantu a fadin Najeriya ke dawowa sabuwar zangon karatu ta shekarar 2025/2026 a yau Litinin, iyaye sun koka kan mummunar ƙalubalen tattalin arziki da ke hana su samun sauƙin biyan kuɗin makaranta da sauran kayayyakin karatu. Rahotanni daga jihohi daban-daban sun nuna yadda tsadar rayuwa da hauhawar farashin kaya suka zame wa iyaye da ɗalibai babban cikas, inda wasu ke neman rance domin ganin ’ya’yansu ba su zauna a gida ba. Kukan Iyaye A hirarraki da aka yi da iyaye da dama, sun bayyana cewa duk zangon karatu yanzu yana zama tamkar shiga jana’iza, inda suke binne albarkatunku da nutsuwarsu da farin cikin gida. Misis Victoria Edem, uwa ce mai yara uku daga garin Kalaba a Jihar Kuros...
    ’Yan ta’adda sun kashe aƙalla mutum 63 a wani mummunan hari da suka kai a garin Darul Jamal, kusa da kan iyakar Najeriya da Kamaru, a yankin Bama na Jihar Borno. Gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum, ya tabbatar da cewa daga cikin waɗanda suka rasa rayuka akwai sojoji 5 tare da fararen hula 58. Tsagin NNPP na ƙasa ya yi watsi da korar Abdulmumin Jibrin Kofa ’Yan bindiga sun kashe jami’an Sibil Difens 8 a Edo Wannan harin ya faru ne da daddare a ranar Juma’a, inda maharan haye a kan ɗaruruwan babura, suka fara harbe-harbe da ƙone gidaje. Wani mazaunin garin, Malam Bukar, ya shaida wa manema labarai cewa: “Sun shigo suna ta kabarbari da harbi kan mai uwa...
    “Haka nan, ‘yan bindigan, suna sake kawo wani harin a wannan gari namu na Galadi da misalign karfe 10:15 na daren ranar Laraba, inda suka kewaye baki-dayan Galadin; illa bangare guda shi ma saboda gulbi ya tare wannan gefen ne, inda suka bude wa Galadin wuta ta kowane gefe baki-daya,” in ji shi. Kazalika ya kara da cewa, “Babu shakka, wannan hari ya yi sanadiyyar asarar rayukan mutane biyar, inda kuma wasu hudu ke kwance a gadon asibiti. Sai dai, Allah cikin ikonsa ya sa ba su samu damar tafiya da ko mutum guda ba,sakamakon dauki da aka samu daga wasu jami’an tsaro da suka garzayo daga Shinkafi. “Duk da cewa, a nan muna da jami’an tsaro; amma a lokacin...
    “Tun daga ranar farko, na gaya wa abokan aikina da ke cikin jam’iyyar PDP cewa kuna daba wa cikinku wuka. Idan kuka bari abubuwan da ke faruwa su ci gaba a haka, za ji a jikinku. Kuma me na ce? Ba za ku iya fitar da dan takarar shugaban kasa da shugaban jam’iyya na kasa su fito a yankin guda ba,” in ji Wike.   Tsohon gwamnan Jihar Ribas ya zargi PDP da rashin yin adalci wajen rarraba mukamai da kuma watsi da kiraye-kirayen yin adalci da daidaito, a cewarsa, wannan mataki su ne makasudin rashin nasarar jam’iyyar a zaben bara.   “Yana da kyau tun yanzu a warwaren matsalar tikitin takarar shugaban kasa kuma na shugaban jam’iyyar na kasa...
    Miliyoyin mutanen kasar Yemen sun fito zuwa dandalin taron mutane a dukkan garuwan kasar a bikin murnar zagayowar ranar haihuwar manzon All…(s) a kasar a jiya Alhamis. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Sayyeed Abdulmalik al-houthi, a jawabin da ya gabatar a karshen tarurrukan, zuwa ga hadin kan kasashen musulmi saboda ma’abucin wannan ranar (s). Ya kuma yi tir da allawadai da ci gaba da kissan kiyashin da HKI take aikatawa a Gaza. Ya kuma yi addu’a ga shahidan gwamnatin kasar wadanda HKI ta kashe a makon da ya gabata. Har’ila yau a cikin Jawabinsa Sayyid Huthi ya bayyana cewa, mutanen yemen da yardarm All..suna daga cikin wadanda suke raya addinin musulunci bayan rauninsa. Sannan daga cikin...
    Miliyoyin mutanen kasar Yemen sun fito zuwa dandalin taron mutane a dukkan garuwan kasar a bikin murnar zagayowar ranar haihuwar manzon All…(s) a kasar a jiya Alhamis. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Sayyeed Abdulmalik al-houthi, a jawabin da ya gabatar a karshen tarurrukan, zuwa ga hadin kan kasashen musulmi saboda ma’abucin wannan ranar (s). Ya kuma yi tir da allawadai da ci gaba da kissan kiyashin da HKI take aikatawa a Gaza. Ya kuma yi addu’a ga shahidan gwamnatin kasar wadanda HKI ta kashe a makon da ya gabata. Har’ila yau a cikin Jawabinsa Sayyid Huthi ya bayyana cewa, mutanen yemen da yardarm All..suna daga cikin wadanda suke raya addinin musulunci bayan rauninsa. Sannan daga cikin...
    A yanzu haka yankuna da dama wadanda a baya ba su fuskanci kalubalen matsalar tsaro ba, a yanzu haka sun fara dandana ukubar ta’addanci da bakuntar sansanin ‘yan gudun hijira. Kalubalen tabarbarewar tsaro da kiran da shugaban rundunar tsaro ta Kasa, Janar Christopher Musa ya yi kan ‘yan Nijeriya su dauki matakan kare kai ya haifar da cece- kuce musamman ga galibin jama’a da ke ganin gwamnati ta kasa. Da yawan jama’a na ganin duk da makuddan kudaden da gwamnati ke kashewa a sha’anin tsaro da kwarewar jami’an sojoji amma ‘yan ta’adda sun rinjaye su har suna ikirarin jama’a su dauki matakan kare kai. Janar Musa wanda daga baya ya janye kalamansa, tun da farko ya bukaci ‘yan Nijeriya da...
    Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin mayar da tsohon Shugaban Gidan Talbijin na Nijeriya, NTA da aka sauke kwanan nan, Salihu Abdullahi Dembos. A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Bayo Onanuga ya fitar, ya ce Dembos wanda Shugaba Tinubu ya naɗa a watan Oktoban 2023, a yanzu zai dawo domin kammala wa’adin mulkinsa na shekara uku. ’Yan bindiga sun sace basarake a Kogi ’Yan sanda sun kama ɗan bindiga da shanu 10 a Kebbi Haka ma shugaban ƙasar ya bayar da umarnin maido da Mista Ayo Adewuyi a matsayin babban daraktan sashen labarai na NTA, domin shi ma ya ƙarasa wa’adinsa na shekara uku da zai ƙare a 2027. A ’yan kwanakin nan ne aka...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce shi da takwarorinsa na Rasha da China sun aike da wasika ga Majalisar Dinkin Duniya, inda suka yi watsi da matakin da Birtaniya da Faransa da Jamus suka dauka a baya-bayan nan na yunkurin maido da takunkumin kasa da kasa kan Iran a matsayin mataki marar ma’ana. Abbas Araghchi ya bayyana hakan ne a cikin wani sakon da ya wallafa a jiya a Shafin X, kwanaki hudu bayan da kasashen Turai wadanda suka rattaba hannu kan yarjejeniyar nukiliya ta 2015 suka sanar da kwamitin sulhu na MDD cewa, sun yi amfani da tsarin dawo da dukkanin  takunkumin MDD a kan Iran. Ya ce, a cikin wasikar hadin gwiwa da suka aike wa...
    Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Manjo Janar Abdolrahim Mousavi ya bayyana cewa, rundunar sojin saman kasar Iran a matsayinta na bangaren da ke sahun gaba na kare ikon sararin samaniyar kasar, ya rataya a kansu wajen ci gaba da kara kokarinsu na bunkasa tsaon sararin samaniyar kasar, domin tabbatar da cewa an dakile duk wata barazana ta makiya  a kan akasar. A cikin sakon da ya aike na ranar tsaron sararin sama ta kasa, Janar Mousavi ya yi tsokaci kan yadda yanayin tsaro na yanki da na duniya ke ciki, inda ya  bayar da misali da irin abubuwan da al’ummar Iran suka samu a tsawon shekaru 8 a bangaren ayyukan tsaro da kariya, wanda kuma ya tabata a yakin...
    135-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane, Rastan na Aya. Shahid Murtada Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa na maulana jalaluddin Rumi. Ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ////…Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Hassan Al-mujtapa (a) jikan manzon All..(s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata, mun bayyana yadda aka yi yaki kan ruwan furat, bayanda sojojin mu’awiya ya hana sojojin...
    135-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane, Rastan na Aya. Shahid Murtada Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa na maulana jalaluddin Rumi. Ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ////…Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Hassan Al-mujtapa (a) jikan manzon All..(s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata, mun bayyana yadda aka yi yaki kan ruwan furat, bayanda sojojin mu’awiya ya hana sojojin...
    Jakadan shugaban kasar Rasha na musamman kan al-amuran yaki a Ukraine ya bayyana cewa masu son yaki a cikin shuwagabannin kasashen turai suna zagon kasa ga kokarin shugaba Trump na kasar Amurka yake yi na kawo karshen yaki a Ukraine. Tashar talabijinn ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Kirill Dmitriev yana fadar haka, a shafinsa na X , inda yake zargin shuwagabannin kasashen turai da hana tsaida yaki a Ukraine. Dmitriev ya kara da cewa Brussels na zangon kasa ga shirin tsaida yakin tare da dorawa shugaban kasar Ukraine gabatar da bukatun ba zasu taba yiyuwa Rasha ta amince da sub a. Ya kara da cewa shuwagabannin kasashen Turai suna tsawaita yakin har zuwa lokacinda Al-amura zata sake komawa...
    Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana cewa Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara da ’yan majalisar dokokin jihar za su koma kujerunsu a ranar 18 ga Satumba, lokacin da dokar ta-ɓaci a jihar za ta ƙare. Wike, ya bayyana haka ne a ranar Asabar bayan ya kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen ƙananan hukumomi da ake gudanarwa a jihar. A shekara 2 Gwamnatin Tinubu ta ware wa Legas ayyukan N3.9trn Gwamnan Taraba ya shiryawa gwamnonin Arewa Maso Gabas liyafa Ya kaɗa ƙuri’a a rumfar zaɓe mai lamba 7 a mazaɓa ta 9, Rumuepirikom, Ƙaramar Hukumar Obio-Akpor. Tsohon gwamnan jihar, ya ce zaɓen na gudana cikin lumana idan aka kwatanta da zaɓukan da suka gabata. Ya bayyana cewa zaɓen Ƙananan Hukumomin ya...
    A ranar Juma’a ne Birtaniya da Faransa da Jamus suka gindaya wasu sharudda guda uku ga Iran game da batun dage mayar da takunkumin Majalisar Dinkin Duniya a kanta,a  cikin wata sanarwar hadin gwiwa da aka fitar gabanin wani taron sirri na kwamitin sulhu na MDD. Kasashen uku da aka fi sani da E3  sun ce a shirye suke su dage mayar da takunkumin har na tsawon watanni shida idan Tehran ta amince da sake baiwa masu binciken nukiliya na Majalisar Dinkin Duniya damar shiga cibiyoyinta na nukiliya, tare da  magance abin da suka kira damuwar da suke da ita game da yawan tataccen sinadarin uranium da ta ke da shi, da kuma shiga tattaunawa da Amurka. Sabanin haka, jakadan...
    Sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya ya kira mummunan halin da ake ciki a Gaza a matsayin abu mafi muni a wannan lokaci ta fsuakr mawuyacin hali da dan adam yake ciki. Yayin da yake magana da manema labarai a birnin New York a ranar Alhamis, Antonio Guterres ya bayyana yadda ake lalata tsarin abinci da ruwan sha da na kiwon lafiya a Gaza, lamarin da ya sa mutane ke fuskantar yunwa. Guterres ya bayyana damuwarsa kan mamayar da sojojin Isra’ila suka yi a birnin Gaza, yana mai cewa hakan na nuni da wani gagarumin ci gaba a yakin. “Daruruwan dubban fararen hula-da suka gaji kuma sun gaji-zasu sake tilastawa yin gudun hijira, tare da jefa iyalai cikin mawuyacin hali. Dole...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A ’yan watanni da suka gabata, matasa da yawa a Najeriya sun dukufa don ganin hakar su ta cimma ruwa wajen samun kudaden kirifto.   Amma alamu na cewa a baya-bayan nan wasu daga cikinsu sun sare sun kuma saduda sun dawo daga rakiyar harkar. NAJERIYA A YAU: Matakan da ciwon suga ke bi kafin illata mai fama da shi DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan dalilan wasu matasan na yin watsi da harkar kirifto. Domin sauke shirin, latsa nan
    3. Karuwar allunan sola ta samar da damar samun karin wutar lantarki, inda ake sa ran samun karuwar wutar lantarki da za ta kai fiye da kaso 5% a wasu kasashe 16 dake nahiyar Afirka. Tambaya ita ce: me ya sa allunan solan kasar Sin samun karbuwa a Afirka? Domin suna da araha, gami da inganci. Kamar yadda muka sani, ana sayar da allon sola mai karfin watt 420 kan farashin kusan dalar Amurka 60 a Najeriya, kuma yana iya samar da wutar lantarki na kWh 550 a duk shekara. Sai dai idan za mu ci gaba da samar da wutar lantarki ta janareta mai amfani da man dizal, kamar yadda aka saba yi, to, a farashin man dizal na...
    Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’a da na kasa da kasa ya bayyana cewa: Shirin dawo da takunkumi kan Iran za shafi mu’amalar Iran da IAEA Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’a da na kasa da kasa, Kazim Gharib-Abod yayin da ya dawo daga shawarwarin karshe na shawarwarin da aka yi tsakanin Iran da tawagar kasashen Turai uku a birnin Geneva, ya bayyana cewa: A cikin wannan zagaye na shawarwarin, Iran ta bayyana a fili ga kasashen Turai cewa, ba su da hurumin aiwatar da doka ta yadda za a iya sake dawo da takunkumi da wa’adinsa ya kare kan kasar Iran, kuma babu wata hujja ta shari’a kan matakin...
    Wakilin dindindin na kasar Rasha a kungiyoyin kasa da kasa a Vienna  ya sanar da cewa: An sake dawo da ayyukan IAEA a cibiyar Bushehr Wakilin dindindin na kasar Rasha a kungiyoyin kasa da kasa a Vienna, Mikhail Ulyanov, ya sanar da dawo da ayyukan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa a cibiyar makamashin nukiliya ta Bushehr dake kudancin kasar Iran. A cikin wani sako da ya aike a shafinsa na X, Ulyanov ya rubuta cewa: Iran ta sake tabbatar da cewa, ko da bayan hare-haren da sojoji suka kai wa cibiyoyin nukiliyar kasarta na zaman lafiya da ke gudana karkashin hukumar ta IAEA ba bisa ka’ida ba, abin kunya ne, a matsayinta ta mamba ta hukumar...
    Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa Birtaniya, Faransa da Jamus suna shirye-shiryen mayar da takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta kakabawa Iran a shekarun baya. Kasashe uku na Turai, da aka fi sani da E3, sun gana da jami’an Iran a ranar Talata a wani abin da aka bayyana a matsayin dama ta karshe na ceto huldar da ke gabansu na yin amfani da batun yarjejeniyar nukiliyar 2015, wanda wa’adinsa zai  kare a tsakiyar watan Oktoba. Duk da cewa jami’an diflomasiyyar Turai sun yi iƙirarin cewa tattaunawar ba ta samar da hanyoyin warware batun kamar yadda suke bukata ba, amma Tehran ta nanata cewa tana nan a shirye don tattaunawa mai ma’ana, muddin aka mutunta haƙƙinta da...
    Shugaba Bola Tinubu ya dawo Abuja, bayan ya kammala ziyarar aiki a ƙasashen Japan da Brazil. Mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya ce jirgin shugaban ƙasa ya tashi daga filin jirgin sama na Brasília a ƙasar Brazil da ƙarfe 12:57 na rana a ranar Laraba. A cewarsa ya iso Abuja da safiyar ranar Alhamis. Ga hotunan yadda wasu manyan jami’an gwamnati suka tarbi shugaban:
    A lokacin ziyarar, ya gana da Shugaban Brazil, Luiz Inácio Lula da Silva, da sauran manyan jami’an ƙasar. Ƙasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniya guda biyar da suka shafi sufurin jiragen sama, harkokin waje, kimiyya da fasaha, da kuma noma, da wasu muhimman fannoni a ci gaban Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya ce ba zai tsaya takarar kowanne irin mukami ba a zaben 2027, inda ya ce burinsa kawai ya samar wa jiharsa da Najeriya nagartattun shugabanni. Ya bayyana hakan ne ranar Laraba a Kaduna, lokacin da ya karbi wasu matasa karkashin jagorancin Aliyu Bello da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar hadakar ’yan adawa ta ADC. NAJERIYA A YAU: Matakan da ciwon suga ke bi kafin illata mai fama da shi Ruftawar katanga ta yi ajalin uwa da ’ya’yanta 2 a Zariya El-Rufa’i ya kuma soki lamirin gwamnati mai ci, inda ya ce ’yan Najeriya na ganin gazawarta karara ba tare da wani ya musu karin bayani ba. “Ba abin da wannan gwamnatin ke...
    Ya yi alkawarin cewa, gwamnatinsa za ta kara hada kai da hukumomin tsaro domin dawo da zaman lafiya, tare da samar da kayayyakin agaji da tallafi ga wadanda abin ya shafa.   Majiyoyin yankin sun ce al’ummar yankin sun sha fama da hare-hare akai-akai a ‘yan makonnin da suka gabata, lamarin da ya tilastawa mazauna yankin kauracewa gidajensu.   Ku tuna cewa, Gwamna Radda a ranar 18 ga Agusta, 2025 ya bar kasar don hutun makonni uku domin duba lafiyarsa a kasar waje.   Gwamnan ya samu rakiyar manyan jami’an gwamnati da shugabannin hukumomin tsaro na jihar da kuma kungiyoyin bayar da agajin gaggawa ga al’umma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun...
    Ƙungiyar Malaman Jami’a (ASUU) reshen Jami’ar Tarayya Kashere (FUK), ta yi zanga-zangar lumana, inda ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta aiwatar da yarjejeniyar da suka yi da sauran buƙatunsu da ba a cika ba. Zanga-zangar ta fara ne daga ofishin ƙungiyar, ta bi ta ginin shugaban jami’ar, sannan ta ƙare a bakin ƙofar shiga makarantar. Dilan ƙwaya ya shiga hannu a Borno Ambaliya: Gwamnatin Yobe ta samar wa magidanta 250 matsugunin wucin gadi Shugaban ASUU na jami’ar, Dakta Shehu El-Rasheed, ya ce gwamnati ta kasa cika alƙawuran da suka jawo yajin aikin watanni takwas a shekarar 2022. Ya ce har yanzu ba a biya malamai albashin baya ba, haka kuma babu ƙarin albashi na tsawon shekaru. Ya ja hankalin gwamnati cewa...
    Ƙungiyar Malaman Jami’a (ASUU) reshen Jami’ar Tarayya Kashere (FUK), ta yi zanga-zangar lumana, inda ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta aiwatar da yarjejeniyar da suka yi da sauran buƙatunsu da ba a cika ba. Zanga-zangar ta fara ne daga ofishin ƙungiyar, ta bi ta ginin shugaban jami’ar, sannan ta ƙare a bakin ƙofar shiga makarantar. Dilan ƙwaya ya shiga hannu a Borno Ambaliya: Gwamnatin Yobe ta samar wa magidanta 250 matsugunin wucin gadi Shugaban ASUU na jami’ar, Dakta Shehu El-Rasheed, ya ce gwamnati ta kasa cika alƙawuran da suka jawo yajin aikin watanni takwas a shekarar 2022. Ya ce har yanzu ba a biya malamai albashin baya ba, haka kuma babu ƙarin albashi na tsawon shekaru. Ya ja hankalin gwamnati cewa...
    Babban Hafsan Hafsoshin kasar Iran ya bukaci kasar Pakistan ta bada hadin kai da JMI don kawo karshen ayyukan ta’addanci a kan iyakokin kasashen biyu. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Manjo Janar Abdurrahim Musavi yana fadar haka a lokacinda yake zantawa ta wayar taro da tokwaransa na kasar Pakistan Fiel Mashal Asim Munir a yau Talata. Musavi ya godewa kasar Pakistan da taimakawa kasar a yakin kwanaki 12 na watan yunin da ya gabata., sannan yayi nuni da bukatar kasashen biyu su hada kai don murkushe ayyukan ta’addanci a yankin Sisitan Balucistan na kasar Iran da kuma cibiyarsu dake cikin kasar Pakistan. Ya ce akwai bukatar kasashen biyu su hada kai a wannan fagen bayan an...
    “Mun yi tattaunawar gaskiya, amma gwamnati tana yi mana wasa,” in ji shi. Ya ce an yi watsi da rahotanni masu muhimmanci, an kafa manufofin da ke cutar da ilimi, sannan an jefa malaman da suka yi ritaya mummunan hali. “Wannan gwamnati ta raina ilimi da malamai. Mun gaji,” in ji shi. Shugaban ASUU ya yi gargaɗin cewa idan gwamnati ta ƙi ɗaukar mataki, za ta ɗauki alhakin duk wata matsala da za ta biyo baya. Ya kuma kira mambobin ASUU da su fito ƙwansu da kwarkwata wajen tarukan da za a gudanar a manyan jami’o’i a ranar Talata, 26 ga Agusta, 2025, yana mai cewa wannan shi ne mataki na farko da ƙungiyar za ta ɗauka don nuna rashin...
    Ministocin harkokin waje na Iran da Saudiya sun bukaci hadin kan kasashen musulmi don magance matsalolin da al-ummar falasdinu take faskanta a gaza. Sun bayyana cewa akwai bukatar kasashen musulmi su san yadda zasu yi don nisar da abinci zuwa yankingaza da kuma kawo karshen kissan kiyashin da HKI take yi a yankin. Tashar taabijin ta Presstv ta bayyana cewa Abbas Aragchi ya tattauna da tokwaransa na kasar Saudia Faisal bin Farhan al-Saud ne a gefen taron ministocin harkokin waje na kasashen musulmi OIC na gaggawa wanda aka gudanar a birnin Jidda na kasar Saudiya . Banda haka ministocin sun yi maganar karfafa dangantaka tsakanin kasashen wadanda suka hada da kasuwanci, yawon shakatawa, da kuma al-adu. Sun kuma ya magana...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Yakasai ya kawo misalin tattaunawa da aka yi da kamfanoni a kasar China lokacin gwamnatin Abdullahi Ganduje, inda aka kawo tawaga Kano don duba yiyuwar saka hannun jari amma rashin wutar lantarki ya kawo cikas, ganin cewa dokar gwamnatin tarayya a wancan lokaci ta hana jihohi samar da wutar lantarki ta kansu. Ya bayyana roƙo ga gwamnatin Kano ta yanzu da ta mayar da hankali wajen tabbatar da isasshiyar wutar lantarki, musamman ta hanyar wutar solar ko haɗin gwuiwa da manyan kamfanoni kamar Dangote da BlackRhino, don farfado da masana’antun jihar. A cewar Yakasai, damuwa mafi girma ita ce yadda albarkatun Arewa ake dauka zuwa wasu jihohin kudu don a sarrafa, daga bisani kuma a dawo da su a sayar...
    Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce a shirye yaki da zauna da Trump da Kuma Putin a gefe guda don tattaunawa da kuma kawo karshen zabar da jinin mutanen kasashen su. Tsahar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar gwamnatin kasar Ukraine na fadar haka, ta kuma kara da cewa shugaban kasar Amurka Donal Trump a dayan bangaren ya bayyana cewa a shirye yake ya shiga tsakanin kasashen biyu don fita daga wannan yakin wanda ya gajiyar da dukkan bangarorin. Kafin haka dai Donal Trump ya bayyana cewa idan Zeleski yana bukata to zai iya kawo karshen yakin a rana guda, amma da sharadin ya yi watsi da gurinsa na shiga kungiyar tsaro ta Nato sannan ya...
    An kammala taron tattaunawa tsakanin shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da takwaransa na Amurka Donald Trump a birnin Alaska na kasar Amurka, inda bangarorin biyu suka bayyana taron a matsayin mai matukar amfani. Fadar Kremlin ta tabbatar da cewa tattaunawar ta yi armashi, yayin da manzon musamman na Rasha Kirill Dmitriev ya bayyana cewa yanayin taron ya yi kyau. Putin ya jaddada aniyar kasashen biyu na kawo karshen kiyayyar da suke yi da kuma bukatar cimma matsaya domin kawo karshen yakin Ukraine. Ya yaba da yadda Trump ya fahimci muradun Rasha da kuma burinsa na fahimtar ainihin rikicin. A nasa bangaren, Trump ya tabbatar da cewa tattaunawar ta kai ga cimma matsaya a kan batutuwa da dama, yayin da wasu...
    “Tsarin mulkin ADC ta bayyana cewa duk wanda ke neman zama shugaban jam’iyyar, dole ne ya kasance mamba nagari na jam’iyya. Wannan shi ne muhimman bukata ta asali wadda ba za a iya yin watsi da ita ko kauce mata ta kowace hanya ba. “A cewar tsarin mulkin ADC, hanyar da ta dace don cike gurbin jagoranci bayan tafiyar Cif Nwosu ita ce, ta hanyar taron kwamitin zartarwa na kasa.” Tsaagin jam’iyyar ta sake tabbatar da cewa Alhaji Nafiu shi ne halastaccen shugabanta na kasa tare da kira ga ‘ya’yan jam’iyyar da su ci gaba da kasancewa cikin kwanciyar hankali da hadin kai. Ya kuma bayyana kwarin giwa kan ikon hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) na kiyaye...
    Shugaban hukumar kula da wasanni ta ƙasa (NSC), Bukola Olopade, ya ƙaryata rahotannin da ke cewa Super Falcons ba su samu kuɗin alawus ɗin da aka yi musu alƙawari ba, yana mai cewa an riga an biya duk ƴan wasan, sai kaɗan daga cikinsu da ke da matsalar asusun banki. Ya ce ya tabbatar da hakan ne daga shugabar ƙungiyar, Rasheedat Ajibade, da kuma hukumar kwallon ƙafa ta ƙasa (NFF). Olopade ya ce ba daidai ne a yi iƙirarin cewa ba a biya kuɗin ba, inda ya ƙara da cewa bai kamata a jefa Ajibade cikin matsalar musanta kalaman da ba ta faɗa ba. Ya bayyana cewa waɗanda ke da matsalar asusun banki su kaɗai ba su samu ba, amma...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Suna buƙatar kawar da makaman nukiliya da kuma kawo ƙarshen maganganun rashin jin daɗi Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Ismail Baqa’i, ya yi kira da a dauki matakin gaggawa kan kawar da makaman nukiliya da kuma amincewa da laifukan tarihi a hukumance kamar harin bam din da aka kai kasar Japan. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya nakalto wasu bayanai daga cikin sanarwar da masu rajin kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya suka fitar kan bikin cika shekaru 80 da hare-haren nukiliyar da Amurka ta kai a garuruwan Hiroshima da Nagasaki na kasar Japan. Hare-haren nukiliya na Amurka, wanda ya kashe mutane 150,000 a Hiroshima da 80,000 a Nagasaki, ba...
    130-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka  barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shirin wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafai wadanda suka hada da littafin Dastane Rastantan na Aya. Shaheed Murtadan Muttahary ko kuma cikin littafin mathnawi na Maulana Jalaluddeen Rumi ko kuma cikin wasu littafan, da fatan masu sauraro za su kasashence tare da mu a cikin shirimmu na yau. ///… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan Al-Mutaba, (a) dan Fatima (s) diyar manzon All..(s) da muke kawo maku, a cikin shirimmun da ya gabata mun bayyana yadda Amirulmuminina Aliyu...
    Shugaban hukumar makamashin nukliya na kasar Iran wato (AEOI) Muhammad Eslami ya bayyana cewa babu jada bayana a shirin nukliyar kasar iran, duk tare da takurawar kasashen yamma. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Eslami yana fadar haka a wani taro nay an jarida a nan Tehran a jiya Talata. Ya kuma kara da cewa kasashen yamma masu babakere kan al-amura a duniya suna son haramtawa mutanen kasar Iran ilmin zamani da kuma ci gaba a fasahar Nukliya. Amma gwamnatin kasar Iran ta dage kan cewa yakin kwanaki 12 da suka dorawa kasar ba zai hana ta ci gaba da shirinta na makamashin nukliya ba. A wani bangare a maganarsa, shugaban hukumar makamashin nukliya na kasar Iran...
    Alausa ya ce dakatarwar, wacce ta shafi dukkan nau’o’in manyan makarantun gwamnatin tarayya an yi hakan ne da nufin dakatar da maimaici da barnatar da dukiyar gwamnati, inda za a yi amfani da kudin domin inganta makarantun da ake da su. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dakatar da Shugaban Karamar Hukumar Rano, Alhaji Muhammad Naziru Ya’u, na tsawon watanni uku sakamakon zarge-zargen aikata ba daidai ba. An yanke wannan hukunci ne a zauren majalisa ƙarƙashin jagorancin Shugaban Majalisar, Alhaji Jibril Isma’il Falgore, bayan kwamitin majalisar kan ƙorafe-ƙorafe ya gabatar da rahoton bincikensa. Yayin gabatar da rahoton, Shugaban Kwamitin wanda shi ne shugaban masu rinjaye, Alhaji Lawan Hussaini Dala, ya ce binciken ya samo asali ne daga ƙorafin da kansiloli tara daga cikin goma na Rano suka sanya wa hannu. A cewarsa, ƙorafin ya zargi shugaban da yin sakacin kuɗi, sayar da shaguna, da karkatar da takin zamani da aka ware wa ƙaramar hukumar, tare da wasu zarge-zarge daban. Lawan ya bayyana...
    A wani bayanin hadin giwa wanda ministocin harkokin wajen kasashe 27 suka rattabawa hannu, ya bukaci firai ministan HKI Benyamin Natanyahu ya bude hanya don shigoda abinci cikin gaza, don kawo karshen yunwa da ta bayyana a fili. Tashar talabijan ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa daga cikin kasashen da suka sanyawa bukatar hannu har da kasashen Faransa da Burtaniya da kuma tarayyar Turai a yau Talata. Bayanin ya kara da cewa lalle musibar yunwa da ta sami Gaza, ta kai matsayinda mutum ba zai sawwara shi ba, suna bukatar Natanyahu ya bada izinin a shigar da kayakin agaji zuwa gaza ba tare da bata lokaci ba. A wani labarin kuma yawan mutanen da abincin da ake jefawa...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce dole ne dukkan kasashen duniya su yi kokarin kawo karshen laifukan da Isra’ila ke aikatawa a zirin Gaza da kuma kawo karshen killacewa da take yi wa yankin. Pezeshkian ya bayyana hakan ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin da yake karbar takardar shaidar sabbin jakadun kasashen Habasha, Estonia, Djibouti, Laos, Cambodia, Burundi, Latvia, Myanmar, da Nepal. Ya ce gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana ci gaba da  kara zafafa laifukan da take aikatawa a kan al’ummar Palastinu marasa kariya da ake zalunta a zirin Gaza. Shugaban na Iran ya jaddada cewa: Dole ne dukkan kasashen duniya musamman kasashen musulmi su kara himma da hadin gwiwa wajen dakile wadannan laifuka a Gaza, da...
    Yawancin ‘yan Nijeriya sun nuna damuwa game da yadda majalisar dattawa ta 10 ke gudanar da harkokin majalisa, suna cewa ‘yan majalisar sun gaza bayar da muhimman ayyukan da aka ɗora musu na binciken ɓangaren zartarwa don kare ‘yan Nijeriya. Ana zargin majalisa dattawa ta 10 da ƙin tilasta wa gwamnatin tarayya wurin magance tarin ƙalubale da ke fuskantar ‘yan Nijeriya, ciki har da tsadar rayuwa, talauci, yunwa, yawan rashin aikin yi da rashin tsaro, da sauran su. Rahotanni su bayyana cewa akwai tsofaffin gwamnonin 13 da ke majalisar dattawa ta 10 a halin yanzu, wanda suka haɗa da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio (Akwa Ibom), Aliyu Wammako (Sakkwato), Abdulaziz Yari (Zamfara), Aminu Waziri Tambuwal (Sakkwato) da Adams Oshiomhole (Edo)....
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi da takwaransa na Masar, Badr Abdel Ati, sun tattauna batutuwan da ke faruwa a zirin Gaza da Lebanon, inda suka jaddada bukatar daukar matakan gaggawa daga kasashen musulmi domin dakile kisan kiyashin da ake yi a Gaza da kuma hare-haren da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ke ci gaba da kai wa kasar Labanon. A wata tattaunawa ta wayar tarho da bangarorin biyu suka yi, ministocin biyu sun tattauna kan tabarbarewar al’amuran jin kai a zirin Gaza sakamakon killace yankin da kuma shirin Isra’ila na mamaye yankin gaba daya. Sun kuma jaddada mahimmancin tabbatar cewa an shigar da agajin jin kai na kasa da kasa cikin gaggawa. Har ila yau, sun tattauna batutuwan da suka shafi...
    Cin zarafin Amurka ta hanyar haraji ya kuma lalata amincinta tsakanin sassan kasa da kasa. A halin yanzu, fannin shigar da kayayyaki na Amurka ya yi kasa zuwa kashi 13% kacal a kasuwannin duniya.   Har ila yau, a jiya Alhamis 7 ga wata, bayanai sun nuna cewa, a cikin watanni bakwai na farkon shekarar nan, cinikayyar kayayyaki ta Sin ta ci gaba da nuna kyakkyawan ci gaba, inda ta samu karuwa tsakaninta da kasashe membobin kungiyar ASEAN, da Tarayyar Turai, da Afirka, da Asiya ta Tsakiya, wanda ke nuna karfin juriya da kuzari. Hakan ya kuma tabbatar da cewa, cin zarafi ta hanyar haraji ba zai haifar da alfanu na dogon lokaci ba, maimakon haka, budadden tsarin hadin gwiwa...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk bayan shekaru hudu, Najeriya na kara yin zabe kuma ko wanne lokaci ‘yan takara kan dauki alkawura. Ko shekaru nawa wadanda ake zabe ke bukata don cika alkawuran da suka dauka? NAJERIYA A YAU: Mummunan Tasirin Rashin Bambance Zazzabin Lassa Kan Lafiyar Al’umma DAGA LARABA: Me Ke Sa Matasa Zama Karnukan Farautar ‘Yan Siyasa A Kafafen Sadarwa Na Zamani? Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai. Domin sauke shirin, latsa nan
    Babban Hafsan Hafsoshin sojin Iran ya bayyana cewa; Martanin da Iran za ta mayar kan duk wani hari zai kasance murkushewa ne, kuma ba zata jira izinin kowa ba Babban hafsan hafsan sojin kasar Iran ya gargadi makiya, yana mai cewa: Suna yi wa shahidai alkawari cewa: Za su ci gaba da bin tafarkinsu, kuma duk wani sabon harin wuce gona da iri kan Iran zai fuskanci azamar mayar da martani daban da na baya. Babban hafsan hafsoshin sojin kasar ta Iran Manjo Janar Abdulrahim Mousavi ya jaddada matsayin wadanda suka yi shahada a safiyar yau Alhamis a yayin bikin tunawa da ranar shahidan Iraniyawa a hare-haren wuce gona da iri, yana mai daukar su a matsayin ginshikan tabbatar da...
    Ana zargin ‘yan sandan da karya hannun Sawore   Ana zargin wasu ‘yan sanda daga Sashen Binciken ‘yan sanda na Qasa sun kutsa inda  Hukumar ‘Yan sanda ta Qasa ke tsare xan gwagwarmayar neman haqqin bil’Adama Omoyele Sowore a Abuja, inda suka fita da shi da qarfin tuwo zuwa wani wuri da har yanzu ba a sani ba. Haka kuma kamar yadda Sowore ya sanar a shafinsa na sada zumunta na Facebook, ya yi zargin cewa an karya hannunsa yayin da jam’an suka finciko shi da qarfin tsiya daga inda yake tsare wajen qarfe 6:00 na safiyar yau Alhamis a qoqarinsu na kai shi kotu ba tare da sanar da lauyansa ba.. jiya Laraba ne dai Sowore ya masa...