Aminiya:
2025-08-04@21:41:12 GMT

Gwamnatin Kano ta karɓi rahoton binciken Kwamishinan da ya yi belin Danwawu

Published: 4th, August 2025 GMT

Gwamnatin Kano ta karɓi rahoton kwamitin bincike da ta kafa domin gano haƙiƙanin gaskiya kan zargin da ake yi wa Kwamishinan Sufuri na jihar, Ibrahim Ali Namadi da shiga sha’anin belin wani da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi.

Shugaban kwamitin, Barista Aminu Hussain, ne ya miƙa rahoton ga Sakataren Gwamnatin Kano, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, a ranar Litinin, inda ya bayyana cewa sun gudanar da cikakken bincike na adalci, tare da tuntubar dukkan masu ruwa da tsaki.

WAEC ta saki sakamakon jarabawar 2025 Za a mayar da gidan yarin da ya haura shekara 100 zuwa gidan tarihi a Kano

Babu dai cikakken bayanin abin da rahoton ya ƙunsa, to sai dai matakin da gwamnati za ta ɗauka ne zai fayyace abin da kwamitin ya gano a binciken nasa.

“Mun tattauna da shi kansa kwamishinan, wanda ya gabatar mana da bayanai har a rubuce. Haka kuma, mun ga cewa akwai buƙatar mu tattauna da Abubakar Umar Sharada, mai taimaka wa Gwamna kan sha’anin siyasa, da kuma Musa Ado Tsamiya, mataimakin gwamnan kan kula da magudanan ruwa,” in ji Barista Hussain yayin miƙa rahoton.

Ya ce kwamitin ya yi zurfin nazari tare da neman shawara daga hukumomi da dama ciki har da Hukumar Tsaro ta SSS, da takwararta ta hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi NDLEA da kuma Kungiyar Lauyoyi ta Nijeriya (NBA), domin tabbatar da sahihancin rahoton da kwamitin ya fitar.

“Mun samu duk kwafin takardun da suka shafi batun a hukumance kamar yadda doka ta tanada. Mun yi amfani da duk wata shaida da ke akwai kuma mun tsaya kan gaskiya da adalci a yayin bincikenmu,” in ji shi.

Barista Hussain ya yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa yadda ya bar kwamitin ya gudanar da aikin sa ba tare da tsoma baki ba, yana mai cewa hakan alama ce ta gaskiya da kiyaye doka da oda a tafiyar da mulki.

“Muna godiya ga Gwamna saboda yadda ya bai wa kwamitin dama ya yi aikinsa ba tare da wani tsoro ko son rai ba,” ya ƙara da cewa.

Da yake karɓar rahoton a madadin gwamnati, Sakataren Gwamnatin, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, ya yaba wa kwamitin bisa irin ƙwazon da suka nuna.

“Zan fara da miƙa godiya ta musamman ga shugaban kwamitin, Barista Aminu Hussain, da sauran mambobin kwamitin bisa jajircewa da ƙwarewa da kuka nuna a wannan muhimmin aiki da ya ɗauki hankalin jama’a,” in ji shi.

Ya kara da cewa, “Duk da cewa akwai matsin lamba da aka riƙa fuskanta daga bangarori daban-daban, kwamitin ya tsaya kai da fata a kan gaskiya.

“Kowa ya shaida cewar wannan kwamitin ya yi aiki da amana. Kuma ba tare da bata lokaci ba, zan miƙa wannan rahoto ga Mai Girma Gwamna domin ya duba ya kuma ɗauki matakin da ya dace.”

Dalilin binciken

Ana iya tuna cewa a watan Yulin da ya gabata ne rahotanni suka bayyana cewa Kwamishinan Sufuri na Kano, Ibrahim Namadi, ya tsaya a matsayi mai karbar belin wani da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi — Sulaiman Aminu Danwawu — a kotu.

Bayanai sun ce a watan Mayun da ya gabata ne aka kama Danwawu a unguwar Tudun Yola da ke Kano, sannan aka mika shi ga hukumar NDLEA.

An gurfanar da shi gaban Kotun Tarayya a Kano a ranar 28 ga Mayu bisa tuhuma kan mallakar da kuma mu’amala da haramtattun ƙwayoyi.

A ranar 16 ga Yuli, wata kotu a Kano ta bayar da belin Danwawu bisa sharadin biyan Naira miliyan uku da kuma samun kwamishina mai ci a matsayin wanda tsaya masa, inda Kwamishina Namadi ya gabatar da rantsuwar cewa shi ne zai tsaya masa, lamarin da ya janyo zazzafar suka daga jama’a.

Daga bisani, a ranar 25 ga Yuli, Namadi ya janye matsayin nasa na mai tsaya masa da hujjar kare mutuncinsa, yana mai cewa bai da wata alaƙa ta kusa ko ta nesa da Danwawu, sai dai kawai ya yarda ne saboda wasu abokai na kusa sun nemi alfarma a madadinsa.

Wannan batun dai ya janyo zazzafar muhawara a ciki da wajen jihar, inda wasu ke ganin bai kamata mutum mai matsayi irin na kwamishina ya karɓi belin mutumin da ake zargi da taimakawa wajen assasa ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a jihar.

Lamarin da ya sa wasu ke ta kiraye-kirayen sauke shi daga muƙaminsa.

A nasa martanin, Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda ya amsa kiraye-kirayen jama’a ya kafa wani kwamitin mutum bakwai ƙarƙashin jagorancin Barista Aminu Hussain, domin bincikar gaskiyar lamari da ba da shawarar matakin da ya dace.

Abba ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na yaƙi da safarar da shan miyagun ƙwayoyi, tare da nanata cewa gwamnati ba za ta lamunci duk wani hawan ƙawara da wani jami’in gwamnati zai yi wa doka ba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ibrahim Ali Namadi Jihar Kano Sulaiman Aminu Danwawu miyagun ƙwayoyi kwamitin ya

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Kano Za Ta Mayar Da Gidan Gyaran Hali Na Kurmawa Gidan Tarihi

Sabon ginin na Janguza mai dauke da fursunoni 3,000, gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ce ta gina shi.

 

An gina gidan yarin na Kurmawa ne a shekarar 1910 a karkashin gwamnatin mulkin mallaka. Daga nan ya zama daya daga cikin fitattun alamomin tarihin mulkin mallaka da ke Kano.

 

Kano tana da gidan yari guda goma. Biyu a cikin birni—Kurmawa da Goron Dutse, yayin da sauran kuma suke a kananan hukumomin Wudil, Kiru, Rano, Sumaila, Bichi, Tudun-Wada, Gwarzo, da Dawakin-Tofa.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kwamitin Bincike Ya Miƙa Rahoto Kan Kwamishinan Sufuri Ga Gwamnatin Kano
  • Kwamitin Binciken Ya Miƙa Rahoto Kan Kwamishinan Sufuri Ga Gwamnatin Kano
  • Kwamitin Binciken Ya Kammala Rahoto Kan Kwamishinan Sufuri Ga Gwamnatin Kano
  • Gwamnatin Kano Ta Karɓi Rahoton Binciken Kwamishinan Sufuri Kan Belin Wanda Ake Zargi Da Safarar Kwayoyi
  • Gwamnatin Kano Za Ta Mayar Da Gidan Gyaran Hali Na Kurmawa Gidan Tarihi
  • An kama dilallan ƙwaya 28 a cikin barikin sojoji a Kaduna
  • Sauyin Yanayi: Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da shirin dashen bishiya miliyan 5
  • Yadda Kwamishinan Kano Ya Karɓi Dala $30,000 Domin Yin Belin Dilan Ƙwaya A Kotu – Rahoto
  • Yadda binciken zargin tallafa wa Boko Haram ke tafiyar hawainiya a Majalisa